Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 82 of 94
    Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 7ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
.......Alhamdullah yau Lulu zata ce kasancewar abubuwa sun tafi mata yanda take so. Dan duk da zaman shari'ar yau aka fara Alhmdllh tana hango nasara a cikinta. Bayan barin kotu da Hassan yazo ya kaita da kansa office ya sake maidata, ta É—an taÉ“a aiki bayan sallar azhar ta fito. Tana jan mota ta fita Security É—in nan ya dannama Smart waya ya sanar masa. Godiya yay masa sannan shima yay kiran wanda ya saka ya dinga bibiyar masa ita akan yabi bayanta da napep É—in. Kai tsaye anguwar da mijin Hawwah yake ta nufa, da tambaya ta isa gidansu Sa'id. Mai Napep da ke binta ya kirasa ya sanar masa. Sosai Smart yay mamakin abinda ya kaita, har ya dinga jin son yazo amma dai ya dake da Æ™yar dan son ganin iya gudun ruwanta. Sama-sama ta gaishe da maigadin tare da tambayarsa ko hajiyar gidan na nan? Amsa mata yay da eh cikin washe haÆ™ora. Fuska ta yamutse cike da izzarta ta ce, “Sanar mata tana da baÆ™uwaâ€. Babu musu ya amsa mata da to yana nufar cikin gidan. Mintinan baifi uku ba sai gashi ya dawo ya ce ance ta shiga.
     Kallon gidan ta dingayi side by side tana taÉ“e baki, a irin dukiya ta gidansu gidan su Sa'id É—in ba komai bane ba, sai dai ba laifi suma dai da gani akwai kuÉ—in sai dai ko kama Æ™afarsu basu isa yi ba. Ƙofar da take Æ™yautata zaton falon gidan kenan ta nufa, cikin sa'a ma sai ta hango wata yarinya tsaye kamar tana kuka da alama mai aiki ce, isowarta kusa da ita ya sata daina kukan ta risina ta gaisheta. Sau É—aya ta amsa mata ta É—auke kanta. Yarinyar ce ta mata iso cikin falon, babbane sosai ya kumaji É—irka-É—irkan kujeru kamar bana dattijuwa ba. Kallo É—aya taima matar dake zaune a falon ta fahimci itace mamar mijin Hawwah É—in, dan ko'a ido ka kalleta kasan za'a zuba da ita kam. Zama tai kanta tsaye tun kan ma ace ta zauna, maman Sa'id dai kallonta take alamar rashin sani, duk da Lulu ta fahimci hakan sai ta basar, cikin É—aukar kan nan nata na isa da Æ™asaita ta ce, “Hajiya barka da rana. Sunana Barrister Mawaddat Isma'il JiÆ™amshi.â€
   Sai da zuciyar maman Sa'id ta motsa jin Æ´ar waye, sannan sunan kansa na Mawaddat É—in duk mai bibiyar harkokin mata a fanin fyaÉ—e dole zai santa, ita kanta dama tunanin ina tasan wannan fuskar takeyi. Lulu data lura da hakan ta cigaba da faÉ—in, “A yanzu haka matar Aliyu M. Idris Mawashi yayan matar É—anki dan bana tunanin kin halarci bikin sati É—aya daya shigeâ€.
   Gaba É—aya Mama duk sai ma taji ta daburce, dan tabbas Sa'id yata roÆ™arta zuwa bikin amma tace bazataje ba dan ba'a gayyaceta ba, koma an gayyacetan bazataje bikin matsiyata ba dan tasan dai bai wuce tuwo da waina da zoÉ“o ba. Harga ALLAH bata san É—iyar wa Aliyun ya aura ba. Da É—an jimami ta ce, “Da gaske kece matar Aliyun?â€.
      Lulu dake mata wani kallo a yamutse ta amsa da, “Oh baki yarda bane? Zaki iya tambayar É—anki ni yanzu ba wannan ne ya kawoni ba. Nazo nan ne game da case É—inki da Hawwah, kinyi Æ™oÆ™arin zuba mata mai dake saman wuta da nufin Æ™onata, ba kuma wannan ne karo na farko ba da hakan ta faru. Kinci arziÆ™in É—anki shiyyasa banzo da police ba a yanzu haka domin kamaki. Amma nazo da kalaman gargaÉ—i a gareki a karo na farko. Su iyayenta sun barki saboda jin nauyin karamcin É—anki. To ni kuma a matsayina na mai kare hakkin mata kuma matar Yayanta bazan iya barinki ba. Kin haifi Sa'id ba kin haliccesa bane, yana kuma da damar yin aure tunda bake zaki auresa bane, matsayinki daban matsayin uwa matsayin matarsa daban matsayin mata. Nan gidan aurenki ne, shi kuma nan gidan da aka haifesa ne, kina zaune da mijinki lafiya dan haka itama ki barta ta zauna da nata mijin lafiya. Wannan takardar da kike gani na tattara dukan abubuwan da kikai mata ne, tare da bincike mai yawa akanki a wajen Æ´an anguwa da Æ´an uwanki dana mijinki, kuma sun bani duk wani information a kanki har ma wanda bakiyi zato ba. Haka ma mijinki nayi waya da shi yanzu haka, dan haka kina da zaÉ“i biyu zaki saka hannu zan saka hannu Sa'id zai saka hannu hakama Hawwah da sharaÉ—in zaki fita rayuwar aurensu ki zauna a matsayinki na mahaifiyarsa, zakuma subar wannan gidan su koma nasu, sannan kije da kanki gidansu ki bata haÆ™uri ki bama iyayenta haÆ™uri. ZaÉ“i na biyu Æ™in amincewa da shawarar farko na shigar da wannan case É—in kotu mu zuba shari'a wlhy har sai na kaiki jail dan har video ke gareni na randa kika kusa kasheta a dalilin hankaÉ—ota daga saman upstairs gashiâ€. Ta É—aga mata wayar tana mai playing video É—in, jikin maman Sa'id ya fara rawa, Lulu ta sake shiga wani ta ce, “Ga kuma na randa kika watsa mata ruwan shayi harta Æ™one a wuya shimaâ€. Sosai Lulu taga ruÉ—ewa a idanun Mama. Tai murmushi da kaÉ—a kanta cike da isa. “Ba waÉ—annan kawai ne ba, akwai wasu tari-tari kuma duk Hawwahn ke ajiyesu, bata nuna bane saboda mutuncin É—anki. Amma ni yanzu na shirya fiddosu a gaban alÆ™ali. Kin san dai mijinki siyasa yake yi har yana shirin fitowa takara a shekara mai zuwa ko, sannan yayanki a yanzu haka É—an majalissa ne, to a dalilinki duk zan iya tarwatsa wannan damammakin, dan bayan kasancewa jinin JiÆ™amshi jinin Alhaji Sufi Ado Garko nake kuma. Sai ki zaÉ“a na baki nan da kwanaki uku kacal. Na barki lafiyaâ€. Ta faÉ—a tana miÆ™ewa murmushi É—auke da fuskarta ta É—aga mata yatsu biyu tai ficewarta. Sosai jikin maman Sa'id ke rawa da kakkarwa. Dan kuwa Lulu ta daketa ne a inda taji zafi sosai. Videos É—in nan sun matuÆ™ar tayar mata da hankali, har tana mamakin yaushe Hawwah duk ta É—aukesu batare da ita ta sani ba. Na biyu matsayin Lulu da hatsabibancinta akan shari'ar duk da ta saka a gaba. Na uku zancen siyasar mijinta da tai matuÆ™ar Æ™wallafama rai da buri a yanzu tare da matsayin É—an uwanta da shima take taÆ™ama da tinÆ™aho da shi a duk inda ta shiga. Idan wannan damar duk ta kufce musu ai ta shiga uku wlhy, dan za'a mata dariya matuÆ™a. Itafa dama kishiyar uwar yarinyar nan ce ke sake tunzurata akan tsanarta (Umma), duk da dai dama bata sonta kasancewarta Æ´ar talakawa, dan taso ace Sa'id yay auren kece raini ne na Æ™warya tabi Æ™warya. Amma ya Æ™are da auren Æ´ar malam shehu......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.