Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 63 of 89

Page 105

~ASLAM~

Bayan fitar ta daga dakin dafe goshi yayi ya kama fareti a dakin, yakai gwauro yakai mari ya kasa zama, can dai ya naushi iska tare da cewa"oh my god, yanzu miye mafita" dan tsayawa yayi daga faret din da yakeyi da alama wani tunani yayi, can kuma ya furta "yesss" kafin ya fice daga dakin da sauri kitchen ya fara nufa bata nan, dan haka ya duba falo nan ma wayam, nan take ya tabbatar tana dakinta tunda bata wuraren nan biyu daya duba, dakin nata ya nufa cikin sauri sauri har ya mika hannu ya kama handle din kofar zai tura, take wani shakkar ta ya lullubeshi , zuciyar shi ta shiga ce mishi yanzu in ka shiga mai zaka ce mata, take yaba zuciyar shi amsa da babu, da baya da baya ya dinga yi har ya bar kofar dakin.

Tunda ta shige daki ta lalubi bakin bed ta zauna dabass, take duk abinda ya faru tun daga fara ciwon Aslam har zuwa yau ya shiga dawo mata tsab a brain dinta, ta tuna yadda yake tsananin jin jiki da yadda kullum Daren duniya yake fama da matsanancin zazzabi, Ashe duk karya yake mata dan dai kawai ya samu ya rabi jikin tane, bata son karya, balle ma irin wannan karyar da zaka ma Wanda ya aminta dakai, take Kamal dinta ya fado mata a rai, Kamal bai taba yi mata karya ba, hawaye taji yanaziraro mata tunawa da irin yadda Kamal ya nuna mata soyyaya da kulawa, a fili ta furta"Allah sarki ya Kamal, Ashe dai nida kai baza mu zamto abokan rayuwar juna ba" daga haka kuma ta zame ta kwanta girkin da bata karasa ba kenan, haka tayi ta tunane taunane daga nan kuma barci barawo ya sace ta mai cike da mafarkan kamal.

Aslam ganin bata fito ba har azahar gaba daya hankalin shi yayi matukar tashi, kusan so biyar yana zuwa kofar dakinta da zumar shiga, sai kuma ya kasa, haka yata zarya bashi falo bashi daki, ko abinci bai samu daman ci ba, kai yunwar ma gaba daya bai jita ba, sai gurin yamma da yaji ulcer na shirin tirnike shi, ya shiga kitchen ya Samar ma kanshi abin tabawa.

Sai gurin karfe biyu ta farka, a firgice, take ta shiga furta astagfurullah, mafarkin da tayi a yanzu ya tayar mata da hankali, ta sani ya kamal ya haramta a gareta, tunda ya kasance a yanzu mijin yar uwa kuma kanwarta,amma yadda ta kwanta tana tunanin shi barci ya kwashe ta yasa har take mafarkin shi, kallon agogon dake manne jikin wall din dakin tayi biyu harda minti 10, lokacin tuni har an idar da sallan azahar a masallatai, alwala ta dauro ta fara gabatar da sallah, bayan ta idar kuma ta koma ta kwanta, Aslam ne ya fado mata a rai, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, samun zuciyarta tayi da son sanin wani hali yake ciki yanzu, take taji zuciyarta na azalzalan ta akan ta tashi ta fita ko ganin shi ne kawai tayi, da'ker ta samu tayi yaki da zuciyarta ta tayi fatali da wannan umarnin da take bata, wayar ta ta dauka ta kunna data ta shiga WhatsApp d'inta Wanda rabonta da shi yafi sati, message na gama shigowa ta fara bi daya bayan daya tana dubawa Wanda zata amsa tayi Wanda zata share ta share, haka har takai kan message d'in Khadijah, budewa tayi, idanunta ne ya sauka akan wasu zafafan hotunan da Khadijah ta turo mata yau kimanin kwana uku kenan, hotunan ta ne ita da kamal masu shegen kyau, kala kala cikin wanin irin yanayin da ita kanta baza ta iya fassarashi ba take bin hotunan da kallo, gasu fess da su sunyi wani fresh shar dasu, kallo daya zakama hotunan kasan ma'abota hotan cike suke da tsantsar so da kaunar junan su, yanayin murmushin dake dauke a fuskokinsu kadai ya ishi mai kallo shaidar hakan balle kuma idan ka kalli yanayin styles d'in hotunan, a kasan hotunan ta rubuta, "komai ya daidaita a tsakanin mu yar uwata fatan kema haka daga naki bangaren"

Bata sanda ruwan hawaye ya fara wanke fuskar ta ba sai gani tayi yana diga akan screen d'in wayar, ta bata lokaci akan kallon hotunan fiye da awa daya, can kuma Kamar wata tabbabiya ta saki wani kayataccen murmushi, a fili ta shiga furta "na taya ki murna yake yar uwata Khadijah, hakika Allah ya baki miji daya tamkar da dubu, Allah ya zaunar daku lafiya,ya Allah wannan soyayyar junan su da na gani kwance akan fuskokin su Allah ka dauwamar musu dashi har abada" reply ta mata da "wow masha Allah, perfect mach, gsky hotuna sunyi matukar kyau yar kanwata, tunda nake ban taba ganin couples d'in da suka yi marching sosai da juna irin wadan nan ba, kyawawan masoyan asali, Allah yabar kauna romeo & Juliet " a karshe ta kawata rubutunta da emoji kala kala, na murna dana murmushi tayi sending, sauka tayi a WhatsApp din ta koma gallery folder daya ta ware na hotunan kamal zallah, take ta shiga folder ta fara deleting d'in duk wani photo da ta Sani na shi dake wayarta, yadda take deleting hotunan shi haka takeji yana fita a zuciyarta, saida tayi deleting duk wani abu daya shafi kamal a wayarta, daidai da app da tasan shi ya saka mata a wayar saida ta goge dan kar ta dinga tunawa da shi, bata bar komai ba hatta da phone number dinshi saida tayi deleting a wayarta, take taji zuciyarta ya samu wani irin space mai girma wanda a da babu shi a zuciyarta ta, lallai kamal ba karamin wawakeken gurbi ya samu a zuciyar ta ba,wasai take jin kanta a yanzu babu kowa a zuciyarta.

Wayar ta da yayi ringing ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, sunan da ta gani na yawo a saman screen d'in wayar yasa bata san sanda ta saki kayataccen murmushi ba, cike da dauki ta daga wayar tare da cewa "Assalamu alaiki yake ummin mu" daga daya bangaren ummi tayi murmushi mai sauti sannan ta amsa mata da "wa'alaikissalam Asma'ul-husnah fatan kuma lafiya ya my son yake da fatan ana kula da shi sosai ko" murmushi tayi cike da jin kunyar maganar ummi tace "yana lafiya umminmu" ummi tace " masha allah yana gida ne ko ya fita don nata kiran wayar shi yanzu kafin na kira naki bai daga ba" Asmah tace "gsky bansan ko yana nan ba ko ya fita" ummi cikin zare ido tace "na shiga uku ni Aminatu, ban gane bakisan ko yana nan ko ya fita ba" Asmah cikin ko in kula tace "wlh umminmu ni rabona da shi tunda safe" ji tayi ummi ta rabka wani uban salati, kafin tace "Asma'u! kardai kice min zaman da kukeyi kanan ke da Aslam d'in wata da watan ni, Ashe baki da wayau ke shashasha ce ban Sani ba" tuni Asmah ta shiga zazzaro ido jin kalmomin dake fitowa daga bakin ummi, take ummi ta rufeta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, hankalin Asmah bai kara tashi ba saida ta tsinci muryar ummi na cewa "nasani, nasan abinda yasa kika ki bama Aslam dama duk da irin tarin soyayyar daya yake miki, kamal ne ko? To wlh ki kama kanki dan kamalu tuni ya shafe babinki, yanzu haka zancen da nake miki Nana Khadijah ciki ne da ita har na wata biyu, ke kina nan kin tsaya wasa da daman ki " tuni hawaye ya gama wanke fuskar Asmah, cikin muryan kuka ta bude baki tace "ummi wlh b" cikin tsawa ummi ta katseta da cewa "wlh me? ni babu abida zaki gaya min a yanzu, ki Sani shi so da kike gani tamkar tsuntsune dake sauka akan bishiya domin yayi kiwo, idan ya sauka a bishiya ya rasa abin da zai kiwata dole zai fira daga wannan bishiyar ya koma wata, idan kuma ba'ayi a hankali ba bazai sake wai wayar wannan bishiyar ba kenan har abada, idan zaki kama kanki ki kama, Aslam yayi miki laifi mai girma a baya kuma ya gane kurensa, tunda kika ga Allah ya sake hada ku a karo na biyu shi kadai yasan abinda ya boye a tsakanin ku, kiyi hakuri ki rungumi kaddararki da hannu bibbiyu, bari na tuna miki wani abinda kika manta kinsan dai bake kadai bace mace a gurin Aslam ba ko? ina fatan kina tune da zainab" take gabanta yayi wani irin faduwa,jin abinda ummi ta fada tabdijam har ga Allah ta manta da wata zainab matar Aslam, wahayenta ne suka kara karfin gudu, take ta kara yunkurin yin magana dan ta kare kanta, ummi lura da ta yi jikinta ya gama yin sanyi yasa wannan karon ta bata daman cewa wani Abu, baki na rawa tace"wlh umminmu ba abinda kike tunani bane, wlh ummi a halin yanzu babu burbushin soyyayar ya kamal ko digo a zuciyata," take kuma ta shiga bama ummi labarin abinda ya faru yanzu yan mintocin da suka gabata, kasancewar basa iya boye ma ummi komai dake damunsu a rayuwar su.

Sauke ajiyar zuciya ummi tayi yanzu hankalin ta yadan kwanta jin hakan daga bakin Asmah, tasan komai zaizo sa sauki tunda babu kowa yanzu a zuciyarta, kwantar da murya ummi tayi cikin sigar lallashi ta fara cewa" alhmdllh naji dadin jin wannan maganar daga bakin ki Asmah, yanzu kuma lokacin yayi da zakiba Aslam dama domin ya mallaki wani fili daga zuciyar ki, Aslam yayi miki laifi kuma ya gane kurensa a halin yanzu ya kamata ki saurare shi, tunda kikaga haka Allah kadai yasan menene ya boye a tsakanin ku, kuma nasan keme bazakice a yanzu bakijin Aslam ko kadan bane a ranki, ko nayi karya?" Ummi ta tambaya, shiru Asmah tayi ta kasa bata amsa, dan kam idan har tace batajin shi a ranta yanzu tayi ma Allah karya, jin shiru yayi yawa yasa ummi tace "uhummm ke nake saurare fa" cikin sanyin murya tace "umminmu a halin yanzu wlh bana jin kin yaya Aslam a raina kuma kai tsaye bazan iya cewa ina sonsa ba,nasan dai ina jin matsanancin tausayin shi a raina, kuma nakan ji kewan shi idan baya kusa dani bayan wadanan, bazance ga wani Abu da nake ji game da shi ba Ummi" murmushi ummi tayi a daya bangaren a zuciyarta tace ahaf magana ya kare, a fili kuma tace "naji hakan ma wani ci gaba ne da sannu zaki soshi, amma fa sai kin saka ma ranki hakan, nidai yanzu abinda nake so dake, idan har bakyaso nayi mummunan fushi dake, na baki nan da sati guda naji kyakkyawan sauyi, a zaman takewarku, idan kuma ba haka ba wlh zanje na samu Alhaji baba, da mallam na gaya musu, sannan kuma na samu mummyn ku da daddy na gaya musu suma, kinsan dai wanene Aslam a gare su baza suji dadi ba idan sukaji abida kike masa" girgiza kai takeyi kamar a gaban ummi take, ummi nayin shiru ta shiga cewa a firgice "dan Allah ummi kiyi hakuri kar ki gaya musu Wlh zan sauya, insha Allah zan karbi kaddarata da hannu bibbiyu" wani wahalallan ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan tace "alhamdulillahi naji dadin hakan, kuma ina nan ina tsumayen jin daddadan labari, nifa so nake kafin shekara ta zagayo kowaccen ku ta ajiye min jika, inso samu ne ma yan bibbiyu ko uku uku nake so" dariya Asmah ta kwashe dashi, daga nan kuma ummi ta shiga janta da wasa kamar wasu kawaye , karshe kuma ta shiga koyar da ita dabaru kala kala wadan da zasu amfaneta sosai nan gaba , Asmah taji dadin hakan sosai, nan ta bude memory tana ta saving dinsu, suààaààà£
Aàqnfi awa biyu suna waya kafin sukayi sallama.

Komawa tayi da baya ta kwantap akan bed dinta tayi lamo maganganun da sukayi da ummi ya matukar shigar ta , jikinta gaba daya yayi sanyi kalau, musamman kan cewa da ummi tayi zata fadama su mummy abinda ke faruwa,koba komai mummy da daddy sune mutanen da take matukar so bayan iyayenta, kuma baza suji dadi ace taki abinda suka haifa ba, koba komai Aslam jininsu kuma jinin mutum mafi daraja a idanunta Alhaji baba...........

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.