Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 72 of 94
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 6ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
........Cikin sa'a kuma ya gane muryar Daddy. Amma sai ya danne bai nuna ba, cikin dai nutsuwarsa ya ce, “Assalamu alaikumâ€.
  “Da sallamar nake da buÆ™ata da ita zan maka ai. Miye dalilinka na hana Mawaddat fita office ka kuma kulleta?â€.
     Shiru Smart yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya furzar da numfashi kaÉ—an yana gyara kwanciyarsa. Sake tausasa muryarsa yay fiye da É—azun ya ce, “Kayi haÆ™uri Daddy sallama wajibi ne ga musulmi, haka ma amsata ga wanda akaimawa. Kai ya kamata ka tunatar da ni hakan a matsayinka na mahaifi. Dan haka kayi haÆ™uri ka amsa min sallamata kafin muyi maganar da kake son. Assalamu'alaikum!â€.
    A cinkushe Daddyn ya amsa masa, Smart ya É—an girgiza kansa sannan ya tashi zaune sosai. Cikin sake tsantsan da kai na girmamawa ya ce, “Daddy ina kwanaâ€. Bai amsa masa ba nan kam. Shima sai bai damuba ya É—ora da faÉ—in, “Zan sake baka haÆ™uri a karo na biyu Daddy, dan ALLAH karka saka baki a wannan zancen dan a yanzu Mawaddat tana Æ™arÆ™ashin na ne. Inada damar zartar mata da hukunci akan abinda ya dace da kuma banbance mata wanda bai dace ba. Kai mana fatan alkairi kawai shi mukafi buÆ™ata da sanya albarkar ku, na riga na gama yanke hukunci akan hakan babu kuma tunanin canjawa a tattare dani amin afuwa. Na Barka lafiyaâ€. Daga haka ya yanke wayar tare da kasheta gaba É—aya ya koma yay kwanciyarsa ransa fal mamakin halin surukin nasa.
   Ƙaramin hauka ne ya kusan samun Daddy da ga can jin Smart ya yanke wayar bayan ya gama datsa masa zafafan magana kamar yanda zuciyarsa ta fassara masa. ƘoÆ™arin sake kira yayi amma sai wayar switch up. KaÉ—an ya rage ya maka wayar da Æ™asa. Amma sai ya fasa ya maida akalar kiran kan Uncle Yousuf. Suna zaune shi da yara da akaima shirin makaranta suna breakfast kiran Daddyn ya samesa. Bai kawo komai a ransa ba ya É—aga, sai dai kiran sunansa da Daddy yay a tsawace ya sashi rumtse idonsa. Sai kuma ya miÆ™e yabar daining É—in ya nufi bedroom É—insa. Cikin tausasawa ya ce, “Yaya lafiya dai kuwa?â€.
    “Yousuf yanzun nan ka kira É—an iskan yaron can ka faÉ—a masa ya sakar min yarinya tunda ba ubansa ya haifa min ita ba, har ni yake da bakin gayama Mawaddat ta koma Æ™arÆ™ashin ikonsa ya kuma yanke hukunci a kanta bazai canja ba kamar shine ya haifa min ita.â€
   “Ya Salam. Yaya Please calm down dan ALLAH muyi magana mana. Wlhy sam ban fahimci mi kake son faÉ—a min ba. Mi Aliyun yay maka ne?â€.
    “Miye ma bai mun ba, babu abinda ya manta na rashin kunya bai faÉ—a min ba. Shiyyasa tun farko na faÉ—a maka yaron nan É—an zafin kai ne zai iya bamu matsa ta duk inda bamuyi zato ba. To gashi ya fara, ya kulle gida ya hanata fita aiki, ta masa magana ya ce sai next week babu inda zataje, ta kirani nai kiransa nai masa magana amma ya daddatsamin magana son ransa tsabar shi ya cika cikakken É—an iska.â€
     Girgiza kai Uncle Yousuf yayi, kafin ya ce, “Dan ALLAH kayi haÆ™uri ka kwantar da hankalinka, ka dai san mi É“acin rai ke haifar maka a yanzu. Zan kira shi na masa magana sai naji dalilinsa. Sai dai ma yaya banda abunka ai bai kamata ka biye mata kai kiransa ba, karfa ka manta yau kwana biyu kawai da tarewarsu, ai bai dace ba ta fita aiki sai mutane suyi magana kadai san yanda al'amarin yake yanzu mutane sun bar damuwa da al'amarin su sun koma hango na wasuâ€.
     “Yousuf bana buÆ™atar jin komai, sannan ni babu ruwana da wasu mutane ko abinda zasu faÉ—a, farin cikin yarinyata kawai na sani. Shi wanene da zai tauyeta bayan da aikinta ya ganta, sannan waya faÉ—a masa shi É—in har ma yanada wani Æ™arfin iko a hannunsa a kanta da zaima mutane wani gadara koda ace auren nasu mai muhimmanci ne. Wannan shine na guda tun farko amma ka kasa fahimtata, shiyyasa kuma nace ayi komai a rubuce amma nan ma ka wani kakkaresa gashi nan tun kan aje ko ina ya fara nuna halinsa, a haka kwanakin da kace É—in zai cika yay abinda ake so? an faÉ—a masa akan Æ´ata zai nuna gargajiyancinsa neâ€.
    “Naji duk na É—auka kayi haÆ™uri zanyi magana da shi yanzun.†daga haka Uncle Yousuf ya yanke wayar batare da ya jira cewar Daddy É—in ba. Hannunsa ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya girgiza a hankali ya É—ago yana murmushi mai sanyi. A fili ya furta, “Yaya yaya kenan, kai da gaske jiran cikar lokacin kake kenan? Humm aiki ya sameka. Aliyun dama shine ai dai-dai da kai game da lamarin Mawaddat duka kai da itan. Ashe babu daÉ—i lokacin da ka dakatar da Aunty Kareema fita aiki a dalilin Marigayiya, duk da hakan ya mata ciwo kuma ta haÆ™ura iyakarta kuka ta share hawayenta, ashe ita daga sama ta faÉ—o? Kai gashi hana fitar kwanaki kawai da akai ma taka É—iyar ya zafafaka har haka. ALLAH na gode maka da ka kaini da rai da lafiyar ganin irin wannan ranar, shiyyasa akace yanzu ma tun a duniya ake fara hisabi basai an mutu ba. Muje zuwa yanzu aka fara wasan ai. Mai Æ™arfi sai yaci kofinâ€. Ya Æ™ara sakin murmushi. ƘoÆ™arin kiran Smart yayi sai ya samu wayar switch up. Ya sake sakin murmushi da faÉ—in, “Kaga mazan Æ™waraiâ€. Da ga haka ya miÆ™e ya fito abinsa. Ya samu yara har sun wuce, sai Aunty Saliha da ke zaune tana tsumayen fitowarsa dan ya sakata a ruÉ—ani.
    “Abban Ra'is lafiya dai ko?â€.
  Ajiyar zuciya ya saki yana kaiwa zaune, ta turo masa kunun data sake zuba masa dan wanda ya bari ya huce. Sai da yasha kusan sau uku sannan ya dubeta. “Yaushe zakuje gidan Mawaddat É—inne?â€.
    “Sai zuwa anjima kaÉ—an dan muje mu dawo da wuri koâ€.
   “Inaga ku kuyi zamanku, su Hussain suje sukai mata, motocin ta kuma a barsu ba yanzu ba.â€
     “Amma wani abu ya faru ne?â€.
   “Zai dai faru Saliha.......†nan ya zayyane mata komai daya faru. Cikin damuwa ta ce, “Amma Yaya da bai kirashi ba ai. Dan Aliyun ya fishi gaskiya, yaza'ai amaryar da aka kai gidan miji shekaran jiya kuma a ganta a office yau dole zai iya zama abin magana. Inda waÉ—an nan Æ™ananun matsalolin zai dinga sawa iyaye na neman sakin Æ´aÆ´ansu ai da kowama ya zama babu aure kenan. Ni sai nake ganin kamar maganar Aunty Kareema zata iya zama gaskiya....â€
    “Hummm ku mata kullum tunaninku iri É—aya ne, miyasa komai a rayuwa idan yazo mana a yanayin da ba haka muke tunanin ganinsa ba sai mu dinga É—aukarsa asiri. Nasan asiri yana É—aya daga cikin abinda al'ummar mu suke kallon babbar mafita ga al'amuransu a halin yanzu, sai dai bai kamata muna tsuke dukkanin zukatanmu waje guda ba akan kowanne bigire muyi masa kallon asirin. Amma dai bari nai miki wata tambaya, shin ku minene dalilinku na kallon al'amarin Yaya matsayin asiri?â€.
    Duk da maganganunsa na farko sun shigeta sai bata gaza wajen faÉ—a masa hujjojin da suke kallonba su. Ta ce, “Na yarda da zancenka nima, sai dai ka kalla wani abu Abban Ra'is. Kafin auren marigayiya kai da kanka ka bani labarin ba haka Yaya yake ba sam, sannan Yaya nada ilimin addini mai zurfi da yasan minene aure da Æ™addara. Amma kaga yanda idanunsa suke rufewa ta yanda idan wani aka faÉ—amawa da bai gani ba zai iya ma Æ™aryatawa. Dolene muyi tunanin akwai sammu tattare da shiâ€.
     Murmushi yay da cewa “Hummm! Saliha kenan. Duk ilimin mutum bakwa tunanin son zuciya zai iya sakashi ajiye ilimin gefe ya aikata abinda baida alaÆ™a dana masu ilimin. A al'amarin Yaya babu wani asiri, akwai É“oyayyen al'amarin da yake É“oyewa dai tun kafin auren Mawaddat É—in, sai da ya auretanne ya fara fitowa, wanda tamkar ALLAH ya jarabcesa da sanya masa tsoron faruwar irinsa akan Mawaddat ne, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai dan itace mafi soyuwa a ransa ko kuma ana masa barazana da ita, shiyyasa ma tun farko ya gagara yarda da kowa game da kula da al'amarin ta, a tunaninsa shi zai iya kareta akan komai, sai kuma akai rashin sa'a Æ™addarorinta ba'a fatar jiki suke ba ko mahallin zamanta balle yay tunanin kuÉ“utar da ita a yanda yaso da kuma Æ™arfinsa da wayonsa. Dan haka kuma bar damuwa da al'amarin sa ana gab da zuwa gaÉ“ar da zai fallasa kansa da kansa batare da ya sani ba. Yanzu Mawaddat itace mafi Æ™ololuwar abar tausayi, dan ina matuÆ™ar jin tausayin rayuwar yarinyar a dalilin halin data tsinta kanta a ciki.â€
   Yanda ya Æ™are maganar cikin matuÆ™ar damuwa da É“acin rai yasa Aunty Saliha tasowa ta dawo kusa da shi tare da dafa kafaÉ—arsa. “Kayi haÆ™uri Abban Ra'is, tabbas tausayin Mawaddat dolene ga duk wanda ya fahimci muhimmancin rayuwa. Sai dai namu addu'a ce a yanzu tsakaninmu da ita, mu kuma cigaba da bama Aliyu goyon baya akan abinda ya fara, dan a yau na sake gamsuwa da fahimtar hikimarka ta haÉ—a wannan auren. Inaga kuma lokaci yayi da shima zaka fara aiwatar da shirinka na taimakonsa da tun farko shine dalilin jawosa jikinka da kayi, dan namiji bazai yiwu ya rayu babu abinyi ba yakan ja masa Æ™asÆ™anci tsakaninsa da mace, musamman irin Mawaddat da tunda ta tashi bata san minene babu baâ€.
     “Hakane kam, insha ALLAHU kuma a yanzu haka ina kan shirye-shirye ni da Hameed, dan kin san al'amarin nasa sai anbi ta bayan fage yazo a bazata tamkar yanda maganar auren nan tazo a bazata. Dan bayyanawa na nuna zaburar da mai Æ™ullin neâ€.
   “Tabbas hakane, ALLAH ya bada nasara yasa shima iyakar wahalar tasa ce tazo. Ku kuma da kuke Æ™oÆ™arin ALLAH ya saka muku da alkairi ya hana bayanku kukaâ€.
   “Amin ya rabbi. Bara na kirata idan naga da yiwuwar kuje É—in toâ€.
  “To ba damuwaâ€.........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.