Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 84 of 94
      _______________★
 Â
  Kwanaki uku kenan da fara fitar Lulu aiki, kullum kuma Smart ke kaita office da safe sannan shima ya koma gidan yay shirin tashi fitar a Napep. Idan ko fita ta kamata a yinin mai Napep É—in nan da bata san da shi ba na biye da ita. Duk kuma inda ta saka Æ™afa ana sanar masa. A lissafinsa dai babu wani abu dake faruwa, dan ranar farko ta sayi bread wanda bai san a tsakkiyarsa aka saka mata kayan shaye-shayen ta ba, kamar yanda takeyi sai zata kwanta tasha hakan tayi, shiyyasa bai gane komai ba sai ya É—auka kawai gajiyar aikin data koma ce tunda tayi Æ´ar zirga-zirga. Washe gari dai yaga ta tashi a tsayenta bakamar kwana biyu datai wani sukuku ba. Rana ta biyu ma sai da tai amfani da dabarun nasu ta amsa, hakama jiya. Yau cikon kwana na uku yaso ya É—an fara tsarguwa, amma dai baice komai ba. Yana son mata tambaya akan zuwa gidan su Sa'id sai kuma dai yay shiru. Sai kuma gashi a yau yana tare da Coach kira ya sameshi da ga Ammah wai yazo da sauri idan yana kusa. Ya Isa gidan da tunani kala-kala sai ya É“ige da samun mahaifiyar Sa'id da wasu Æ´an uwanta maza uku dan dangin mahaifinsa sun rantse bazasu zo ba, ita data É“ata taje ta gyara sun dai zo na farko. Ba Smart kaÉ—ai ba kowa ma na gidan nan yau mamakin jin maman Sa'id wai sunzo bada haÆ™uri ne da neman afuwar Hawwah dan ALLAH tai haÆ™uri ta koma yake. Smart yace shifa Æ´ar uwarsa bazata koma wannan gida ba, anyi kenan takardar saki kawai yake buÆ™ata Sa'id ya kawo, dan suna sonta baza'a kashe musu yarinya ba. Sosai Maman Sa'id ke faman magiya akan wancan ma daya faru tsautsayi ne da munafuncin munafukai, amma yanzu ta gane gaskiya. Ankai ruwa rana matuÆ™a kafin Smart ya haÆ™ura zata koman amma ba wannan gidan ba. Da sauri Mama tace ta yarda, Hawwah ta zaÉ“i duk inda take so a gidajensu a gyara mata. Wannan abu yaba kowa mamaki, Umma na son magana tana tsoron ta tanka Maman Sa'id tai mata bankaÉ—a tunda taji tana shaguÉ“e akan munafukai, ba kowa kuma ne mai zuwa É“ata Ammah da Hawwah a wajenta ba sai ita dama. Bayan wucewarsu kowa ya shiga mamaki, Abba ya tsare Smart akan miya ma maman Sa'id É—in har tai irin wannan sakkowar lokaci É—aya. Ya tabbatar musu bashi bane, dan shi target É—insa akan jiran dawowar mahaifin Sa'id ne ai. Yana son kawo Lulu a ransa wani gefe na zuciyarsa na musa masa. Amma dai duk da haka bayan ya koma gida da daddare sai da ya kasa haÆ™uri yay mata tambaya. Dariya kawai tayi taÆ™i faÉ—a masa komai, hakan ya tabbatar masa itace kenan tayi koma miye. Sai kawai ya zuba mata ido yana jin wani abu mai girma na Æ™ara ratsashi a kanta. Jin kaifin idanunsa a kanta ya sata dakatawa da ga abinda take a system ta É—ago, harararsa tai da faÉ—in, “Malam wannan kallon fa? Ni fa bana son kalloâ€. Ta Æ™are maganar da murguÉ—a baki. Murmushi ya saki mai sanyi batare da ya janye idanun ba, sai ya samu kansa da furta, “Kullum sake mamaye komai da komai kike yiâ€. Bata fahimci ina ya dosa ba, sai dai yanda yay maganar a Æ™asan maÆ™oshi da tausasa fitar sautin matuÆ™a ya sata tsayawa kallonsa, “Lafiya kake kuwa? Kodai kaima ka fara ban sani ba?â€.
     “Na fara mi?â€.
  “A hawa network manaâ€.
Ƙaramar dariya yay yana girgiza kansa. “Tom maybe na fara amma nawa ba irin naki bane gaskiya. Kema fata nake ki daina wannan ai ki dawo wannan irin nawanâ€.
    Nan É—in ma dai ba fahimtar tai ba, dan haka ma ta taÉ“e baki da miÆ™ewa tana faÉ—in, “Ai kai kam wani lokacin kamar mai aljanu. Dolene na sanarma Ammah ta fara maka addu'ar su ko ka kwaso a drivern cin ba'a sani baâ€. Daga haka ta wuce bedroom ta barshi yana murmushi.........âœï¸
    Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 8ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
.........Washe gari gidansu ya wuce bayan ya sauketa, anan ne yake samun Abba da Ammah da batun shifa yana zargin Mawaddat ce tayi koma miye. Dan an sanar masa taje gidan a ranar monday. Mamaki sukaitayi suma da tunanin to mita faÉ—a ma maman Sa'id da har ta risina haka da sauri. A gefe kuma Æ™aunar yarinyar na sake shigar musu zukata. Kamar yanda akace sati É—aya cikin satin Hawwah ta fara shirin komawa sabon gidanta danÆ™arere. Hankalin Umma ya sake tashi, da bin Æ™wanÆ™wanto ta gano Lulu ce tamayi koma miye har komai ya dai-daita. Hankali a tashe ta nufi gidan Hajiya Naqiba Æ™awarta. Acan suka baje faifain zagin Ammah da bata san sunayi ba da ƳaÆ´anta suna neman mafita dan abubuwa fa nata faman kufce musu a hannu, sai dai gaba É—aya hankalinsu da mugayen Æ™udirinsu sun tattara ne ga Lulu yanzu. Dan sun fahimci shigowarta gidan abubuwa da yawa ke neman taÉ“arÉ“arewa. Duk da su basu fahimci cewar asirin jikin Smart ma ya gama warwarewa gaba É—aya ba. Ga aikin Malam na-zuru yaÆ™i yiwuwa, dan kayan Lulu da Smart dai sun gagara É—akkuwa. Hajiya Naqiba ce cikin dogon tunani ta ce, “Aminiya anya bazamu canja taku ba?â€.
    “Kamarya? Fito kimun dalla-dalla, kin san bana son kwana-kwana faâ€.
   “Ina nufin ba asiri bane kaÉ—ai yanzu ya kamata musa gaba dole mu haÉ—a da makirci da kissa. Kamar dai yanda nai akan shegun yaran can na baÆ™ar dagar tawa.â€
  “In dai wannan ne ai mun jima munayi Aminiya, yanzu ko ita akan wannan shegiyar da zata koma Hawwah ai kinga sai da muka haÉ—a da makirci waccan shegiyar da bamu san mitaje tayi ba ta É“ata mana komai.â€
     “Kwantar da hankalinki karki damu, murnarsu zata koma ciki ne. Yanzu mu fara kai wannan baÆ™uwar hauren Æ™asa tukunna dai. Dan wannan Æ´ar iskar amaryar da aka jajubo muku na fahimci da Æ™arfinta tazo, gashi yarinyar nada ilimi fiye da tunaninki kuma goyon turai, ga kuÉ—i a gida, kuÉ—i a mota, kuÉ—i a Office, kuÉ—i a banki. Idan mukai sake fa komai zai koma wanwarne, ni ko da kishiya da yaÆ´anta su ji daÉ—in duniya ko komawa sama dani gara ace kowa ya mutu a Æ™asar, ke ama busa Æ™ahoâ€.
    Dariya Umma tayi da faÉ—in, “Hajjaju ke bala'i ce ai, shiyyasa nake sake tausayin Matar gidan nan naki. Yanzu ke miye shawararki?â€.
       “Dole ne muyi bincike akan yarinyar mu samo wanda zamu shiga jikinsa nata mu mata rugu-ruguâ€.
    “Tab babbar magana ta yaya kenan? Bayan kin san daga wane gida ta fito, gate É—in gidan su ma taÉ“a shi ba masifa bane balle shiga gidanâ€.
  “Kwantar min da hankalinki. Akwai matar nan mai min Æ™unshi ranar ana labarin dukiyar da aka zubar a auren ita yarinyar da aka kai gidanku take cewa ai ita taga zahiri dan itace kema matar Alhaji Garko Æ™unshi shekaru kusan shidda kenan, shiyyasa tasan abubuwa da yawa a gidan nan ko shagalin bikin nan duk akan idonsu akai komai. Ita kanta taci rabonta dan tayi Æ™unshi sosai a gidan, sai dai ta fahimci kamar matar Alhaji Garko bata son auren fin Æ™arfinta akayi, yarinyar da É—an uwanta aka saka mata biki lokaci guda ta birkice wai sai yaron gidankuâ€.
   “Kai haba da gaske wai? Anya ba asiri suka mata ba ma kuwaâ€.
  “Wlhy haka tace, babu abinda Hafsatu bazata iyaba wlhy, wama ya sani. Shiyyasa nake ganin ya kamata muje gidan Alhaji Garko mu kunnowa Hafsatu wutar da zata Æ™oneta Æ™urmus har Æ´aÆ´an nata a wannan karon. Ba suna murna sun samu É—iyar biloniya ba. Zasuci ubansu neâ€.
   Dariya suka kwashe da ita suna tafawa......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.