Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 85 of 89

Page 128

Ganin yayi shiru ya tsaya yana kallon ta alamar ya faɗa tunani, yasa tace "dan Allah ya Aslam duk abin da zaka yanke ya zama adalci, kada ka dube ni ko wani, ubangiji zaka duba ka dubu haƙƙin ta dake wuyan ka, tana zaune ne a gidan saboda kai saboda soyayyar da take maka, nasan tayi maka laifi mai girma kuma alhmdllh daga baya ta gane kurenta ta nemi yafiya, dan Allah da manzon sa ka yafe mata haka, taci koda albarkacin little ne da ta haifa maka, ka duba halaccin da ta maka, ta rainar maka cikin da ka cire rai dashi a jikin ta na tsawon watanni tara ta haife shi ba tare da sanin ka ba, ta shayar da shi ta raine shi, duk baka da masaniya ta kawo shi gareka a lokacin da kake tsananin bukatar shi, anty zee tana kaunar ka ya Aslam dan Allah ka tashi kaje gare ta ka share mata hawayen ta." Tsura mata idanun yana kallon ta har kai karshen zancen ta, ganin bai amsa ta ba,yasa ta mike ta isa gaban shi ta kama hannun shi ta shiga janshi da niyyar ta miƙar dashi tsaye, kasa wa tayi dan bai bata wannan daman ba, sai ma shi daya jawo ta ta faɗo jikin shi, dago da kanta yayi suna kallon cikin idanun juna, a hankali ya furta "ba kya kishi na ko husnah, kin dena sona ko?" Da sauri ta shiga girgiza mai kai cikin rawar murya tace "wlh ina son ka ya Aslam kuma ina tsananin kishin ka, son da nake maka ne yasa nake kwadaitar da kai kayi adalci a tsakanin matan ka domin bana so ka tashi da shanyayyen rabin jiki ranar gobe." Tana magana hawaye na taran mata a ido kamar kar ya ambaci kishi, ai sai taji hankalin ta ya fara tashi, ƙokarin mayar da hawayen ta ta shiga yi dan bata so ta basu daman da zasu zuba dan idan tayi haka zata karya mai zuciya ne har ya kasa tafiya wajen zee ɗin. Yace " zaki iya kwana ba tare dani a gefen ki ba." Karfin gyada mai kai tayi alamar eh, girgiza kai yayi yace " To ni banajin zan iya kwana ɗaya ba tare dake a gafe na ba." Da sauri tace "zaka iya dole zaka yi tunda haka Allah ya riga ya rubuto maka a cikin shafin kaddarar rayuwar ka, kullum kakan ce min na roke ka ko meye a duniya idan kana da halin shi zaka min, to yau gashi ina rokon ka dan Allah kaje wajen anty zee jiki na yana bani tana cen tana kukan rashin ka." Sauke ajiyar zuciya yayi kafin yace "Zanje gareta saboda ke da kuma little, amma bawai dan wani abu ba, zata ci darajar ku da kuma darajar su daddy sai kuma darajar igiyar aure." Murmushin yaƙe ta saki wanda yafi kuka ciwo jin hawaye na shirin ziraro mata yasa tayi saurin shigewa jikin shi ta boye fuskar ta a kirjin shi yadda bazai gane yanayin da take ciki ba, sun jima a haka, ganin baida niyar tashi yasa ita ta fara zare jikin ta sannan ta kama hannun shi dan tayar dashi a karo na biyu wannan karon bai hana ba miƙewa yayi jallabiyar shi ta mika mishi ya daura akan ƙananan kayan jikin shi, riƙo hannun shi tayi ya fara janshi jiki a sanyaye ya biyo ta ji yake kamar ya fasa tafiya, har bakin ƙofar falo ta rako shi sake mishi hannu tayi ta coge daga nan kallon ta yayi, ta sakar mishi murmushi, yace "muje mana." Ta girgiza kai, tare da komawa bakin falon daga ciki ta tsaya, kallon ta yake yi,itama daga bakin kofar da take tsaye ta zuba mishi idannu tana kallon shi fuskar ta dauke da murmushin karfin hali tana hannu ta shiga ɗaga mashi alamar bye bye, ganin bai tafi ba yasa tace "ka tafi mana honey." Girgiza kai yayi yace "kedai ki fara tafiya." Maƙe kafaɗa tayi tace "naƙi." Yace "zan dawo fa." Bubbuga kafa ta shiga yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa, ganin haka yasa yace "to ya isa naji bari na tafi." Ya fada yana juyawa domin tafiya har yayi taku biyu tace "baka ji ba." Ya juyo tace "ina son a samo mini baby yau dan Allah." Gadan gadan ya nufo ta ganin haka yasa ta shige da gudu tare da banko kofar ta murza key, murmushi yayi sannan ya juya ya nufi part ɗin zee zuciyar shi babu daɗi. Jingina bayan ta da jikin kofar tayi tana sauke wasu irin ajiyar zuciya a jejjere, duk abin da take yi karfin hali ne, kawai amma zuciyar jin shi take kamar tayi bindiga.

Jiki ba kwariya ƙarasa kofar part ɗin zee har zai danna doorbell sai kuma ya gwada murɗa handle din kofar, cikin sa'a kofar ta buɗe shiga yayi da sallama ciki ciki, sai dai ga yadda ya zata bata falon, ga dai komai a kunne harda su TV,bin falon ya shiga yi da kallo, rabon shi da shigowa falon nan har ya manta, zama yayi yana jiran fitowar ta , shiru har yana Neman kwashe minti 30, hakan yasa ya tashi ya nufi bed room ɗin ta, tun kan ya karasa yake ta jiyo sautun kukun ta tare da shesheka mai karfi, da sauri ya karasa dan ji yayi babu daɗi a zuciyar shi, yana shiga ya hangota durƙushe a bakin bed ta kifa kanta a bed sai kuka takeyi bata san ma ya shigo ba,cikin wani irin murya mai cike da tsananin tausayawa yace "zainab!" Cak ta tsayar da kukan ta kamar an kashe engine, tabbas taji muryar kuma taji kiran, amma bata gaskata ba, ganin haka yasa ya sake maimaita ta kiran "zainab." A hankali ta fara juyo da kanta kaɗan kaɗan zuwa inda ta juyo sautin muryar, jajayen idanun ta da suka rine tsabar kuka ta sauke a cikin nashi, cike da tsantsar mamaki take kallon shi yayin da shi kuma yake bin ta da kallon tsananin tausayi, fuskar ta gaja gaja da hawaye , sai ajiyar zuciya take saukewa, ta kasa dauke idanunta akan shi shima a nashi bangaren haka ne, ji yayi wani abu na tsungulin shi a zuciya, a hankali ya fara taka sawayen shi yana nufar ta, tsoro taji ya lulluɓe ta dan bata san da wanne yazo ba, sai dai ga mamakin ta tsugunawa yayi ya ɗago ta ya miƙar da ita tsaye tare da bata wani irin kyakkyawan runguma, jinta yau a jikin Aslam ɗin ta yasa taji kamar ba'a duniaya take ba, wani irin kuka ne mai masifar karfi ya kufce ce mata cikin kuka ta shiga cewa "Aslam ka yafe min wlh ina kaunar ka, na tuba nabi Allah nabi ka kayi hakuri." Bubbuga bayan ta ya shiga yi alamar rarrashi, ganin taki yin shiru yasa ya buɗe baki yace "ya isa haka my love ki daina kuka na yafe miki, karki sake kwatan ta abubuwan da kikayi a baya kinji."gyada kai tayi, tare da kara yin lamo a jikin shi, sai sauke ajiyar zuciya take yi akai akai, ganin tayi shiru yasa ya dago fuskar ta kallon cikin idanun juna suka yi, take ya sakar mata wani irin kyakkyawan murmushi, wanda yasa ta shagala da kallon shi, ganin haka yasa ya hura mata iskar bakin shi a fuska cikin raɗa yace "na canja ne." Samun kanta tayi da sakin murmushi tace "sosai ma, anty Asmah ta iya kiwo." Jim ta ambaci sunan ta sai da yadan tsaya yayi jim, gudun kar ta zargi wani abu yasa yace "Really." Tace "uhumm." Sai kuma ya saki wani murmushi mai sauti, Jan ta yayi suka nufi bed zaunar da ita yayi shima ya zauna a gefen ta ya kamo hannayenta ya rike cikin nashi, zura mata idanu yayi yana karewa fuskar ta kallo sai yau yake mata cikakken kallo mai sunan kallo tun bayan dawowar ta gare shi. Tana nan a zee babyn ta, babu abinda ya canja sai dai yaga tadan rame mishi kadan a ido. Ganin kallon da yake mata yayi yawa yasa tace "kana kallon duk yadda na tsofe ko, soyayyar ka da ɗanka ne suka mai dani haka." Murmushi yayi yace "waye yace kin tsofe gaki kamar bake kika haifi boy ba sai naga kin ƙara min yarinta sosai, kamar wata yar 15." Dariya ta kwashe dashi wanda tà dade bata yi irin shi ba, tsura mata ido yayi yana kallon ta, yana jin wani abu na sukar zuciyar shi game da ita.

Ranar sun raya wannan daren sosai cike da ɗokin juna,sun sha soyayya kamar su kadai je a duniya, lokacin da yaji shi rungume da zee samun kanshi yayi da jin kunyar asmah sai yake ga kamar bai kyauta mata ba duk da ita ta bashi dama, Aslam ya tausaya ma zee sosai ya kuma tabbatar ba ƙaramin kaunar shi take yi ba, take yaji a ranshi bai kyauta mata abin da ya mata, sai dai kuma a wani bangare na zuciyar shi sai mamaki yake yi, lallai ya tabbatar da zancen hausawa da suke cewa mata suna suka tara, sun sha romanace zafafa, wanda shi karan kanshi yasam yayi missing dinsu, domin ba karya zee gwana ce sosai a wajen romance sai dai kuma lamarin ya canza lokacin da ya shige ta, salam yaji kamar gari ba sugar, haka dai ya daure ya bar abin a ranshi ko a fuska bai nuna mata komai ba.

A bangaren Asmah kam ranar bata iya barci ba sai juyi kawai takeyi a makeken gadonta, tana yi tana zirarar da hawaye, zuciyarta na hasaso mata ga ya Aslam ɗinta cen da zee suna soyayya, tayi kuka kamar me har sai da tayi dana sanin tura shi gurin zee ji tayi dama ta kyale shi kawai duk ranar daya ga dama yaje gare ta, haka zuciya tai ta hasaso mata mugayen abubuwa, har da kudirin cewa baza ta sake bari Aslam ya je gurin zee ba idanunta sun rufe kishi kawai ke kwakwular zuciyar ta, cikin ikon Allah kamar daga sama taji wani bangare na zuciyar ta na cewa, me kike yi haka kuma Asma'u? So kike ki kwashe ladar ki a wajen Allah maza kiyi istigfari, samun kanta tayi da cewa astagfirullah a baiyane, kamar kuma an tsungule ta, ta diro daga kan bed din ta fada toilet ta dauro alwala, nafila ta gabatar sannan ta shiga addu'o'i daga karshe ta dauki kur'anin ta ta shiga karan tawa a nan gurin barci ya kwashe ta mai cike da daddadan mafarki wai tana dauke da juna biyu. Da a suban fari ta farka take mafarkin da tayi ya shiga dawo mata dalla dalla, daga hannu tayi sama tace "ya Allah ka tabbatar da wannan mafarkin nawa kasa wata rana ya zama zahiri ba mafarki ba." Sakayau ta farka zafin da zuciyar ta ke mata na kishin zee ya ragu sosai sai ɗan burbushi wanda baza a rasa ba. Bayan ta gabatar da salla wanka tayi ta shiga gyara gidan ta bayan ta gama kuma ta shiga kitchen ta haɗa breakfast bata haɗa da Aslam ba, sanin cewa yana gurin zee iya ita da boy kawai ta haɗa suka ci abinsu suka koshi ta dawo falo ta zauna zaman jiran shigowar Aslam dan wlh kewar shi take kamar ta bishi take ji, tana yi tana kallon agogo har karfe takwas babu shi babu alamar shi, take taji ranta yana so ya ɓaci, cikin taimakon Allah harshen ta ya shiga karanto innalillahi wainnailaihi rajiun, tana nan dai zaune a falo karfe Tara da minti goma dai dai taji an danna doorbell, da rawan jikin ta, tashi ya shiga buɗe ƙofa sai dai abin da ta gani ya kusa tarwatsa zuciyar ta...

Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book ɗin ga duk waccce ta rasa mahaifiya allaha kajiƙan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.