Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 29 of 94
  Kusan a tare Uncle Yousuf da Ahmad suka iso wajen. Kowanne ya fito a motarsa da sassarfa zuwa inda suke zagaye da Smart da ke kwance a Æ™asa kansa bisa jikin coach da ke faman shafa masa ruwa yana fatan ya farfaÉ—o, dan bai son su kai shi gida a wannan yanayin musamman daya tuno irin tashin hankalin da Ammah ta shiga last da abin ya faru da shi. Har rige-rige ake tsakanin Uncle Yousuf da Ahmad, sai dai kowanne ya samu nasarar kai hannunsa jikinsa. Ganin yanda aketa faman saka masa ruwa babu alamar zai farfaÉ—o Uncle Yousuf ya cema coach “Hameed muje asibiti kawai dan banga alamar zai farfaÉ—o ba a hakan nanâ€.
    Cikin damuwa coach ya dubesa shima da bashi amsa da “Yousuf zuwa asibitin nan babu abinda zai canja. Dan mun gwada yin hakan a baya sai dai mu gama zaman banza dan su amsa É—aya ma suke bamu zuciyarsa ta tsaya da aiki. Al'amarin nasa ne fa kamar abin sihiri gashi nan dai. Gida kawai ya kamata mu kaisa duk da gaskiya hakan na sakani fargaba dan tayarwa iyayensa hankali kawai zamuyiâ€.
    “Gaskiya kar a kaishi can Brother†Ahmad ya faÉ—a cikin damuwa. Bai jira cewar kowa ba ya cigaba da faÉ—in, “Mizai hana muje wajen mutumin nan da ya taÉ“a bashi magani sanda abun ya takura masaâ€.
   “Shawara mai Æ™yau Ahmad, da ni duk nama rikice wlhy hakan bai zo min a rai ba. Kunga ku kamashi kusa a motaâ€.
  A bayan motar Uncle Yousuf aka saka shi kamar yanda ya buÆ™ata, shi da coach suka shiga gaba Ahmad a baya ya riÆ™e Smart. Kai tsaye Æ™ofar ruwa suka nufa, gudun da coach keyi ya sakasu isa cikin Æ™anÆ™anin lokaci. Gidane irin na talaka mai Æ™aramin Æ™arfi, sai dai da ga waje shafe yake da siminti tsaf da shi da milk É—in fenti. Da ga gaban gidan kaÉ—an islamiyya ce ta Æ™anan yara da keta karatu kasancewar akwai ta safe zuwa Æ™arfe É—aya. Tsaiwar motar ta saka wani saurayi da ke tsaye da ga jikin barandar Islamiyyar matsowa garesu yana musu sannu. Basu wani tsaya jan maganar ba suka buÆ™aci ganin Malam. Kafin ya basu amsa sai ga malam É—in ya fito da ga gida..........âœï¸
    Â
_Yau dai Smart ɗin ku ya ɗan bani tausayi🥲_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 2ï¸âƒ£8ï¸âƒ£
_Ya rabbi ka gafartama *Sheikh Abubakar Giro Arugungun*. Ka yafe masa kurakuransa, alkairan da ya isar garemu na wa'azantarwa da koyarwa kasa ya amfanar da mu duniya da lahira. ALLAH ya albarkaci zuri'arsa. Suma iyayenmu ALLAH ka gafarta musu, damu baki É—aya ðŸ˜âœï¸_.
........Wata nannauyar ajiyar zuciya Smart ya saki mai Æ™arfin gaske lokacin da malam ya shafa masa ruwan addu'oi da yayi tofi a ciki, sautin karatun suratul Naazi'aat da É—aliban malam ce ta fara shiga cikin kunnensa da wani irin Æ™arfi tamkar a iya cikin kunnen nasa akeyi. Ya sake sakin ajiyar zuciya sai kuma ya kai hannunsa ya dafe goshinsa dan kansa wani irin ciwo yake kamar zai tarwatse. Uncle Yousuf ne ya fara ambatar sunansa, dan haka ya sake yunÆ™urin buÉ—e idonsa a karo na biyu sai dai ya kasa. A rikice duk suka dubi malam. Ya karkaÉ—a musu kansa da faÉ—in, “Kamar yanda na faÉ—a muku tun wancan karon ku sake jajircewa wajen addu'a da sadaka akansa, dan al'amarin nasa akwai ruÉ—ani kamar na sihiri mai Æ™arfi. Sai dai ban tabbatar ba dan UBANGIJI shine kawai masanin gaibu. Amma gaskiya al'amarin nasa yana nuna kamar bugewar junnu ne. Na fara baku ruwan addu'oi a wancan karon amma sai aka daina zuwa a karÉ“a kwata-kwata, dama ba komai bane face addu'oin karya sihiri wanda ya kamata ma ace duk musulmi kan dingayi a gidansa domin shi da iyalinsa koda lafiya lau ake dan rayuwa kake baka san mike biye da al'amarin ka ba. Koba sirihi akwai baki (kambun baka) da yafi sihiri kaifi a wasu lokutan. Koda ma bazaku juri zuwa nan É—in a karÉ“a ba to ku dage da yi masa a gida dan ALLAHâ€.
   A tare suka amsa da “In sha ALLAH malam†sai kuma suka ɗora da godiya. Ganin yanda Smart keta faman jujjuya kansa malam ya ƙara masa addu'a tare da basu umarnin kaisa asibiti mafi kusa. Godiya sukai masa dan a wancan karon ma haka yay musu. Suka ajiye masa sadaka shi kuma ya basu ganyen magarya da ayoyin da zasu karanta da ga cikin Alkur'ani mai girma. Kai tsaye asibitin suka nufa kuwa, inda aka bashi gado dan a kallo ɗaya idan kai masa dole ne ya baka tausayi, kai kace ba a yanzu kaɗai ya kasance a kwance ba yanda yay sharɓan. Sun bashi taimakon gaggawa har sai da ya samu barci suka ɗan samu nutsuwa. Sun yanke shawarar sanar da gidansu amma sai coach ya ce adai ɗan dakata idan basu sallamesa zuwa yamma bane sai a sanar musun. Hakan ya musu, dan haka sukai yunƙurin fitowa aka barsa da Ahmad ya zauna da shi kafin suje su dawo.....
     ★★★★★
  Duk yanda taso cigaba da gudanar da al'amuran gabanta na wannan yinin hakan sai ya nema gagararta. Ba Æ™aramin tsaya mata a rai abinda drivern nata yay mata yayi ba. Dole ta hakura da tattara bayanan case É—in da zata fara tunkara a safiyar litinin kan dukiyar wasu marayu da wan mahaifiyarsu ke Æ™oÆ™arin handamewa dan zuciyarta a cinkushe take matuÆ™a. Steering da take murzawa ta kaima duka a karo na babu adadi. Ta cije lips da masifar Æ™arfi da faÉ—in, “Sai na koya maka hankali!â€. Kalmace data ambatata yafi sau shurin masaÆ™i. Ga takaicin daren jiya da ma na cigaba da ci mata rai dan a duniya tai masifar tsanar wani namiji ya raÉ“eta da sunan taÉ“ata ko soyayya. Shiyyasa shima Tajuddeen lissafinsa ya shiga cikin jerin lissafin abubuwa masu Æ™una da ajiyewa a kudin tarihinta na wannan yinin da take ganin yazo mata a birkice. Office ta koma, inda ta tarar da baÆ™i kashi-kashi na jiranta. Tabbas batajin magana, sai dai a É“angaren aikinta ita É—in jajirtacciya ce, dan ma É—abi'arta ta shaye-shaye na matuÆ™ar maidata baya a lokuta da dama, dan badan wata hikima ta UBANGIJI ba da Lulu ta jima da daina zuwa wajen aikin ma gaba É—aya ne. Mummunar hallayya mafi muni tattare da Mawaddat shine sakaci da addini, sam babu abinda ta sani akan addininta sai abinda ba'a rasa ba sakamakon karatun ta na lawyer. Bata san a kira salla ta tashi tayita akan lokacinta ba, to idan ma tayin babu maganar yinta a yanda MANZON ALLAH ya koyar damu. (Kuyi haÆ™uri ba Lulu kaÉ—aice a wannan matsalar ba. Wlhy da yawan mutane sunayin salla ne ba'a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. Dan bawai fa muna nufin Lulu bata san salla ba, a'a itama ta tashi ne a yanayin yanda akeyi kawai nakeyi batare da samun ilimin yinta ba kamar yanda da yawa mutane suka kasance. Mafi yawanmu idan da zaman tsayawa akan ibadarmu ta salla za'ai tun daga tsaiwarta ma zamu fara samun gyara. Please Dan ALLAH a wannan gaÉ“ar kowanmu ya nutsu ya kalla sallarsa da kuma bincike akan yaya ake salla kamar yanda MANZON ALLAH S.A.W ya koyar mu gani ko zamu ribantu da gyarawa). Sanda ta gadama take salla, tana kuma yin tane a yanda kawai taga anayi kasancewar karatun addinin ma gatan mahaifinta ya zame mata cutarwar da bata samesa ba. Masifarta kam wannan halitta ce, wani mai haÆ™uri wani saÉ“ani haka. Sai É—abi'ar shaye-shayen data jima tana binnewa wanda har yanzu bamu san tushen farawarta ba ko dalilinsa. WulaÆ™anta mutane da takasu a duk yanda taso kuskuren mahaifinta ne da ya É—orata a turbar komai take so zata samu. A duk sanda ka nunama yaro komai yake so zai samu tofa kansa zai Æ™ara girmane da tunanin yafi kowa daraja da power a rayuwa, sannan akan komai shine sama da kowa. (Iyaye sai mu kula hakan ba soyayya bace)....
    Yanda ta zube wayoyinta da zama jagwab cikin lallausar kujerar office É—in nata ya sake bayyanar da É“acin ranta akan fuska. Hand bag dinta ta jawo tare da fiddo key É—in drower É—in jikin decks É—inta da bata yarda kowa ya taÉ“a saboda abinda take ajiyewa a ciki ta lalubo. Tana Æ™oÆ™arin buÉ—e drower É—in sakatariyarta ya shigo office É—in da sallama. Wani takaici ya sata É—ago idanunta da suka kaÉ—e da gajiya. Sai dai gaba É—aya tama kasa mata masifar da ta saba yi mata a duk sanda tai mata kuskure. Da sauri sakatariyar ta ce, “Please am sorry maa. Wlhy abinda matar can tazo da shi ne yay matuÆ™ar tayarmin da hankali. Jiya ma tazo nace mata ta dawo yau dan kina up 2days sai yau ne zakiyi res.....â€
    Hannu Lulu ta É—aga mata alamar gajiya da saurarenta. Murya a shaÆ™e ta ce, “Zainab ba wanda zan iya saurare a yau koma minene akazo da shi. Ki sake bama duk wanda ya dace sabon appointment banda yau da gobe. Duk case É—in da kuma kika sani bani da buÆ™atarsa a teburina karma mai shi ya shigomin office okâ€.
       Zainab da damuwa ta bayyana ma a fuska Æ™arara ta gyaÉ—a kanta da ke Æ™asa. Sai kuma cikin rawar murya dan har ta fara hawaye ta furta, “Aunty matar can fa mijinta ne yayma yarinyarta da taje agolanci da ita gidansa fyaÉ—e. Kuma yarinyar shekararta tara kwata-kwata. Sunje asibiti da yarinyar amma anÆ™i karÉ“arsu tun jiyan wai sai da Æ´an sanda. Taje police station É—in kuma Æ´an sandan nata mata yawo da hankali. Wlhy bakiga a yanda sukazo da yarinyar ba a jiya da yamma abin babu Æ™yan gani....â€
   Wani irin matse idanu da damƙe kujera Lulu da jikinta ya fara tsumar mazari tayi. (Mawaddat calm down. Mawaddat calm down. Mawaddat calm down). Wani sashe na zuciyarta ke ta ambata mata. Sannu-sannu ta fara sassauta damƙe kujerar da rumtse idanun nata da tai, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya sunyi jajur matuƙa kamar wadda tasha wani abu a lokacin.
“Shigomin da itaâ€.
  Ta faɗa ƙirjinta na ƙara ƙarfin sukar da yake mata. Ga jikinta bai daina tsumar da yake ba. Da ace tanada ilimin addini da addu'a tafi cancanta da harshenta a irin yanayin. Amma sai aka samu akasin hakan a gareta. Da sauri sakatariyar ta ta fice cikin matuƙar sassarfa. Minti biyu basu rufaba sai gasu sun shigo. Matar dai da ka ganta kaga wadda ke'a cikin mawuyacin hali, sai dai da zata samu kulawa ƙyaƙyawar mace ce dirarriya. A lamarin Lulu da talaka a teburin aikinta kawai suke iya shan inuwa ɗaya, shima akan abinda ya shafi aikintane kawai babu ruwanta da rayuwarka. Har ƙasa matar ta kai ga alamun ciki da ya turo a jikinta zata gaida Lulu. Bata hanata durƙusawar ba amma dukkan hankalinta na gareta, sai kuma katseta da ga gaisuwar data fara da tai...
    “Kinga wannan gaisuwar baida amfani faÉ—amin ina yarinyar take?â€.
  Cikin gyaÉ—a kai da share hawaye matar ta ce, “Tana gidan Æ´ar uwata da ta rakoni nan jiya, saboda yanda jikin nata yake ne Æ´ar uwar tawa tace na dawo yau ita ta kula min da itaâ€.
      “Wane police station kukaje domin kai Æ™arar?â€.
    “Na nan unguwarmu ne sai kuma da mukazo nan wajen Æ´ar uwar tawa itama ta kaimu na nan É—in. Sai dai shima basu É—auki abin da muhimmanci ba shiyyasa ta ce zata rakoni nan inda take da tabbacin za'a share mana hawaye. Hajiya dan ALLAH ki taimakeni kamar yanda ALLAH ya taimakeki. Yarinyar nan marainiya ce mutuwar mahaifinta ta sani auren wannan tsinannen da tunda na aure shi ban sake farin ciki a rayuwata ba......â€
   Cikin jan tsaki da takaici Lulu ta katseta da faÉ—in, “Kika zauna da shi kuma har ya miki ciki. Malama ni ba rayuwar aurenki nake buÆ™atar ji ba. Ki tashi kuje zan haÉ—aki yanzu da wanda zaku sameni a asibitiâ€. Ta Æ™are maganar tana miÆ™ewa cikin matsanancin É“acin rai. Waya takai kunnenta, da ga can aka É—aga. Kirari aka fara mata ta katse da faÉ—in, “Musa ka sameni a office yanzu kai da Shu'aibu Please inada emergency case.â€
     “An gama ranki ya daÉ—eâ€.
Musa ya faÉ—a ransa fes dan yasan yau aljihunsu zai kasance a cike. Dan aiki da Lulu yafi masa zaman cikin station aita kayan hamma balle tsaiwar kan titi amsar na goro. ÆŠan rubutu tai a takardar data yago ta miÆ™ama sakatariyar ta dake tsaye har yanzu. “Idan sun zo ki basu wannan, suje da ita sai su sameni a wannan asibitin dana rubuta. Kibasu 5k da zasu saka mai a motaâ€. Daga haka ta fisgi hand bag dinta da É—ayar wayarta da key tai waje...
Batako kalli sauran mutanen da ke zaune a inda table É—in sakatariyarta ya ke ba ta fice. Taja Æ™aramin tsaki lokacin da take dana unlock É—in motar tunkan ta Æ™arasa gareta. Bazata iya jure wannan zirga-zirgar tuÆ™in ba fa gaskiya. Dan tun farko ita dama ba gwanar sonyi driving bace. Cikin Æ™ara jan tsaki lokacin da take ficewa a gate É—in ta dannama Uncle Yousuf kira. Sai da ta shiga ta tuna abinda ya faru jiya da wasan É“uyan data Æ™udiri aniyar farayi da shi. Da sauri ta rarumi wayar zata katse sai dai harya É—aga. Babu alamar wasa a muryarsa ya ce, “Lafiya?â€.
   Kamar ta fasa ihu haka taji, amma sai ta dake cikin pretending da Æ´ar shagwaÉ“a ta ce, “Uncle Barka da safiya. Dama no É—in mutumin nan zaka turamin koka kiramin shi Please ya sameni a Shira's hospitalâ€.
    Ɗan jimmm yay kamar bazai amsa mata ba sai kuma cikin dakewar da takan bata tsoro a Duk sanda yayita ya ce, “Wane mutumin?â€.
      Yanzu kam sai da taji bugawar zuciya. Da É—an rawar harshe ta ce, “Driver fa my papaâ€.
  Har zaiyi yi mata tambayar yaya akai bashi ya kaita office ba sai kuma ya fasa saboda tare ya ke da abokinsa Hameed. “K kina ina yanzu?â€. Ya faÉ—a cikin goce tunaninsa.
    “Ina hanyar Shira's hospital É—inne â€.
   “Sai kin Æ™arasoâ€.
Ya faÉ—a kawai yana yanke kiran.......âœï¸
    Â
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.