Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 37 of 94
   Tofa Uncle You mi kake ƙullawa haka kaima😂🥱?.
    ★....★
 Â
  A washe gari data kasance safiyar alhamis a duka É“angarorin huÉ—u kowa ya tashi da shirinsa game da abinda ya kwana da shi a rai. Æangaren su Hon. HD. Nakowa sun shirya tsaf da shirin zuwa neman auren Mawaddat a wajen Alhaji Sufi Ado Garko kamar yanda ya basu dama. Haka ma a É“angaren Alh. Sulaiman da É—ansa sun gama tsara komai a daren jiya domin cikar burinsa da kuma burin É—ansa Tajuddeen da ke Æ™aunar Mawaddat har cikin zuciyarsa. Æangare na uku shine MM Atik Kumo da shima ya tunkari iyayensa da maganar samo mata da yay, sai dai ya gagara tunkararta yana son iyayen nasa su fara zuwa masa neman izinin nemanta ga nata iyayen. Sosai mahaifinsa da Mom É—insa suka shiga matuÆ™ar farin ciki, dan babban burinsu dai a rayuwa shine suga auren É—an nasu daman. Sun samu wannan damar kam bazasuyi sakaci da itaba, musamman ma da sukaji yarinyar ta fito ne da ga zuri'ar Alhaji Sufi Ado Garko da duk wani É—an siyasa a jihar Kano ke masa kallon uba. Hakama Æ´an kasuwa domin a duk É“angarorin biyu yana taka rawar gani da tarihi bazai iya mantawa da shi ba ko bayan ransa. Rukuni na gaba sune gidan allurar da kowa ke iyo cikin Æ™aton kogin domin nema, wato _Mawaddat Isma'il Ibrahim JiÆ™amshi_.
    Mawaddat da tun a daren jiya ta dawo cikin hayyacinta sam bata san duk wannan babban yaÆ™in basasa da ake shiri a É“angarori uku domin ita kaÉ—ai ba. Hasalima ita ta wayi gari ne da babban shiri akan mijin matar nan da yay ma yarinya fyaÉ—e. Har yanzu yarinyar na asibiti cikin mawuyacin hali. Da farko ta hana Æ´an jarida yayata zancen har sai ta kama shegen, sai dai a yau wani tunani datai yasa zata bama Æ´an jarida damar fitar da komai, tana ganin hakan zai taimaka musu wajen kamashin. Yau da wuri ta kammala shirinta cikin wandon jeans dark blue da milk color É—in riga. Rigar nada É—an tsaho musamman ta baya. Ƙaramin veil ta naÉ—a a kanta tare da bulbula Æ™amshin nan nata. Cikin takunta na yanga da izza ta fito, babu alamar jama'ar gidan wani ya tashi, sai su Iya Tabawa dake ta aikin gyaran gidan. Gaisheta suka shigayi cikin girmamawa. Hannu ta É—aga musu sau É—aya tai ficewarta dan bata cikin mood É—in yin magana yau. Karo suka kusan ci da Uncle Yousuf da ke Æ™oÆ™arin shigowa a main falour. Tai saurin komawa baya da faÉ—in “Sorry Papa ban san ka taho baâ€.
    “Ina zaki haka?â€.
  Ya faɗa a dake maimakon amsa maganarta ta farko. Ɗan kallonsa tai da mamaki, sai dai ganin yanda shima ke kallonta babu alamar wasa a tattare da shi ya sata maida kanta ƙasa cikin tsarguwa, dan dama dauriya take kawai, amma tun a daren jiya take ƙullawa da kwancewar ta yanda zata iya haɗa ido da shi, da kuma yanda zata shukama drivern ta rashin mutunci a wannan karon tunda har ya sake bari Uncle Yousuf ɗin ya ganta a cikin wannan yanayin.....
   “Baki ji bane? Ina zaki je?â€.
 Ya sake faÉ—a cikin katse mata tunani. Firgigit ta dawo hankalinta. Cikin in ina ta ce, “Uncle You office, amma zan fara zuwa nai magana da Æ´an jarida akan case É—in yarinyar nan shiyyasa zan fita da wuriâ€.
   “Shi kuma naki case É—in kiyi yaya da shi?â€.
  Da sauri ta É—ago ta dubesa. “Uncle case É—ina kuma? Ni ai babu abinda ya faru da niâ€.
      “Zai farun ne ai. Biyoniâ€.
    Kamar wadda aka bugama guduma a kai haka Lulu ta tsinta kanta a wannan lokacin. Sai dai bata da zaɓin da ya wuce bin bayan nasa kamar yanda ya bata umarni. Duk abinda ke faruwa Daddy na kallonsu da jinsu. Ya haɗiye hawayen da ke neman zubo masa. A daren jiya ko sau ɗaya baiyi barci ba, sosai jininsa ya hau har bugun zuciyarsa ya fara canjawa. Sai da Mommy ta bashi shawarar yin karatun Alkur'ani sannan ya samu ƴar nutsuwar ganin wayewar gari lafiya. Mommy dai bata san ainahin mike faruwa ba. Amma zuciyarta na bata akan Mawaddat ne, dan a yanzu babu wata damuwa da ke neman kai mijin nata ƙasa sama da al'amarin yarinyar, bayan kuma tun farko shine yay shukar datai tsirran da ya samar da ita a haka.
    A falon baÆ™i da ke a garden kam babu abinda zuciyar Lulu keyi sai bugawa da sauri-sauri. Ga Uncle Yousuf yay matuÆ™ar É—aure fuska ta yanda bata taÉ“a gani da ga garesa ba. Zama tai jiki babu Æ™ari da faÉ—in, “Uncle ganiâ€.
    “Na ganki aiâ€.
   Ya bata amsa shima kai tsaye yana gyara zama. Tambayar da tai matuÆ™ar girgiza mata zuciya ya jefa mata. Babu shiri ta É—ago a firgice ta dubesa. Sake maimaitawa yay babu alamar wasa a tare da shi. “Nace wanene Hon. Haruna Dauda Nakowa a gareki? Miye alaÆ™arku?â€.
  “B...b...bamu da wata alaÆ™a wlhy Uncleâ€. Ta faÉ—a cikin in ina da firgici.
     “Amma yaje neman aurenki ga Baba a daren jiyaâ€.
  “What!! Uncle You aure fa? Ni kuma Mawaddat?!â€.
      Cikin sigar harara Uncle Yousuf ya bata amsa da “K É—in fa, bayan shi kuma Tajuddeen ma ya dawo. Dan a jiya mahaifinsa a gabanmu ya sake gabatar da zancen ku ga Baba. Nasan kuma baki manta da alwashi Baba ba na cewar duk wanda yazo neman aurenki ko da amincewarki ko babu ko da tamu ko babu zai aura masa ke. Kinga hakan na nufin a cikin biyun nan dole ne ki zaÉ“i É—ayaâ€.
    “Wlhy Uncle You bana son kowa a cikinsu. Kuma shi tsinanne Haruna É—in nan ni ban taÉ“a magana da shi ba ma balle maganar aure na rantse maka Uncleâ€.
   “Ni wannan ba matsalata bace Mawaddat. Dan a yanzu haka ma Baba nacan na zaman jiranmu ni da ke da Yaya akan wannan maganar dan haka ma na dakatar da ke daga fita. Idan kuma kina da wanda kike so sai ki faÉ—a mana yanzu mu nemosa aje da shi gaban Baba ki kuÉ“utar da kanki, dan hakanne kawai zai hana Baba bama É—aya da ga cikin waÉ—an can É—in aurenki kamar yanda kika san shi baya magana biyuâ€.........âœï¸
    Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 3ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
........“Na shiga uku Uncle, ni ban shirya yin aure ba wlhy. Dan ALLAH ka faÉ—a mini ya zanyi?â€.
  “To ni Mawaddat taya zan san ya zakiyi. Yanzun ma na faÉ—a miki ne dan bana son a miki abinda nasan baki so. Dan Baba bazai taÉ“a canja ra'ayinsa ba a wannan karon kin sani na sani. Ga kuma Yaya wajen Æ™oÆ™arin ganin ya kare ki sai ya sake wata É“aranÉ“aramar wai kina da wanda kike soâ€.
    Fuska ta kuma kwaÉ“ewa idanunta na cika da Æ™walla. “Uncle You wlhy guduwa zanyiâ€.
  “Guduwa kuma? A ganinki itace mafita Mawaddat?. To ai ina ganin dan kin gudu kinyi a banza, dan in dai Baba ne zai aurar da ke É—in babu fashi ya kuma saka mijin taddaki har inda kika je É—in ko shi yaje da kansa ya dawo da ke ya danÆ™ama mijin. Kinga anyi ba'aiba kenan ko. Ni dai ina ganin kawai mu É—auki kariyar da Yaya ya baki muyi amfani da ita dan ki kuÉ“uta gaba É—ayaâ€.
     “Uncle wacce kenan?â€.
  “Samo wani matsayin wanda kike so kuma zaki aura. Sai dai ni da ke ne kawai muka san ba haka bane, bayan Æ™ura ta lafa shike nan sai ki cigaba da sabgarki, idan Baba yayi magana muce iyayen yaron muke jira dan sunce a É—an jinkirta musu zai Æ™arasa gininsa ko dai mu samo wani abu da zai É—auke hankalin Baba da ga kanki gaba É—ayaâ€
   “Hakan yayi, to amma Uncle kasan fa baba da shegen bin Æ™waÆ™wÆ™wafin abu idan kuma ya gano fa?. Sannan ma wa zamu iya samu ya mana wannan aikin batare da an samu wata matsala ba?â€.
      “Eh kuma fa kema kinzo da maganar dubawa gaskiya. Dan Baba kam zai ma iya sawa ai masa bincike. To amma ina ganin mizai hana shi wanda zamu samar É—in kawai ki yarda kuyi auren contract da shi, komai mune zamu tsara masa ayi auren amma bayan wata É—aya ya rabu da ke, sai dai da sharaÉ—in kada kowa ma yasan ya sake ki har sai bayan wasu shekaru.â€
   Shiru Lulu tai tana auna zancen Uncle É—in nata. Sai dai da ace tana da ilimin addini da ya kamata tai hasashen yin hakan fa zai iya zama kamar ta zurma kanta ne. Amma a maimakon hakan ita wani tunani take da ban, dan tana Æ™iyasta faruwar al'amarin ne cikin sauÆ™i kasancewar a inda ta girma cikin turawa wannan ba komai bane yin auren yarjejeniya.. ganin yanda tai nisa Uncle Yousuf ya katseta da faÉ—in, “Mawaddat bamu da wani isashen lokacin dogon tunani a yanzun faâ€. Firgigit ta dawo hankalinta, sai kuma ta langaÉ“e kai cikin shagwaÉ“a. “Uncle You ni gaba É—aya ma kaina ya kulle ne, dan ban san inda zan samo wanda zamuyi hakan baâ€.
     “To mizai hana ki yarda da batun Tajuddeen kawai, yaron nan yanada hankali da nutsuwa ga ilimi. Yana aikinsa sannan yana matuÆ™ar sonkiâ€.
  “Uncle wlhy ni bana son sa, na tabbatar kuma bazan taÉ“a son shi ba. ALLAH idan aka matsamin kan na auresa zan iya halakash....â€
    “No! no! Kar na sake jin haka. Tunda har baki sonshi shike nan kawai abar maganarsa. Mu koma kan maganar mu kawai ta nemo wanda zai zame mana makamin kuÉ“uta da ga Baba.â€
   “Uncle bazan É“oye maka ba wlhy na tsani duk wani abinda zai haÉ—a mu'mulata da wani namiji bayan ku, balle ma ace mu kasance wai ma'aurata. Impossible hakan ya kasance dan bazan taÉ“a aure ba.â€
    Har cikin rai kalmar (Bazan taÉ“a aure ba) ta daki Uncle Yousuf, dan a karo na farko zuciyarsa ta fara hasaso masa wani al'amari mai girma dangane da Mawaddat É—in. Dolene akwai abinda ya kamata su sani da ke É“oye a Æ™asan zuciyarta, sanin kuma na nufin haÆ™urin bin matakan daya dace. Wannan tunanin ya sashi cigaba da faÉ—in, “Mizai hana muyi amfani da Aliyu, dan yaron nada nutsuwar da bazai taÉ“a iya bamu ciwon kai ba koda anan gabaâ€.
    “Aliyu kuma? Waye shi?â€.
   *_“DRIVERN KIâ€_*
 Fitar kalmar da ga bakinsa da zaburowar zuciyarta tamkar ragabzane a tsakanin jirgi da jirgi a sararin samaniya. Badan Uncle You bane, da bayan zaburar da tai abinda zai biyo baya shine lailayo masa zagi mai kawuna bakwai ta dire masa shi a tsaye sannan ta tisa da wanke fuskarsa da marin da sai ya hango yanda yaÆ™in duniya na uku zai kasance tun kafin lokacin faruwarsa. Sai dai kash furucin ya fito da ga bakin da ko harara bazata iya binsa da ita ba balle É—aukar mataki. Uncle Yousuf da ya zuba mata idanu, sai dai a Æ™asan ransa dariya ce ke cinsa yana dannewa da Æ™yar yay mata nuni da kujera, tare da faÉ—in, “Sit mana kika wani zabura kamar wadda na faÉ—ama mummunar magana. Nifa ba nace dole bane, shawarace kawai dan neman mafita. Amma idan batai miki ba muje kawai dan lokaci ma ya cika gashi ana jirana a office. Kije ki zama cikin shiri da yin sabon tunani akan wani tunda naga baki aminta da zancen shi Aliyu baâ€.
    Bakin data tura gaba ta buÉ—e zatai magana sallamar Daddy ta dakatar da ita. Alamar zip Uncle Yousuf yay mata wai kar Daddy yaji. Daddy da gaba É—aya ya gama jin tattaunawar tasu dan tun É—azun a laÉ“e yake dama sai ya sake fuskewa cikin pretending ya ce, “Wai mi ake tattaunawa ne kuka shige haka shiru?â€.
    Cikin É—an É—age kafaÉ—a Uncle Yousuf ya bashi amsa da “Sirri ne tsakanin baba da Æ´arsa yayaâ€.
   Dariya Daddy yayi, sai kuma ya juya hanyar fita yana faÉ—in, “Oh to bari nayi nan tunda ba'a buÆ™atar najiâ€.
   A karan farko Lulu tai dariya tana mai kamo hannun Daddyn nata cike da shagwaɓa. A haka suka fito suna ƴar dariya.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.