Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 67 of 89
Page 111
Cike da tsananin zaƙuwa dukkansu suka mike tare da rige rigen yi mata oyoyo, ƙamƙame juna sukayi gaba ɗayansu, suna tsalle kamar wasu ƙananan yara, ko nauyin jikin su basaji.
Sauran yan tsurarrin mutane dake falon tuni suka bar abinda sukeyi suka shiga kallonsu, sake juna sukayi kafin kuma ta shiga binsu ɗaya Bayan ɗaya tana rungumewa, lokacin data rungume Amira kam tsayawa tayi jin tudun Abu ya tokareta, dagowa tayi ta matsar da ita baya kaɗan tana ƙare mata kallo, tun daga sama har ƙasa, gane abinda take kallo yasa Amira saurin kai duka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,Asmah ta bata kunya, kuma ga ummi a wajen, dariya ta kwashe dashi, tare da cewa "kaiii masha Allah Abu yayi kyau aure yayi albarka"
Ummi dake kallonsu tana murmushin ganin abin nasu bana ƙarewa bane yasa tace "to ya isa haka ku kyalemin ƴa tazo ta gaisa da umminta," sai lokacin Asmah ta lura da ummi aikam dai kwasa da gudu tayi ta faɗa jikin ummi dake zaune kan kujera, ta ƙamƙame, tana tsallen murna, ummi kam cewa take "yi a hankali Asma' u karki kada umminki" ina ko sauraren ummi batayi ba, saida taji muryar ya Rabi'ah a bayanta tana mata magana sannan ta sake ummin ta dago fuskarta fal farin ciki, duk sunyi cirko cirko a tsaye suna kallonta kowacce cikin matuƙar farin ciki.
Ya Rabi'ah tace, "yayi kyau wato ta ƙawayenki da umminki kawai kikeyi ko" ƙarasawa tayi ta rungumeta itama tana cewa "sorry yayana kema ai zan dawo gareki" ummi kam sai binta takeyi da kallo kuri, i tafa ta hanga ta hango bataga wani alamar cikin a jikin Asmah ba, idan idanunta ba karya suke mata bama sai tace taga kamar har yarzu a virgin dinta take, dan daga yanayin tafiyarta kawai ta gane hakan, dan ummi Allah ya mata wani baiwa irinsu ne matan da da summa mace kallon ɗaya suke gane yanayin da take ciki, shiyasa kallon ɗaɗɗaya tama su zahra ta gane kowacce nada kunshi, gabanta ne ya faɗi, jin tunanin daya faɗo mata arai na cewa to kodai har yanzu basu sasanta bane, tabdijam aiko da sake, bari dai ta natsu koma meke ciki zantaji.
Zama sukayi nan gaban ummi aka shiga firan yaushe gamo kowa na fadin irin yadda yayi missing din sauran ana dariya, batool ce ta kalli zahra ganin, yadda taketa zare idanu, yunwa takeji dan tunda ta samu cikin nan da taci abinci ko awa bata iya kaiwa zataji cikinta kamar anyi yasa, gashi daga zuwanta aka bata abinci taci, bai wani daɗe ba, gashi bata son tace zataci abinci kar suyi zargin wani Abu,dan kuwa a irin tulin abincin data narka ɗazu, idan tace tana, jin yunwa yanzu dole su saka mata alamar tambaya, itako baza taso haka ba, son kunya takeji , tunda tazo taketa muku muku da abinta, tunda cikin bawai ya fito bane, na Amira ne kawai ya fito sosai saiko na Khadijah wanda shima idan mutum ya kura ido zai iya gani, saidai fa ta makaro don tuni ummi ta gane kaf ciki ne dasu saidai bata nuna ma ta gani ba, batool tace "kekuma lafiya, kiketa muzurai kamar me jin kashi" hararanta tayi tare da cewa"A'a maijin zawo dai" dariya su Amira suka kwashe dashi, ummi tace "oh Allah na gode maka ni Amina, anyi aure, yau watan ku biyar rabonku da ganin juna amma hakan baisa kun fasa wannan hali naku ba ko, kullum kamar masu ganin hanjin juna minti biyu shiri minti biyu faɗa"batool cikin dariya tace "ummi kalla fa yadda take yamutsa fuska tana muzurai kuma kawai dan na tambaya sai ya zama laifi" ummi tace "to aikena bakiyi tambayar a mutunceba, ya zakice mata kamar maijin kashi" batool tace "wlh ummi nayi missing ɗinta ne sosai so nake mudan tuna baya" dariya suka sa dukkansu ummi tace "to kin kyauta" Zahra kuma tace "kedai wlh baza ki canza ba"Khadijah ce ta faki idanunsu ta saka hannu cikin dan pos ɗinta da tunda tazo yake kamkame a hannunta ta ballo farin kasarta(kalba) ta afa a baki tana tsotsa a hankali,Asmah data lura tace "sisto abin kuma yar haka ne, wani daɗi kika samune, kike ci ke kadai, to kowa yaci shi ɗaya ya mutu shi ɗaya" zaro ido Khadijah tayi jin Asmah daga zuwa zata tona mata asiri tun dazu take Ballan abinta babu Wanda ya lura sai ita, Amira tace"haba shiyasa tun dazu nakejin kamshi na buso ni to a sammana, tunda sai mun roƙa " ta faɗa tana mika hannu zata dauki pos dinta dake ita ke kusa da ita, aiko saurin tayi wuf zata kamkame abinta, saidai cikin sa'a Amira ta rigata fisgewa, cakumota tayi zata amsa da sauri ta wurgawa ya Rabi'ah, aiko tana caɓewa ta balle botir ɗin pos ɗin ta saka hannu a ciki, saiga farin kasa cike da Santana.
Daga ledar tayi tana nuna musa tare da cewa"Lalalalaaa kice abin yazo inji mai tsoron wanka, masha Allah naga biyu, kice gaba nan gaba inada suyan rago kashi kashi, saura su O'o da O'o, Allah ya raba lafiyar mrs kamaludden " tuni Khadijah ta saka kanta a cikin cinyoyinta ta dunkule wuri daya, duka dariya suka saka mata, suna tsokananta ta kasa dagowa saboda ummi, ummi kam dake musu dariya ganin abin zaiyi yawa sun sakata gaba karma batool da tafi zakewa yasa tace"kyale su oh Khadijah, ai bake kadai nabe naga kema batool ai cikin ne dake ko?" da sauri batool ta dago tana kallon umminsu, zaro mata ido ummi tayi tace"eh haka nace kema cikin ne dake ko nayi karya," kasa bata amsa batool tayi, ta maida kallonta kan zahra tace "dakema zahra" aiko dai zahra tayi tsuru tsuru Ashe duk boyon banza takeyi tun ɗazu, ummi taci gaba da cewa "a toh naga gara ayi tone tonen tunda haka kuma zaɓa, ga Abu a jikinku kuma, amma kun take kun saka min ƴa a gaba" shiru kakeji batool baki ya mutu, ya Rabi'ah kam guɗa ta daddage ta rangaɗa iya karfinta, kafin tace "masha Allah alhmdllh, waiko mummy Nada wannan labarin kokuma ni zan fara mata albishir," ummi tace "ta ina zata sani nima duk yanzu na gansu da abubuwan su" ya Rabi'ah tace"to ummi banji kinyi lissafi da madam misisi ba matar oga" kallon Asmah ummi tayi tace "kai ita naga kamar babu ko?" ta fada tana kallon Asmah alamar ita take tambaya, ya Rabi'ah kuwa kallon Asmah tayi ta rike haba tare da cewa "ke ko ma'ulle me kika tsaya jira haka, ake neman a barki a baya," ummi tace "barni da ita, zata gaya min bayani ne anjima" ta faɗa tana dan haharan Asmah, Wanda ita kaɗai ta fahimci hararan me ummi ke mata, duk tasha jinin jikinta dama tun da taji kowa nada ciki banda ita jikinta yayi sanyi.
Zahra kam silalewa tayi ta shiga kitchen, ta samu abinci a nan ta zauna ta shake flate ta hau ci, koda ta fito duk sun shiga ciki don yin sallan la'asar da, aketa kira, itama cikin ta nufa, a dakin da ummi ta sauka ta samesu suna sallah.
Bayan sun idar zahra tambayar ya Rabi'ah tayi ko akwai aikin da Za'ayi ne, ya Rabi'ah tace "ba wani aiki duk ayyukan ba'anan za'à yi ba a can family hause dinsu za'ayi raɗin suna, duk abinda ya shafi raɗin sunan a cen za'ayi, ni kuma nawa abinci yourbawa zasuyi,saidai ko ku jera drinks da ruwan da aka kawo dazu a fridge kubi duka fridge din da kuka sani a gidan nan ku cikashi da ruwa da drinks harda na dakunan bakin cen dake rufe Na waje, bari Na Baku keys " ta faɗa tana mikewa ta dauko keys din a cikin side drower ta mikawa Amira, amsa tayi tace "to kumuje mu gama ko kafin fira ya barke mu kasa tashi" zahra tace "aikuwa dai muje" miƙewa sukayi zasu wuce Ummi Na zaune kan pray mat tana addu'a, gyaran murya ta musu duk suka juyo suna kallonta,nuna Asmah tayi sannan ta mata alamar ta tsaya ita, cikin sanyi jiki ta dawo ta zauna a bakin bed, gaba ɗaya walwalarta ya ragu, haka kurum takeji kamar ta aikata wani zunibi ne, ganin duk yan uwanta da aka musu aure tare suna da juna biyu amma ita har yanzu tana nan matsayin virgin bama akai ga maganar ciki ba tukunna, su batool kuwa tafiya sukayi suka kama aikin da zasuyi.
Bayan ummi ta idar ta shafa addu'an bata rai tayi sannan ta juyo ta kalli Asmah, ganin yanayin fuskar ummi saida gabanta ya faÉ—i, da gani tasan babu wasa a fuskarta, umminsu kenan Zuma ga zaki ga harbi, ita kuma ummi tayi haka ne dan ta samu Asmah ta faÉ—a mata gaskiyar abinda take son sani don idan ta sake mata fuska zata iya mata karya duk da ba halinta bane karya, zataji kunyar gaya mata wasu abubuwan idan taga dariya a fuskarta.
Cikin dakakkiyar murya tace "wato bakiji maganar dana gaya miki rannan ba ko, wai yaushe kika zama mai kunnen kashi ne Asmah, bansanki da wanna halin bafa" take idanun Asmah suka Tara kwalla, ummi bata saurareta ba taci gaba da cewa "wato ke baza'a miki magana kiji ba ko, kin tsaya shashanci da sunan baki son miji kin manta da abinda ke gabanki ko, waya gaya miki ana wannan yayin yanzu, ko mutanen da, da suke da duhun kai basuyi wannan kauyancin ba balle ku yaran yanzu da kuke a waye, Na gaya miki rannan namiji duk sonda yake ma mace idan bai samu kulawarta ba wlh soyayyar nan bacewa takeyi bat a zuciyar shi, take zakiga ya fara hangen wata, to balle naki ma da yake da wata matar a gefe, wlh idan ya gaji ajiyeki zaiyi a gefe ya dawo da matar shi, shikenan kin shiga uku, keda mijinki saidai hange daga nisa" nan fa ummi ta rufeta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, don ita duk a tunaninta har yanzu Asmah bata ba Aslam dama bane, tunda gashi har yanzu auren nasu bai cika ba.
Tuni Asmah ta duƙar da kai kasa ta fara kuka harda sheshsheka, jikinta ya ƙara yin sanyi musamman da ummi ta tuna mata da zee, saida taji ummi tayi shiru sannan ta dago kai idanu gaja gaja da hawaye, cikin muryarta mai dauke da amon kuka tace "umminmu wallahi tallahi abinda kike tunani ba haka bane, wallahi ummi tun daga ranar da kikamin magana, komai ya fara daidaita a tsakanin mu" katseta ummi tayi da cewa "rufe min baki karya kikeyi, idan komai ya daidaita mai yasa har yanzu babu abida ya shiga tsakaninku ta fannin auratayya" cikin kuka tace "wallahi ummi ba laifina bane , ba daga gurina bane matsalar wallahi ba daga ni bane" ummi jin ta fara kamo bakin zaren yasa ta kara bata rai tace "to daga waye" ganin ba wasa a fuskar ummi yasa batayi tunanin wani batun kunya ba tace "shine bai taba nuna yanaso ya kusanceni ba" ummi cikin zaro ido jin abinda Asmah tace dan ta ji tsoro kar ace baida isashen lafiya ne tace "ban gane ba kina nufin kodan romance haka dasu dan kiss bai taba yi miki ba" Asmah tace "yana duk wannan amma bai taba wuce haka ba, koni abin Na damuna umminmu"
Gyara zama ummi tayi a bakin bed, tufka takeyi tana warwarewa,a zuciyarta, ta yarda da batun Asmah Na cewa sun daidaita, tun daga yanayin yadda Asmah keta zuba mata rantsuwa, kuma ta gamsu Aslam kalau yake tunda yana da sha'awa, tunda gashi har yana iya wasanni da ita, to daga ina matsalar take ne? Jin amsar da zuciyar ta ya bata yasa ta juyo da sauri ta kalli Asmah tare da tsatsare ta da idanunta masu kaifi a kansu tace,"ya taɓa nuna yana bukatar kusantarki koda so ɗaya ne kin hana" da sauri Asmah ta girgiza mata kai, a fili ummi tace "A'a to meke damun son ne wai" shiru tayi ta dafe kai, cen kuma tace "to ko yana nufin cewa ke zaki fara neman shi" shiru Asmah tayi don bata San amsar da zata bata ba, ganin bata bata amsa ba hakan ya tabbatar mata da cewa bata San amsar da zata bata bane, tace "aiko dai idan ma hakan yake nufi to kuwa yayi wauta dan kuwa hakan bazai taba saɓuwa ba wai bindiga a ruwa inji hausawa, dole shizai fara nemanki don wannan ba tarbiyar mu ta Mallam bahaushe bane, sai kace wasu ƙabilu,zamuyi maganin shi, inyasan wata ai baisan wata ba"
"Ki bani hankalinki da kyau, ki amsamin tambayata, idan kuna wasannin kina mayar mai damartani ne?, girgiza kai Asmah tayi kafin tace "A'a ummi bana iyawa kunya nakeji" ummi tace "OK hakan ma yayi, to kina jin alamar abinshi ya miƙe idan kuna wasan" dagowa tayi bata gane me ummi ke nufi ba hakan yasa tayi shiru"ki bani amsa nace kinajin alamar abinshi yana miƙewa so nake Na tabbatar kalau yake dan insane irin matakin da zan dauka" Asmah cikin rashin fahimta tace"ummi wani Abu" daƙuwa ummi ta mata tare da cewa "gidanku Asmah, kibani amsa ba wasa nakeyi dake ba, nace kina ji ko ganin abin shi Na maza abin fitsarin shi nake nufi, kinaji yana yin karfi idan kuna wasa" sai lokacin Asmah ta fahimci ummi, take wani irin kunya ya lulluɓeta ba shiri takai tafukan hannayenta ta rufe fuskarta ganin haka yasa ummi cewa aɗan kausashe "zanci gidanku fa ki bani amsa, ko kinga wasa a idona" girgiza kai tayi still idanunta na rufe, ta tuna sometimes takanji abin ya miƙe ya zama ƙato yayi karfi kamar katako, har taji yana zungurinta wani bin, duk da dai bawai ta taɓa taɓawa bane, ,takanyi mamaki, har ta tambayi kanta to dama haka nasu yake da karfi ko kuwa nashine haka, da'ker ta daure tace "umminmu ban sani ba amma shidai nashi abin yana da karfi sosai kamar katako " tafa hannu ummi tayi tare da cewa "to wlh garau yake wulakanci ne so yake ya ƙure ki, to kuwa saidai ke ki ƙure shi, ina fatan set din kayan da addawiyya ta haɗa miki suna nan baki kyautar ba" Asmah tace "eh ummi suna nan banma taba buɗe kwalin ba" ummi tace "yawwa to yau inkin koma gida ki kulle kofarki, dakyau ki farke kwalin duka kayan ki daukomin hotonsu a wayarki gobe kizo dasu zan nuna miki waɗanda zakiyi amfani dasu, sanna zan buga ma anty maryar muktar yar zamfara ta aiko min da turaren (kokaƙi Allah) dashi zamu yi amfani ta ruwan sanyi duk taurin kanshi, saiya sauke shi, ke ko aljanu ne ke hanashi sai sun sake shi a lokacin, yanzu bari na baki tsarabar dana zo muku dashi, tunda naga sauran duk suna da kunshi, kene me bukatar su a yanzu, wani ƙaton jaka ta dauko ta buɗe take ta shiga fito da magunguna, magungunane masu kyau da inganci Wanda tayi orden su a gurin anty maryam muktar ana saura kwana biyu zata zo, amma ba bata lokaci har kayanta ya iso cikin sauƙi, nan ta ba Asmah waɗanda tasan ya kamata tayi amfani dasu tace taje ta fara sha kafin goben tazo da hotunan waɗancen na gurin ta,amsa tayi tana yamutsa fuska ganin haka yasa ummi cewa "bani nan da ganin yadda kike yamutsa fuska ba abin arziki Zakiyi ba", da kaina zan dinga baki, waɗanda zata iya sha a nan take ummi ta ritsata tasha sauran da sai anjima kuma ta saka mata a jaka tare da ja mata kunnen akan ta tabbatar tasha a gida .
Daidai nan su zahra suka dawo, batool tace tana bin kayan magungunan dake barbaje a ɗakin da kallo "wai ummi ƙusƙus din me kukeyi ne tun dazu fiyye da awa ɗaya" ya Rabi'ah kam cewa tayi"ayya ummi wato tunda kinfi ɗasawa da ya Aslam shine kika ware tashi matar kike gyara mashi ita mu kuma ko oho ko" dariya Rabi'ah ta bata, ummi tace "eh mana ai zamanin kowa kanshi ya sani nima ɗana kawai na sani," kallon Amira da Khadijah tayi tace "ku kuje gurin mummy ta gyaraku, itace sirikarku" batool tace "to mu gurin wa zamuje umminmu" ya Rabi'ah cikin dariya tace kowa taje gurin uwar mijinta, daƙuwa ummi tama ya Rabi'ah, sannan ta kalli su batool tace " daughters ni zan gyaraku, to kuma naga kowacce taci wake ta koshi, ya za'ayi kenan, amma dai bari na gani ko akwai irin naku" wani ummi ta dauko a roba anyi sillin din bakinshi ta mikawa batool, zahra tace "ummi nifa" ummi tace ke bazan baki shi ba saboda bake kaɗai bane gurin Barr in nabaki zamu shiga hakkin maryama, kukan shagwaba zahra tasa tana diddira ƙafa tace "ummi don Allah ki bani sai Musha tare da ita ai" tafa hannu ummi tayi tare da cewa "iyyee yaran mummy fa angirma" batool dake dudduba robar maganin da ummi ta bata cak ta tsaya tare da dagowa ta kalli zahra dake kukan abata itama tace"wait zahra naji kamar kince a baki magani kuje kusha da kishiyar ki?" Zahra ta harareta tare da cewa "haka nace what is ur problem" dariya batool ta kwashe dashi tana nuna zahra cikin dariya take cewa "kuji wani ɗiɗiɗi, yau naga zallar iyayi da neman suna,lallai zahra baki da hankali kishiya zaki ba kayan mata ta sha" su Amira da Khadijah kam batool ce ta basu dariya, nan suka shiga yi, ummi ma saida ta gama cin dariyarta sannan tace "to ina ruwanki batool, zaman lafiya ne ya kawo haka, koba haka ba zahra " ummi ta karkare maganar tana kallon zahra data cika fal tana aunawa batool harara, nan kuma aka koma caftar kishiya da kishi, batool na basu labarin budurwar Dr bash, data nace tana sonshi wai ita Dr basira, nan ta shiga basu labarin diraman da suke kwasa da Dr bash akan basira suna ta shan dariya gwanin sha'awa, ummi na jinsu kawacce na kawo nata firan da abinda ya shafi nata gidan, ummi na jinsu duk in taji abinda zata gyara masu ta gyara musu , tana yi tana kara koyar dasu dabarun zama da miji da yadda zasu samu rabo duniya da lahira, a haka aka kira mangariba suka tashi domin zuwa su gabatar da sallah.
Bayan ya ajiye Asmah bai zame ko ina ba sai asibiti gurin Dr bash, saida ya shiga harabar asibitin yayi parking sannan ya daga waya ya kira shi, yana dagawa yace "gani na kawo maka ziyara asibiti" Dr bash dake zaune a office É—inshi É—aga kai yayi ya kalli harabar asibitin, inda ake parking motoci, aiko idanunshi ya sauka kan motar Aslam, sai lokacin ya yarda, don da jinshi kawai yayi, aiko cikin son ya jashi yace, "aiko dai ka makaro, dan yanzu nabar asibiti, kaima, kayi ganganci kasan yau weekend ne ba kowani time zaka sameni a asibiti ba" Aslam da idon shi kekan motar Dr dake fake a kusa da shi yace"to shi kuma motar nan na uban waye, Mallam karka raina min hankali mana" dariya bashir ya kwashe dashi yana cewa "ta kaima irin wannan ziyara haka ba notice" Aslam yace "to ko na koma ne" da sauri bashir yace "ni na isa nace ka koma yi hakuri ka karaso babban yayan mu" kashe wayar yayi batare da ya amsa mashi ba, ya fito ya kulle motar shi tare da nufar cikin asibitin.........
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
FisabilillahðŸ™.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOk
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
112
Yana shiga office ɗin Dr bash ya taso da sauri hannun shi rike da hanky ya shiga kakkaɓe mai kujeran dake gaban table ɗinshi, yanayi yana faɗin "sannu da zuwa babban yayan mu, sannu da zuwa sannu da zuwa maraba maraba lale lale" da jin ma yadda yake maganar kasan harda shaƙiyanci a cikin lamarin, yana gama kakkaɓewa yace "bismillah yaya ga gurin zama" Aslam bai tanka shi ba ya nemi guri ya zauna, fridge Dr bash ya nufa ya ɗauko mai ruwa da lemon kwalba da cup ya ajiye mai, sannan ya nemi guri ya tsuguna ta gefen Aslam, harda wani duƙar da kai, irin dai yadda ake gaisar da sirikai, cike da ladabi kamar da gaske yace "barka da yamma yaya, an wuni lafiya ya aiki ya iyalai, ya ɗoƙari" Aslam kam shiru yayi ya kasa amsawa a ranshi yana jinjina shaƙiyancin bashir, jin shiru Aslam bai amsa shi ba yasa ya dogo ya kalle shi tare da cewa "yaya a dai ta hakuri damu bansan laifin da nayi ba baka amsa gaisuwata ba," share shi Aslam yayi bai tanka ba saima wayar shi da ya zaro a aljihu ya shiga lalubar lambar Asmah, bashir ƙin tashi yayi a tsugunen,kallo fuskar Aslam yakeyi yana karantar shi, sai yake ga kamar akwai damuwa a tattare da shi, Aslam kuwa share shi yayi, ganin haka yasa bashir miƙewa tare da cewa "wlh Aslam kai mugun dan air ne, " kallon shi yayi ya watsamai harara tare da cewa "har nakai ka, ai baka cika babban dan iska ba tunda ka tashi ai na ɗauka a wurin zaka kwana" dariya Dr bash ya kwashe dashi, yana zagayawa ya zauna a nashi kujeran irin mai jujjuyawa da mutum ɗin nan, yace "to yane meye labari kwana biyu saduwa tayi wuya" Aslam yace "wlh Abubuwan ne yanzu sai a slow" Dr bash yace "wlh fa sai a hankali, to ya amarya ya Amarci, fatan dai anci Amarci lafiya" kallon shi Aslam yayi "tare da cewa ina ruwanka, tunda kai kaci naka ai shikenan" dariya Dr bash yayi tare da cewa "faɗi ka kara naci sosai kuwa inama tsakiyar cine yanzu haka, kaii aure da daɗi wlh nake gaya maka ma Mallam, abin sai wanda yayi, my teema duniya ce" hararan da Aslam ya watsamai yasa yayi sauri daura hannu a baki, yana zaro ido, can kuma yace "au na manta a shefa kai sirikina ne yanzu bai kamata na dinga faɗa maka irin wadannan maganganun ba" Aslam yace "kaidai ka sani da iskancinka, kuma wlh Abi min kanwa a hankali ba motar hawan mutum bace da zaike hawa any how" Dr bash yace "sannu fa yaya mai kanwa, inace kaima kanwar wani ka ajiye a gidanka, kake hawa " Aslam yace "karya kakeyi ba kanwar kowa na ajiye ba kanwata ce" bash yace "nafa ga alama, daɗin abin nima dai inada kanwowi bama kanwa ba" Aslam yace "to naji parrot sarkin surutu, ni yanzu duk ba wannan ya kawoni ba" gyara zama bashir yayi, ya maida hankalin gaba daya ga Aslam dama tun farko ya fahimci kamar yana da damuwa, "ina jinka friend meke damunka" huci mai zafi ya furzar daga bakin shi, sannan ya kalli Dr bash fuskar shi ta koma serious alamar abinda zai fada mai mahimmanci ne yace, "wlh neman mafita nakeyi shawara nakeson ka bani" bash yace "ina saurarenka abokina menene damuwarka"tiryan tiryan Aslam ya shiga ba bashir labarin abinda ya faru tun farkon aurensu har zuwa halin da suke ciki a yanzu.
Tun kafin labarin yayi nisa wani mugun dariya ya turnike Dr bash, matsewa kawai yakeyi saboda yana son yaji karshen labarin kuma a yadda Aslam yaci serious akan maganar yana yin dariyar nan zai bata komai karshenta ma yayi zuciya ya tashi ya wuce, saidai idan ya faÉ—i abinda bazai iya jurewa ba yayi sauri ya tsuguna kasan table É—in dake tsakiyarsu kamar yana duba wani Abu anan zai samu yayi dariyar shi mara sauti sannan matse ya dago yaci gaba da sauraren Aslam yana gyada kai kamar yana jimamin maganar.
Saida Dr bash ya tabbatar Aslam yakai karshen labari, ya kalle ya kece da wata irin dariyar keta har yana dukewa yana rike ciki,a hargitse Aslam ya zaro ido yana bin bashir da kallo, a fili yace "kan bantan uba " ina bashir baisan yana yi ba, a fusace ya miƙe tare da dukan table din dake tsakiyar su da karfi, sannan ya juya yayi hanyar fita, bugun table dinne ya dawo da bash hankalinshi, da sauri yabi bayan Aslam ya riko mai hannu, still kuma bai daina dariyar ba, Aslam kallo shi yakeyi a zuciyar ji yake kamar ya buga mai kulli a baki sai hakoranshi sun zubo kasa,
Fisge hannun shi yayi, ya kara yunkurin fita a office din, a karo na biyu Dr bash ya sake riko hannun shi, Aslam yace"bashir sakeni ko na maka gula wlh, wato ga kasurgumin mahaukaci ko, na baka labari ka sakani gaba kana min dariya wato ga sabon kamu daya kwanto daga sakatiri" da'ker bashir ya sausauta dariyar shi, yana haki yace"dan Allah da manzonsa friend kayi hakuri, wlh in ban samu nayi dariyar nan ba bazan iya magana bane, dan Allah kayi hakuri ka koma ka zauna pls for d sake of Allah badan niba" zare hanninshi yayi cikin na bashir ya koma ya zauna ammafa fuskar shi babu alamun rahma.
Shima bashir mazaunin shi nada ya koma ya zauna, da'ker ya saisaita kanshi sannan ya kalli Aslam yace,"A gaskiya Abu baiyi dadi ba abokina sannu fa da hakuri, har ina tambayar ka ya amarci,mutanen gari duk inda kabi ana ango kasha mai ashe ko ruwa baka sha, Ashe kai har yanzu muna ango ne, ayya wlh abin tausayi, amma fa indai zan faÉ—a maka gaskiya kaji, zance kayi wauta, ta yaya zakace mace budurwa ba wai bazawara ba diyar Mallam bahaushe ta fara nuna bukatar ta akan ka sannan ka kusanceta, na farko fa bawai kun tabayi bane fa, haba haba Aslam kaima kasan wannan lamarin bamai yuwuwa bane, kumama kai ba wai ka taba nuna kana so bane fa ta hana balle kace ka kyaleta sai Randa ta so, yoo ni dana nuna inaso aka hana ai ban tsaya daukar wannan iskancin na amaren zamani ba kof daya na mata kawai aka wuce wurin, to balle kai dana tabbata a yanda ka bani labari irin soyayyan da kukema juna wlh baza ta hanaka ba, ka cire tsoro ka jaraba abokina wlh zakazo ka bani labari nina gaya maka, idan kuma baka da isashen lafiya ne kana tsoron karta rainaka, ka faÉ—a min na hada maka yan kwayoyin da zasu taimake ka baza ta gane ba " harara Aslam ya watsamai tare da cewa "an gaya maka kowa ma irin Kane,ni duk ba wannan ne ke damuna ba" Dr bash yace "to meke damunka, na gane Mallam kawai tsoronta kake, me tsoron mata kawai" ya kare maganar cikin sigar zolaya, Aslam yace "kaima shaida ne niba matsoraci bane, koda cen balle yanzu" Dr bash yace "na sani ai ba tsoron kowa nake nufi ba tsoron Asmah nake nufi" Aslam yace"ko ita bana tsoron ta" bash yace "karya kake yi meyasa ranar da asirinka ya tonu ta gane ciwon karya kakeyi ka kasa tun karanta kai tsaye saida kaga ka kasa bacci sannan kaje " Aslam yace "ai laifi na mata shiyasa bawai dan tsoro bane" Dr bash ya kwashe da dariya tare da cewa "ka yarda kawai Mallam kana tsoronta" ran Aslam fa ya fara baci ganin yadda Dr bash ya dage akan tsoron Asmah yake" haka sukaita musu, Aslam na magana a zafafe, yayinda yake ta kokarin kare kanshi, bashir kuma nata kwasan dariya da gangan kuma yaketa kokarin kunna Aslam din" saida ya tabbatar ya kunnu iya kunnuwa sannan yace" yanzu naji, kadai dage ba tsoron ta kake ba, to naji amma fa bawai na yarda bane, idan kana so na yarda yau ka tabbar min da hakan ni kuma Wlh idan har yau kayi dis virgin dinta zan yarda ba tsoron ta kake ba, musa bet ma wlh ka faÉ—i duk abinda kake so " Aslam cikin huci yace "haka kace ko to shikenan ni kuma zan tabbatar maka da hakan yau basai gobe ba" a haka suka ajiye wannan caftar suka kama wata, basu suka bar asibiti ba sai da ana kiran mangaruba, a masallacin bakin asibitin sukayi sallah bayan sun fito bash yace "sai ina yanzu" Aslam yace "gidan Rabi'ah zanje na dauketa muje gida daga nan kuma mu gaisa da ummi" bash yace "nima nan zani na dauki batool to amma da nace sai nayi sallan isha'e amma muje kawai kasan ance tafiya bibbiyu yafi dadi" kowanne motar shi ya shiga suka dauki hanyar anguwan fadukwai inda gidan ya Rabi'ah yake.
Suna isa kofar gidan motar Abban hanifa na shawo kwana ta dayan hanyar, dukkansu kusan a tare sukayi parking nan suka shiga gaisawa, Dr bash sai lokacin yamai barka baki da baki, nan kuma ya kira Rabi'ah ya gaya mata gashi dasu Aslam, sannan suka shiga, bama kowa a falon duk suna ciki, zama sukayi Abban hanifa kam dakin shi ya nufa, basu fi 5 minutes da zama ba Ummi tayi sallama a falon, fuskar washe take cewa "oyoyo yarana sannunku da zuwa ina azkar naji Rabi'ah na fadin isowarku" daidai nan ta karaso ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, Dr bash ne ya fara saurin sauka daga kan kujera ya shiga gaisheta tare da mata barka da isowa lafiya, Aslam kam matsawa yayi gabanta ya tsuguna tare sa kamo hannunta daya ya rike fuskar shi cike da farin cikin ganinta yace"sannu da zuwa ummi fatan kin iso lafiya," murmushi tayi tana daura daya hannunta akan tarin suman kanshi, tace "lafiya qalau my son fatan na sameku lafiya" yace "lafiya qlau , nayi kewarki sosai ummi " tace "nima haka my son, ya aiki ya iyali" yace "alhmdllh ummi" tace "masha Allah, Allah ubangiji ya muku albarka, baki daya,ya karamuku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya Baku zuri'a dayya ba" kusan haɗa baki sukayi dukkansu bashir, Aslam, ya Rabi'ah da batool da fitowarsu kenan daga ciki da kuma Amir da shigowar shi kenan falon, gurin cewa "amen ummin" sai sannan ta sauke hannunta akan Aslam shima sakin hannunta yayi ya nemi guri kusa da kafarta ya zauna, Amir kuwa hannu yaba Aslam da Dr bash sukayi musabaha, sannan ya tsuguna ya gaida ummi, kafin ya koma kusa da dr bash ya zauna, ya Rabi'ah data zagayo ta zauna kusa da ummi ne tace "ya Aslam ya Amir da Dr ina wunin ku" Amir ya amsa da lafiya qalau sisto, Aslam ya amsa da ina gajiya yayinda Dr bash yace lafiya qalau anty Rabi'ah barka fa Allah ya raya, da amin suna amsa, batool ma karasowa tayi ta gaida Aslam da Amir ta nemi guri ta zauna, a fakaice Dr bash ke hararanta,ganin ta gaida kowa ban dashi, hararanta ummi tayi tace "shi bashir din uwa ya kashe miki hala" kallon ummi tayi tana dan zumɓuro baki sannan ta kalleshi tace "to ina wuni" duk dariya suka saka mata, banda Aslam daya kalleta ya dauke kai, shifa har yanzu baijin zai iya sake musu fuska , don rashin son raini a jninsa yake, Asman shi ne kawai zai laminci ta raina shi ita ma albarkacin soyayya.
Daidai nan Amira ta shigo falon samun tayi suna dariya, bata San ko na meye ba, ta dai ƙaraso, zama tayi a hannun kujera kusa da ya Rabi'ah ta kalli su Aslam da Dr bash ta gaishesu a tare, amsa mata sukayi, gaba daya, sannan ta maida kallonta kan Amir da tunda ta sawo kai falom yake ta binta da kallon luv yana murmushi tace "yayana barka da dare, ka dawo lafiya ya aiki" fuskar shi a washe cikin farin ciki da annashuwa ya amsa mata cike da kulawa, ya Rabi'ah tace "oh ni Rabi'ah duniya mutane kala kala wancen taki gaida nata mijin,wannan kuma saida ta ware shi dabam sannan ta gaishe shi bata hadashi cikin jam'in mutane ba,lallai yaran mummy kuma sha'anin ku, kai kuma ya Amir babu ko kunya kake mata irin wannan kallon a gaban mu " hararanta Amir yayi, sukan dan taba wasa da Rabi'ah kasancewar su abokan wasa, ummi ce ta kalle ta tare da cewa "ya isheki haka Rabi'ah saka idon ki ya fara yawa ina ruwanka wai" dariya ya Rabi'ah tayi.
Su Asmah da zahra da khadijah ma fitowa sukayi bayan gaisuwa suka zazzauna aka shiga dan fira jefi jefi, ya Rabi'ah ta mike ta kawowa su Aslam Abinda tabawa, Abban hanifa ne ya fito yayi wanka ya canja kaya, kallonsu yayi yana ba amir hannu Wanda shine basu gaisa ba yace " Ah'ah guys kuce duk kana nan kenan" matar shi ta amsa da "ba dole ba kowa ya biyo sahu" dariya yayi sannan ya shiga gaisar da ummi, daidai nan kuma aka fara kiran isha'e, kallon yayi yace "nidai nayi masallaci" Amir ne ya mike tare da cewa "muje nima" sauran ma suka mike, Aslam ya kalli ummi yace" umminmu bari muyi sallah" tace "to sai kun dawo" sannan suka fice.
Suma matan ciki suka koma sukayi sallah, dama sun riga sunci abinci, nan ummi ta bude jakar Asmah ta kwaso sauran magungunan data bata tace "karbi ki shanye ki bani hannu tunda kinci abincin anan shikenan yanzu inkinje gida ba lallai kisha ba" saida ummi ta mata kat a lokacin nan, sannan ta barta haka.
Koda su Aslam suka dawo basu shigo ba' Abban hanifa ne daya shigo ya shaida musu, mazajensu na jiransu waje, kowacce kuwa ta tattaro kayanta sukayi sallama da ummi suka fito har main falo suka rakosu, har Asmah zata fita daga falon ummi ta kira ta a kunne ta raɗa mata "daga yau ki dinga mayar mai da martanin kinji" cike da kunya ta gyada kai, Rabi'ah data gama kasa kunne bata jiyo komai ba tace"wai umminmu nifa ban gane ba" ummi tace "ai baza ki gane ba rabi, kuje oh abinku karku ɓata musu lokaci sai da safe, kuzo gobe da wuri kunji ko" da to ummi suka amsa sannan suka fice.
Kowacce motar mijinta ta shiga suka dauki hanyar gidansu,suna fita layin kamal na shigowa, shima bai wani dale ba ya dauki deejanshi suka wuce.
A hankali yake tukin cike da kwarewa, zuciyar shi kuwa cike take da annashuwa, yanayi yana kallon ta yana murmushi, itakam Asmah gaba daya hankalinta naga maganganun da sukayi dazu da ummi, babu abinda yafi tsaya mata arai irin cewa da ummi tayi, ta dinga mayar mai da martani, Aslam ganin tayi nisa yasa ya kunna wakar *saida ke* na hamisu bireka yana bi a hankali, sautin wakar ne ya dawo da hankalinta kanshi a kan dan bakinshi ta sauke idanunta inda yake motsashi a hankali yana bin wakar.
Karki barni, sahibaaata♪
Karki ƙini ki fahimmmta♪
Saidake zani huuuta♪
Zuciya ta dake ne ta lallabo♪
Ta amince ki madani dan dako♪
Shiru tayi tana sauraren wakar da yakeyi, har cikin zuciyarta ko wani baiti daya na wakar ke tabawa, ji take kamar ita aka rairawa wakar,har suka karaso gida babu Wanda yayi ma wani magana cikinsu, bayan ya kashe motar yayi parking, zagayowa yayi ya buÉ—e mata kofa, dagowa tayi ta kalle shi fuskarta dauke da murmushi tace "nagode Mr Aslam" kashe mata ido yayi tare da cewa "u ar wlcm" fitowa tayi ya kulle motar tare da daukar Jakarta suka shiga ciki, suna shiga falo ya zauna a kujera yana cewa "wash yau nagaji gaba daya jikina ciwo yake min" ita kam Jakarta ta dauka tare da karasawa ciki, wanka tayi ta shirya cikin kanana kaya marasa nauyi tayi wanka da daddaÉ—an turarenta sannan ta fito fallon, tana baza kamshi, a tsaye ta same shi, yana niyyar shiga ciki, kallonta yayi tayi mai kyau sosai, murmushi ya sakar mata tare da cewa "har kinyi wanka," murmushi tamai itama ba tare da ta tanka ba, yace "to nima bari nayo nazo ki bani labarin abinda ya faru yau a gidan aikin suna" tace "aiko je ka dawo kasha labarai bari na Samar maka abinda zakaci kafin ka fito" yace "OK tnx" ya wuce ya shiga ciki ita kuma ta wuce kitchen.
Jelop din spaghetti da yaji kifin gwangwani da kayan lambu ta mai, sharp sharp kuwa ta gama ta kwashe, ta kawo dinning , tana cikin jerawa ya fito shima cikin ƙananan kaya, kujera yaja ya zauna, tare da cewa "masha Allah yar aljannah sannu da kokari" murmushi tayi tare da daukar plate ta shiga serving dinshi, shake plate tayi taf sannan ta tura mai gaban shi, fork ya dauka ya d
É—ibi taliyar ya kai loma daya bakin shi, ajiye fork din yayi yana lumshe ido tare da muymuy da baki, hannu yakai ya rike kunnenshi daya yana murzawa yana gyada kai, tana ganin ya fara haka tasan karshen maganar, dariya ta kwashe dashi,tana cewa "zaka fara kenan ko" bude idanu yayi yana murmushi yace "to aike ne wlh kin iya girki mai dadi da saka mutum santi, test din girkin ki daya dana mummy, kai naki ma yafi nata dadi, dan yanzu ita tadan manyanta komai nata ya rage quality" zaro ido tayi tace "innalillahi Mummyn kake cema haka, to kuwa sai na gaya mata" dariya ya kwashe dashi yana cewa "ai nasan baza ki iya bane yarinya", haka yake ta cin abincin suna fira cikin nishadi harya kammala.
Falo suka dawo ya zauna akan 3 sitter tare da daukan remote yana chanza Chanel, zuwa tayi ta kwanta a kujeran daya zauna tare da yin pillow da laps dinshi tana kallon fuskar shi, shima kallonta yayi bayan ya gama canza Chanel din ya saka Wanda yake son ya kalla, kashe mata ido yayi tare da cewa yanzu kuma sai ki bani labarin abin da ya faru yau a gidan Rabi'ah, murmushi tayi tare da cewa "oya karkabe kunnenka kasha labari" karkabewan kuwa yayi, tiryan tiryan ta fara bashi labarin tun daga zuwanta gidan irin rungumar da suka ma juna ita dasu batool da irin farin cikin da sukayi na ganin juna, har aka gangaro batun ciki.
Kallon fuskarta yakeyi, babu ko keftawa zuciya cike da wani irin rauni, tunda ta fara bashi labarin batun cikin da yan uwanta keda shi zuciyar shi ta karye tausayin Kansu ya kamashi, daga yanayin yadda take bashi labarin cike da zakuwa da shauki ya tabbatar mai da abin ya shigeta sosai, take yaji a zuciyar shi ya zama wajibi yau shima ya ajiye duk wani Abu gefe ya kusanceta, ko suma zasu samu nasu cikin, gefe guda kuma ga bet dinshi da Dr bash dake dawo mai dalla dalla a zuciya kamar a yanzu suke kullawa.
tuni idanunshi sun rine ya ma daina fahimtar labarin da take bashi, da wani irin sauti ya kira sunanta, take hankalinta ya dawo kanshi ta dago da idanunta ta sauke a cikin nashi, ji tayi gabanta ya fadi meya same shi ne haka yanzu yanzu, shima yana kallon cikin idanunta yace "kina son ciki kema" jim tayi kaÉ—an kafin a hankali ta gyada mai kai don da gasken tanaso itama, ya sake cewa, "kin amincemin a yau na baki ciki da yardan ubangiji"duk da ta daÉ—e tana jiran wannan rannan saida gabanta ya yanke ya fadi......
Me kuke tunani zai zama amsar Asmah, yes or no, 😅
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
FisabilillahðŸ™.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO ~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.