Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 65 of 94
(😂Lulu karki bamu kunya dan ALLAH)
    Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 6ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
.......Dai-dai nan Lulu ta buɗe ƙofar ita kuma waya a kunne ta tana magana da Uncle Yousuf cikin shagwaɓa akan a aiko mata da wayoyinta. Miƙewa Smart yay ya nufosu, sai dai yana isowa Lulu da batama lura da shi ba ta riƙo hannun Asma'u suka shige ciki tana mata murmushi. Turus ya ɗan tsaya yana bin ƙofar da kallo, sai ma ya rasa wane irin tunani zai yi. Sai kawai ya ɗan furzar da isa ya nufi ɗakin daya kwana al'amarinta na ƙara ɗaure masa kai, ya fahimci gane ainahin yarinyar nan sai an shirya.
    Huwaila da ke kallon komai ta cika tai fam, dan ita babu abinda zuciyarta ya bata sai wulaÆ™antata da nuna mata wariya. Wayarta ta É—auka tai kiran Umma, bugu É—aya kuwa ta amsa, daga can cike da zumuÉ—i Umma ta ce, “Ya ya kin É—ebo ko?â€. Sosai Huwaila ta tunzura baki gaba, idanunta akan hanyar corridor É—in nasu kamar zata saki kuka ta ce, “Umma bayan munafukar yarinyar nan itama tazo, gashi can ya jata sun shige É—aki wajen matar tasa sun barni ni kaÉ—ai a falo, dama tunda ya buÉ—en Æ™ofar yake min kallon banza kin san shi dai da baÆ™in halin tsiya, balle yanzu yana ganin ya auri Æ´ar masu kuÉ—i kamar yafi kowa a gidanmu.â€
     Ƙwafa Umma tai da Æ™arfi zuciyarta na sake Æ™untata, cikin fusata da jin haushin lusarancin Huwailar ta ce, “To ke bazaki tashi ki bisu ba. Kije duk ma uwar da akeyi a É—akin ayi da ke. Ki kuma tabbatar kin kwaso min abinda na sakakiâ€. Ƙitt ta yanke kiran batare da Huwaila ta sake samun damar cewa wani abu ba. Tasan hanlin Ummar su sarai akan jarabar tsiya, dan haka ta miÆ™e ta nufi inda taga Asma'u ta shiga. Ba knocking ba komai balle aje batun sallama ta afka musu. Asma'u da ke gyaran gado tai saurin jiyowa, hakama Lulu da ke waya da Sakatariyarta Zainab yanzu idanu ta zubama Huwailar.
    “Kai Adda Huwaila ALLAH har kin ban tsoro shigowa haka ba sallamaâ€. Asma'u ta faÉ—a cikin jin takaici sai dai ta tausasa harshenta. Harara Huwailar ta zuba mata da taÉ“e baki ta nufi sofa É—in bedroom É—in mai azabar Æ™yau da É—aukar ido ta zauna, itama sai Asma'un ta watsar da ita ta cigaba da gyara gadon cikin takaici. Harta kammala ta shiga toilet shima dan ta gyara Huwaila na cigaba da harare-harare, sai dai fa É—akin ya mata masifar Æ™yau, ji take inama a cikin Æ´an É—akinsu ne suka samu wannan duniyar haka.
   Lulu kam tun kallo ɗayan datai mata bata sake ba tana cigaba da wayarta da Zainab da kuma gyara gashinta data kammala busarwa, so take sai ta kammala taji wace ita da kuma dalilin shogo mata ɗaki haka ba knocking. Asma'u data fito daga Bathroom alamar ta kammala ta yafito da hannu, koda ta iso batare da tayi magana ba ta miƙa mata ribbons da yimata nuni da gashinta alamar ta ɗaure mata. Amsa Asma'u tai da murmushi akan fuskarta, ta shaƙi fitinannen ƙamshin da gashin keyi ta lumshe idanu tana tattarosa cikin hanunta. Dai-dai nan Smart ya shigo ɗakin da sallama. Yayi masifar ƙyau cikin wani kwantaccen yadi da ya sake fiddo nagartarsa ta cikakken bahaushen arewacin Nigeria nutsatstse, daga ita har Asma'un ya zubama ido, sai kuma ya ɗan kalla Huwaila da ke gefe ta baje cikin couch tana ta wani faman hura hanci, sai dai shigowarsa ta sata ɗan nutsuwa dan tasan halinsa sarai.
“Ku tashi mu wuce ku kuma ko?â€.
Ya faÉ—a babu alamar wasa tattare da shi. Asma'u ta ce, “To Yaya can gidan zaka kaimaâ€. Kansa ya É—aga mata kawai batare da yace komai ba, amma sai Lulu da ke É—an kwallonsa ta cikin mirror ta juya kujerar tana dubansa da Æ™yau tare da janye wayar kunnenta alamar ta kammala. Kallon ido sukaima juna, kowanne ya janye nashi cike da basarwa. Ƙasa-Æ™asa ta ce, “Please ka barmin Auta anan dan su Afrah ma na zuwa kawo min phones É—inaâ€.  Â
     Zuba mata idanu yay sosai da alamar mamakinta, dan shi dai bai san yaushe ta fara son mutane haka ba da har ma tasan ana kiran Asma'u da Auta. Maimakon bata amsa sai ya dubi Huwaila da Asma'u. Da sauri suka fice dan dama Asma'u ita tayi niyyar yin hakan, Huwaila ce dai dake kallonsu ta Æ™asan ido bata da wannan niyyar. Lulu da ke kallon yanda yaran ke rige-rigen ficewa ta wani taÉ“e baki, “Kai kowa ma sai ka nuna masa halinka ne, jibi yanda yara ke fita kamar zasu ci da kaâ€.
   “Oh ni har wani hali ne da ni kuma wanda ban sanshi ba?â€. Ya faÉ—a cikin É—an É—age gira É—aya da Æ™anÆ™ance idanunsa. Nata tai saurin É—aukewa da Æ™ara taÉ“e bakin ta koma ta juya ga mirror É—in batare data bashi amsa ba. Ƙarasa takowa yay jikin mirror É—in shima ya É—an jingina tare da É—aukar wayarsa ya duba dawa-dawa tai kira. Ganin number Uncle Yousuf da dama yana da ita, data Zainab da itama dai yana da itan dan tun randa ya kaita gida ya amsa saboda wataran. Ya É—an ji nutsuwa dan shikam yanzu ya fahimci sai yayi takan tsantsan, tunda har jiya tai amfani da shi wajen sayo mata Æ™waya batare da ya fahimci komai ba dole ne ya nutsu ya fahimci duk wani dabarun su. Iska ya É—an furzar kaÉ—an da gyara tsaiwarsa da Æ™yau sai kuma ya fara magana a hankali tare da maida hankalinsa sosai ga kallon yanda take tufke jelar gashin bayan ta sharceta da comb. Yana matuÆ™ar son gashi a jikin mace, dan haka natan ke matuÆ™ar É—aukar masa hankali.
    “Zanje na gaida su Ammah na dawo bazan jimaba, sai dai ki sani kar fita ta ta baki damar aikata wani abu daban, dan shaye-shaye babbar hanyace ta maida É—an Adam baya akan dukkanin nasarorinsa da kima da mutuncinsa. A duk inda mai wannan É—abi'ar yake zakaga baida farin jinin al'umma, kowa bai san raÉ“arsa balle huÉ—É—a da shi da ga sanda aka fahimci yanayi. Shi a karan kansa kuma yakan rasa damammaki da yawa na cikin burinkansa ko nasararsa ta duniya da lahira. Misali ga barin salla, da wahala a samu mai wannan É—abi'ar da tsaida salla akan lokacinta, hakan kuma babban naÆ™asu ne ga rayuwa. Karatun Alkur'ani, ambaton ALLAH da sanin mi rayuwa take ciki kota dosa duk dama ce dake kufcewa a hannunsa. Ga É—iya mace in har tana wannan É—abi'ar hanya mai sauÆ™i ce a samu damar keta mata mutuncinta. Shin mi kika rasa a rayuwa na ni'imomin ALLAH da bai miki ba, miyasa ki ka zaÉ“i gode masa ta wannan hanyar? Miyasa kika zaÉ“i sakama iyayenki da wannan tukuycin da duk iyayen da suka fuskanci yaransu nayi basu da sauran nitsuwar zuciya, ki tuna kema uwa ce wataran. Bazance miki ki kiyaye ba, dan ban isa hanaki ba, sai dai ki sani wannan itace É—abi'a ta biyu da bazan É—auka ba bayan barin salla. Ki zauna kiyi nazari. Ga break fast can su Asma'u sunzo da shi. Nima yanzu zan dawo sai na karya a nan É—in, ina son yin abu mai muhimmanci ne acanâ€. Da ga haka ya nufi hanyar fita abinsa batare da ya ko waiwayo ba balle yaga halin da tasirin da maganganunsa sukayi gareta. Lulu da tun fara maganarsa abu ya tokare mata maÆ™oshi ta raka bayansa da kallo wani shegen takaicinsa da mamakin gadarar nan tasa da yake son fara bayyana mata a fili. Wai mi wannan mutumin ke nufi da ita ne? To duk abinda ya shirya ita a shirye take da mafiyinsa su zuba ita da shi a gidan nan É—an halak ka fasa, ina ruwansa da rayuwarta....
   Dawowar Asma'u da kayan shara É—akin ya maidota hayyacinta. Ta kalleta tana É—an waro idanu waje. “Ya barki ne?â€. Cikin zumuÉ—i Asma'u ta bata amsa da “Eh, amma yace yana dawowa zan wuce. Shiyyasa zanyi sauri na shashshare miki aunty dan shifa Yaya baya magana biyuâ€. Yanda ta Æ™are maganar da Æ´ar shagwaÉ“a ya sanya Lulu sakin murmushi. “Uhhm kudai autocin nan ko'a ina sai kun nuna hali. Kinga bar batun sharar nan karki wahal da kanki nace su Amrah su taho da Iya tabawa zatazo duk ta gyara ko'inaâ€.
    “A'a aunty ki kirasu ma kice su barta basai sunzo da ita ba. Zan gyara yanzun nan dan nan ma sharane kawai da gogewa ya rage. Nifa kin san ina son aikin gida sosai, shiyyasa su Aunty Bilkisu idan suna jin lalacinsu har zuwa suke su É—aukan na musu hutu koda Ammah zataita Æ™orafi ne sunta lallaÉ“ata kenanâ€.
   “Uhhmm sannu busy body ke baÆ™ya gajiya ma kenan. To nidai bazakimin aiki ba, amma zanso Ammah ta bari ki dawo mana nan kinga na samu abokiyar hira ko.â€
     “Tab aunty Ammah bazata bari ba, ba irin nacin da mijin Aunty Bilkisu baiyi ba kan a basu ni amma taÆ™i ita da Abbah. Amma ke Æ™ila taji kunyarki ta yarda ko weekend nake zuwa dan tasan dai halin Yaya bai son yin magana sai yaso, kina buÆ™atar abokiyar hiraâ€.
   “Zan gwada na gani to, ALLAH yasa su bani, bari na shirya naci abinci ina É—an jin yunwa kaÉ—an-kaÉ—an, kema ajiye kayan sharar nan Pleaseâ€.
   Magiya Asma'u tai taima Lulu har sai da ta barta tai aikin nan, dan danan kuwa ta tsaftace ko'ina ta baza kayan Æ™amshi. Itako tana zaune a falo tana tsakurar abincin da su Asma'u suka kawo, sai dai tana buÉ—e wanda Huwaila ta kawo ta maida da sauri ta rufe saboda jin Æ™amshin korin da aka zambaÉ—a a miyar fankason ta dakar mata hanci, sam ita bata Æ™aunar kori a abinci shiyyasa ma idan har an saka batacin sa komai son da take masa. Sai kuma ma akai rashin sa'a fankasu ba abincinta bane shima, duk randa ma Iya Tabawa tayisa a gidan to ita sai dai ai mata wani abun, hakama idan taje gidan Uncle Yousuf ko gidan Grandpa ta tarar anyi bataci, bata son su shi da tuwo sam musamman miyan yauÆ™i ko wani taga yanaci sai zuciyarta ya hau tashi. Wanda Asma'u ta kawo ta buÉ—a, a hankali ta saki ajiyar zuciya ganin lafiyayyen yam balls ne a kular farko, ta biyu farfesun naman kaza ne yanata tashin Æ™amshin attaruhu da albasa. Sai jug irin mai riÆ™e zafi É—in nan É—auke da kunun gyaÉ—a da yay Æ™yau yanata Æ™amshi har da su Æ™wa-Æ™wa a cikinsa. Sai shayi a flaks da yaji kayan Æ™amshi shima, anan kam ajiyar zuciya ta sauke harda sakin guntun murmushi ta zuba kunun gyaÉ—ar da farfesu kaÉ—an ta fara tsakura tana bin Asma'u da keta aikinta a nutse da kallo da sauraren labarin da take bata akan yanda suke matuÆ™ar jin daÉ—in abinda take yi game da case É—in fyaÉ—e. Haka kawai jin Æ™aunar yarinyar take a ranta, balle jin abinda take faÉ—a na yanayin da suke shiga na jin daÉ—i har itama tana burin zama lawyer kamarta........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.