Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 28 of 89

Page 53 & 54

Waige waige ta farayi alamar tana neman wacce ya kira da my husnah, daidai nan su batool suka qaraso , suma ganin Aslam ya basu mamaki , gaidashi sukayi, sannan suka ce, zahra , da Asmah suzo suje ya kamal na jiran su a get, yau bazai qaraso ciki ba sauri yakeyi, kafinma su gama rufe baki tuni Asmah ta kama hanyar get, ranta fal mamakin Aslam, to kodai kunnenta ne ya jiyo mata karya, kai ina kunnenta ne ,bataji mai ya fad'a da kyau bane, anan ta watsar da maganan bata wani dauke shi da muhimmanci balle ya dameta,

haka suka qarasa har wurin motar ya kamal , suka shiga ya ja su zuwa gida,

Aslam kam suna barin shi a wurin , ya naushi iska , ranshi na matuqar tafasa , ganin yadda ta wuce ta barshi a tsaye kamar wani sakarai , a fili ya furta wato daga an ambaci sunan shi ko tsayawa ta saurareni batayiba ta tafi gareshi ni kuma ta barni a tsaye kamar mara aikin yi ko, zakuyi bayani wlh
Daga ke har shi yau zan kawo karshen wannan cin amanar naku

zabura yayi ya fad'a mota ya bi bayan su kamal a guje, kamar ana binshi a baya, ranshi na tafasa, yau zaije ya samu kamal ayi wacce za'ayi , yau za'ayita ta qare komai zai faru ya dad'e bai faruba

Zee taga idi yau, dan mami tunda ta haura sama bata qara waiwayarta ba , yunwa ne ya fara sakadarta, tun tana daurewa, hardai ta miqe zaune ta rafka tagumi , da hannu bibbiyu, ta ajiye waya , juice da ruwan da mami ta ajiye mata d'azu tuni ta shanye, sai goru nan,

Ya kamal na fakin ,suka fito zasu wuce, Jakarta ya dauka kamar yadda ya saba har ta kama hanya zata bi bayan su zahra ,ya kira sunanta da "my Asmah", juyowa tayi tana kallon shi da murmushi a fuskarta itama cikin sassanyar daddadar muryarta tace "na,am my kamal" murmushin fuskarshi ne ya fad'ad'a, bata taba kiranshi da wannan sunan ba sai yau wani dad'i yaji ya lullubeshi,

Yace "me Aslam yajeyi a makarantarku" dan shiru tayi kafin tace"nima ban sani ba kawai ganin shi mukayi kuma kafin wata magana ta had'a mu, ka iso shi kenan muka wuce muka barshi a can" wani d'an murmushi takaici kamal ya saki kafin yace"ni nasan meya kawo shi, na riga na gama gane take takensa tun ba yau ba , amma kuma na lashi takobin wannan karan bazai taba bari yayi nasara a kaina, inason na roqeki wata alfarama dan Allah asma,u" kallan shi tayi da daradaran idanunta , da suka fi komai fusgar mutum idan yana kallonta, cikin sanyi jiki tace"wacce irin alfarma ce wannan ya kamal, ka fad'e ta, indai batafi qarfina ba zan maka bi'izinillah" yace "inaso ki bani dama na sanar ma magabatan mu batun soyyayar mu, domin na fara ganin alamun wasu suna mana bita da kulli" bata fahimci inda maganarsa ya dosa ba amma bata wani tsaurara binkice ba tace"nà amince maka indai hakan zai faranta ranka masoyina"

don ba qarya itama yanzu ba kadan ba take jin ya kamal din har cikin zuciyarata , saboda kulawar da yake nuna mata da irin soyayyar da yake nuna mata , da irin kyautatawan shi a gareta, har , yakai matakin da zata iya hakura da karatun ta, ta auri Kamal , ta amince daga baya ta qarqare karatun a d'akin sa , tunda tasan ba zai hana ta ba,

Kallonta yayi cikin tsananain farin ciki fuskarshi na qara fad'ad'a da murmushi yace"da gaske kike my luv " gyada mai kai tayi itama tana murmushi,

Daidai lokacin Aslam ya danno kan motar shi cikin gidan a guje , hangosu suna sakarma juna murmushi ya qara fusatashi aikuwa ya nufo Kansu gadan gadan , zuciyarshi na gaya mai yabi takan kamal kawai kowa ya huta ,

Da wani irin zafin nama kamal ya kauce ganin mota ya nufosa gadan gadan, Asmah kam duqewa tayi ta daura hannu akai ta Riga ta gama sadaqarwa ta mutu kawai, daidai da ita ya taka wani irin mahaukacin birki ,

A wani irin fusace ya fu bud'e murfin motar ya fito , zagayowa yayi ya kama , hunnun Asmah cikin bacin rai da rufewar ido ya figeta zuwa part din mummy , da sauri kamal ya rufa musu baya,

Dan Allah kuyi hakuri wlh kwana biyu bana samun time sosai ne , kuyi manage da wannan ba yawa, karkuyi fushi fa mutanena😄

Oum ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa Mahaifiya, Allah kajiqan iyayen,}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.