Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 32 of 94
   Â
   ★★★
★.★.★★
  Tabbas a daren jiya yanda yaga rana haka yaga dare dan ko sau É—aya bai rintsa ba. Sai faman bulbulama cikinsa hayaÆ™in cigarette da yay tayi dana shisha. Baya taÉ“a neman abu ya rasashi, haka ma bai taÉ“a harar mace sau biyu ba ta zille masa sai a kanta. Duk da É“acin ran da ya tsinta kansa dalilin rasata a jiya bai ji ko É—igon sha'awarta ya ragu masa a rai ba. Sai ma Æ™aruwa yay yana sake azalzakarsa da sake tunzura buÆ™atarsa. Neman hanya ta uku ya tsunduma a tunani, sai dai zuciyarsa ta rabu gida biyu. ÆŠaya na tabbatar masa ya nema aurenta kawai itace hanya mafi sauÆ™i. ÆŠaya na tabbatar masa bazata amince ba, dan haka kota halin Æ™aÆ™a kawai ya kore Æ™ishirwarsa, kai koda sakawa a sace masa itane. Ganin ya rasa makamar riÆ™ewa sai kawai ya yanke shawarar neman shawarar abokinsa. Gabanin asuba yay kiransa, bugu biyu kuwa aka É—aya dan shima a lokacin yana cikin club ne a Abuja..........âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 3ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
.........“Mtsoww! Kaifa baka da aiki sai gantali, a ina kuma kake haka irin wannan lokacin?â€.
    “Kai mai maganar a ina kake? Kujimin sa ido. Kodan kaje Kano kai ka koma É—an gargajiyaâ€.
  Ƙaramin tsaki Mm atik yay da faÉ—in, “Ɗan iska banda time É—inka. Nifa magana mai muhimmanci na kira muyi, ka É—an fita gefe Please nasan kana nan nane da cingam gal É—in nan takaâ€.
    “Naji, na matsa É—an shiga sharo, ina saurarenkaâ€.
  Ɗan tsaki MM Atik yayi, dan harga ALLAH ya tsani budurwar abokin nasa da tabi ta kanainayesa ta hanashi rawar gaban hantsi. Cikin ture batunta ya ce, “Akan yarinyar nan ce dana faÉ—a maka. Plan É—in mu na jiya fa ya rushe bata shiga tarkon baâ€.
   “Whart! Wai kana nufin ka aiwatar?â€.
  “Eh mana yau É—in nan ma, amma sai.....†ya zayyane masa komai da ya faru. Da ga can Arman yay Æ´ar dariya da faÉ—in, “Wai driver? To ko dai shima yana hutawar ne?â€.
     “Mtoww bana jin hakan gaskiya. Dan randa na fara haÉ—uwa da ita na gansa. Yanda ta yarfashi ma sai ya baka tausayi. Kawai dai irin mutanen nan ne masu shegen shishshigin tsiya. Nidai yanzu manta bani mafitaâ€.
   “Ni dai mafita É—aya na hango maka nasan kai kuma baka buÆ™atartaâ€.
  “Waccece? Please tell me!â€.
“Aure!â€.
“Mtsoww auren Æ™aniya. Nima ina tunanin haka, sai dai banda shiri gaskiya na zama da mace yanzu, ban san takura kai ma ka sani....â€
    “Ka tsaya nakai Æ™arshe manaâ€.
  “Oh sorry ina jinkaâ€.
“Abinda nake nufi bawai auren nata zakai ba. Tunda ka riga ka Æ™wallafa ranka ka zama cingam boy kuma ita bazata samu ta sauÆ™i ba kawai kasa su Dad gaba aje maka neman aurenta.....â€
    “Baka da hankali! Dad fa? Kasan waye Dad kuwa?!â€.
   “Calm dawn mana my man. Lamarin fa duk lissafine. Yanda Dad keda alfarma na tabbatar sun san juna da babanta tunda kace itama Æ´ar manya ce. So da zarar magana ta shiga kai kuma sai kaita jan ra'ayinta harka samu cikar burinka. Daga haka mu Æ™irÆ™irar mata laifin da shi Dad É—in da kansa zai ce bazaka aurenta baâ€.
   “Woow! Woow woow my dear wannan salon yayi kuma zai Æ™ayatar. Sannan ita kanta zan firgita lissafinta tasan ba irinmu ake ja a Æ™asa ba. A safiyar yau É—in nan zan zauna da Dad, nasan zai matuÆ™ar É—aukar abin da muhimmanci tunda dama burinsa kenan shi da Mom. Kai dai ALLAH ya barka da cingom gal taita Æ™arar maka da ruwan kai byeâ€. Ya yanke wayar yana wani jin matuÆ™ar farin ciki tamkar ya samu Lulu Æ™amshi É—in ya gama ne.
 Â
   Ni ko na ce, “Hummm!â€
  Â
   ★★★
Kamar yanda Alh. Baita da Hon. Nakowa suka girgiza da jin Mawaddat ɗiya ce ga Alhaji Isma'il Jiƙamshi haka shima Hon. Misau yay matuƙar girgiza da batun. Dan abune da ko'a lissafin hasashe basu taɓa kawowa ransu ba. A take suka zauna teburin shawara. Dan kuwa tabbas wata dama ce a yanzu tazo hannunsu akan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Kuma lokaci ne na ɗaukar fansa da zai goge tarihin baya labarin yazo da salon alƙalamin da sune zasu zama masu rubuta shi.
   Tsaf suka kammala tsara komai a yanda suke buƙata. Fatansu kawai nasara da kuma sake sabon bincike dan ƙara riƙe hujjoji masu ƙarfi musamman akan Alhaji Sufi Garko da suka yanke shawarar tunkara a farko. Dan tabbas babban ɗaurin huhun goro suka shirya yima uban da ƴar gaba ɗaya dan su kasance gaba ɗaya a tafin hannunsu. Basu sa wasa ba tun a ranar suka nema appointment ɗin ganawa da babban ɗan kasuwar, kuma ƙusa a ɓangaren siyasar arewacin kasar musamman ma Kanon ta dabo Alhaji Sufi Ado Garko. Tsoho da kuɗi kenan abokin tafiyar yara, manyan kuwa baba suke kiransa dan ya kere ya kuma zarce koda a tsaransa. An tabbatar musu yaje Umrah sai dai nan da kwanaki biyu idan ya dawo washe gari su shigo. Sun samu wannan damar ne dalilin shaƙama babban yaronsa kuɗaɗe masu kauri, sai kuma mulki da Hon. Nakowa da Hon. Misau ke riƙe da shi wannan ma babban makami ne.....
   ★★★....
Ga Alhaji Sulaiman Sufi Garko ma ya gama shiryawa tsaf domin tunkarar mahaifin nasa game da auren Tajuddeen da Mawaddat. Dan a wannan karon ya ɗau aniyar koda yardarta, ko babu sai wanan auren ya ƙullun. Dan ya gama tanadar kalaman da zai tsara mahaifin nasa da su tsaf komai ya tafi dai-dai. Tajuddeen ya samu cikar burin shima ya samu nashi.....
   ★★★....
A ɓangaren Lulu ƙamshi da bata san mi suke ba gaba ɗaya hankalinta na kan case ɗin yarinya da akaima fyaɗe ne. Dan anata neman mijin matar amma an rasashi wai ya gudu yabar gari tun a randa yay abun. Wannan takaicin ne ya taru yay mata yawa ta tada hankalin su Sha'aibu ɗan sanda dama na duk wanda ke mata aiki idan irin wannan case ɗin ya taso. Hatta Daddy bata barsa ya huta ba. Ga takaicin Smart yaƙi dawowa aiki itako ta gaji da tuƙi dan sunata zirga-zirga. Shiko Uncle Yousuf ne yace ya zauna gida ya huta har sai jikinsa yay masa ƙarfi. A washe garin kwana na biyu da take saka ran dawowar Grandpa ɗinta da ga umra duk da tarin ayyukanta haka tai wancakali da su ta shiga tawagar ƴan tarbarsa a airport dan ya kwana biyu baya Nigeria, saboda daga uk ganin doctor ɗinsa ya wuce Saudiya Umrah. Tana kewarsa dan tana matuƙar so da ƙaunar kakan nata daya haifi mahaifiyarta da bata sani ba sai a hoto. Shi takema kallon uwa ga shi kuma shine kaɗai ya rage mata a kakanninta dama. Shima kuma a karan kansa yana nuna mata tsagwaron soyayya kasancewar ta ɗiya ga Mawaddat dinsa da ya rasa dan ita kaɗai ya taɓa rasawa a cikin ƴaƴansa shiyyasa yake matuƙar tausayin Lulu.
     Ƙarfe kusan sha biyu jirginsu ya sauka. Duk da hango Æ´an uwanta jikokin Alh. Sufi Garko da tai su Tajuddeen da sukazo tarbarsa suma Æ™in fitowa tai tana daga motar har sai da taji ance jirgin da ya taso da ga Saudiyan ya sauka sannan ta fita. Sanye take cikin gawn ta material mai taushi da santsi da sukai matuÆ™ar mata Æ™yau da fidda mata Æ™yaÆ™yÆ™yawar surarta kamar wata Æ´ar tsanar roba. ÆŠaurin kanta da Amrah (Hussaina) tai mata yayi Æ™yau ya kuma rufe mata gashi, sai ta gaba kaÉ—an da aka zamashi ake iya ganinsa baÆ™i siÉ—ik a kwance, Kasancewar a É—aure yake da ribbon sai yay tilluwa a cikin É—ankwalin da aka rufesa da shi ruf. Siririn mayafi kalar material É—in ta É—ora a kafaÉ—a babu zancen yafawa. Sai dogon takalmi kamar koyaushe duk da kuwa ita É—in doguwa ce amma bacan ba tsaka tsaki. Ƙaramar handbag É—in hanunta ta sake gyarawa da gilashin idonta da ya sake Æ™awata kwalliyar tata duk da kuwa a fuskarta babu ko É—igon kwalliya bayan hoda dan itafa bata kwalliya, sai lips glose data saka a lips É—inta kaÉ—an. Yanda take taku kamar wata tarwaÉ—a da sautin da takalmanta ke badawa ga Æ™amshin turarenta data bulbula ya sata janyo hankulan mutane gareta musamman na kusa da ita. Sosai numfashin Tajuddeen ya dinga kaikawo a Æ™irji har ta Æ™araso garesu. Ya haÉ—iye busashen yawun da ya kasa wuce masa a maÆ™oshi yana É—an sakin murmushi. ÆŠauke kanta tai kamar bata gansa ba, sai ma yatsu biyu data É—aga musu a taÆ™aice tare da faÉ—in, “Hy girls and boysâ€. Duk wanda yasan Lulu a family É—in yasan ba kanwar lasa bace, ba kuma wani take ragawa ba. Duk da mafi yawansu sunada labarin tushen asalin arzikin mahaifin nata da ga kakansune wani bai isa furtawa ba tai masa wankin babban bargo ita babu ruwanta. Yanda tai musu gaisuwar cike da raini ya zafi wasu musamman ma matan amma babu wanda ya nuna, to ita bama ta tsaya sauraren amsawar tasu ba tuni tai gaba, dan a dai-dai nan Alhaji Sufi Garko ke fitowa da ga jirgi gefensa p.a É—insa ne da shima zai iya kai sa'annin su Daddy. Lallai ya tsufa kam, damma harka irin ta masu hannu da shuni mai wahalar sha'ani. Amma irin wannan tsoho ai kamata yay ace yana zaune gida jikoki zagaye da shi yana hutawa kawai. Cike da É—oki da farin cikin murmushi mai bayyana haÆ™ora da ke da tsada a fuskar Lulu dan kafin ka gansa ka yara ta nufi kakan nata ta rungume. Shima tashi fuskar Æ™awace da murmushin ya tarbi abarsa yana mai farin ciki da jin kewarta har cikin ransa. Sai da ta gama nata farin cikin sannan sauran yaran suma suka matso garesa su Tajuddeen. Suma ya nuna jin daÉ—in ganinsu dan yana son Æ´an jikokin nasa da a yanzu duk suka zama manya samari da Æ´ammata har ma da masu aure, dan su Lulu kusan sune Æ™anana ma duk da dai suma akwai waÉ—anda suka girma. Da ga haka aka É—unguma zuwa gida, inda Lulu ta tubure motarta zai shiga dole kuma akai hakan dan kowa yasan rigimarta original ce. Yanzu kam a hankali take tuÆ™in dan Alhaji Sufi yayi gargaÉ—i. Daga shi sai ita ne a motar, dan haka taketa masa hira shiko yan biye mata. Tausayinta yake ji fiye da kowa a cikin zuri'arsa saboda maraicinta, ga kuma Æ™aunar da yakema mahaifiyarta itama ya shafeta. A gidan ma koda suka iso sai suka samu Æ´aÆ´ansa maza da mata da ke cike da gidan duk dai akan dawowar tasa. A duk sanda akai irin wannan taron da wahala kaga Lulu batai kuka ba koda a É“oye ne saboda jin buÆ™atar mahaifiyarta itama. Yanzu É—in ma da Æ™yar take iya danne hawayenta, tama Æ™i shiga gidan, tana ganin Æ´aÆ´ansa sun janyesa ta zame jikinta ta gudu. TuÆ™i take tana hawaye da jin kewa mai tsanani, tasan Mommy uwa ce a gareta, amma da gaske tana buÆ™atar É—umin mahaifiyarta koda sau É—aya ne inda ace hakan zai yuwu, sai dai tasan har gaban abada bazai yiwun ba kuma. Gefen titi ta gangara a hankali ta kashe motar ma baki É—aya ta lafe cikin kujerar idanunta lumshe tai shiru, so take tai kuka amma tana Æ™oÆ™arin hana kanta hakan. Bata cika son shan komai da rana ba musamman a lokacin aiki, sai dai a yanzu babu abinda tafi buÆ™ata kamar tasha É—in. Duk yanda taso hana kanta taji shan kawai take buÆ™ata. Cikin rawar jiki ta jawo handbag É—inta, faudanta ta zaro tare da buÉ—eta acan Æ™asa ta ciro wata takarda da'aka naÉ—a kamar Æ™ullin magani. Tana warwareta sai ga Æ™wayoyi a ciki. Gaba É—aya kusan fin biyar duk da Æ™ananu ne sosai ta afa batare da neman ruwa ba ta haÉ—e abinta tana wani sauke ajiyar zuciya. (Kamar wadda ta haÉ—u da uwar tata da take nema😔🤦. Ya rabbi ka shiryemu ka shirya mana zuri'a ka rabamu da mummunar Æ™addaraðŸ˜ðŸ™)...........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.