Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 89

Page 15 & 16

Sosai abbah kema aslam fada mami na tayashi.. Saida suka tabbatar jikin shi yayi sanyi sannan suka qyaleshi ganin dare yayi, bayan sun qara tabbatar mai lallai lallai ya nemi gafarar iyayen shi da kuma alhaji baba domin fushinsu a gareshi ba alkhairi bane.....dole aslam ranar a gida ya kwana don dare yayi sosai,

Washe gari gida ya tashi a hautsine sakamakon farkawa da sukayi da wannan mummunan labari ...

Baqi da sukazo daga nesa duk suna nan wasun su dama yau zasu wuce, sai ga wannan labari mara dadi,

Duk wani masoyin wannan familyn saida yaji ba d'ad'i akan abin da aslam ya aikata...abune da bai taba faruwa ba a tarihin familyn ...yayinda a daya bangaren wasu da dama keta farin ciki da faruwan hakan kamar su zuna ruwa a qasa su sha saboda tsabar farin ciki, bama kamar zeee don tuni labari ya isketa kunsan abin duniya baya boyuwa mussan abin da bana alkhairi ba irin wannan an dinga yama d'id'i dashi kenan,

Alhaji baba da kanshi ya sanarma kakan asmah Wanda yake babban aminin shi abinda ke faruwa, bai samu halartar bikin ba saboda baya qasa yaje aikin hajji kasancewar lokacin aiki haji ne... baiji d'ad'i ba amma kuma haka ya d'auki qaddara karshema shiya koma rarrashin alhaji baba Dan ganin alhaji baba yafishi d'aukan zafi akan lamarin ...

Baqi dangin mahaifin asmah da dangin mahifiyarta da suka zo daga garuruwa mabanbanta don halarta bikinta a ranar suka jujjuya da labari Mara dadi ...suka bar asmah a gidan ba wanda yace zai tafi da ita tunda sunsan nan ne gidanta don tun tana qarama alhaji baba ya d'aukota bayan rasuwar mahaifanta yazo ya danqata a hannun mummy da daddy suka zame mata sabbabbin iyaye suka hadata da nasu yayan suka riqe ba tare da sun nuna mata wani banbanci ba ,,, yayinda a gefe guda alhaji baba da alhaji Mallam kankan asmah su kadai suka San dalinsu na zaman asmah a gidan..

Ba wani dalili bane kuma illah nason hada zuri'a a tsakanin su domin tun akan yayansu sukeda wannan burin, sai kuma ya kasance yayansu duka maza suka haifa alhaji baba Nada yaya uku, abdullahi mahaifin aslam Wanda ya kasance shine babba yana da matar shi d'aya Aisha mummy yayansu hudu Muhammad aslam ne babbah Wanda yaci sunan alhaji baba sai mai bi masa rabi'ahtu itama taci sunan hajiya mama ne tayi aure last year harda yarta daya hanifa, sai
kuma yan biyu mummy wato zahra da batool

Sai mai bi mishi Amina take auren wani Dan uwanta suna zaune a abuja itace mahaifiyar, amir Wanda ya kasance amini kuma Dan uwa ga aslam kasancewar tsararrakin juna Dan rana daya akayi bikin ta Dana daddy saboda kasancewarta mace,

Sai kuma Yusuf shine mahaifin kamal da amira shima matan shi daya maryam mami, amira tsaran su batool ne shi kuma kamal ya kasance mate din rabi'ah ,
Daddy da abbah dukansu suna zaune ne a gida daya da mahaifinsu babban gidane kowa da part d'inshi

Shi kuma alhaji Mallam kamar yadda jikokinshi ke kiran shi yaya biyu ya haifa kuma duka maza mahaifin asmah aminu shine babba sai kuma qanin shi Ahmad mahaifin Khadijah,

Amintarsu ya samo asaline tun akan iyayensu da suka kasance suma aminai haka aka haifesu suka tashi tare ko ina zasu tare makaranta da gida yau suna gidan can gobe suna can har suka gama secondary school alhaji baba mahaifin shi shararren Dan boko ne kuma Dan kasuwa yayinda mahaifin alhaji Mallam ya kasance babban malamin addini.... Haka kowannensu ya gaji mahaifinsa yanzu haka alhaji Mallam babnan malamine da akeji dashi a fadin Nigeria,, inda iyayensu suka rasu suka barsu, amintarsu har taso tafi na iyayensu Dan daya baya aiwatar da komai saida shawaran daya....lokacin da sukayi aure sun qudurci niyyan idan Allah ya basu zuri'a zasu hadasu aure domin zumunci ya tabbata na har abada... saidai kicin ikon Allah yayansu suka kasance maza mace daya alhaji baba yake da ita Amina kuma sai ta kasance tsaran aminu( mahaifin asmah )saboda alhaji baba ya Riga alhaji Mallam yin aure Dan haka ya rigashi haihuwa,,lokacin da amina ta isa aure kasancewarta mace aminu ya mata yaro don haka tayi aurenta da wani Dan uwanta ta dangin mahaifinta....

Haka su alhaji baba suka haqura da wanna burin nasu na hada zuri'a ganin yadda Allah ya tsara lamarinsa, saidai lokacinda da suka fara samun jikoki burinsu nason had'a zuri'a ya dawo sabo dal ganin Allah ya fara azurtasu da jikoki maza da mata... Iyayen asmah sun rasa ransu ne ta dalilin hadarin mota da sukayi lokacin asmah na noziri sun ajiyeta a school kenan zasu wuce anguwa da kannenta biyu kasancewar ita ta fara zuwa school baza aje da itaba suka biya suka ajiyeta tana kuka zata bisu suka mata wayau suka wuce basuyi nisa da school dinba tayar motar ta fashe, motar ta dinga tambul akan titi, nan dai gaba dayansu suka mutu, sai mummunan labari alhaji Mallam yaji, sunji mutuwarnan sosai kowa sai tausayin asma u yakeji , bayan share makoki alhaji baba ya nemi abashi riqon asmah ya hadata da yan biyu tayi karatu don tafi sakewa cikin yara tunda nan ba wasu yaran tunda lokacin Ahmad baiyi aure ba ana dai shirinyi ne, anan alhaji baba yace idan ta girma kuma sai a hadats aure da dan'uwanta aslam,, nan take alhaji Mallam yayi na am da hakan saidai yace shi baida burin ya mace tayi karatu mai zurfi yafison tayi iya secondary in yaso in mijin ta ya aminci taci gaba a gidanta, take kuwa alhaji baba ya mishi alqawarin indai tagama secondary zai aurad da ita ga aslam din taci gaba a gidan shi anan suka binne wannan sirrin nasu suka barshi a ransu sai lokaci yayi kowa yaji inda sukayi fatan Allah ya hada kan aslam da asmah kafin lokacin don komai yazo musu da sauqi, sai dai kuma hakan bata kasance ba,

Zuwan asmah gidan lokaci tanada shekara hudu a duniya yayinda aslam keda goma sha hudu, hannun mummy da daddy alhaji baba ya danqa amsah inda suka hadata dàsu batool suka riqe tsakani da Allah amira qaurowa tayi daga part din mami ta dawo part din mummy kullum tanacan in akace tazo ta wuce part dinsu har kuka takeyi ganin haka yasa mami barinta wa mummy ta hada duka su hudun ta riqe yayinda mazan kuma suka kasance yan dakin mami

...tun fil azal aslam baya qaunar asmah domin tun ranar daya fara ganinta ya dauki karan tsana ya daura mata bata mai komai ba shidai kawai abinda ya Sani idan ya hada ido da ita gaban shi faduwa yakeyi tun daga gani na farko hakan yasa ya tsaneta baya so ganinta har mayya take kiranta a cewarshi inba maitaba ya za'ace daka hada ido da mutum gabanka ya ringa faduwa, haka ya takura wa rayuwarta kwata kwata a gidan idan aslam nanan asmah bata da sukuni... Wani irin mugun tsoranshi ya dasu a zuciyarta saboda yadda yake azabtar da ita, duka zagi mari punishment haka yake sakata, yasha kulleta a toilet tun safe sai yamma, suma sauran qannenshi bawai sun sha bane a hannunshi suma yana dukansu amma ba kaman na asmah ba, a haka har suka shiga jss 1lokacin ne kuma aslam ya gama secondary school shida amir inda aka shiga fafutukar naman musu admission a qasar waje har lokacin ba abinda ya canja a tsakanin aslam da asmah yanda yakejin mugun tsanarta itama haka ta tsane shi.......
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayenmu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.