Best / Popular Hausa Novels

Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: FURAR DANKO 1.txt

Chapter 86 of 94

____________

.......Dada tayi tunanin Lulu zata sake dawowa gidan, amma bayan duk ƴan rakkiyar Baba sun dawo sai gashi babu ita, sai ma sanar mata da akai ta wuce gidan ta. Hakan ya sake girgiza Dada ta kuma tabbatar da eh lallai da alamar ƙamshin gaskiya a zancen mutanen nan asiri yaron nan yay ma jikarta. A take ta dannama Fulera mai ƙunshi kira, batare dako amsa gaisuwar ta ba tace ta sameta yanzun. Fulera ido a kuɗi tuni tai tsalle tayo waje da ga gidan su, dan dama dai zawarci take kusan shekara tara kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gata a Garko house. Ta sami Hajiya Dada tare da mai aikinta dake mata irin waɗan nan ayyukan na sirri, dan Dada tunda jajayen sawu ƴan hannun bin malamai ne kam. Cikin gurfana Fulera ta miƙa gaisuwa, Dada ta amsa cike da isa. Babu wani jan lokaci ta sanar musu abinda take son a mata. Zasuje wajen mutumin da tace mata a Zuru ita da mai aikinta. Ba haka Fulera taso ba, amma dai babu damar musu dan haka ta amsa da to. Mota Dada ta bada akaisu tare da kuɗin amma sai ta damƙawa mai aikin nata. Nan ma Fulera taji zafi, ta dai danne, damar fara fita data samu kafin mai aikin Dada ta kimtso ta samu ta dannama Hajiya Naqiba kira ta sanar mata komai. Dariya Hajiya Naqiba tai da faɗin, “Kai tsohuwar nan mayyace akwai shegen wayo. Barta ai inta san wata bata san wata ba. Kwantar da hankalinki bari na kirashi kafin ku isa.”
     Haka kuwa akai hajiya Naqiba tai kiran malam na-zuru, duk yanda suke so haka ta tsara masa, shima da yake shegen kansa ne yace karta damu. Abinka da lafiyayyar mota basu sha wahala ba, dan bayan azhar kaɗan suka isa zuru saboda gudu na masifa da drivern yayi. Malam na-zuru da yake yasan da zuwansu kafin ma su faɗi abinda ya kawosu ya shiga zayyane musu wai ai ya gani ne a cikin aikinsa. Tuni mai aikin Dada ta ruɗe ta danna mata kira, nan ma fa sukai magana da malam Na-zuru ya sake fanfa Dada da kalolin sharri wa Smart dangane da auren Lulu, harda cewa ai asiri Smart ɗin yay musu dan yaga kuɗi. A yanzu haka ma yana Niger yaje anyo masa wani babban ƙulli, zaita kwantar musu da kai ya nuna shi na ALLAH ne sai anan gaba kaɗan zai bayyana halayyarsa da mugun nufinsa. Tsaf Dada tahau ta zauna saboda tayi imani da malaman tsubbu matuƙa gaya. Malam na-zuru ya haɗa musu kayayyaki suka sake ɗakko hanya....

      WASHE GARIN Lahadi Lulu da ƴan kwananta ta zubasu a mota ta kaisu sabon Saloon da ta fara zuwa yanzu ana mata gyaran jiki. Tsaf aka gyara ƴammatan nan suka fito tas da su kamar basu ba. Daga Saloon sun shiga wani joint suka ɗan sha ice-cream da abinda baza'a rasa ba. Daga nan suka koma gida. Kasancewar duk sun gaji kuma basa tare da yunwa suka shige ɗakin dake matsayin masaukinsu masu kwanciya nayi masu fira nayi. Itama anan falo ta ɗan kwanta dan ta haɗiyi kayan nata duk da kaɗan take sha dan kar yaran su fahimta. Wayarta ce ta shiga ruri, takai hannu ta ɗauka tana jan ƙaramin tsaki. Ganin Dada ya sata waro idanu waje, sai kuma ta ɗaga da sauri. Kafin tace komai Dada ta ce, “Ina mai gadin naku anata horn kamar ya mutu”. Da mamaki Lulu tace, “Mai gadi kuma Dada? A ina wai?”.
       “Gidan da aka kawoki mai kama da bukkar fulani”.
    Dariya Lulu tai tana miƙewa. Ta ce, “Uhm Dada baƙya gajiya dama mutane sharri idan baki son su. Wannan gidan ko makaho ya shafa ai yasan badaga nan ba. Ina zuwa”. Ta yanke wayar tare da zura slippers ta fita. Da kanta ta buɗe musu gate ɗin. Dada na hakimce a bayan danƙarereiyar motar da sukazo baƙa wulik, sai drivern ta. Koda ya samu waje yay parking sai da ya buɗe mata ta fito tana wani yamutse fuskartar ta tsufa da bin gidan da kallon banza. Yi Lulu tai kamar bata fahimceta ba ta rungumeta tana murnar ganinta. Dada ta tureta da faɗin, “Ni karki kadani fitinanniya”.
      “Ni na isa kadaki Hajiyar Baba Garko. Yanzu yana asibiti yana fama da kansa ke kina nan kina yawo”.
     “Oh kijimin yarinya da ƙulli, yanzu zuwa na dubakin kuma bammayi miki gwaninta ba kenan”.
           “A'a kimun yi haƙuri muje ciki”.
      A falon ma dai Dada sai yamutse-yamutse take duk da ya mata ƙyau matuƙa. Nan ma Lulu tai kamar bata lura ba taje ta kawo mata ruwa da lemo. Tana zama ta jeho mata tambayar “Ina yaran dana ganki da su ɗazun?”. Cikin rashin damuwa Lulu ta nuna ɗakin da su Maryam suke. Ɗan jimm Dadan tai sai kuma ta miƙe, “Kinga muje ɗakin ki magana nazo muyi”. Babu musu Lulu ta miƙe suka nufi bedroom ɗinta da Asma'u ta gyara ƙal sai tashin uban ƙamshi yake yi. Nan ma dai sai da Dada ta gama ƙare masa kallo sannan ta ja numfashi. “Kaya har kaya anzo an zubesu a wannan takurarren gidan.” ƙin cewa komai Lulu tayi, dan haka Dadan ta cigaba da faɗin, “Game da zuwa duba Alhaji ne. Shin zakije ne?”. Ɗan jimm Lulu tayi, sai kuma ta nisa da faɗin, “Ina son naje kam Dada, sai dai yanzu Aliyu yayi tafiya maybe ya dawo gobe. Idan ya dawo mukai magana sai kiji”. Sosai zantukan lulun ke sukar Dada da sake gaskata fa amma jikarta asiri, yo Mawaddat ɗin ta data sani mai zafin nan da ƙyamar abu ga murɗaɗɗen hali wai namiji ke juyawa haka. Namijin ma talaka ɗan talakawa fitik mai amsa sunan drivern ta. Kai wannan al'amari akwai ayar tambaya. A zahiri kam murmushi tai da cewa, “To ba laifi hakan ma yayi. Af kinga zan manta ga wannan kisha maganin ciwon maran nan ne dake damunki dama nace zan amso miki, inata shiririta sai kwanaki aka amso kinata zuwa gidan kuma ina mantawa. Shiru Lulu tayi tana kallon goran ruwan kamar tace a'a sai kuma dai ta amsa, dan ranta bazai taɓa bata Dada acikin jerin wanda zasu iya mata wani abu daban ba, sannan tana saran ganin period ɗinta nan da kwana uku, tasan kuma azabar da take sha na ciwon maran. Amsa tai ta ajiye gefe, amma sai Dadan tace tasha mana. Ai ba'a wasa da magani. Badan Lulu taso ba ta buɗe tasha kusan rabi ta ajiye. Daga haka suka cigaba da hirarsu da Dada wadda duk bugun cikine akan auren nan da son sanin wanene Smart. Ita dai Lulu tana bata amsar abinda ta sani ne kawai, har cikin ranta kuma bata kawo komai ba. Sai da Dada take cemata tafa kula, karta yarda yaron nan ya mata wayo ya kwanta da ita, dan yanda kwanakin nan suka kusa cika zai iya shirya mata muguntar maza. Lulu tai murmushi da faɗin, “Dada kenan nace miki ki kwantar da hankalinki, Shifa Aliyu ba irin waɗan nan da kike tunani bane. Na tabbata tunda har ya amince da auren nan na wata ɗaya ne kuma zai sake ni bazai taɓa saɓawa ba zai sake nin, yanzu haka ma jiran dawowarsa nake mu fara maganar dan shiyyasa nace ki dakata da batun tafiyar nan, cases ɗin dake gabana zanyi ƙoƙarin kammalasu na ɗan ɗauki hutu daga duba Grandpa zan ɗan huta kafin na dawo Nigeria gaskiya”.
     Sosai Dada taji daɗi dan haka ta shiga sanya mata albarka. Daga haka ma sai ta miƙe tana faɗin, “To bara na wuce tunda na kammala abinda ya kawo ni. Sai na jiki ɗin”.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.