Best / Popular Hausa Novels

Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: FURAR DANKO 1.txt

Chapter 42 of 94

          ★★.....

Sosai mamaki ya dabaibaye Uncle Yousuf da ke sauraren Baba. Dan ya masa bayani ne akan zuwan su M Atik Kumo kafin hukuncin da ya yanke a yanzu-yanzu saboda labarin da ya samu na shirin ɗansa da jikansa. Cikin girmamawa da godiya Uncle Yousuf ya tabbatar masa yanzu nan zai tura a isar da saƙon in sha ALLAHU. Suna yanke wayar kuwa yay kiran abokinsa Coach ɗin su Smart Abdull-Hameed, wanda ta sanadinsa ya fara sanin Smart ɗin dama. Tun yana waya da Hameed ɗin kiran Yayansa (Daddy) ke shigowa, bai ɗaga ba har sai da ya kammala da Hameed ɗin. Wani kiran ne ya sake shigo masa, ya ɗaga yana kaiwa kunne da faɗin, “Yaya irin wannan kira lafiya dai ko?”.
       “Inafa lafiya Yousuf! Wai kaji suma su M Atik Kumo sunzo nemawa ɗansu izinin neman Mawaddat. Anya abunnan na lafiya ne? Ni bama wannan ya damen ba, dan M Atik mutumin kirki ne, ɗan nasa ne kawai sai a hankali, dan wlhy da ace ya kasance mutumin kirki kamar mahaifinsa da hankalina zaifi kwanciya da aura masa Mawaddat fiye da yaron nan daka kawo....”
       Cikin gatse Uncle Yousuf ya ce, “To kodai a bama ɗan M Atik ɗin dama kawai, tunda shi dai ai ba wani abu ya taɓa aikata mana ba. Sannan a a bayyane ban taɓa jin ance ga aibun yaron ba...”
     “No no no Yousuf bar wannan maganar kai dai. Dan wlhy ina gama waya da Baba yanzu na ɗan fara bincike kan yaron wajen wani aminina al'amarin babu daɗin ji, dan akuyace lulluɓe da fatar kura bai gado uban nasa ba. Kayi haƙuri bakwai kushe yaron nan Aliyu nake ba. A'a kawai ina tunanin taya zai iya riƙemun yarinya bashi da aikin yi, danni ban ɗauki direbanci wani abunyi ba face hanyar maƙalewa domin rage matsaloli...”
           “Humm Yaya kenan. Nifa ban tsawwala ba, idan akwai wani da kake ganin hankalinka ya kwanta da shi game da Mawaddat ƙofa a buɗe take ka kawosa mu canjashi da Aliyu dan shi dama bawai ya ɗauki abun da girma bane tunda auren wata ɗaya kacal ne zai saketa, ni kuma na gaji da maimaita magana ɗaya”.
       “Ina ai zancen wani ma bai taso ba auta. Yanzu fa Baba ke sanar min kuma munafukin can abinda yake ƙullawa akan ɗansa. Kaga ko ai bamu da wani isashen lokaci. Mu ƙarasa da Aliyun kawai sai dai zamuyi komai a rubuce da ƙa'idoji dan karma da ga baya wani abu saɓanin wanda akai a rubuce ya biyo baya tunda mun samu Mawaddat ɗin ta amince babu rigima. Sannan zan basu gidan da zasu zauna a kuma canja masa aiki”.
       Sosai takaici yake neman shaƙure wuyan Uncle Yousuf. Amma sai ya danne ya ce, “Nima munyi waya da baban yanzu. Yanda kuma kake so haka za'ayi. Zan cema Aliyun ya tsaya idan ya kawota sai muyi maganar, idan kuma zamu bari ne sai zuwa weekend zaifi a nutse”.
     “Eh weekend ɗin yayi kawai ALLAH ya kaimu”.
    Sallama Uncle Yousuf yay masa tare da kashe wayar gaba ɗaya ma. Takaici yakeji na ɗan uwan nasa da halayyar da yake nunawa akan al'amurin Mawaddat mara fasali. Ya rasa wane irin soyayya yakemata irin haka. Ya kamata ace yayi nadama da neman hanyar gyara. Sai dai kash, nadamar tasa alokacin da ya ganta cikin wani hali ne kawai yake yinta.....

★★.....★

    Duk wannan cakwakiya da ƙura da take cigaba da tashi a wannan yini da ga mai gayya da aiki kam normal ne. Dan tuni ta tattara komai ta watsar ta tattara hankalinta akan case ɗin yarinyar nan da akaima fyaɗe dake neman caza mata kai. Tun bayan isarsu office bata wani zauna ba ta fito suka sake fita. Kasancewar hankalinta ga a inda yake ya sa yau tsakaninta da drivern nata babu masifa. Sun ɗanyi yawace-yawace har kusan bayan sallar la'asar sannan suka koma office. A hanyar komawar ne ya fahimci ana binsu a baya. Da farko bai kawo komai a ransa ba sai da ya ga bayan ta shiga office tai zaman kusan mintina talatin ta fito zai maidata gida a hanya ya sake ganin motar ɗazun ɗin nan dai da napep a biye da su. Yaji a ransa cikin biyu dole ai ɗaya. Kodai su Honorables, ko kuma Alhajin nan da ya sa aka sace shi wancan karan a yau kuma ya ganshi a gidan Baba. Yafi buƙatar ya kaita gida lafiya daga nan koma mizai farun ya faru, dan haka ya take motar ya tsere musu cikin salon canja titi gaba ɗaya..........✍️
         

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣

.......Mawaddat da ke da burin amsar saƙo ta kallesa fuska babu wasa. “Malam miye na canja hanyar? Dalla ka koma tacan ina buƙatar amsar saƙo”.
      Shiru kamar bazai tanka mata ba sai kuma ya bata amsa a taƙaice. “Akwai holdup ta canne, ga shi lokacin sallah ya kusa bana buƙatar rasa jam'i”.
          “To ɗan iya wannan kuma matsalarka ce. Bai kuma damen ba. Ka koma ta inda nace bana buƙatar sharhi”.
      Hanyar ya canja batare da ya sake cemata komai ba, amma kuma ba wadda dai take son abi ɗin ba dai ce. Dan zuciyarsa ta bashi kayan shaye-shayen nata ne zata amsa. Takaici ya turniƙe Lulu. Dama ga gajiya na nuƙurkusarta, ai tuni ta balbale sa da masifa amma yay biris da ita kamar yanda ya saba, bai ƙara tari ba har suka iso gida. Buɗe motar tai a fusace ta fito, dai-dai da shima yana fitowar da nufin buɗe matan. Ta zabga masa uwar harara da wani banzan kallo. Nunashi tai da ɗan yatsa tare da tattaro dukan ƙarfinta na zazzage masa abinda ke a ranta amma ko kalma guda ta gagara fita mata a harshe saboda yanda ya wani tsareta da idanunsa data raɗama suna irin na macizai. Sai lips ɗin ta ne kawai ke rawa kamar wanda ya ɗaureta da idanun nasa. “Kaje na koreka, da ga yau bana buƙatar sake ganin wannan shashashar fuskar taka illiterate velleger...!”
        A hankali ya lumshe idanun nasa sai kuma ya sakar mata wani shegen murmushi da ya kusa fisge mata numfashi gaba ɗaya. Jitai kamar zata zube a wajan tsabar wani ƙudu dun takaici da murmushin sa ya haifar mata. Dan bata fassarashi a komai ba face na rainin wayo. Fahimtar ya samu nasarar ƙular da itan da yake buƙata ya sashi matsota a hankali, cikin ƙasa da murya da wani maidata can ƙasan maƙoshi ya furta, “Oh! Kin fison sake ganin angon naki kawai a ɗakin barcinmu ke nan AMARYA, ba damuwa a bani albashina dan da shi zan biya sadaki”.
         “What!!!” ta faɗa da ƙarfi tare da kai ma fuskarsa mari da gaba ɗaya ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata a jiki. Baya yay cikin wani salon da ta samu iska shuuu, ya ɗago yana murmushi tare da kashe mata ido ɗaya, sai kuma ya nuna fuskar tasa da yatsa yana ɗan sake matsota harda ranƙwafowa kaɗan. “Duk randa wannan hannun ya sauka kan wannan fuskar da sunan mari to kisa a ranki MAZA sun faɗi, faɗuwa irin ta MUTUWA. dan itace kawai damar da ƘYANWA zata iya samun yin birgima a gaban ZAKI yanda take so”. Ya ƙara kashe mata ido ɗaya yana ɗaga mata yatsu biyu da faɗin, “Bye *MATAR ILLITERATE*”. Yay gaba abinsa.
       Yuuuuu!! Lulu ta dinga jin hajijiya na neman kwasarta, wato itace ma ƙyanwar yake nufi. Dariya sosai Uncle Yousuf da ke cikin motar dake a kusa da su batare da sun san akwai mutum a ciki ba ke tuntsurawa harda ƙwalla. Ashe zaton da yakema yaron nan ya wuce nan. Kai jama'a har ya fara tausayin ƴar tasa gaskiya. Dan tabbas akwai babban wasa a wannan tafiya yanzu ne kuma za'a fara. Ganin yanda ta wuce tana haɗa hanya ga hawaye sun wanke mata fuska ya sashi daina dariyar ya buɗe motar ya fito, sai dai duk yanda yake son binta ya haƙura dan lokacin sallah yayi. Ya kai dubansa ga su Smart da ke alwala sai kawai ya nufesu yana gyara yanayinsa kamar bashi ya gama kwasar dariya ba a mota...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.