Best / Popular Hausa Novels

Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: FURAR DANKO 1.txt

Chapter 50 of 94

        A motar tuƙinsa yake tayi, yayinda ita da Deen suketa surutunsu da dariya. Dan indai Lulu da Deen ne kam babu mai shiga tsakani. Sai ya ƙulleta da haushi ta mammakesa da kiransa mai shegen surutu kamar akku. Sun tsaya a wani ƙaramin super market Uncle Yousuf ɗin ya fita shi ɗaya. Bai jima ba ya dawo, sai kuma a wajen masu fruits, nan kam da ga motar ma yay bayanin abinda yake so aka kawo masa ya bada kuɗin suka cigaba da tafiya. Lulu dai bata tambayi ina zasuje ba. Hasalima hankalinta gaba ɗaya naga Deen ne. Sai da motar ta tsaya ne sannan hankalinta ya dawo ga inda suken. Kallon anguwar take a ɗan yamutse, duk da ba wani datti bane ko makamancin hakan, hasalima titi ne shimfiɗe da ya miƙe samɓal kasancewar gidan su Smart na a farkon shiga layinne. Sai dai yanayin gine-ginen da kai kawon mutane dana ababen hawa riiiii yasa zaka tabbatar dai irin tamu ce dangin malam Shehu....
       “Papa nan fa?”
   Cewar Lulu a gatsine.
Maimakon bata amsa wayar da yake dannawa ya kai kan kunne. Ta daiji yana amsa gaisuwa, sai dai bata fahimci mi ake cewa da ga can ba. Sai kuma taji Uncle Yousuf ɗin na cewa, “Kai dai kaɗai ne a ɗakin ko? Okay gani nan shigowa”. Daga haka ya yanke wayar tare da buɗe murfin yace, “Oya ku muje”.
        “Uncle.....”
    “Shiiiii...” yay saurin katseta tare da mata alamar zip a baki. Dole ta haɗiye abinda take son fadar dan babu alamar wasa akan fuskarsa. Shi da kansa ya kwashi ledojin, ita kuma ta fito riƙe da hannun Deen tana ta faman yamutse fuska. Sauƙin ma babu kowa a ƙofar gidan. Wanda ke iya hango su kuma ba sosai suke iya ganinsu ba duk da harda masu leƙe saboda son gulma irin ta mutane. Soron ta dinga bi da kallo duk da shima dai fes yake gashi kuma lailaye da sumintinsa. Hakama koda suka shigo gidan ko'ina fes babu wani datti, ga gidan shiru babu yawan hayaniya sosai dan yaran sun wuce ismaliyya, sai ma matan anguwa da wasu a dangi dake ta faman shigowa yin ALLAH ya sanya alkairi da auren Smart ɗin da ba'a san da shi ba. Sai kuma wanda suka san baida lafiya na ɗorawa da jajanta yaya jiki musamman maƙwafta. Anan dai ta inda suke basu haɗu da kowa ba har suka shige sashen ɗakunan samarin gidan da ke a farkon shiga. Anan sun ɗan haɗu da wasu. Bakowa bane kuma sai Mubarak da kema Smart wankin kayansa na ciki, sai Abdull a gefensa yana kallon film a waya da eirpiese a kunnensa. Mubarak ya shiga musu sannu da zuwa cikin girmamawa dan ya gane Uncle Yousuf, itako Lulu dama kallo guda tai musu ta ɗauke kai gefe a ranta tana ƙunƙunin ina ne nan Uncle You ya kawosu. Duk da dai gidan babu wani makusa tare da shi a ɓangaren tsafta a ginensa dai na masu ƙaramin ƙarfi ne. Ita ba hakanne ya dameta ba, kawai bata cika son zuwa irin wajejen nan bane, shiyyasa ko aikinta ya ratsa da hakan zaka ganta cikin rashin sakewa da son a gaggauta abar wajen. Abdull da Mubarak ya zungura shima ya shiga gaishesun. Duka dai Uncle Yousuf ne ya amsa da tambayarsu ko Aliyu na nan? Duk da yasan yana nan tunda dai yayi waya da shi. Sun amsa masa da girmamawa Abdull ya tashi yay musu iso.
        Tunda Uncle Yousuf ya ambaci Aliyu ta kafesa da idanun son jin ƙarin bayani, sai dai bai kulata ba yay gaba dole suka bisa a baya. Yana zaune a saman katifarsa da ƙarin ruwan da doctor ya ƙara saka masa babu jimawa saboda rashin ƙarfin jiki da ya tashi da shi. Wando ne 3 quarter a jikinsa da ƙaramar t-shirt data kama masa jiki sosai. Ainahinsa na tsayayyen mutum ya fito sosai. Fes ɗakin yake ga ƙamshin turaren wuta mai daɗi da Maryam ta saka masa bayan ta share. Gefensa kaɗan flaks ɗin shayinsa ne da cup da ya sha sai kayan tea a wani basket mai ƙyau harda bread alamar dai nan ɗin ne wajen ajiyarsu. Sai kuloli biyu da jug mai riƙe zafi da aka dama masa kunun gyaɗa. Sallamar Abdull da ta Uncle Yousuf ta sashi ɗago idanunsa da ke kallon tv ya zubama ƙofar tare da amsawa. Abdull ya fara shigowa da faɗin, “Yaya Smart baƙi ne”. Kalmar baƙin ta bashi ɗan mamaki, dan shi a tunaninsa Uncle Yousuf ɗin ne kaɗai kasancewar su Daddy basu jima da tafiya ba su. Kafin ya kai ƙarshen tunaninsa Abdull ya gama ajiye ledojin da ya amsa a hannun Uncle Yousuf Deen ya shigo, Uncle Yousuf biye da bayansa Lulu a ƙarshe. Harga ALLAH sai da gabansa ya faɗi, bawai na tsoro ko makamancin hakan ba, shi dai kawai ya samu kansa da jin bugawar ƙirji. Sai dai kuma abinda bai sani ba bashi kaɗai ba. Ita kanta Lulun sai da nata ƙirjin ya harba. Hannu ya miƙama Deen yana faɗin, “Welcome my little handsome”. Cike da farin ciki Deen ya nufesa shima yana murnar ganinsa. Zama Uncle Yousuf yay a sofa ɗin ɗakin ƙwara ɗaya yana murmushi, yayinda Lulu ta wani cakuɗe fuska da yamutse ta duk da taji shock ɗin ganin inda Uncle You ɗin ya kawo ta ta danne, dan tunda tai masa kallo ɗaya a yayin shigowarsu bata sake ba.
          Smart da ke sauraren surutun Deen da ya karaɗe ɗakin ya dubi Uncle Yousuf cike da girmamawa ya ce, “Uncle Barka da safiya”.
      Shima cike da kulawa yake kallonsa da tausayawa. Amsawa yay da “Barka dai Aliyu yaya jikin naka?”.
       “Alhmdullah ai na miƙe”.
   “Kana dai dauriya Aliyu ga shi harda su ƙarin ruwa. ALLAH ya baka lafiya yasa kaffara ne”.
    “Amin ngd”.
Ya faɗa can ƙasan maƙoshi yana bin Lulu da ta dogare tsaye da kallo ƙasa-ƙasa. A take wani abu ya tokare masa maƙoshi akan shigar jikinta. Lallai yasan akwai babban yaƙi a tsakaninsu. Dan shifa bazai yarda da wannan shigar shegantarkar ba gaskiya. Uncle Yousuf da shima ya juya yana kallon Lulun ya nuna mata gefen katifar yana faɗin, “Zauna mana kikai mana tsaye a kai Mawaddat. Ba kuma kiga Aliyu babu lafiya ba?”.
       Kamar zata fasa ihu taji, ta sake yamutse fuska da ɗaureta a taƙaice ta ce, “Uncle nan ma it's ok”. Sai kuma ta dubi Smart fisha cike da gatsali ta ce, “Sannu fa”.......✍️

*_Kuma sannu fa🙋 dangin Smart 😂🤣🤩. Dangin mu Lulu's team Barka da rana😚😘😉._*

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.