Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 12 of 94
    Haka suka yini ranar zubir a asibitin. Shi kansa bai samu kansa ba sai wajen goma na dare bayan ya maida Aunty Saliha matar Uncle Yousuf gida da yaransa yace ya dawo masa da motar ya wuce kawai shi dole zai kwana anan saboda Daddy shima dole an bashi gado. Dr Khalifa kuma yace bazasu sallamesa ba har sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da rai. Godiya yay masa da hakan dan harga ALLAH ya matuƙar gajiya dama ga yunwa dake cin hanjinsa kasancewar bai wani samu abincin kirki yaci a yinin ba sai wata ƴar gurasa. Sai dai babu yanda zai yi tunda hanyar neman abincinsa ce. Koda ya shiga gidan bai nema kowa ba ya shige ɗakinsa. Sai da ya kammala komai na al'adar rayuwarsa sannan yay zaman cin indomie ɗin daya saya wajen Haladu mai shayi. Tare da shayinsa daya sabarma kansa sha yaci, dan ya samu an dafa masa sabo a flaks. Yasan aikin ƙannensa ne dan basa gajiya da hidimarsa. Hatta ɗakinsa ƙal yake da gyara, dan ko kayansa ƙananu basa ƙyashin zama su wanke masa fes su goge, manyan kayanne dai irinsu shadda sai dai ya kai wanki. Badan kuma bazasu iyaba yake kaiwar, sai dan rage musu aiki ne. Ya jima baiyi barcin ba yana ƙullawa da kwancewa akan al'amuran rayuwa da suka haye masa badan ya tsara su a cikin rayuwarsa ba. Tun yana yaro a kullum burinsa shine buga ƙwallon ƙafa da yin kasuwanci, sai gashi yau ya tsinta kansa a wani matsayin ɓoyayyen aiki da ya zame masa haye. Dan lamarin wannan ɗan taran da bai san miye manufarsa ba yana sake kutso rayuwarsa cikin rayuwar mutanen da har yanzu ya kasa samun amsa ko dalilin dangantakar da ALLAH ya ƙulla a tsakaninsa da su batare da su sun san ma'anar hakan ba suma na cimasa rai. Su dai kawai kallon driver a ƙarƙashinsu suke masa kamar yanda Uncle Yousuf ɗin ya ɗakkosa tun farko yi. Sai kusan ɗaya da wani abu ya samu barcin ya ɗauke sa mai cike da mafarkai marasa daɗi da suka shafi Jiƙamshi family, kodan ya kwanta da tunanunsu ne a rai oho. Ai ko sai gashi ya kusa makara da asuba. Da ƙyar ya iya tashi yay alwala ya wuce massalaci...
   Sashen Abba ya fara shiga kamar yanda ya saba a kowace safiya duk da sunga juna a massalaci. Gaishesa yayi cikin girmamawa da Æ™anÆ™an da kai tare da masa bayanin komawarsa aiki jiya. Karan farko Abba yay É—an murmushi irin na manya. Tare da faÉ—in, “Naji daÉ—in haka sosai, ina kuma maka addu'ar fatan alkairin ALLAH ya baka ikon jurewa. Aliy ba sonka bane banayi da kaga ina maka faÉ—a. Zaman nan naka ne bana so a hakan. Kai ba aiki ba, ba aure ba, ba wani sana'a Æ™waÆ™wÆ™wara ba. Ka duba Æ™annen bayanka kusan huÉ—u sunyi aure har ma ana batun yima wasu ukun. Ba maganar mata nake ba dan su dama dan hakan ta faru ba komai bane ba ai tunda mataneâ€.
   “Kayi haÆ™uri Abba in sha ALLAHU zaku cigaba da samuna a yanda kuke fata. Ku gafarceni da duk É“ata muku da nake yiâ€.
     “ALLAH ya yafe mana baki É—aya, amma ka dage dai ka nema matar aure zamanka ya isheni haka, kaima ina son ganin jininka kafin Æ™asa ta rufe idanunaâ€.
  Ɗan murmushi kawai yayi kansa a ƙasa. Yau ya ɗan jima a wajen Abban har wasu a cikin ƙanensa suka ɗan shigo gaida Abban. Bayan barinsa nan cikin gida ya shiga. Kowane ɗaki sai da ya leƙa suka gaisa, a ɗakin Ammah ya ɗan sha shayi a tsaitsaye yay mata sallama ya fito ganin yana neman makara. Wanka yayi a gurguje yay shirinsa cikin uniform ɗin aikinsa ya fice a gidan....
   ★ Yau ma dai gidan Uncle Yousuf ya nufa kai tsaye, saÉ“anin jiya ya sameshi a compound zaune tare da baÆ™o. Bai zauna wajen maigadi ba ya nufesu. Uncle Yousuf dake dubansa da murmushi ya ce, “Uncle Smart na yaraâ€. Murmushi yayi da É—an shafa kansa suka gaisa cikin girmamawa. BaÆ™on nasa ma suka gaisa. Yana Æ™oÆ™arin barin wajen Uncle Yousuf ya tsaida shi tare da nuna masa wajen zama. “Kaga zauna muyi magana shima É—an gida ne. Dama kuma akan abinda ya shafi aikinka muke maganar. Sunansa Tajuddeen, surukina ne kuma É—an uwana. Yaso Muwaddat da muka kai asibiti jiya kuma yana akan sonta dan har ranar aure an saka musu shekaru uku da suka gabata, sai dai taÆ™i yarda ai bikin. Abinda yasa nace maka zaman ya shafeka saboda taimakon da muke son kai mana ne tare da sake roÆ™onka kan ajiye aiki da kai niyyar yi. Aliyu a haÉ—uwarku É—aya da Muwaddat kawai na fahimci zaka iya bamu taimako akanta, dan kafin kai mun saka drivers da yawa tun dawowarta Æ™asar nan amma tsoronta sukeji saboda azababbiyar yarinya ce da kake ganinta, gashi bata shakkar kowa. Shiyyasa basa iya yin komai kan al'amarin ta. Akan Muwaddat kam nasan aikine mai wahalar gaske zamu baka amma dan ALLAH ka taimakemu kaine kawai hope É—inmu a yanzu game da yanayin da take ciki.â€
    Ganin yanda yakai Æ™arshen maganar kamar a yanayin son jin ta bakinsa ya sashi nisawa. Cikin dakewar nan tasa ya ce, “Alhaji zan iya taimaka muku, sai dai fa akwai matsala dan zamanmu inuwa É—aya da ita bazai yiyu ba. Kayi hakuri bazan iya É—aukar Æ™asÆ™anci ba, idan tace zata wulaÆ™antani bana zaton kallonta matsayin wadda nakema aiki zan É—auki mataki kanta ako ina ne kumaâ€.
    “Na baka wannan damar, dan hakan nafi buÆ™ata nimaâ€.
   “Shikenan, wane irin taimako kuke buÆ™ata da ga gareni?â€.
   “Sanya mana ido akan al'amuranta, ƙawayenta, abokan mu'amalarta, inda take zuwa bayan wajen aiki. Kai hatta waya da zatayi idan san samune musan dawa take yi. Bayan ka gama sanin waÉ—an nan sai muje mataki na gabaâ€.
      “Indai wannan ne babu damuwa in sha ALLAHUâ€.
   Godiya sukai masa, tare da tabbatar masa zai fara aiki da ita da zarar an sallamota asibiti. Sun kuma ninka masa albashinsa..........âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
____________________
https://youtu.be/y6YMU120RZI
Please subscribe to Rukayyat khalid YouTube channel fisabilillah. I only uploads videos na karatun Qur'an a tashar Please help me reach 1k subs soon insha Allah *RUKAYYAT KHALID*
*Assalamualaikum warahmatullah*
*Yar uwa shin mene amfanin wayar hannunki da bazaki koyi sana a da ita ba?*
*Kullum kina yawo a social media irin su Facebook, WhatsApp, tiktok,Instagram, twitter da ma sauransu.*
*Kina asarar data a banza kina zuba adashinda babu ranar dauka*
*bakya chas bakya as? Se chart kika iya 🤔*
*kin damu mijinki da BANI BANI?? Kizo nan ni* *~Graphics by Rukayyat~* *zan koya miki sanaar Graphics design wanda zaki samu abin dog dogaro da kai. Kina zaune daga gida kina sanaarki.*
*Ga mai bukata a masa design ko wani iri, munayi insha Allah*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.