Best / Popular Hausa Novels

Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: FURAR DANKO 1.txt

Chapter 76 of 94

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣3️⃣

.......Juyawa yay ya kalleta, sai akai sa'a itama ta kallesan suka haɗa ido. Harararsa tai ta ɗauke kanta. Shima sai ya maida nasa gefe kaɗan yana ɗan murmushi. Bata saka hijjab ba amma ta ɗaura Abaya a saman kayan jikinta tare da yane kanta da ɗankwalinta. Tray ɗin hannunta ta ajiye musu fuskarta da murmushi da shagwaɓa bayan ta gaida su ta dubi Uncle Yousuf da faɗin, “Papa i miss you ALLAH”. Dariya Uncle Yousuf yayi da jin daɗin ganinta yanda yake fata tunkan aje ko'ina. Sai da ya karɓi kofin ruwa data zuba masa sannan ya furta, “Mu kewarki ma bamu san yanda zamu misalta ta ba ai Mawaddatan'warahmah. Na gaban goshinki na can yau da ƙyar ya yarda zaije makaranta”.
     Murmushi tayi da faɗin “Uncle Please a kawo min shi to mana”.
          Shima sai yay ɗan murmushin da faɗin, “Tom ki ƙara hutawa, in dai waɗan nan ne sai kin gaji da su a gidan nan. Dan yanzu haka ma su Auntynki na zuwa”.
       Sosai taji farin cikin hakan, duk sai zumuɗi ma ya hanata zama ta juya ciki wai bari yaje ta shirya kafin su iso. Shi da Uncle Yousuf da kallo duk suka bita, yayinda Coach hankalinsa ke kan takardun nan. “Ina fata dai babu wata damuwa ko?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin katse tunanin Smart. Kansa ya jinjina masa cikin sauke numfashi ya ce, “Da sauƙi dai kam. Dan na fahimci wani lokacin tana da sauƙin kai musamman akan lagon mahaifiyarta da ka bani, dan in har zan jingina mata sunanta akan abu zatayi sa babu musu”.
       “To Alhamdullah, naji daɗi sosai dan hakan ma ci gaba ne. Ka ƙara haƙuri na haɗaka da aiki, amma nasan nan gaba kaɗan zaka gode min kaima. Dan Mawaddat nada wasu ɓoyayyun al'amura musamman halayen masu ƙyau, a yanda ta tashi taga kanta ne kawai babbar matsalar, sai dai duk da haka tsiwa da jin kanta sama sosai a jininta yake, dan mahaifiyarta tamkar tayi kaki ne ta ajiye, itama haka take kamar wata jinin sarauta wajen izza. Bambanci su kawai ita ta samu tarbiyya fiye data Lulu ne, da kuma kasancewar ita da girmanta ta haura wata ƙasa karatu ba kamar Mawaddat ba. Sai dai fa Aliyu yanzu yaƙin bana Mawaddat bane kawai, sannan ba ita kaɗai bace a filin dagar. Na farko sai munyi haƙuri da Yaya, na biyu Alhaji Sulaiman da ɗansa, dan nasan duk da baya ƙasar nan hankalinsa na nan, kuma gab yake da dawowa tunda jikin Tajuddeen ɗin da sauƙi.”
          “Karka damu Uncle Yousuf ku dai ku cigaba da mana addu'a. Daddy kuma insha ALLAH babu komai a tsakanina da shi sai girmamawa, na kuma fahimci son da yake mata ne mai tsanani da tausayinta ke rinjayarsa”.
      “To Alhamdullah nagode daka fahimci haka. Yanzu sai ka fara shirin nan da kwanaki zakaje Legos ɗin kamar yanda suka buƙata”.
               “ALLAH ya kaimu”.
       Da Amin suka amsa su biyun. Da ga haka suka ɗan sake tattaunawa shi da Coach akan abinda ya shafesu na harkar ball ɗin dan yanzu kam zai koma filin daga saboda training, sunja lokaci sosai dan har aka kira sallar azhar kafin su bar gidan su uku suna tsokanarsa da dariya wai yanzu ya koma ɗan 23years. Uncle Yousuf harda faɗin yanzu Lulu ma ta girmesa tunda gashi ma harya fara tsoronta dan yanzu ma dai sai da aka taɓa drama. Dariya yayta yi shi dai abinsa, dan koda ya koma ciki domin kiran Lulun suyi sallama da su Uncle Yousuf a ƙofa ya tsaya saboda gudun karta sake rutsashi. Dan ya manta bai zare key ɗin ba. Kamar kuwa ya sani tayi target ɗinsa akan hakan ALLAH dai ya taimake sa, amma duk da haka sai da tace bafa zai fita ba, sai da Coach ya bata haƙuri akan su Aunty Saliha na zuwa shiyyasa zai fita dan bai kamata su samesa a gidan ba haka akeyi sannan ta haƙura ta barsu, amma yasha harara kamar idanunta zasu faɗo....

Suna barin gidan su Aunty Saliha na isowa, hakan yay matuƙar ɗauke kewar Lulu da sanyata a farin ciki. Sai a yau taga lefenta na wajen Smart. Tayi mamakin ganin kayan da aka kai ɗin da shan jinin jikinta akan anya kuwa babu wani abu a ƙasa da su Uncle Yousuf ɗin ke shirya mata, wai tayaya aure wata ɗaya duk akaima wannan irin kisan kuɗin. Dauriyar dannewa tai dai batace komai ba har suka kammala abinda zasuyi bayan la'asar suka wuce. Suna wucewa kamar wani shiri sai ga Nadiya da wasu ƙawayensu da sukan haɗu a wajen shaye-shayen su, sai dai ita Lulu bawani tana kulasu bane sosai dan itafa dama can ba ma'abociyar shiga sabgar tarkace bace kasancewar ta wayayyar yarinya, ga kuma ƙawaye da ta daɗe da ajiye babinsu a rayuwarta. Ƙoƙarin rufe ƙofar tai tamkar ma bata gansu ba amma Nadiya ta iso da sassarfa ta riƙe cikin roƙo da magiya. Lulu da gaba ɗaya ganin Nadiyar ya sakata jin fusata ta ɗaga hannu ta ɗauketa da mari haggu da dama, sannan ta nunata. “Wannan shine hukuncin da fuskarki zata cigaba da fuskanta a duk lokacin da kikai yunƙurin nuna min ita, Nadiya duk abinda na ajiye tofa idan baki sani ba da ga yau ki sani na ajiyesa ne har abada dan bana jeka ka dawo, FURAR DANƘO NA KE A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. duk ramin da maciji ya sareni sau ɗaya bana ɗaura ƙafata a wajen karo na biyu. Ni nan da kike gani na fiki fiye da abinda kike tunanin kin iya, bana cin amana ba kuma na zama da maci amana, ki fita a rayuwata, dama ke kika sakko kanki cikinta ban ganyyaceki ba”. Da ga haka ta maida ƙofar ta rufe da ƙarfi har sai da duk suka zabura.
        “He he he babbar bala'i mai citta da kayan sanyi, wai dama haka yarinyar nan take bata da mutunci? Akan kawai saurayi ya bita inda bata gayyacesa ba take wannan tada jijiyar wuyan, ƴar iska bayan ance mana rainon turai ce wane kalar iskanci ne basayi a can amma zatazo nan tana nuna mana ita wata kamila ce. To wlhy zamu bata mamaki, dan wannan marin da tai miki sai ta fansheshi da abinda har abada kuka bazai bar kwaranya a idanunta ba, zata san ta haɗu da ƴan tasha na asali, dan ƙarshen iskanci a Nigeria aka haifesa da yanke masa cibi aka kuma rainesa a ciki yay girma yay furfura, idan ma ya mutu anan za'a biznesa sai ranar bayyanar judal su tashi tare su haɗa ayari”.
        Murmushi takaici Nadiya tai da janye hanunta da har yanzu ke a kan kuncinta tana maida ƙwallar data cika mata ido. Ta ce, “Shuwa Lulu ta wuce duk yanda kike tunaninta, ki kuma iya bakin ki dan ta fiki in dai jidali ne. Lolipop ma tayi bataci riba ba. Ni nai mata laifi dan tun farko ta gargaɗeni akansa amma banji ba, nai mata ma farko tace karna sake na biyu amma na sake kuma, na san nice da laifi dan Lulu ta ƙyautata min a rayuwa, na kuma san bata ƙaunar huɗɗa da maza amma na sake maimaitawa. Shiyyasa nace muku bazan zo ba sai nan gaba ta sake hucewa amma kuka matsa, ga shi abinda sakamakon hakan ya bada kun jamin tozarci...” kafin wani cikinsu ya ce wani abu ta nufi motarta da sukazo ciki ta shiga, bin bayanta sukai da sauri suma duk suka shiga. A guje tabar anguwar damma ba yawan hayaniyar mutane a aria ɗin kasancewar sa babbar anguwa......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.