Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 77 of 94
     __________★
  Bayan magrib Smart ya koma gida, ya iske Lulu cike fam da taicin su Nadiya har lokacin. Kasancewar bai san abinda ya faru ba sai ya É—auka fushi take na daÉ—ewarsa. Dan haka yayta satar kallonta da ga inda yake tsaye dan tunda ya shigo batako É—aga kai ta kallesa ba balle ya samu sannu da zuwa. Aikinta take tayi a laptop da shan chocolate da su Hussain suka kawo mata lokaci-lokaci. Ice-cream É—in da ya sayo mata da shawarma ya ajiye gabanta, batare da yayi magana ba shima ya wuce bedroom. Wanka yay har zai kabbara salla sai kuma ta faÉ—o masa a rai, amma sai ya ture zancenta gefe ya kabbarra sallarsa, sai da ya idar sannan ya miÆ™e, fitowa yay inda ya sake samunta har yanzu ido a laptop babu alamar ma ko kallon kayan da ya kawo matan tayi. Babu alamar wasa a harshemsa ya ce, “Kinyi sallar magrib da isha'i?â€.
   Shiru babu alamar zata tanka masa, ya É—an rumtse idanunsa da sake buÉ—ewa cikin sake kausasa harshe da buÉ—e deep voice nashi fiye da farko ya sake maimita mata. Yanzu kam dole ta É—ago ta É—an kallesa, cikin harara ta ce, “Miye naka a ciki idan nayi ko banyi ba? Wai nikam dan ALLAH miyasa kake son shiga min rayuwa da yawa ne haka? Ko gadin rayuwata aka baka ne bani da labari. Bana son damuwa kabar ganin ina É—aga maka Æ™afa ka dinga ganin zaka cigaba da latsani a duk sanda kake so fa, dole ne duk abinda nayi ko baka nan sai na faÉ—a makaâ€.
    Idanunsa kawai ya zuba mata, sai dai baiyi magana ba sai hannunsa kawai da ya rumtse waje guda alamar É“acin rai matuÆ™a tattare da shi amma yana controlling temper É—insa. Dan baya son ko sau É—aya ya Æ™wace wajen bayyana mata É—ayan side É—insa a yanzu. Tsaye kawai ta gansa a gabanta, batare da yay magana ba ya É—auke lap-top É—in gefe gaba É—ayamta ya É—auka kamar É—azun. Yanzu kam ba duka ba har da su cizo takai masa amma ko gezau, bai direta ko ina ba sai bathroom É—in É—akinsa, dama a farce take, sai hakan ya Æ™ara tunzurata, sai dai kafin furucin bakinta ya ida fita ya taka mata birki da faÉ—in, “Shiiiiii!! Idan ki ka sake cewa tak wlhy sai kin sha mamaki yau.†da ga haka ya juya yay ficewarsa ya barta a toilet É—in. Tsabar rasa abinyi sai kawai ta saki kuka, hawaye sosai tayi kafin tayi alwalar, koda ta fito batako kalla inda yake ba tai ficewarta, shima sai bai ce da ita komai ba dan ya riga ya kai waya É—akin nata ya ajiye ta yanda in ma batai ba zai gani. Sai dai kuma Alhamdullah, koda ta shiga can É—in sallar tayi dan da gaske dama batayi magrib É—in ba, Azhar da la'asar dai da yake aunty Saliha na gidan tare ma sukayi. Bayan ta idar ta jima zaune a wajen tana tunani akan nasihar da Aunty Saliha ta sake mata musamman akan ibada. Da ga baya ta sake fitowa falon, anan ta sameshi kwance. Inda lap-top É—inta ta ke ta koma ta zauna ta cigaba da harkar gabanta batare data kulashi ba, shima kuma baice mata komai ba yay shiru ne ma a kwancen kamar mai barci yana tunanin abinda ya faru a yinin yau É—in gaba É—aya. Sai da ta shagala a abinda take yi yaje ya É—akko wayarsa, koda ya duba ya ga tayi sallar sai ya sake samun nutsuwa..........âœï¸
    Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 7ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
.........Haka abubuwa suka cigaba da tafiya a gidan Smart da É“angaren kwallonsa. Dan matuÆ™a ya dage da training da kuma kiyaye cin abubuwa tare da miÆ™ama UBANGIJI al'amuransa, harda azumin kwana uku yayi da sadaka. Maganar shaÆ™uwa ko hirar arziÆ™i kam tsakaninsa da Lulu babu. Babu mai shiga sabgar wani ta É“angaren lalama, garama shi wani lokacin yakan É—an tsokaleta ita kuma tai masifa. Idan lokacin salla yayi kuma ko baya gidan zai tura mata text message akan tayi dan ALLAH, tai ma mahaifiyarta kuma addu'a. Sosai yake karya lagonta da hakan shiyyasa a yanzu kam Alhamdullah da wahala kaga lokacin sallar ma ya shige bata tashi tayi ba, daya turo saÆ™on ko batai niyya ba zata tashi taje tayi. Idan kuma yana gidan zai mata magana nan ma tayi. Girki ma dai kullum da rigima ake yinsa na safe dana rana idan har yana gidan, idan kuma ya fita na safen kawai akeyi ita dama ba damuwa tai da abincin ba, da dare kuma shi dama ba damuwa yay da cin abinci ba balle yanzu da yake sake Æ™oÆ™arin daidaita jikinsa. Kayan shaye-shaye dai duk da ya toshe ko'ina da samunsu hakan baisa zuciyarsa ta samu nutsuwa ba, a duk motsinta kaffa-kaffa yake yi, ita kuma duk da ta daure kwana biyu a cikar kwana na biyar sai da yanayinta ya canja saboda matuÆ™a take buÆ™atar su, ta rage kulashi suyi faÉ—a, ta zama shiru-shiru, wani lokacin ma yakan shigo gidan ko É—akinta ya ganta zaune a lungu ta takure kanta cikin damuwa koma tana kuka, sosai take bashi tausayi, dan haka a duk sanda ya ganta a yanayin sai ya zauna yayta mata nasiha ne cikin tausasawa, yana kuma Æ™oÆ™arin bata ruwan addu'oin da malam ya basa a É“oye batare da ta sani ba, magani ma na nan zuwa da malam É—in yace zai haÉ—a mata inasha ALLAH akan shaye-shayen dai. A É“angaren karatu da suka fara duk da dai suna É—an kai ruwa rana wasu lokutan kafin ayi, Alhamdullah ya fahimci tana ganewa, dan a É—an tsukun kwanakin a É“angaren salla abubuwa da yawa Lulu ta gyara, tana kuma Æ™oÆ™arin riÆ™e addu'oi. Nacin fita aiki kuma bata daina ba, shi kuma bai kulata ba. Washe garin da suka cika kwana biyar ranar asabar Aunty Bilkisu da Hawwah da Maryam da Asma'u sukazo gidan, ranar yana gida bai fita ba, dan dama fitar tasa dai ba ko yaushe bace ba, ba kuma ta wuce zuwa gidansu, stadium training, sai É—an kaikawo akan case É—intan nan na yarinyar nan da yake mata bincike tunda su Uncle Yousuf sun shigar da Æ™ara court da mahaifiyar yarinyar da kuma taimakon Æ´an sanda. Duk sanda ya fita kuma baya yarda ya daÉ—e idan yayi tunanin ya barta ita kaÉ—ai dan a É—an zaman sun nan ya fahimci bata son kaÉ—aici, sai kuma sauran kai kawon da suke da su Coach akan batunsa na abubuwan da suka saura dole da kansa zaiyi. Tarba suka samu ta muntunawa ga Lulu irin wadda su kansu basuyi zato ba, sai suka ji Æ™aunar matar É—an uwan nasu ta Æ™ara mamayesu. Fargabar da suke ta wataran zai iya aure matarsa ta rabasu da shi ta fita fit a zuciyarsu. Yana É—aki yana barci hayaniyarsu ta tada shi, bai san kosu waye ba dan haka ya tashi badan barcin ya ishesa ba ya fito, turus yay yana kallonsu, sai bin Lulu daketa faman murmushin yake da kallo, a zuciyarsa kuma yana wani tunani, musamman akan maganar malam da yace tana da É“oyayyun halaye masu Æ™yau, to amma miyasa masu aikin gidansu su take musu duk yanda taso? Kodan su suna a Æ™arÆ™ashin ta ne take gani, na biyu ya fahimci bata son kaÉ—aici sam, dan koshi idan zai fita gidan sai ya ga yanayinta ya canja zuwa damuwa koda bazatace komai ba. Maryam ce ta fara hangosa, cike da jin daÉ—i ta ce, “Yaya Hydar sannu da fitowaâ€. Da kai ya amsa mata, yayinda sauran ma duk suka juyo harda Lulu, sai dai kallo É—aya ta masa ita ta É—auke nata idon. Falon ya Æ™araso ya zauna, cikin girmamawa ya gaida Aunty Bilkisu, su Hawwah ma suka gaida shi. Daga haka aka É—an cigaba da hira sai dai basu yarda sunyi wani abinda Lulu zataji a ranta kamar ita barece a cikinsu ba. Wannan abu yayi matuÆ™ar tasiri a zuciyarta, sannan yanda suke girmama juna da shaÆ™uwarsu da soyayya mai Æ™arfi ya matuÆ™ar sata jin kewa da jin inama itama haka take da nata Æ´an uwan. Ta kasance cikin farin ciki a wannan yinin, dan ko abinci Maryam da Hawwah ne sukayi basu barta tai komai ba sai Asma'u data gyara gidan, dan wannan shine kema Lulu wahala kuma duk da bata Æ™aunar Æ™azanta. Ta masa maganar mai aiki yaÆ™i ce mata komai, shi kuma ba mai aikin ce baiso ba duk da yasan kuÉ—in biyanta ma a garesa wani abu ne daban, tsoron kar mai aikin ta zame mata Æ´ar aikar sayo Æ™waya yake shiyyasa yay mata shiru. A lokacin da su Hawwah ke kitchen suna girki Aunty Bilkisu kece masa. “Hydar baka ganin ya kamata kayi haÆ™uri Hawwah ta koma É—akinta, mijinta na sonta sannan yana Æ™oÆ™arin sa a kanta, mahaifiyarsa kuma shima tafi Æ™arfinsa ne. Tunda su Abba sun bar komai a hannunka ya kamata ayi haÆ™uri ta koma haka nan ai anja masa kunne, ALLAH tausayi yake ban kullum yana cikin zaryar zuwa gidan nan, ga Nasreen dake damunta kullum ita Abbanta Abbanta, ita kanta Hawwah dauriya kawai takeyi da kuma bazata iya Æ™etare maganarka ba, kayi haÆ™uri ka duba ta koma gidan mijinta kodan halin Umma da bata gajiya da abin faÉ—a kullum ta ALLAH a gidan nan kan Hawwah, haÆ™urin shi yafi komai ko ya kikace Mawaddat?â€. Ta Æ™are maganar tana duban Lulu da ke saurarensu. Jin jina kai Lulu tai da faÉ—in, “Hakane Aunty, to amma miya kawo matsalar har haka? Sa'id É—in bashine na gani a wajen bikin nan ba anata kai da kawo da shi?â€.
   “Shine fa.....†nan ta kwashe komai ta sanarma mata. Sosai Lulu tai mamaki, sai dai kuma hakan baizo mata baÆ™oba dan sun sha cin karo da irin waÉ—an nan case É—in wasu ma sai iyayen mijin sun illata yaran saboda Æ™iyayya, wasu ko yaranne fitsararru, sannan kakarsu Dada ita kanta fitinanniyar mace ce da tasan tana Æ™untatama matan kawun nanta matuÆ™a. Duban Smart tai da faÉ—in, “To amma shi miyasa bazai zauna yay magana ta fahimta da mahaifiyarsa ba, ko kuma yabar gidan nake ganin hakan zai basu masalaha idan basa ganin juna ai Aunty, ko za'a dinga samun matsalolin ba kamar suna zaune waje É—aya baâ€.
    “Kowama haka yake faɗa Mawaddat, to amma maman ce taƙi yarda wai zasu barta a kaɗaici. Shi dai mijinki shi ya kamata yay haƙuri a duba kodan Sa'id ɗin†ta ƙare maganar da kallon Smart.
     Shiru kamar bazaice komai ba sai kuma ya É—an nisa. Cikin É—age kafaÉ—a ya ce, “Aunty Bilkisu bawai zaman nata nima namin daÉ—i bane, sai dai kuma bazan barta ta koma ba haka salin alin, inada shiri nima dan dolene sai mahaifiyar Sa'id ta fahimci kuskurenta ko kuma ya raba musu gidan, inada hikimata na tsaiwa akan hakan dan har mahaifinsa ya dawo sannanâ€.
   Cikin gamsuwa Lulu ta ce, “Hakan da yayi É—in shine dai-dai, inba hakaba komawar tata haka nan babu wani mataki zai cigaba da bada damar faruwar fiye da haka a tsakaninsu......â€
   Haka suka cigaba da tattaunawa har su Hawwah suka kammala girki. Wani abu daya saka Lulu farin ciki lokacin da su Aunty Bilkisu sukai zaman cin abincin da suka zuba a tray É—aya sai ta tsaya kallonsu musamman da Smart ya É—akko nasa spoon yazo tsakkiyarsu ya zauna yana faÉ—in “Ni sai a ware niâ€. Abune da bata taÉ“a gani a gidansu ba, itama saita tura baki gaba tace, “Ni baku so naci da ku saboda ba Ammah ta haifoni baâ€.
   Da sauri aunty Bilkisu ta kamo hanunta ta zaunar kusa da ita kusa da Smart kuma É—an shine a gefenta, har suna haÉ—a baki ita da su Hawwah wajen faÉ—in, “Karkisa Ammah ta dafamu a tukunyarta da jin wannan kalamaiâ€. Murmushi tayi kamar yanda shima Smart ke kallonta ta Æ™asan ido yana yi, sai tana mai jinta kamar sabuwar halitta a yau. Lulu da bata damu da abinci ba yau kam saita saki jiki ta É—an ci. Da son neman magana Smart ya É—auki naman gabanta, hararsa tayi da tura baki itama ta É—auki na gabansa batare da tace komai ba, kallonta yay yana É—an zaro ido ya ce, “Miye kuma na É—auka min nama Madam?â€.
    “Nawa daka fara É—auka naka neâ€.
  Itama ta faÉ—a cikin É—am murguÉ—a baki kaÉ—an. Kai kawai ya jinjina alamar zan rama, su dai su Hawwah sai gimtse dariya suke. Can Lulu ta sake É—aukar naman gaban nasa ta rufe da abinci, sarai ya ganta sai baiyi magana ba sai da ya shammaceta ta É—akko zata kai baki caraf ya É—auke sa daga spoon É—in nata ya lunÆ™uma baki. “What!†ta faÉ—a tana kallonsa, miÆ™ewa yay da mata gwalo yabar wajen dan ya Æ™oshi daman. Da gudu su Maryam suka tashi suna dariya. Lulu ta dubi Aunty Bilkisu kamar zatayi kuka ta ce, “Aunty kin ganshi ko? Shi baiso a zauna lafiya kullum sai anyi faÉ—a yake jin daÉ—iâ€.
   Aunty Bilkisu dake danne dariya da Æ™yar ta harari Smart da dafa Lulu da itama ke hararsa ta ce, “Kinga Æ™anwata barsa zamu rama. Tsarabar dana kawo takine ke kaÉ—ai nama fasa bashiâ€. Murmushi tai da sake hararar Smart itama ta masa gwalo da faÉ—in, “7-6â€. ƘwaÉ“e fuska ya É—an yi shima da yin Æ™wafa ya ce, “Ki jira game over. Aunty kuma gaskiya ba haka akeyi baâ€.
   “To ni haka zanyiâ€. Cewar Aunty Bilkisu tana hararsa. Sai kuma ta kalla Lulu, “Kin san wani abu shi fa dama Hydar akwai zura tun yana yaro, idan aka zuba abinci aka bashi sai yace shi bashi yake so ba na Ammah yake so, idan aka bashi sai kuma yace (Ni wannan ina co) ya sake nuna namu, nan ma a bashi sai ya sake nuna wani nanma yace shi wannan yana co, hankalinsa bazai sake kwanciya ba sai yaga kaf abincin an tara masa gabansa zai bar kunnen kowa ya huta kuma fa ba ci zaiba.
    “Kai aunty miye na faÉ—a mata kuma†Smart ya faÉ—a cikin shagwaÉ“a. Aiko mi Lulu zatai inba dariya ba. Sai ta kallesa tace “Ni wannan ina co†ta Æ™yalÆ™yale da dariya. Sai da takai ya kwashi filos ya fara jefa mata ta tashi da gudu tana cigaba da faÉ—a. Dole aunty Bilkisu ta dara itama tana sake jin Æ™aunar Lulun a ranta. WaÉ—an nan abubuwan sun matuÆ™ar É—auke ma Lulu kewa da sakata a farin ciki a wannan yinin, yayinda gefe É—aya ta takurama Smart da faÉ—in ‘Ni wannan ina co’ har bayan tafiyarsu. Shima sai abun ya koma bashi dariya dan ya fahimci ta samu abin yi.........âœï¸
   Â
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.