Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 30 of 94
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 2ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
........Kaɗan ya rage ta bugama motar gabanta. Tai saurin take birkin da ƙarfi. Ganin yanda mai motar ya dakata shima da alama fitowa zaiyi ya sata sake mata key tabar wajen da saurin dan ba wannan ne a gabanta ba yanzu. Tana hango zagin da mai motar ke mata cikin daƙuwa da wanda wasu ke mata na gefen titi. Oho basu bane a gabanta. Furucin Uncle Yousuf ne ke mata kai da kawo. Ji take kamar ta koma su canja asibiti sai dai ta riga kuma tace su Sha'aibu su sameta a can. Sannan yanda uwar ke nuna yarinyar na cikin mawuyacin hali maganar sakaci daga gare ta ma bata taso ba, dan a yanzu al'amarin su drivern ta ya shafe a zuciyarta yanda zata yaga rayuwar mijin matar nan kawai take ƙullawa. A wannan fanin ba'a gayyacesu ba ma taka rawa suke balle sune da bikin. Ai rawa sai kalar wadda sukaso takawa wlhy.....
     “Da gaske dai Uncle You na asibitin nan? To mi ha kawoshi?â€. Ta faÉ—a a fili tana parking idanota akan motar Uncle Yousuf dan babu ta yanda za'ai motocin gidansu su É“ace mata. Cikin rashin sanin abinda take buÆ™atar sani ta fito a motar. Sai da ta leÆ™a motar Uncle Yousuf ta tabbatar babu kowa a ciki sannan ta bar wajen zuwa cikin asibitin. A reseption kuwa suka haÉ—u da Uncle Yousuf É—in. Karan farko a rayuwa taji bazata iya haÉ—a ido da shi ba, tsoron ma haÉ—uwar tasu take yi. Musamman kuma yanda ya zuba mata idanun nasa duk sai ta nema daburcewa. Shi ya fara É—auke idanunsa da ga kanta yana kai wayarsa da aka kira kan kunne. Hakan ya bata damar nufar inda ake yankar kati, sai dai kuma fa ko sunan yarinyar bata sani ba ma fa ashe. Cikin É—an yarfar da hannu da juyawa gaba É—ayanta tai facing Æ™ofa ta ke faÉ—in “Ouhhh! Saurin banza ma ashe nakeâ€. Dai-dai nan motar Æ´an sanda mai É—auke da matar nan da yayarta da yarinyar suka iso. Shigowar Musa ya sata sauke ajiyar zuciya, shi ya sanar da nurses cewar akwai mara lafiya a waje kafin ya Æ™araso gareta. Kallo É—aya da Lulu taima yarinyar ya sata rumtse idanunta takalminta har yana gullewa sai da ta dafe kantar reseption É—in.......
     “★“★ ∆ ★â€â˜…â€
    “Ranka ya daÉ—e yaron nan fa daka tada hankalinka kansa ba wani É—an kowa bane face wani mutum da ake kira Malam Mika'il Idris Mawashi a anguwar fagge. Shi kansa mahaifin nasa a iya layin nasu kawai aka sanshi balle shi. Kuma da gaske drivern yarinyar ne kwata-kwata bai Æ™ulla sati huÉ—u da fara aiki gidan Alhaji Isma'il JiÆ™amshi b.....â€
   “Kace Alhaji wa?!!â€.
  Alh. Baita yay saurin tarar numfashin yaronsa da suke kira Goga a kamar razane da jin sunan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Bashi kawai ba hatta Hon. Nakowa da ke tare da shi dan tunda suka baro gidan MM Atik Kumo da ya basu aro anan gidan hutawar Alh. Baitan suka ƙarasa kwanan nasu. Shine tun da farar safiya kuma suka nemi babban yaronsu na bangar siyasa Goga suka sakashi binciko wanene Smart ta hanyar ɗan bayanai da suka samu ga Nadiya wadda itama ta samune ga Lulu randa taje saloon shagonta....
    “Alhaji Isma'il JiÆ™amshi nace Æ™warai da gaske oga. Dan shine mahaifin ita yarinyar ma ai.â€
   “Babbar magana Æ´arsa ta cikinsa?â€. Hon. Nakowa ya faÉ—a wani irin abu mai ma'anoni da yawa na tsirga masa tun daga saman kai har tsakkiyar Æ™afafunsa. Cikin tabbatarwa Goga ya gyaÉ—a masa kai. Tare da masa Æ™arin bayanin da zai gaskata hakan duk da shi bai san dalilinsu na jinjina sunan ba tunda shi dai a É—azun yaga hankalinsu akan yaron yake ba ita yarinyar ba.
   “Kaga jekaâ€.
Honorable Babale ya faÉ—a cikin katse masa tunani. Dai-dai Goga na miÆ™ewa ya sake faÉ—in ka jiramu a waje nan zamu nemeka.†shi dai da to ya amsa musu ya fice kamar yanda suka buÆ™ata. Yana kuwa fita Hon. Nakowa ya firta, “TabÉ—i jan inji mata. Dama Æ´ar iskar yarinyar nan É—iyar Isma'il JiÆ™amshi ce? Haba shiyyasa bata zubar a banza ba.†sai kuma ya wani Æ™yalkyale da dariya alamar hakan ya masa daÉ—i Æ™warai da gaske. Shima Alh. Baita dariyar ya fara. Sai kuma ya buga Æ™afa da faÉ—in, “In kere na yawo zabo na yawo tabbas faÉ—ar masu iya magana watarana za'a gamu. Honorable Please kira mana Hon. Misau mana. Dolene ai wannan shagalin da shiâ€.
   “Ƙwarai ma kuwaâ€. Cewar Hon. Nakowa yana wani bula-bula da babbar riga wajen laluben wayarsa. Cirota yay tare da yin danne-danne ya kai kunnensa......
   Tofa masu karatu wata sabuwa kenan. Mi'a haɗin Daddy kuma da su Honorables?🤔.
     ∆★∆★∆★∆
  Tun bayan wucewar É—an nasa yake ta faman kai kawo a lafiyayyen office É—in nasa. Abubuwa da yawa ne ke masa sukur-sukur a brain game da buÆ™atar autan nasa a karo na biyu. Tabbas zai fi kowa farin ciki da Æ™ulluwar wannan auren dan koba komai dai Mawaddat É—iyar Æ´ar uwarsa ce Mawaddat. Ƙanwarsa mafi soyuwa garesa a duk cikin Æ™annensa. Wadda yasha bama sirrin al'amuransa batare da tunani ko jin É—ar ba har ALLAH ya É—auki ranta. Zai kasance mai yin farin cikin ganin jininsa da nata sun zama abu É—aya. Sai dai kuma matsalar itace Isma'il. Isma'il shine babban bakangizo mai razani da ya gitta a tsakkiyar wannan Æ™aunar zumunta mai cike da ababen burgewa ga duk wanda zai iya jin asalinta da wanzuwar ta. Dan tarihin ratsawar Isma'il a cikin labarinsa dana Æ´ar uwarsa uwa É—aya uba É—aya ya juya akalar waccan Æ™ayataccen labarin zuwa É—imautacce mara armashi a yanzu. Ata wani fanin kuma kamar zai zo da sabon armashin kansa da kansa dan labarin zai canja ne da ga na shi da Æ´ar uwarsa zuwa na shi da Isma'il Ibrahim JiÆ™amshi mijin Æ´ar uwarsa da Æ´arsa. Ƴarsa da yasan yana matuÆ™ar Æ™auna fiye da komai a rayuwa. Kafin yau da faruwar matsalar farko na tusguÉ—ewar aure tsakanin Mawaddat da Tajuddeen labarin ba a haka ya tsarashi ba, sai dai yana ganin wata dama ce da zai masa editing dan ya zauna dai-dai da zamanin nan na 2023 a ajiye wancan Æ™arnin dan ya koma tsohon yayi. Ya wani lumshe idanu da dunÆ™ule hannunsa ya ce, “Yess!! Sulaiman Sufi Ado Garko kai mai nasara ne akoda yaushe. Isma'il JiÆ™amshi sabon game, sabbin players and sabon stadium ka zama cikin shiriâ€.
    Wata sabuwar kuma dai🤔.
★★★★★
     Duk da a yanda take jin matuÆ™ar gajiya bata huta ba har sai da doctors suka rufu akan yarinyar nan da lamarinta ya taÉ“a duk wanda ya ganta a cikin asibitin. Dan hatta Uncle Yousuf tuni ya ajiye batun takaicin Lulu gefe da shi akai komai na ganin likitoci sun tsaya a kanta. Abin tausayi ita uwar ma zuciyar ta bushe ko kukan zahiri ta kasa sai na zuci. Ganin komai ya natsa dan ana neman uku na rana ma Uncle Yousuf ya kai dubansa ga Lulu da alamunta suka nuna gajiyarta matuÆ™a. Dan sai faman yamutse fuska take. Tausayi ta bashi, dan haka ya cigaba da kallonta a kaikaice cikin tausasawa da mata addu'ar shiriya akan halayenta marasa Æ™yau. Isowar Ahmad wajen ta sakashi maida hankali garesa. Fuskarsa da murmushi yay ma Lulu magana, amma sai ta amsa masa a É—an É—age. Bai damu ba dan ya santa ya san halinta. Hasalima ya taÉ“a nuna sonta amma ta taka masa burki lokacin tana farkon dawowarta da ga Uk. Uncle Yousuf da yanda tai masa É—in ya bashi takaici ya harareta, sai kuma ya maida hankalinsa ga Ahmad É—in da ke faÉ—in, “Yaya ya farka, doctor É—in ma ya sallamemu dan ya matsa zaije gida. Kasan Mawashi fa sam bai son asibiti.â€
    Murmushin Uncle Yousuf yay, cikin yanayin tsokana ya ce, “Kai haba kamar wani yaro ko maceâ€.
     Dariya Ahmad yayi, dai-dai nan Smart ya fito a wani ɗaki da ke kusa da inda suke. Coach riƙe da hanunsa kamar wani ƙaramin yaro sai ɓata fuska yake. Dan da gasken fa bai son asibiti shi sam a rayuwarsa. Kuma bai san allura. Yanzu ma ba ƙaramar badaƙala akasha ba kafin ai masa shine ma Ahmad yay fushi ya fito. Ilai kuwa hararar Ahmad ɗin yayi tare da ɗauke kansa duk a lokaci guda, cikin rashin sa'a ya saukesu akan Lulu da tai kicin-kicin da fuska saboda kasancewar Ahamd a wajen, ita ala dole kar a kawo mata raini, dan duk wanda ya taɓa furta cewa yana sonta ko ya nuna basa ƙara shan inuwa ɗaya kuma. Ƙoƙarin janyewa yake sai kuma yay dai-dai da ɗagowarta cikin shirin miƙewa tabar wajen. Ta wani yamutse fuska fiye da yanda take sai kace wadda taga kashi. Shima ƙara tsuke tashi fuskar ya ɗanyi tare da ɗauke kansa gaba ɗaya irin bai ganta ɗin nan ba ma....
     “Ga Aliyu nan babu lafiya sai ki masa sannu. Dama ina son ki gama da wannan kai kawon ne muje ki dubashi ashe ma zasu sallamesa yanzuâ€. Uncle Yousuf ne yay maganar cikin katse hanzarin Lulu dake niyyar barin wajen abubuwa masu yawa na mata kai da kawo musamman ganin drivern nata a nan. Dakatawar tai, sai dai ta kasa cewa komai sai É—an hararsa da take Æ™asa-Æ™asa.
   “Wai nikam bada Mawaddat nake ba?!â€. Uncle Yousuf ya faÉ—a cikin É—an kaushin murya dan ya san taurin kanta na tsiya da gadara. Sosai taji haushin hakan, amma babu yanda zatai dan Uncle Yousuf ne. Ta É—an sake É—agowa ta kallesa, a taÆ™aice ta furta, “ALLAH ya bada lafiyaâ€.
    Coach ne ya amsa da “Aminâ€. Cikin murmushi. Shi kam a zuciya ya amsa mata. A zahiri kam ya É—auke kansa gefe kamar bai san da shi take ba. Sosai ta sake tunzura da salon rainin nasa. Tana mai tabbatar ma kanta a zuciya sai ta koya masa hankali da sauke masa wannan girman kan nasa. Batare da ta sake kallon kowa ba ta ce, “Uncle You ni na koma Office. Uncle Hameed ka gaidamin Aunty Rukayya sai nazo gaishetaâ€.
    Coach yay ɗan murmushi da faɗin, “Zan sanar mata idan da gaske kike Daughter. Dan na sanki ke da sabgoginki marasa ƙarewa.†karan farko da ta saki sassanyan murmushinta da kan ƙawata ƙyawun fuskarta, sai dai batayinsa sai ta gadama. Kai Ahmad da zuciyarsa tai wani irin tsargawa ya ɗauke gefe. Dan Lulu cikakkiyar mace ce da kan iya jan hankalin mafi yawan maza musamman irin matasanmu na yanzu masu fifita ƙyale-ƙyale ga mace fiye da nagarta. Sai kuma ka kwasa ka kai gida ka samu fanko ce ko addininta bata sani ba sai duniyar kawai aka saka a gaba da son birge al'ummar cikinta....
    Suma a tare suka fito su huÉ—un, Coach da Ahmad da Smart suka shiga motar Ahmad da ya koma ya É—akko. Uncle Yousuf kuma ya shiga tasa motar dan Lulu kafin su fito ma har ta bar asibitin. Babu wanda ya sake bi takanta. Godiya Smart yay ma Uncle Yousuf sosai tare da su coach É—in ma gaba É—aya. Da ga haka kowa yaja motarsa. Har gida suka kaisa. Ahmad yay masa rakkiya har cikin É—akunan kasancewar ba baÆ™onsa bane É—akin dama. Bai wani zauna ba saboda Yayansa dake jiransa a mota. Yay masa ALLAH ya Æ™ara lafiya ya tafi.......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.