Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 87 of 94
   Da sauri yabar jikin ƙofar ya shige bedroom ɗinsa. Wani irin harbawa zuciyarsa keyi da sauri-sauri. Dan shigarsu ɗakin babu jimawa ya shigo gidan. Duk da yay mamakin ganin mota baƙuwa a waje yay zaton kota Lulu ce aka kawo saboda bai ga driver ba, ashe ya ɗan fita miƙe ƙafa. Ya shigo gidan yaji shiru, ya wuce ɗakinsa kai tsaye ya ajiye kayan hannunsa shine ya nufo ɗakin Lulu da tunanin ko barci take. Kawai yaji Dada na magana a hanakali cikin salon makirci na tsoffin mata tana bugar cikin Lulu, shine fa ya nutsu. Jin komai ya sake tada masa da hankali, dan yanzu ne ya fahimci ainahin abinda take nufi da wata ɗaya wata ɗaya da take ta ambata masa zata koma free. Zuciyarsa ta sosu da tunanin shima Uncle Yousuf yaudararsa yake kenan? Sai kuma wata ke kwaɓarsa akan kada yay zargi cikin fushi, ya bincika dai sannan. Sunayen ALLAH ya shiga ambata har ya samu nutsuwar ajiye tunanin a ransa gefe, sai kawai ya faɗa wanka. Lokacin da yake fitowa yaji fitar motar data kawo Dada, sai kawai ya ƙarasa kimtsawa da yin shirin fita sallar magrib ya fito.
     Lulu da ke kwance a falo ta wani É—an zabura alamar tsorata da ganinsa. Murmushi ya sakar mata da lumshe idanu yana kaiwa zaune kusa da Æ™afafunta. “Matsoraciya relax ba aljani bane ni ne?â€.
   “Taya zan yarda da haka bayan kace sai gobe ne zaka dawo, kuma ina wajen banga sanda ka shigo baâ€.
  Murmushin ya sake sakar mata, a nutsensa da deep voice É—in nan tasa dake fita da sanyin damuwar abinda yaji na tattaunawar ta da Dada duk da yana Æ™oÆ™arin dannewa ya ce, “Mun gama abinda ya kaimu ne shine kawai muka yanke dawowa gida. Sanda na shigo kuma kina É—aki ne da baÆ™uwa. Namayi zaton har zan kammala wanka nazo mu gaisa duk da bansan wacece baâ€.
     KaÉ—an ta sauke numfashi da É—age kafaÉ—unta. “Dada ce kuma ta wuce. Tazo ne akan maganar zuwa duba Grandpa da aka wuce da shi London jiyaâ€.
   “Ya salam jikin nasa ne dai?â€.
  “Wlhy kuwa, fiye ma da yanda ake tsammani, dan a shekaran jiya doctors suka gano wai anyi poising É—insa ne da gubar da bata baiyana kanta sai tai kwanaki a jikin mutumâ€.
        “What! Sai kace wani a film?â€.
    Lulu ta ce, “Hummm a tunaninka a Film kawai ake waÉ—an nan abubuwan? To a Nigeria ma a zahiri anayin fiye da haka. Kasan Grandpa ya Bama siyasar nan amanna matuÆ™a, shiyyasa muke tunanin ko'a cikinsu ne musamman daya kasance a hasashenmu a zuwa Legos É—in nan da yay abun ya faru. Yanzu dai haka jami'an tsaro sun duÆ™ufa bincike kan al'amarin maâ€.
   MatuÆ™a Smart ya girgiza. Dan baiyi zato ko tsammanin wai da gaske irin wannan abubuwan da ake gani a Film na faruwa a zahirin rayuwar mutanen Æ™asarsa ba. Kiran salla ta sashi miÆ™ewa yana faÉ—in, “Ina Æ´an hutun naki? Naji gidan shiruâ€. Bedroom É—in da suke ta nuna masa. “Suna ciki fa, tunda muka dawo saloon suka kwanta wai sun gajiâ€. Kallonta ya tsayayi kamar zai yi magana sai kuma yay shiru dan shi dai bai san da wani fitarsu saloon ba. Zuciyarsa ta lallashesa akan a tari gaba. Yanzu zantukan ta da Dada ya kamata ya maidama hankali. KafaÉ—a ya É—an É—age hannayensa duka a aljihu, ya ce, “Okay bari naje salla na dawo. A É—an samamin wani abu mai ruwa-ruwa haka yunwa nake jiâ€.
   Harararsa tai da faÉ—in, “Kafa dawo zaka fara takurama mutane da mulkinka koâ€.
   “Ni na isa. Karki damu cikin su Maryam wani yayi ki huta abinki. Ki dai tashi kiyi salla. Bara naje sai na dawoâ€. Daga haka ya fice kafin ma tace wani abu..........âœï¸
    Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 8ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
........Bayan an idar da salla har ya nufo hanyar gidan sai kuma ya dakata. Napep ya tare ya shiga tare da gaya masa inda zai kaisa. Cikin ka Æ™anÆ™anin lokaci suka iso. Ya biya sa kudinsa sannan ya shiga gidan bayan sun gaisa da maigadi. Ahmad na zaune a falonsa ya barbaza takardu ga laptop a gabansa Smart ya shigo. ÆŠagowa yay yana kallonsa cikin nuna mamaki. Smart ya watsa masa harara da faÉ—in, “Lafiya kake kallona?â€.
   “Inafa lafiya, kai da nake tunanin kana can kana aikin ALLAH yanzu kodan kewar juna da akai amma sai na ganka ananâ€.
      Ƙaramin tsaki Smart yay yana kaiwa zaune da faÉ—in, “Banza É—an iska kaifa baka tauna magana kafin ta fito maka a bakiâ€.
   Dariya Ahmad yayi da cewa, “Gara na dinga muku É“aro-É“aro kuyi ku aurar dani kuma ku huta. Amma fa sai naga kamar kana cikin damuwa. ALLAH dai yasa ba wani abu ka tarar a gidan ba?â€.
     Smart baida yawan magana. Sannan akwai zurfin ciki. Duk abinda kaga ya bayyana shi ga waninsa to lallai ya matuÆ™ar girgiza shi ne. Sosai ya nisa da furzar da iska mai zafi. “Ahmad akwai matsala neâ€.
    “Ya salam matsala kuma Mawashin. To tami? Akan kuma mi?â€.
  Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya É—ago yana kallon Ahamd É—in da shima ya zuba masa idanu. “Badan ina son fara tona sirrin gidana bane, al'amarin ya girgiza nine ina buÆ™atar shawara dan kar na aikata abinda ba haka yake ba. Bayan kun saukeni na shiga gida sai na samu.......â€
    Tsaf ya zayyane masa abinda yaji tsakanin Lulu da Dada na tattaunawa. Shima kansa Ahmad yasha mamaki. Amma sai ya dafa Smart yana jinjina kansa. “Niko kaga ko bana jin shi Yaya Yousuf da wata manufa yay hakan. Domin idan ka auna zancen tsohuwar zaginsa take akai-kaice shima. Sai naga yayine domin ma Mawaddat wayo kawaiâ€.
      “To miye na wayon anan Ahmad, aure ne fa kuma ta isa aure tunda ba gunkinta zasuyi su kafe a gidan ba. Kawai dai akwai abinda suke shiryawa a kaina na yaudaraâ€.
   “No no relax kar kabari ka yarda da hakan. Sam sam bazaiyi hakan ba. Amma ina zuwa daiâ€. Waya Ahmad ya É—akko yay kiran Uncle Yousuf. Da Æ™yar ya samu ya shiga kasancewar har yanzu bai dawo Æ™asar ba. Sun gaisa cikin mutunta juna batare daya nuna yana tare da Smart ba. Uncle Yousuf daga can cikin tsokana yace, “Yaya dai Auta ko batun auren ne ya tashi akeso na fara haÉ—o lefe?â€.
       Dariya Ahmad yayi da faÉ—in, “Kai haba Yaya a'a. Wannan ai sai kun yarda da zaÉ“ina sannan zamuje wannan matakin. Duk da nasan ma kunaji da gudu zaku amince. Wani abu ne fa da na jiyo ya girgizani. Sai nace bari dai na kiraka ko kasan da zancenâ€.
    “Oh to Masha ALLAH, ALLAH ya tabbatar da khairan sa. Minene kake son ji haka?â€.
   “Uhm wlhy Yaya nafaje gidan Smart ne É—azun sai na samu Mawaddat na waya cewar ai ta kusa komawa free nan da 4days aurenta zai Æ™are da Aliyu. Abin ya girgizani matuÆ™aâ€.
     “Ya Arrahamanâ€. Uncle Yousuf ya faÉ—a daga can cikin dafe kai. “Yaya kama sani kenan?â€. Numfashi Uncle Yousuf yaja da saukewa. Sannan cikin nutsuwa ya sanarma Ahmad yanda akai zancen ya fito, ya É—ora da faÉ—in, “Ni ko ma Aliyun bamma maganar ba dan ba haka bane a raina. Wannan auren ina fatan sai mutuwa ce zata rabashi. Na saki jiki ne da tunanin tana zuwa gidansa zaibi duk hanyar daya dace wajen mantar da ita wannan shirmen. To ashe wata sabuwa ita hakan na ranta. Dole ne na kira Aliyu na sanar masa komai sannan kuma ya É—auki duk ma matakin daya dace akan hakan. Amma zanyi Æ™oÆ™arin dawowa nima duk da ban gama abinda nake ba. Dan ALLAH kaima ina son ka zaunar da Aliyu ka nuna masa abinda ya dace akan wannan batun. Idan ma yana ma Mawaddat saku-saku ne ya ajiye gefe ya koma wuta-wuta tasan shi bamu bane ba. Idan komai ya daidaita ya mata sauÆ™inâ€.
   “Shike nan Yaya insha ALLAHU yanda mukai da shi zakajiâ€. Daga haka ya yanke kiran. Smart yaji komai dan a hansfree yasa baya buÆ™atar Æ™arin bayani, sai ma ajiyar zuciya da ya sauke dan ya fahimci Uncle Yousuf É—in da manufarsa akan hakan. Ya kuma daina ganin laifinsa dan ko shine abinda zai yi kenan domin toshe kowace matsala da zata iya ta taso a lokacin.... Ahmad ne ya katse masa tunani da faÉ—in, “Mawashi a yanzu fa wannan yaÆ™in naka ne bana wani ba. Kai ya kamata ka nuna mazantaka komai ma za'ayi ayi karka biye mata. Sannan na fahimci kamar ido ka kawo ka zubamata shiyyasa ma take ganin komai normal ne. Dole fa kai Æ™oÆ™arin dashen shukarka dan hana kowace irin barazana tasiri. Dan hatta da ita kanta hakan da zakai zai karya lagonta dan bazata taÉ“a yarda a tunÉ“uke wannan shukarbaâ€.
   Tsaf Smart ya fahimcesa dan haka yay É—an gajeren murmushi yana girgiza kai. “Ahmad bazaka fahimta ba. Mawaddat fa ta wuce duk yanda kake tunani. Sannan ni harga ALLAH bana son zuwa gareta batare da amincewarta ba. Shiyyasa na sake mata tare da nuna mata har yanzun a Æ™asan nata nake dan hakan ne kawai zai iya karya lagonta harta saki jiki dani. Kuma Alhmdllh naga hakan yana tasiri sosai akanta . Taya kake tunanin yanzu na tunkareta da wannan sigar ai babu zaman lafiyaâ€.
“Humm kaifa na manta ashe sunanka namiji É—aya tilo a tsakkiyar Æ´aÆ´a mata shiyyasa. Mawashi na yarda da yanda ka tsara É—in kuma hakan ma hanyar maslaha ce mai Æ™yau da anan gaba ita kanta sai tayi alfahari da kai. Amma kai ya kamata ka memo hanyar da zakabi ta amince maka da kan nata ku zama É—ayan. Mudai fatan mu ai ayi shukar dan shi kaÉ—aine nake ganin zai hanata kowane irin motsi musamman daya kasance a yanzu tanada defenders a gefe kuma masu Æ™arfi.â€
    “Na yarda da kai, amma kuma tayaya zanyi hakan batare dana É“ata abinda na fara ginawa a zamanmu ba?â€.
   Dariya sosai Ahmad ya shigayi har sai da Smart ya fara Æ™uluwa sannan ya sassauta. Ya ce, “Shiyyasa nace kaifa gata yay maka yawa na kasancewarka É—a namiji É—aya tilo a tsakkiyar mata shiyyasa abubuwa da yawa kai hoto ne. Karka damu wannan aikina ne. Kai dai yanzu tashi ka koma gida ka maida komai ba komai ba. Amma yaran nan data cika gida da su ka tattarasu gobe su koma gidaâ€.
      Cikin É—an taÉ“e baki Smart yace, “Dama zasu koma goben ne ai saboda school. Amma ka faÉ—amin mi zakayi?â€
   “Babu ruwanka da abinda zanyi, ai kasan dai bazan cutar da kai ba.â€
“Na sani, amma dai ya kamata ace na sani koâ€.
“Karka damu zaka sani, nima sai nayi mazariâ€
  Daga haka suka fito anan massalacin Æ™ofar gidan su Ahamd sukai salla. Ya amshi key É—in motar Ahmad ya wuce gida. Yanzu kam ya samesu su duka a falo suna kallo. Sannu da zuwa suka shiga masa a zatonsu isowar kenan. Ya zauna yana amsa musu da tambayar lafiyarsu. Lulu na zaune a Æ™asa tana shan fruits da aka yayyanka a bowl. Ta sauya kaya alamar wanka tayi, dan wando ne da riga marasa nauyi a jikinta. Kan babu É—an kwali ya dai sha gyaran da sukayo yau sai Æ™yalli yake yi. Idanunsa ya É—an lumshe da sake lafewa cikin kujerar zantukan Ahmad na dawo masa a rai dalla-dalla. Shi yasan akwai Æ™ura, dan ko za'a kaisa jail sakinta bazai taÉ“ayi ba koda a mafarki ne. Maryam ce data kawo masa abinda yace a masa cikin hikima ta janye su Amrah suka koma É—aki tunda acan ma akwai tv. Lulu ta bisu da kallo tana faÉ—in, “Ku kuma ina zaku muna hira?â€. Da dariya Maryam tace, “Aunty muna zuwa sirri zamuyi mu dawo yanzunâ€.
    “To ALLAH dai yasa bani za'a Æ™ullawa baâ€.
  Dariya suka shige sunayi, yayinda Smart ya sakko ya zauna a Æ™asan kusa da ita. Hannunta ya riÆ™o ya kai apple É—in data ciro jikin cokalin bakinsa. Juyowa tai ta hararesa. Yay murmushi da É—an kashe mata ido É—aya. “Idan ma ke zasu Æ™ullawa ba gani a kusa da ke ba sai na kunceki tsaf na maida igiyar kansu Madamâ€.
    “A'a Granny Æ™arewar Madamâ€. Ta faÉ—a tana sake balla masa harara. Dariya yayi yanzu kam fararen haÆ™oransa na bayyana da Æ™yau. Sai da taji wani zuuu cikin kanta amma tai azamar É—auke idanun cikin basarwa. Shiko ya cigaba da faÉ—in, “Ai ki godema ALLAH da baki zo a kakar tawa ba. Gaskiya da Kinga takanki dan sai na addabekiâ€.
    “Sai dai ko mu addabi juna. Dan kaima kasan Lulu Æ™amshi ba kanwar lasa bace.â€
   “Niko nasan hakaâ€.
 Ya faÉ—a cikin É—age gira. Kankanar data tsiro ta tura masa a baki tana harararsa. Ya shiga shan abarsa yana murmushi. Itako ta maida hankalinta a kallon da sukeyi dan tana matuÆ™ar son film É—in duk da horro ne. Shima gyara zamansa yayi ya matsa jikinta sosai ya jingina bayansa da kujera kamar yanda tayi. “Wai sai sha kike baÆ™ya bani ALLAH sarki autan Ammah akwai haÆ™uriâ€. Ya faÉ—a a mararairaice. Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta kalla fruits É—in. “Oh kace kwaÉ—ayi ya zaunar dakai nan É—in ba kallo ba ashe?â€.
    “To kusan hakaâ€.
  Ya bata amsa yana shafar sumar kansa da bata da yawa can sosai, sannan tafi saisaye kuma. “Kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne†ta faɗa tana tsiro abarba ta miƙa masa. Maimakon ya amsa cokalin sai ya riƙe hanunta ya kai abarbar bakinsa a haka da nata hannun. Batace komai ba ta janye hanunta daga nasan. Sai ta koma idan ta sha saita tsira ta miƙa masan, shi kuma ya riƙe hannun nata ya kai bakinsa. Harda ɗan kwanto kansa a kafaɗarta kaɗan. Shagala datai a kallon yasa bata maida hankali ba duk da tabbas tana jin kan nasa a kafaɗarta sai dai ba sakar mata nauyi yay ba sosai.
     “Wai ko ki tambaya inda naje, da zan tafi baki tambaya ba. Ina can munyi waya baki tambaya ba. Na dawo ma haka. Anya zaman tare yace haka Mawaddatan'warahmahâ€.
   Yanda ya kirayi sunan nata sai da taji zuciyarta ta motsa. Duk da kuwa Uncle Yousuf kan kirata da sunan lokaci zuwa lokaci. Kansa da ke a kafaÉ—arta ta ture da faÉ—in, “Mi haÉ—ina da tafiyarka da dole zan dage sai naji. Ko salan a kirani mai gulma kumaâ€.
      “Haka ne kuma faâ€.
   Ya bata amsa cikin rashin damuwa. Sai kuma ya jawo tray ɗin da Maryam ta ajiye ya buɗe ƙaramin flaks da ta saka kunun madara a ciki ya zuba a cup, kaɗan yasa suga. Ya fara sha ya lura tana kallonsa. Kofin ya miƙa mata batare da yayi magana ba. Sai ta ɗan yamutsa fuska tana girgiza kanta.
      “Da akwai daÉ—i fa, É—an-É—ana kaÉ—an kijiâ€.
   Kamar bazata amsa ba sai kuma dai ta amsa É—in, kaÉ—an ta É—ibo a spoon É—in takai baki. Sai ta Æ™ara É—ibowa tana kallonsa. “Akwai fa daÉ—i, ni dana ga tanata haÉ—a-haÉ—a sai na É—auka jagwalgwali ne kawaiâ€.
    Murmushi yay mata da amshe spoon É—in yana faÉ—in, “Karkuma ki shanye min to daga tayiâ€.
   “Oh ashe ba daÉ—i ni ka shanye mun fruits É—ina.â€
       “Tofa gori ne abun? To shikenan mushaâ€. Ya faÉ—a yana miÆ™a mata. Amsa tai ta sha ta miÆ™a masa itama, haka suka dingayi yanzun ma dai da spoon É—aya suna kallo. Ya Æ™are ya sake Æ™ara musu wani. Sai gashi sun shanye kunun flaks É—in duka. Farfesun dake cikin kwanon kuma bai ciyu ba. Suna a falon har sai da Film É—in ya Æ™are. Shi ya kwashe kayan ya kai kitchen tare da kashe komai ya rufe Æ™ofar. Ita kuma ta tattara kayanta ta wuce É—akinta ko sai da safe babu. Da kallo kawai ya bita yana girgiza kai, shima sai ya nufi nasa É—akin. Sai da ya kammala komai na al'adarsa kafin kwanciya sannan ya canja kayansa zuwa na barci yasa turare yay brush ya fice. Lulu na zaune a tsakkiyar gadonta tana aiki a system ya shigo. Kallonsa take da mamaki daga sama har Æ™asa. Kafin cikin Æ™arfin hali ta ce, “Lafiya kuwa?â€.
     “Ƙalauâ€.
   Ya faÉ—a a taÆ™aice yana hayewa gadon.......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.