Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 20 of 94
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 1ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
........Smart kam tuni ya shanye titin layin zuwa babban titi, da Æ™yar ya samu napep. Tafiyar da bata wuce mintuna talatin ba ta kawosa anguwarsu. Kasancewar da sauran hasken gari koda ya shiga sai ya É—an watsa ruwa tare da zuwa ya gaida Abba da su Ammah, sai dai ya iske Ammah ma ta fita ita da aunty Amarya Barkan Æ™anwar Aunty Amaryar da ta haihu a can Gadon Æ™aya tun la'asar, sai su Maryam kawai da suka dawo islamiyya. Dan haka bai zauna ba suna gama gaishesa ya fito ya koma É—akinsa. Ba wasu abokai ne da shi ba shi dama sai Ahmad kuma ba anguwar yake ba. Dan Mutum ne mai Æ™arancin kwaramniya. Idan kaga abokinsa da har zasu iya zaman doguwar hira to sai dai abokan karatunsa, amma na cikin anguwa sai gaisuwar mutunci kawai, duk da dai a da anyi abotar yarinta, sai dai kasancewar sa mara sakewa da mutane suke masa kallon mai girman kai duk suka janye jikinsu da shi, shi kuma bai nuna ya damu ba. Abokan karatun kuwa akan jima ma ba'a haÉ—u ba sai ta waya ko wani taro mai muhimmanci ya haÉ—a. Shiru ya kwanta kamar mai barci, da gani kasan duniyar tunani ya faÉ—a, dan babu abinda yake sai furzar da huci akai-akai da ga bakinsa, hakan kamar É—abi'a ce data zame masa jiki in dai yana cikin damuwa.. Abubuwa ne masu yawa ke ci masa rai, ciki harda batun bauÉ—aÉ—É—iyar yarinyar can, shi mutum ne da baya shiga sabgar da ba tashi ba koda kuwa a cikin gidansu ne sai idan yaso, amma sai yake ji zuciyarsa na ingizashi akan taimakon ubangidan nasa da yarinyar, badan komai ba sai dan Æ™annensa mata da bazai taÉ“a fatan su tsinta kansu a irin wannan rayuwar ba. Yasan idan har ya tsamota da ga wannan musifar yayi jihadi, sai dai bai san ta ina zai farama taro wannan al'amari nata ba. Karan farko yaja sirrin tsaki, sai kuma ya tashi zaune yana É—an furzar da huci tare da kai hannunsa saman goshinsa yana É—an murzawa. Ganin yaÆ™i samun nutsuwar hutawar da yake buÆ™ata ya sashi tashi ya fito a É—akin, nan Æ™ofar gidansu ya zauna yana É—an gaisawa da mutane masu wucewa har akai kiran sallar magrib. Bai fito da ga massalacin ba sai da akai isha'i, yana kwaÉ—ayin shiga gidan suyi hira da Ammah dan wannan É—an lokacin kawai yake da damar haka gareta, amma zuciyarsa nata masa tuni akan Lulu da abinda yaji suna magana ita da Æ™awarta zasuyi a daren na yau da sunan wai murnar samun lafiyarta. duk yanda yaso yaÆ™ar zuciyarsa abin ya gagara, saboda yana ji a ransa ba alkairi za'a shuka ba wajen, dan haka ya fito da ga layinsu ya samu Napep zuwa hotoro gra. bai damu da kuÉ—in da suka tsuga masa ba. ÆŠan nesa da gidan ya sauka, amma ya tsayar da mai napep É—in, ya samu jikin wata bishiyar dabino kusa da katangarsu ya tsaya, ya kai mintuna talatin da wani abu a wajen yaji motsin an buÉ—e gate É—in gidan, ido ya zuba na son ganin wanda zai fito. Ilai kuwa Lulu ce, dan a kanta idanunsa suka sauka saboda haske dake tako ina a street É—in, gashi ta sauke glass É—in motar sosai har kana iya hango kalar kayan da take sanye da su. Tayi Æ™yau matuÆ™a ga uban Æ™amshinta na isowa har inda yake tsaye saboda yanda ta gumbuÉ—ashi kamar ba mace ba. A É—an kasancewarsu na kwanaki ya fahimci sam bata tausayawa Æ™amshi, haka kawai sai yaji tanan É“angaren ta É—an samu sassauci a garesa, duk da tana saka nata Æ™amshi ne ba bisa Æ™a'idar da ya kamata ace mace ta saka ba. Da sauri ya Æ™arasa ga mai napep da ke zaman jiransa. “Kabi wannan motar Please, amma karka bari ta fahimci muna biye da itaâ€. Ya faÉ—a yana nuna ma mai napep É—in motar Lulu da ke tafiya a hankali kamar bata son tuÆ™in yau. Yanda take tafiyar ya bama mai napep É—in damar binta cikin hikima har zuwa wata sabuwar anguwa, dai-dai wani gida da alamu suka nuna shima ba'a daÉ—e da kammalashi ba ta tsaya, da ga inda suke yana hangen yanda ta kai waya a kunnenta alamar kira take ko an kirata, tana ajiye wayar ana buÉ—e gate É—in gidan. Da sauri ya fita tare da miÆ™ama mai napep kuÉ—i yana faÉ—in, “Abokina nagode koâ€. Bai jira amsarsa ba ya nufi gidan, kasancewar akwai Æ™arancin haske a anguwar dan kamar ma basu da wuta sai Æ™arar gen... ÆŠin gidan data shiga yake jiyowa ya samu damar bin motar tata ta gefe suka shiga tare batare da mai-gadin ya lura ba. Motoci ne kusan bakwai a gidan duk an parker a babban compound É—in kamar wasu masu biki, tun kafin ta fito a motar Æ™awayen nata suka baibayeta da ihun faÉ—in, “Sai Lu É—in mu!!!, sai Æ™amshin mu!!!â€.
     Fuskarta Æ™awace da wani shegen murmushi ta fito. Wani shegen gown ne a jikin nata ta lafe mata kamar babyn roba. Da sauri ya kauda idanunsa yana mai jan sirrin tsaki da taune lips É—insa da Æ™arfi. Bai sake kallon inda suke ba har suka shige Æ™ofar da yake Æ™yautata zaton ta cikin gidan ce. Huci mai zafin gaske ya furzar tare da gyara tsaiwarsa. A É“angaren su Lulu kam suna can cikin Æ™aton falon gidan da ya sha kayan alatu. Abinda zai baka mamaki bawai iyakar su kaÉ—ai bane Æ´ammatan ashe, akwai dattijan maza a shekaru bawai a cikar kamala ba har su huÉ—u, tun shigowar su Lulu kusan su duka suka zubo mata idanu fuska a washe, yayinda ita kuma nata murmushin ya É—auke ta wani yamutse fuska tana kallon Nadiya, sai kuma ta juya ta fito a fusace. Da sauri Nadiya tabi bayanta tana faÉ—in, “Please Lu ki saurare ni.â€
    “AnÆ™i a saurareki É—in, Nadiya kin san dai na tsani irin wannan ko...?â€
   “Na sani, amma bamu da wani zaÉ“i ne wlhy Lu.., dan ALLAH ki fahimce ni, kin san dai bazanyi abinda zai É“ata miki rai da gangan ba....â€
  “In ba kinyi da gangan É—in ba miya kawo waÉ—an nan tsoffin banzar nan? Ni ban hanaki huÉ—É—a da su ba, amma ki sani duk randa suka zubar da ke bayan gama lalata miki Æ™uruciya kiyi kukanki ke kaÉ—ai kar ki tunkareni. Amma ki daina sakamin su a sabgogin rayuwataâ€.
    Ɗan murmushi Nadiya tayi cikin rashin É—aukar zancen na Lulu da muhimmanci ta ce, “Naji, ni dai yanzu kiyi haÆ™uri mu koma ciki dan ALLAH. Dan wannan fa zaman naki ne, dan ke akayisa, mun riga mun gama tara mutane, su Shony fa tun daga ktn suka taho a yammacin nan domin wannan shagali kawai. Abinda yasa ki ka ga su Alh. Baita anan ma saboda su Shony ne, dan sun riga sun kirasu cewar zasu shigo Kano, amma wlhy badan ke bane baâ€.
   A hankali ta furzar da iska, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. “Shike nan amma ki kiyaye gaba, dan in har kika sake sakamin sabgar waÉ—an nan mutanen a tawa wlhy sai mun rabu. Suma su Shonyn idan suna buÆ™atar haÉ—uwa da su ne suje can su haÉ—u bai shafeni baâ€.
    “Naji na yarda baza'a sake ba. Suma kuma zan musu bayani yanda zasu gane Muje to dan ALLAH suna jiranmuâ€.
  “Bani details É—in mai kayan nan na tura masa kuÉ—insa karna shiga wata sabgar. Sannan wannan gidan na waye uwar kwashe-kwashe kika kawo mu kuma?â€.
    Gidan Nadiya ta kalla tana Æ´ar dariya tare da faÉ—in, “Gidan wanda ya sayar mana da kayan ne, wlhy Guy É—in akwai kirki gashi so handsome kuma, ya bamu shawara ne muzo nan musha shagalinmu dan zaifi mana sirri kasancewar kinga dare ne, ke kuma ba cika son shiga clubs na nan Kano kikai ba kin ce Æ´an hayaniya da Æ´an iska sun cika yawaâ€.
     Cikin rashin damuwa ta É—age kafaÉ—a kawai, batare da ta sake tofa komai ba ta bar wajen. Binta Nadiya tai suka shige tare.... Gaba É—aya zuciyar Smart ta sake jagulewa da takaici, dan duk abinda Lulu da Nadiya ke tattaunawa yana jinsu batare da su sun lura da shi ba. Shigarsu da kusan mintuna uku sautin kiÉ—a ya fara tashi kaÉ—an-kaÉ—an saboda rufe windows da sukai duk dan kar kiÉ—an ya fita wa mutanen anguwa. Kansa ya É—an dafe yana mai ambaton sunan ALLAH, gaba É—aya ma ya rasa miya kamata yayi, duk da yazo nan É—inne da burin ganin abokan sheÉ—anar tata da kuma hanata shan komai. To amma ta ina zai fara ma?. Ya kwashe kusan mintuna ashirin yana Æ™ullawa da kwance ta yanda zai shiga wajen.... Ƙarar hayaniya da ta fara tasowa kaÉ—an-kaÉ—an da ga cikin falon ta maidosa da ga dogon tunanin mafita da ya tafi, ajiyar zuciya yaja kamar wanda aka farkar da ga barci tare da tsurawa Æ™ofar idanu. Wasa-wasa hayaniyar ta daÉ—a karfi har yana iya shaida muryar Lulu saboda tsayawar Æ™arar sautin kiÉ—an da ke tashi, da alama sun kashe ne ko wata matsala ta faru. Falon ya nufa da sauri batare da tunanin komai ba ko neman izinin ya tura Æ™ofar ya shige, yanda ya gansu a yamutse ga Lulu na É—urama wani hamshaÆ™in Alhaji zagi har tanayi kamar zata tsole masa ido da É—an yatsa ya sashi yin turus, mamaki ne ko takaici oho baima sani ba, kayan shaye-shayene da na ciye-ciye ko'ina a barbaje, yayinda alhazan nan guda huÉ—u da ya shaida fuskar biyu a cikinsu kasancewarsu wasu manyan Æ™usoshin attajirai kuma Æ´an siyasa masu faÉ—a aji a garin na kano É—aya ke tsaye cikin fusata kamar zai daki Lulu, sauran ukun na zaune sun zuba mata ido harda wanda take zagin da shi fuskarsa ma Æ™awace take da murmushi kamar bashi akema tujarar ba. Kalaman Lulu ne na Æ™arshe-Æ™arshe da kukan da ta fashe da shi ya dawo da shi hayyacinsa.........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.