Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 60 of 94
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 5ï¸âƒ£7ï¸âƒ£
........Wajen ƙarfe tara ALLAH ya kawo aunty Bilkisu ɗakin zata ɗauki kayan biki data ɓoye dan bama facalolinta da zasu wuce. Da sauri ta ƙarasa gaban gadon tana ambaton sunan ALLAH. Ta kai hannunta a goshin Lulu dake barci. Zafi zau har tana jin harbawar jijiyoyin kan nata. Bargo taja ta lulluɓa mata, sannan ta kwashi abinda tazo ɗaukar ta fice. Bata san yin kwakwazo hankalin mutane ya dawo nan, dan haka ta sallami facalolin nata sannan ta koma cikin raɗa ta sanarma Ammah da ke a cikin danginta da zasu kwana. Hankalin Ammah ma ya tashi, ta miƙe cikin hikima ta shiga bedroom ɗin, itama dai tattaɓa goshin nata tai, sai kuma ta juyo tana kallon Aunty Bilkisu.
   “Yanzu ya za'ayi kenan? Dan nima bana son kowa ya fahimta baki baka san yanda na wani yake baâ€.
   “Hakane Ammah, to kodai a kira Hydar, sai ya samo mata maganiâ€.
  Ɗan jimm Ammah tai na tunani, sai kuma ta É—an sauke ajiyar zuciya da faÉ—in, “Kirashi É—in to. Ki kuma turomin Auntynkuâ€.
     Da to Aunty Bilkisu ta Amsa tana fita, sai da ta fara zuwa tai kiran aunty Amarya da Ammah tace kafin ta wuce sashen samarin gidan. Duk suna waje wajen dj balle ga Æ´ammata dama cike da gida, dan kusan duk É—akunan ma a kulle suke, sai É—akin Smart ne da ya nuna haske ke tabbatar da mutum a ciki. Sallama tayi aka amsa mata sannan ta shiga. Shi da Ahmad ne kawai a É—akin, dan abokansu su kam yau duk kowa ya kama gabansa tunma da safe kasancewar gobe idan ALLAH ya kaimu Monday kowa zai koma kan aikinsa. Ahmad da ke zaune yana shan fura ya dubi aunty Bilkisu da murmushi yana faÉ—in, “Aunty Babba ke da kankiâ€. Murmushin ta mayar masa da faÉ—in, “To ya na iya Ahmad, amaryarku ce babu lafiyaâ€.
   “Ya Salam! Miya faru?â€.
 Ya faÉ—a da sauri. Dai-dai nan Smart ya fito da ga toilet da alama wanka yayi, sai dai sanye yake da jallabiya sai Æ™aramin towel yana goge sumar kansa. Su biyun duka ya kalla saboda jin abinda Ahmad ya faÉ—a, da son jin amsar da Aunty Bilkisu zata bada. Cikin damuwa ta ce, “ZazzaÉ“i ne da ciwon kai mai zafi. Gata can cikin bargo tanata rawar sanyi maâ€.
    Smart ya É—an lumshe ido ya buÉ—e, sai kuma ya É—auki turare ya É—an fesa da faÉ—in, “Inaga hayaniyar nan ce....â€
  “Hakama Ammah tace, shiyyasa ma tace a kirakaâ€. Aunty Bilkisu ta katsesa da sauri. ÆŠan Basket É—in da yake ajiye magunguna ya É—auka, sai kuma ya dubi Ahmad da faÉ—in, “Ina zuwaâ€. Kai ya jinjina masa da mata addu'ar samun lafiya. Su kuma suka fice. Cikin gidan da sauÆ™in mutane dan duk ana waje wajen dj, sai Æ´an tsofaffin ne da suka gaji sukai zamansu. Aunty Amarya ce ta taresu tun a farkon shigowa tace su biyota. Binta sukai sashenta, falon babu kowa sai yara da aka kwantar, kuma duk yaranta ne, dan ita danginta ma duk sun wace sai Æ™anwarta budurwa da zata kwana tana kuma tare da su Maryam. Kai tsaye bedroom É—in ta suka shiga, Lulu da aka maido nan tana kwance a gado cikin bargon da Aunty Amarya ta lulluÉ“a mata. Aunty Bilkisu tace “Yauwa nan aka maidota ashe?â€. Amsa Aunty Amarya ta bata da “Eh nan É—in yafi Æ™arancin hayaniyaneâ€. Sai kuma ta kalli Smart da ya zubama gadon idanu kawai batare daya Æ™arasa ba. Katseshi tai da faÉ—in, “Hydar Æ™araso, Bara a samo ruwa tasha magani, sai dai banajin ma tunda aka kawota gidan nan taci wani abu. Ko a É—an samo mata abinci? Ko tea haka koâ€.
   A hankali ya ce, “Ko tea É—in dai zaifiâ€.
   Babu jimawa Aunty Amarya ta dawo da tea da ruwa. Tana ajiyewa suka fice ita da aunty Bilkisu, sai lokacin ya Æ™arasa gaban gadon. Da ga tsaye ya kai hannu kan bargon ya É—an yaye kaÉ—an idanunsa suka sauka akan Æ™yaÆ™yÆ™yawar fuskarta. Kamar ko yaushe yau ma babu kwalliya, sai wani irin sirrintaccen Æ™yawu data Æ™ara fiye da yanda ya santa. A karo na biyu bayan ranar dinner daya riÆ™e mata hannu ya taÉ“a jikinta yanzu ma. Saukar hannunsa mai sanyin danshin ruwan wankan daya fito ya sata buÉ—e idanu kamar a É—an zabure. Cikin sa'a kuwa suka faÉ—a cikin nasa saboda shima kallonta yake. Sake waro idanun tai da Æ™yau, sai kuma ta kai hannu ta buge masa nasa hannun da har yanzu ke akan goshin nata tana hararar sa. Cikin Æ™arfin hali ta ce, “Kai kuma waya gayyatoka nan?â€. Yanda tai maganar da son yin masifa sai dai babu Æ™arfi yaso bashi dariya, amma sai ya danne abarsa baiyi ba, sai ma kaiwa zaune da yay a bakin gadon har jikinsu na gogar juna sai dai ita a bargo take, kanta ya É—an kifo yana raba hannayensa gefe-da-gefenta ta kasance a tsakkiya. Idanunta data sake rufewa ta buÉ—e da sauri jin saukar numfashinsa saman fuskarta duk da akwai Æ´ar tazara a tsakaninsu, ta sake watsa masa harara ta ce, “Kai kuma wai miye haka? Kake yiâ€.
    Karan farko cikin É—an lumshe idanunsa da buÉ—ewa a lokaci guda ya motsa lips É—insa dan shima dai ciwon kansan nan na tare da shi a yau ma yini guda. Dan ma yanata addu'a da shan addu'oi wajen Malam sannan Abba yay masa kamu É—azun da magrib shine ma ya É—an samu barci sai yanzu ya tashi yay É—an wanka zaiyi sallar isha'i da shafa'i da wutri aunty Bilkisu taje. “Zan dai yi Madam. Amma first ina son sanin mike damunki?â€. Yay maganar cikin tausasa harshe sosai.
   “Meya ruwanka malam nifa bana son shishshigi ka saniâ€. Itama ta faÉ—a cikin tsiwa da takurar yanayin kusancin nasu.
  “Inafa na sani, sai dai yanzu da kika faÉ—a zan kiyaye. Amma yanzu dai ni ba faÉ—a nazo muyi ba, tashi kici abinci kisha maganiâ€.
  “Nace maka ina buÆ™ata ne?â€.
 “Basai kina buÆ™ata ba aiâ€. Ya bata amsa yana É—aura hannunsa saman bargon zai yaye. Tattaro bargon tai ta da sauri ta tattaro cikin hannunta zata fisge daga nashi. Hakan yasa ya ja shima, itama ta ja, ya Æ™ara ja, itama ta fisga cikin sake fusata duk da bata da wani Æ™arfin kirki a jikinta. Ga bakin masifar sai motsi yake alamar magana take son yi amma bata fita. Da É—an Æ™arfi yaja kasancewar Æ™yaleta kawai yake dama, aiko ya É—age bargon. Gaba É—aya ta tattaro da hannunsa da bargon ta fisgo cikin takaici sai kawai ya biyo su shima ya faÉ—a mata a jiki fuskokinsu kan na juna kowa na shaÆ™ar numfashin É—an uwansa, lips É—insa a kan nata. Sosai zukatansu suka hau dokawa da sauri-sauri a tare, sai dai kowanne da dalilinsa. Lulu da wani shuÉ—aÉ—É—en al'amari mai matuÆ™ar zafafa zuciya da Æ™onata ya fara son hasko mata a memory tasa dukan sauran Æ™arfinta ta turesa jikinta na rawa. Hakan bai sakashi yin ko gezau ba, sai dai shima ya matsar da fuskarsa da ga kan nata, sai kuma ya É—agata jininsa na wani yamutsawa. Zaune ta tashi tana Æ™oÆ™arin sauka a gadon kamar wadda ke neman rasa nutsuwarta dan jikinta rawa yake, yay saurin dakatar da ita cikin sassarfar harshe shima. “Ina kuma zaki je?â€. Ganin tana cigaba da janye bargon zata saukan ya riÆ™ota da sauri. Harara ta watsa masa da idanunta da suka kaÉ—a sosai. Ga jikin nata rawa yake da gasken fa. Magana take son yi amma ta kasa, sai idanunta dake cikowa da Æ™walla. Mamaki sosai hakan ya bashi, amma sai ya sake yinÆ™urin riÆ™ota.
      Hannunta ta fisge, sai kuma ta dafe kanta wasu hawaye masu zafi na sake wanke mata fuska. Idanu ya zuba mata ganin yanda jikinta ke Æ™ara Æ™arfin rawa, hakan ya matuÆ™ar sake É—aure masa kai da zuciya, dan yanayine bawai mai nuna Æ™in da take masa ba matsayin wanda bata so ko tafi Æ™arfin aurensa, ba kuma kuya bace. Al'amarin nata kamar dai like wadda ta tuna wani mummunan al'amari mai firgitarwa da ciwo a zuciyarta da yay kamanceceniya da yanayin da suke ciki. Kanta ta sake girgizawa da sake yinÆ™urawa zata Æ™arasa sauka ya miÆ™e da sauri ya zagaya gabanta. Cikin nuna kulawa da son maidota a nutsuwarta ya ce, “Kinga Please relax, ko mima zuciyarki ke son ayyana miki ba haka bane ba, koma ki kwanta kinga baki da lafiyaâ€.
    “Idanunta da sukai masifar kaÉ—awa da ja ta É—ago ta zuba masa. Sai kuma taja da baya da ga kusa da shi har yanzu dai da alamar bata samu nutsuwar da yake buÆ™atar ba. Shima sai ya matsa É—in da kallon Æ™ofa ya kuma sake maido idanunsa kanta. “Kin gane bana son wani ya fahimci akwai wani abu a tsakaninmu saÉ“anin abinda suke kallo a bayyane. Ki daure zuciyarki na roÆ™eki koma mi kike tunani ki ajiyeshi gefeâ€.
    Yaraf ta koma saman gadon ta zauna, hannunta dafe da kanta muryarta na fita da rawa da É—an kaushi ta ce, “Ka kira min wata a cikinsu bazan iya zama da ga ni sai kai a É—akin nan ba in har dole sai jikinka ya taÉ“a nawaâ€.
   “Wancan ma mistake ne, bakuma za'a sake ba, Kinga ga tea kisha sai kisha maganin ki kwantaâ€.
   Tabbas yanda yake mata magana a nutse ya taimaka ma Æ™waÆ™walwarta wajen dawo da ita hayyacinta kan cewar bafa abinda ke mata kai-kawon bane ba. Sannan kuma tunda take da shi bai taÉ“a aikata mata makamancin hakan ba, lallai ta yarda mistake É—inne kamar yanda ya faÉ—a. Hakane, Æ™warai hakanne mistake ne. Zuciyata ta shiga sake tabbatar mata. Sai ta fara sauke numfashi a hankali a hankali jikinta na Æ™ara samun Æ´ar nutsuwa. Gadon ta koma ta zauna ta jingina da fuskar gadon bayan taja bargon ta rufa, sai ya koma shima ya zauna a baki-baki da Æ´ar tazara a tsakaninsu yana sauke Æ™aramar ajiyar zuciya ya miÆ™a mata kofin shayin da har ya É—an fara hucewa..........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.