Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 8 of 94
   Har mota ya musu rakiya. Bayan wucewarsu sai yaji ya kasa komawa cikin gidansu dan baisan da wane irin harshe zaima Ammah bayani akan sake rasa wannan aikin ba shima, duk da dai jikinsa yay É—an sanyi da kalaman Ahmad na Æ™arshe, amma dai bai yanke hukunci ba na sake amsar aikin har yanzu. Sai dai in ya tuno bayanin Abba ya kanji faÉ—uwar gaba. Tabbas yasan wanene Abbansu, sam baya magana biyu. Mutum ne tsayayye da idan yace e to e É—inne da har ransa. Idan kuma yace a'a to a'a É—in ce fa. Da Æ™afa yabar cikin anguwar tasu, rashin abunyi da sanin ina zai dosa ya sashi miÆ™ewa a titi yay ta tafiyarsa kawai. Yayi tafiya mai nisa da bai san ina yake jefa Æ™afa da É—aukewa ba ya fahimci kamar binsa akeyi a baya. Tsamm yayi na tsarguwa tare da tsayawa, sai dai abin mamaki babu alamar wani tare da shi a Æ™afa, wanda ke a kan mashina ma da napep babu alama, hakama na mota. Dakewa yay ya cigaba da tafiyar, still dai ya sake jin tabbas akwai mai binsan. Yanzu kam bai juyo ba sai ya yanke titin ya shiga cikin wani layi, ya É—an yi nisa da layin sosai ya samu rumfar wasu masu kayan kafinta ya É—an dakata cikin dabara kamar mai gyara igiyar takalmi. Ta cikin mirror da aka jingine ya hango wasu samari biyu, sai dai suna É—an waskewa cikin É“adda kama. Hakan ya É—an bashi mamaki, dan shi dai a rayuwa duk da yana da tsatstsauran ra'ayi bashi da abokin faÉ—a. Cigaba yay da tafiyar dan son gane iya gudun ruwansu badan yasan sirrikan layukan inda yake ba. Sai da sukaje Æ™arshen layin sosai ya fahimci akwai matsala, ya É—an ji wani abu a ransa amma sai ya dake, wata hanyar da yake Æ™yautata zaton zata É“illesa da titi ya bi, sai dai yana shan kwanar tsukin wajen suka sami nasarar rufesa ruf ata gaba da bayansa. ÆŠaya bayan É—aya ya bisu da kallo har ya sauke akan napep É—in da aka faka a gabansa. Cikin dakewa da ambaton sunan ALLAH ya ce, “Ku kuma fa?â€.
   “Zaka sani amma ba'a nan baâ€.
Ɗaya ya bashi amsa cikin gatse da nuna masa bindiga dake soke a ƙugunsa. Bindiga bata kasance abar wasa ga kowa ba. Duk ƙarfinka da taurin kai a duk inda mai ita ya kasance shike zama a saman ƙarfin ikon ka. Dan haka ya shiga napep ɗin zuciyarsa na saƙa masa abubuwa masu yawa game da mutanen. Biyun da suka dinga binsa ne kawai suka shiga gefe-da-gefensa, mai napep yaja suka fice daga layin, sai da suka fita gaba ɗaya wanda ke gefen haggunsa ya jefa masa wani ƙyalle a fuska, da sauri na kusa da shi ya kama ya ɗaure masa idanu yayinda wanda ya fara jefa ƙyallen ya ɗora masa bindiga a gefen ciki ta yanda bai isa musawa ba. Duk da ya sake firgita haka ya dake a zahirance, a baɗini kuwa yana mai ambaton sunan ALLAH......
  Tofa, su kuma waɗan nan daga ina?. Wayyo Uncle Smart ɗinmu😫😢
     ∆••••∆ ★ ∆••••∆
  Tun daga main falour na gidan kana iya jiyo tashin sautin kiɗan dake fitowa da ga ɗakinta, duk da kiɗane mai taushi na mawaƙiya Shakira yanda ta ƙure voluen yasa ake iya jiyowa. Tun safe babu wanda zai ce ya ganta yau a gidan har zuwa yanzu da agogo ke nuna ƙarfe takwas da wasu mintuna. Mafi yawan yaran rai a ɓace suke fitowa daga ɗakunan su dan sautin kiɗan data saka ya takurasu da hanasu barcin safen. Hatta da ƙananun Suhaib da Imran da fita makaranta kan hakanasu barcin safen ji suke ta takura musu, musamman Imran dake son ƙarasa Assagment ɗinsa amma ya gagara fahimtar komai. Kaf ɗinsu sun gama hallara a dining, sai dai fuskar kowanne a turɓune da takaici. A haka Daddy da Mommy suka fito suka samesu, a kallo ɗaya zaka fahimci itama Momy ranta a ɓace yake, sai dai shi Daddy kam ko'a jikinsa. Yaran ma na gaidashi bai wani saurarensu ba hankalinsa nakan kiran Tabawa mai aiki. Da ɗan gudu-gudu ta fito a kitchen hannunta riƙe da ƙaramin ludayi da alama girki takeyi.
    “Babyna fa?â€.
Ya faÉ—a kai tsaye yana nuna upstairs. Itama upstairs É—in ta kalla, cikin sake rissinawa tace, “Barci takeyi Alhaji, tace zuwa Æ™arfe tara da rabi na tadataâ€.
   “Shi kuma wancan kiÉ—an da ga ina?â€.
“Itace ta kunnaâ€.
Nunin ta tafi kawai ya mata batare da ya sake cewa komai ba. Mommy da tai kicin-kicin da fuska ya kalla, sai kuma yabi sauran yaran nasa da kallo. Hafiz dake Æ™oÆ™arin kai shayi bakinsa wanda a haihuwa shike bima Lulu ne ya ce, “Humm Daddy yanzu bazakace komai ba kenan?â€.
  “Akan me?â€.
“Aunty Lu. Ai ko kafiri ba kowa ke iya saka kiÉ—a ya kwanta da shi ba. Kuma ina da tabbacin ko sallar asuba batayi b.....â€
   “Kai ban san shashanci da Æ™azafin banza, wai Hafiz ita É—in sa'arka ce? Kuma kai ubanwa yace maka batai sallar baâ€.Â
  “Ai ba sai wani ya faÉ—a masa ba abinda kowa ya sani ne. Ni ban san wane irin makahon so kakema Mawaddat ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kakeyi matsayinta na mace. Da haka kowace yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka ka aura ba matsayin iyayensu Alhaji. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan Mawaddat ne?â€.
Wani banzan kallo ya galla mata ita da yaran baki É—aya yana cika da batsewa, sanin yanzu zasuyi sama ya sata miÆ™ewa tabar dining area É—in zuciyarta na Æ™una da raÉ—aÉ—i. Ta rasa mike damun mijin nata akan babbar Æ´arsu mace, yana nuna mata Æ™azamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin Æ™oÆ™arinta tana yi akan Mawaddat amma abubuwa sake taÉ“arÉ“arewa sukeyi. A hankali hawaye masu raÉ—aÉ—i suka silalo mata saman kumatu.........âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 8ï¸âƒ£
........A can falo kam tashin Mommy dai-dai da shigowar Uncle Yousuf, da murna yaran suka tarbesa. Sai dai ganinsa kamar rai ɓace yasa jikinsu sanyi. Abba da shima idonsa ke kansa ya baro dining ɗin ya nufosa. Kusa da shi ya zauna idanunsa a kansa ɗan uwansa, yana son ɗan ƙanin nasa namiji ɗaya tilo da ya rage masa a duniya.
  “Anya lafiya kake cika kana batsewa haka?â€. Ya faÉ—a cikin kulawa da dafa kafaÉ—arsa. A hankali yace, “Ba komai. Sai kuma ya kai dubansa ga sashen Lulu. “Wannan kiÉ—an fa?â€. Shima Daddyn kallon saman yayi, sai kuma yay É—an murmushi da faÉ—in “Kaima ka sani sai dai Æ´ar gidanka aiâ€.
    Komai Uncle Yousuf bai sake cewa ba, sai rumtse idanu da yay cikin takaicin yayan nasa. Kusan mintuna biyu kafin ya buÉ—e, “Yaya mika yanke akan yaron dana kawo?â€.
   Murmushi Daddy yay mai bayyana haÆ™wara. Ya É—an bigi kafaÉ—arsa cikin sigar zolaya ya ce, “C-mon magajin baba saki fuskar mana, ni idan kana wannan cikar sai naga kamar baba ne ya dawo faâ€.
    Baki Uncle Yousuf ya tura masa kamar mai shirin yin shagwaÉ“e fuska. Sai kuma ya kauda kansa saboda murmushin da ke son kufce masa. Sam baya iya dogon fushi da É—an uwan nasa. Shima Daddyn murmushi ya sake saki da faÉ—in, “Yauwa ko kai fa. Yanzu kamun bayani yanda zan gane. Wane yaro kake magana a kai?â€.
   A taÆ™aice ya ce, “Driverâ€.
 “Okay ni babu abinda na yanke. Dan Babyn ka har yanzu tace tana buÆ™atarsa aiâ€.
  “Shi kuma baya buÆ™atarmu dan ya ajiye aikiâ€.
     “Wannan ra'ayinsa ne ai. Idan itama ta haÆ™ura sai a nema mata wani ba damuwa baneâ€.
  Wani shegen takaici ne ya sake kume Uncle Yousuf. Shi bai san wane irin mutum bane yayansa. Sam bai damu da damuwar kowa ba sai kansa da su ahalinsa. Kai kawai ya jinjina yana miÆ™ewa. Daddy dake binsa da kallo ya ce, “Badai wucewa ba?â€.
  “Yaya to mizan zauna nayi kuma. Ina son dai ka sake tunani a wannan gaÉ“ar. Domin duk a yanda muke kallon rayuwa da É—aukarta yaya watarana sai ta tsere mana ta É—akko wasunmu a madadinmu. Zata iya yuwuwa kuma ta É—akko waÉ—anda muke kallo ba kowa ba su kasance a saman tamu damarâ€.
     “Hakane Auta, sai dai ban san dalilin wannan gugar zanar baâ€.
  Murmushi Uncle Yousuf yay mai ciwo. “Nasan ka sani Yaya, duk da ni ba gugar zana nake maka ba. Sai dai akan Mawaddat kana rumtse idanunka da kunnuwanka domin Æ™in amsar gaskiyaâ€. Daga haka ya nufi part É—in nata. Yanda yake haÉ—a É—an steps É—in shiga sashen da bibbiyu zai baka tabbacin ransa a É“ace yake. Sai da ya rumtse ido lokacin daya É—aura hannunsa kan handle É—in Æ™ofar É—akin nata. Batare da ya yarda ya kalla É“angaren da gadonta yake ba ya nufi kayan kiÉ—an ya kashe. Kafin cikin daka tsawa ya ambaci sunanta. A firgice ta tashi tana mai yaye Æ™aton lallausan bargon data jibgama kanta. Gaba É—aya gashin kanta madaidaici a tsaho ya wani hargitse, sanye take da wando da riga na pyjamas farare tas masu santsi da Æ™yalli. Kasancewar sun mata bujin-bujin yasa basu bayyana mata surar jiki ba. Ya É—an samu nutsuwar ganinta da kayan mutunci, dan haka ya kalleta cikin ido babu wasa a tattare da shi ya ce, “Kinyi sallah?â€.
    Tana son Uncle Yousuf matuƙa dan shima yana sonta da mata gata. Sai dai kuma baya wasa akan tarbiyyarta da gyara lamarinta shiyyasa take tsoronsa idan ya birkice, dan yasha kwasa mata mari mai gigitarwa. Akwai wani lokaci da ƙawaye suka yaudareta suka sakata dawowa gida a wani yanayi da ga club da ya ɗauketa da wani mahaukacin mari sai da ta yini jinta bai dawo ba. Tuni kuma ta watsakke daga makuwar da tayi.....
    “I say kinyi salla?!!â€.
   Ya sake maimaitawa a tsawace fiye da farko. Daburcewa tai ta ɗaga masa kai ta kuma girgiza. Sai kuma ta sauka da gudu a gadon kamar wata ƙaramar yarinya ta nufi toilet ɗin ta. A cikin mintunan da basu gaza biyu ba ta fito fuska da ƙafafu jiƙe da ruwa wai tayi alwala. Abin salla da Tabawa ke faman ajiya a ma'ajiyarsa kamar na ado dan ba sallar take ba sai randa taso ta ɗauka ta shimfiɗa. Akan kayan barcin ta zumbula hijjabin da shima dai baida banbanci da kayan decorations na gida gareta. Uncle Yousuf na daga inda yake tsaye har yanzu cikin ƙunar rai. Fara sallar da bata da fasali balle makama da gamata ba'a ƙulla mintuna biyu cikakku ba. Hankalin Uncle Yousuf ya ƙara tashi. Dan yau ne karan farko da ya fahimci Mawaddat bata iya ko salla a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un†ya shiga maimaitawa jikinsa na tsuma. Baima san sanda ya kai zaune jagwab cikin kujerar kusa da shi ba. Yanzu nan kamar Mawaddat mai shekara ɗai-ɗai har ashirin da huɗu tana cikin ta biyar, mai karatun matsayin cikakkiyar lauya da duk wanda ta tsayama a shari'a zai iya alfahari da itace babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da UBANGIJINTA a ɓangaren bauta masa irin haka. Wane irin sakaci sukan sukai da shagala akan al'amarin yarinyar nan har haka?.....
    “Uncle You! please kayi haÆ™uri kar kai fushi da niâ€.
  Kalamanta cikin damuwa suka katse masa tunani. Tuni ta rarrafo gabansa ma hijjab É—in na harÉ—eta batare da ya sani ba. Idanu kawai ya zuba mata dan shi kam tausayi ma take bashi wlhy. Shi mutum ne mai zafi amma kuma yana da saurin sauka da kuma sauÆ™in kai shiyyasa yaran É—an uwan nasa ke sonsa, dan ya taso ne kamar duk shi ya raine su. A hankali ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarshi a rissine bakamar É—azun ba ya ce, “Mawaddatan-wa'rahmah!â€.
    A hankali ta ce, “Yes Uncleâ€.
  “Mi kikayi haka?â€.
“Uncle salla mana da kaceâ€.
“Bani nace ba ALLAH ne yace ayi kuma ba haka akeyi ba. Mawaddat wannan ranar ita nake gudun zuwa gareki shiyyasa nake zaneki idan kikaÆ™i zama Islamiyya a shekarun baya kafin abar Æ™asar nan da ke, shiyyasa kuma na dage a nema miki malamin da zai koyar da ke addini bayan Yaya ya maidaki can. Yanzu ace kamarki, É—iyan musulmi hausawa Æ´ar Æ™asar Nigeria a arewa amma baki iya salla ba? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Mawaddat da duk mi kike yi ke kuwa a duniyar nan haka? Mi kikaima kanki tanadi na tunkarar UBANGIJI da har kikejin Æ™warin gwiwar baje kolinki a duniya da abinda ke cikinta kawai? Anya kin yarda zaki mutu kuwa? Za ki kuma kwanta kabari? Za kuma a tasheki? Za'a kuma miki hisabi sannan ki Æ™arÉ“i sakamakon makomarki?. Makomar da gida biyune kacal dole kuma ka tsinta kanka a É—aya wuta ko aljanna.........â€
    “Uncle Please kabar zancen mutuwan nan mana. Badai sallan bane kuma nayi. Kaga inama da zuwa court zuwa ten ga shi har nine na neman wucewa.â€
  “Wato shi zancen sallan baida muhimmanci ko?â€.
  “Noo Uncle You! Bance ba fa. Kawai dai ni.....â€
  Sai kuma tai shiru. Kansa kawai ya girgiza dan y fahimci ba irin wannan zaman na kai tsaye Mawaddat ke buÆ™ata ba. Yana buÆ™atar yin nazari akan al'amurinta kafin ya nemo mafita mai É“ullewa. Da hannu yay mata nunin ta tashi da faÉ—in, “Okay jeki shiryaâ€.
   “Yawwa Sweet Papa na!!!â€.
Ta faɗa da ihu tana miƙewa. Kansa kawai ya girgiza yana mai karanto mata addu'ar shiriya wajen UBANGIJI kamar yanda ya saba akoda yaushe ya tashi ya fice dan bata damar yin shirin....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.