Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 33 of 94
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 3ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
........Motar taima key ta cigaba da tafiya duk da ta fara jin kanta ya ɗauka. Da ƙyar ta iya kai kanta office saboda abinda tasha ɗin ya fara aikinsa. A yanda ta shiga duk da bawai tana layi bane yasa mutane da yawa ɗan binta da kallo. Office kawai ta faɗa tare da maidashi ta rufe harda saka key. Tai jifa da handbag ɗinta da key da takalma har ma da mayafi da ɗan kwali. Zama tai jikin kujera ta dunƙule jikinta waje guda tana mai tura kanta data dafe da duka hannu biyu tsakanin ƙafafunta. Surutai takeyi ƙasa-ƙasa irin wanda idan ba kusa da ita kake sosai ba bazaka taɓa iya fahimta ba...
    _(Kai jama'a shaye-shaye baiyi ba. Shaye-shaye kan zubar da mutuncinka kowane matsayi ka taka. Yana maidaka baya komai Æ™arfin ikon ka. Yana Æ™asÆ™antar da kai komai darajarka. Ga lafiyarka kaima da É“arnar kuÉ—i. Miyasa Æ´an uwa? Mike birgemu? Mike ruÉ—armu?. KuÉ—i? Ƙawaye? Abokai? Samari? Gata? Kokuwa son zuciya?. Idan duk sune mu tabbata masu Æ™arewa ne kamar ba'ai ba. Masu zama labarine kamar basu zo ba. Shaye-shaye wafce mana dukkan muhimman damammaki yake na cigaban rayuwarmu ta duniya da lahira. Kuduba ku gani, duk shekaru irin na Mawaddat bama tasan minene addininta ba, duk da tarin damammakin rayuwa da ALLAH ya bata wannan illar É—aya take ta shaye-shaye da ke tare da rayuwarta na Æ™oÆ™arin maidata baya. Tun tana ganin tana kiyayewa akan aikinta gashi ta fara kuma a cikin lokacin aikin, mi kuke tunani? Wataran aikin ma sai ta gagara yinsa gaba É—aya. Da ga sanda ta rasa wannan damar kuma shike nan ta Æ™arasa rushewar baki É—aya sai jiran ta fara bin bola kuma duk da gatan taðŸ˜. ALLAH ka shiryemu ka shiryar mana da zuri'armu da duk masu wannan mummunar É—abia)._
  Â
   ★★.....
    Bayan sallar la'asar Daddy da Uncle Yousuf suma suka shiga jerin Æ´an sannu da zuwa ga Alhaji Sufi Garko. Ya nuna farin cikin ganinsu. Dan mutum ne da ya san mutuntawa. Kallo yake musu suma irin na Æ´aÆ´a tun kan aurattayya ta shiga tsakanin É—iyarsa da Daddy balle yanzu ga Mawaddat ta ratsa duk da babu É—iyar tasa data zama sanadi a duniya. A hirarsu ne ma suke jin cewar Mawaddat ce ta É—akkosa da ga airport, yana Æ™yautata zaton ma har yanzu tana a gidan tare da Æ´an uwanta. Daddy yaji daÉ—in hakan har Uncle Yousuf ma kansa. Basu nemeta bata suka cigaba da hirarsu hankali kwance. Shigowar Alhaji Sulaiman (mahaifin Tajuddeen) ce ta saka Daddy yin shiru, sai kuma ya dubi Alh. Sufi Garko da suke kira da Baba cikin girmamawa ya ce, “Baba inaga bara mu wuce ALLAH ya Æ™ara lafiya yasa kaffara neâ€.
    Alh. Sufi ya tsatstsare Daddy da idanu batare da ya amsa ba, sai kuma ya maida dubansa ga É—ansa Alh. Sulaiman da ya koma can gefe zai zauna. Cikin bada umarni ya ce, “Isma'il koma ka zaunaâ€. Babu musu Daddy ya koma ya zauna É—in. Ya maida dubansa ga Alh. Sulaiman da faÉ—in, “Kaima zonanâ€. Gaba É—ayansu a gabansa sukaje suka zauna kowa na hararar É—an uwansa kamar wasu Æ™ananan yara.
   “Ku yanzu kuna ganin wannan rayuwar bazaku ajiyeta ba. Ko a tinaninku har yanzu ku yarane? Ku duba gashin kawunanku furfura duk ta gitta a ciki. Tunda kun gagara faÉ—amin matsalarku a tsahon shekarun nan ni bazan cigaba da damuwa da sai na sani ba. Sai dai ku sani idan har abinda ya shafeku kuka bari ya shafi zuri'arku bazan yafe ba. Ku shaida hakan ko bayan Æ™asa ta rufe idanuna neâ€.
  (Anzo wajen) cewar Alh. Sulaiman a zuciya. Dan haka ya gyara zama cike da makirci ya sake raunana muryarsa. “Baba ni ba laifina bane, tunda kowa shaidane na biyo hanyar da zamu sasanta da shi a shekarun baya amma ya koma bayan fage ya zuge yarinya komai ya sake rushewa. Shine ya sakama ransa ni maÆ™iyinsa ne kawai. Shiyyasa naso haÉ—in auren Tajuddeen da Mawaddat dan ya tabbatar ba hakan bane ba. Kuma ko a yanzu in har zai amince ya cire komai a ransa ni a shirye nake komai ya zama labari. Mu kuma dunÆ™ule Æ´aÆ´anmu waje guda matsayin ma'aurata dan Æ™ara danÆ™on zumincinmuâ€.
    Wani irin kallon É“acin rai Daddy ke masa. Sai dai baice komai ba. Alh. Sulaiman da ke masa kallon Æ™asa-Æ™asa ya saki wani irin makirin murmushi da kashe masa ido É—aya. Ƙara tunzura zuciyar Daddy tai amma sai ya danne dan jin Baba ya fara faÉ—in, “Ni kaina zanso wannan haÉ—in zumincin, zan kuma so ya zama sanadin canja wannan gabar taku. Sai dai kuma bazan so ya rikiÉ—e daga manufarmu ya koma abinda bashi muke fata ba zumincin ya taÉ“arÉ“are ma fiye da yanzu....â€
    “Amma Baba ai yaran suna matuÆ™ar son junansu. Dama tun farko matsalarmu ce ta tilastasu haÆ™ura a wancan karon maâ€. Alh. Sulaiman ya faÉ—a yana sake sakin makirin murmushi. Baba da ba ganin abinda ke faruwa yake ba ya kai dubansa ga Daddy da baice komai ba. “Isma'il bakace komai ba. Abinda É—an uwanka ke faÉ—a gaskiya ne?â€.
     Murmushin mugunta Daddy dake Æ™ulla murtanin da zai maida ga Alh. Sulaiman ya saki. Cike da sake girmamawa ga surukin nasa kuma ogansa ya jinjina kansa. “Baba duk ina saurarensa. Sai dai na tafi wani tunani ne, kenan Mawaddat Æ™arya tamun ko kuwa rashin jin nata ne ya sata kawo min wani a matsayin miji alhalin suna tare da Tajuddeen har yanzu...â€
    “Miji?â€.
  Alh. Sulaiman ya faÉ—a kamar a É—an razane. Shiko Baba murmushi yayi da faÉ—in “Miji Mawaddat É—in ta fitar?â€.
  “Eh Baba. Dan dama dawowarka muke zaman jira muzo maka da batun. Saboda yanata ma damuwar turo magabatansa amma ina dakatarwa da cewar har sai ka dawo tukunnaâ€.
    “Wlhy Æ™arya kake Isma'il! Wannan makirci ne ka Æ™ulla dan kar Mawaddat ta auri Tajuddeen, an gaya maka tsoronka nakeji wai ne da na gagara É—aukar mataki a kanka tun a bayaâ€. Alh. Sulaiman ya faÉ—a yana miÆ™ewa zumbur. Gaba É—aya falon suka zuba masa ido. Sai kuma duk ya daburce dan fahimtar yana neman yin É“aran É“arama fa.
  “Ka É—auki mataki a kansa! A wane dalili Sulaiman?â€. Baba ya katse shirun. Kame-kame Alh. Sulaiman ya fara, hakan ya bama Daddy damar sakin murmushin mugunta. Sai kuma ya dubi Baba. “Baba Æ™yalesa kawai shirmensa ne. Kasan shi Sulaiman idan ya fusata akan abu baida fahimta. Sannan ya iya sakin duk maganar da tazo masa a baki koda ba hakan bane a ransa. Ni dai ba Æ™in haÉ—in auren Mawaddat da Tajuddeen nake ba. Kawai shashancin da tayi ne na kawo min wani matsayin miji da har na sanar da nawa dangin dama jiranka kawai muke ka dawo a tsaida biki alhalin tana tare da Tajuddeen kuma ne yasa ma harna faÉ—a. Amma ayi haÆ™uri ni zanje ga babanta Yousuf mu sameta a nutse na mata tambayoyi dan nasan halinta bajin magana take ba. Kaga idan Tajuddeen take so ni bazan hana ba, sai nasan dabarar yi wancan ya janye a rabu lafiya mutuncin kowa bai zube ba....â€
    “Mizai hana w kirata yanzu ayita ta Æ™areâ€.
  Cewar Alh. Sulaiman. Shiru kamar Baba bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da faÉ—in, “Ku dukanku kunzo da shawara mai Æ™yau kuma duk na gamsu da maganarku. Sai dai muyi haÆ™urin goben sai a zauna a nutse kan maganar. Amma yanzu ina son a kiramin Mawaddat da Tajuddeenâ€.
   Sosai hankalin Daddy ya tashi, amma ya danne a ransa yana mai addu'ar ALLAH yasa kada Mawaddat ta watsa masa ƙasa a ido. Dan shifa bazai taɓa yarda ya haɗa zuri'a da Sulaiman ba. Shi kansa Uncle Yousuf zancen Yayan nasa ya sakashi a ruɗani. Duk da yasan akwai ƴar tsamar da har yanzu bai san tushen ta ba tsakanin ɗan uwan nasa da Alh. Sulaiman bai san dalilinsa na ambaton wani ba matsayin Mawaddat ta kawo bayan yasan ba hakan bane ba. Kusan a tare suka saki ajiyar zuciya shi da Daddy lokacin da ɗan aiken ya dawo ya tabbatar musu ai Mawaddat ance ta tafi tunma ɗazun. Alh. Sulaiman kuwa bai so haka ba. Amma baice komai ba, sai dai a ransa yana ƙudurta duk Daddy yayi ya gama a wannan karon sai Mawaddat ta zama matar Tajuddeen.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.