Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 9 of 94
∆•••∆ ★ ∆•••∆
  Da Æ™yar ya iya buÉ—e idanunsa da sukai masa tsananin nauyi ya fara bin inda yake da kallo. Falo ne babba mai É—auke da kaya na alfarma. Sai garadan samari guda biyu dake tsaye a kansa da alama sune suka ajiyesa a wajen. Akan mutumin dake zaune cikin kujera mai zaman mutum É—aya ya tsaida idanun nasa. Shima kallonsa yake yi. Fuska ya Æ™ara tsukewa tare da kauda kansa, babu alamar tsoro tattare da shi ya ce, “Su waye ku? Mi nakeyi anan?â€.
   A karo na farko mutumin yay murmushi har ana iya jin sautinsa. Kansa ya jinjina da faÉ—in, “Abinda duk aka faÉ—amin game da kai naga fiye ma da hakan. Sanin ni wanene gareka baida amfani. Abinda ya kawoka nan kuwa shine aiki. Idan kaso zaka iya É—aukarsa a business É—in da zaka Æ™aru kaima, idan kuma kai tunanin bijirewa ko cigaba da wannan zafin kan naka to komai zai iya faruwa. Sunanka shine *_Aliyu M. Idris Mawashi._* Mata huÉ—u ne a gidanku Æ´aÆ´a talatin da biyu. Mahaifiyarka itace ta farko a wajen babanka, ku biyar ta haifa É—aya ya rasu. Kai kaÉ—aine namiji biyu sunyi aure kanada kanne mata biyu yanzu haka Maryam da Asma'u. Yanzu haka suna a ajin karshe a sakadire, islamiyya suna ajin hadda. Babbar yayarka na auren Alhaji Abubakar Azare itace amaryarsa. Bata sonshi mahaifinku ya haÉ—asu, yaranta biyu duk maza. Kanwarka dake bimaka tana auren abokinka Sa'id Ibrahim, yarinyarta É—aya da ciki. Kana cikin matsanancin rayuwa sosai akan al'amuranka daba sai nayi zaman lissafasu ba ka sansu kaimaâ€.
    “Daka sanni har kamar haka, amfanin mi zai maka?â€. Uncle Smart ya faÉ—a cikin zafin rai.
  Ƙaramar dariya mutumin yayi yana wani É—age kafaÉ—a. “Amfani masu yawa kuwa, ciki harda abinda zuciyarka bata kawo maka ba. Dan duk wanda na buÆ™aci alaÆ™a da shi dole ne ya amince min. Inba haka ba zai fuskanci abinda babu shi a lissafin rayuwarsa. Idan kuma ya amince lafiya zamuyi mu gama cikin mutunta juna na Æ™aru ya Æ™aruâ€.
   “Sai kuma gashi ni ba'aimun barazana?â€.
  “Ba barazana nake makaba nima. Ina faÉ—a maka abinda zan iya yine koda a yanzu ne da kake gabana. Aliyu Mawashi! Ko nace Smart Mawashi ni bana faÉ—ar abinda bazan yi ba. Idan na faÉ—a maka zanyi to na gama shirya yanda zanyi É—in ne. Ka kwantar da hankalinka aikin da zakamun bamai wahala bane ba, sannan kaima zaka fita a Æ™angin damuwar rashin abunyi da kake a ciki, maybe ma ka tsallake Æ™asar nan insha ALLAHU a wannan karon ka samu cikar burinka. Mahaifiyarka ta samu kwanciyar hankali da samun salamar hantara daga kishiyoyi da miji, rayuwar Æ™annenka ta inganta kamar yanda kake fata. Mahaifinka ya cire zargin da yake maka da fifita Æ´an uwanka a samanka duk da bawata tsiya suma suke tsinana masa ba.....â€
   “Waye kai?â€.........âœï¸
*_Ku Æ™ara haÆ™uri dani dan ALLAH. Idan na É“alle typing har sai kunce ya isa haka in sha ALLAHUðŸ™ðŸ˜©_*
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 9ï¸âƒ£
........Dariya sosai Alhajin ya kwashe da shi. “Karka damu da sanin ni wanene saboda nasan kai waye? Sanin aikin da zakai min kawai ne yafi muhimmanci. Dan na sanka fiye da yanda na faÉ—a maka a yanzu. KaÉ—an na tsinkulo a sanin danai maka kawai. Gidan daka ajiye aiki nake so ka koma ka cigaba da min aiki. Duk wata zan baka albashin naira dubu hamsin bayan albashin da su suke baka dubu ashirinâ€. Ya ajiye masa wani envelope gabansa da cigaba da faÉ—in, “Wannan shine kundin ayyukan da zakamin a gidan Alhaji Isma'il JiÆ™amshi. Zan iya baka dama ta kwana É—aya kaje kayi tunani, sai dai ka sani ko'a cikin É—akinka idanuna a kanka suke, dan haka da zuciyarka kawai nake buÆ™atar kayi nazari. A duk sanda nake buÆ™atar magana da kai zan nemeka tanan†ya ajiye masa waya akan envelope É—in daya ajiye gabansa. “A yanzu bana buÆ™atar cewarka anan, kaje kayi nazarin na barka lafiya. Ku maidashiâ€. Ya Æ™are maganar da duban yaransa cikin bada umarni
    Da wani irin kallo mai nuna tsananin zafin zuciya Uncle Smart ya bisa. Sai dai da alama ran ƴan maza ya ɓaci dan ya kasa furata komai.....
    Kamar yanda Alhajin ya bada umarni sun maidoshi har kan titin anguwarsu. Kasancewar magrib yayi a gurguje ya Æ™arasa gida domin watsama jikinsa da yay nauyi ruwa. Ya samu wasu daga cikin samarin Æ™annensa sun dawo gidan. Wanda ya samu a waje suka gaishesa. Da hannu ya amsa musu kawai ya shige É—akinsa. Shi mutum ne mai tsafta sosai da Æ™wanÆ™onin tsiya, dan haka ganin É—akin a yanda ya barsa ya sashi jan tsuki yana É—an dafe kansa dake masa ciwo. Har yanzu abinda suka shaÆ™a masa bai gama sakin masa jiki ba. A karan farko ya laluba aljihunsa neman wayarsa, cikin sa'a ya jita. Ƙanwarsa Maryam ya kira, suna zaune a falo suna karatun Alkur'ani kiran ya shigo, cike da zumuÉ—i Asma'u da wayar ke'a gefenta ta ce, “Lah Yaya neâ€. Kallonta Ammi da Maryam É—in duk sukayi, ita kuma ta É—aga da sallama. A hankali ya amsa mata cikin muryarshin nan a dake da wasu ke fassarawa da girman kai da suke kallonsa da shi saboda shiru-shirunsa, batare daya bata damar cewa wani abu ba ya cigaba da faÉ—in, “Zan samu ruwan zafi a wajenku?â€.
    “Eh Yayaâ€.
Ta amsa masa cike da girmamawa. Tana ajiye wayar Maryam tace, “Ya dawo ne?â€. Kai ta É—aga mata da faÉ—in, “Ya dawo, cayay na kai masa ruwan zafi, inaga wanka zaiyiâ€. A hankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya, sai dai batace da su komai ba ta cigaba da laziminta. Tun safe hankalinsu ke'a tashe, dan bai shiga gidan gaishesu ba kamar yanda ya saba. Da farko Ammi tayi zaton koya fita wani uziri ne, sai da ta shiga gaida Abba ya yanka mata baÆ™ar magana son ransa, kamar yanda ta saba yin shiru akan Æ´aÆ´anta idan yana faÉ—a haka yanzu ma ta haÉ—iye, sai da ya gama ta bashi haÆ™uri, sai dai furucinsa akan zai bar masa gida ya matuÆ™ar tayar mata hankali, har ta aika Maryam kira mata shi ko yana É—aki amma suka samu baya nan É—akin ma a buÉ—e, neman number sa ta shiga yi amma sai ba'a É—aga ba, daga Æ™arshe ma ta daina samunsa. Da wannan damuwar ta yini yau ita dasu Asma'un.
    Koda Asma'u takai masa ruwan zafin sai da ta gyaro masa toilet sannan ya shiga, É—akin ta shiga kimtsa masa shima. Kafin ya fito harta kammala ta fice. Kasancewar anyi sallar magriba yay tashi a É—aki sannan ya fice massalaci yin isha'i. Bayan an idar gidan ya sake komawa. Abba bai shigoba, dan haka ya wuce cikin gidan. Kamar yanda ya saba sai da yabi duk É—akunan matan gidan ya gaidasu. Da É—akin Aunty Amarya ya fara. Mace ce mai yawan fara'a da son mutane, sai dai kuma bata da yawan magana itama. Duk da zai iya sa'anni da ita hakan bai hanashi girmamata saboda yanda take girmama Ammi a gidan itama kamar ba kishiya ba. Ya gaidata cikin mutuntawa, ta amsa masa da kulawa. Yaranta dake sabgogin gabansu a falon tun shigowarsa duk suka nutsu dama. Duk sun gaidashi, yayinda Æ™aramar tazo jikinsa tana kawo masa Æ™arar É—an uwanta dake bima babbar É—akin nasu cewar ya karya mata pencil É—inta tana homework. Da sauri yaron mai suna Abbas ya ce, “Yayanmu Æ™arya take ita ta karya abunta a makaranta suna faÉ—a da Ameer. Kuka ta saka itama tana faÉ—in, “Ƙaryane Yaya shineâ€. Hannu ya É—aga musu duk sukai shiru. Aunty Amarya tace, “Ai inba ubansu kaci ba Yayansu ba barin kunnen mutane ya huta zasuyi ba. Tun É—azu suke rikicin nan ni harna gaji ma da maganaâ€.
   FaÉ—a yama yaran cikin sigar nasiha, yace da safe kafin su wuce makaranta Anisan tazo É—akinsa ta amshi sabon pencil. Da ga haka ya fito zuwa É—akin Umma. Itace ta biyu a gidan, amma itace mai manyan Æ´aÆ´a a sakamakon rashin samun haihuwa da Ammah bataiba da wuri, kusan duk sunyi aure kuma. Sai dai tanada sauran Æ´ammata biyu a yanzu haka da samari biyu da basuyi aure ba. Ta amsa masa a É—an fisge, bai damuba dan hakan ba sabon abu bane a garesa. Nusaiba autarta dake gefenta zaune tana cin abinci ta gaidashi itama. Amsa mata yayi yana miÆ™ewa. Dakatar da shi Umman tayi da faÉ—in, “Yau lafiya kuwa bamu ganka da safe ba?â€.
  Ɗan murmushin Æ™arfin hali yay mata da faÉ—in. “Ba komai Umma na fitane da safe sosai wani uziriâ€.
   “Uhhm to yayiâ€. Ta faÉ—a a taÆ™aice.
   Iska ya ɗan furzar da ga bakinsa kawai ya miƙe yana ficewa. Ɗakin Mama ya nufa, mace ta uku a gidan, sai dai ya samu tana sashen Abba dan itace da girki yau. Mansur ƙaninsa ɗanta na huɗu kawai ya samu a falon da yarinyar ƙanwarsu (jikar gidan) tana barci a kujera. Gaishesa Mansur ɗin yayi yana wani nannoƙe kai na rashin kunya, sai dai babu damar yi dan suna tsoronsa a gidan ba kamar sauran yayunsu maza da suke iyama rashin kunya ba. Amsa masa yayi yana kallon askin kansa na rashin tarbiyya.
   “Idan na wayi gari na ganka da wannan askin bisa kai kayi kuka da kankaâ€. Daga haka ya fice. Baki Mansur ya tura gaba yana Æ™unÆ™uni da yarfa hannuwa. Sai dai babu damar yi da Æ™arfi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.