Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO 1.txt
Chapter 73 of 94
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 7ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
.......Zaune take a falo dafe da kanta dake matuÆ™ar sara mata saboda É“acin rai, a yanda take jinta zata iya aikata komai akan mutumin nan, amma ta zauna tsumayen kiran Daddy ne da yace ta dakacesa, sai dai an shafe kusan mintuna ashirin kenan shiru, hannunta ta janye tare da kallon wayarta da idanunta da sukai wani irin jazur. Wayar ta É—auke da tunanin sake kiran Daddy É—in kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Wayar ta tsaya tana kallo kawai, sai da ta kusa tsinkewa ta iya É—agawa ta kai kunne, sai dai tayi shiru dan in har tai magana kuka ma zai iya Æ™wace mata. Ƙaramin murmushi Uncle Yousuf yay da ga can da bazata iya jiyo sautinsa ba, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “My Daughter yau babu gaisuwa ne?â€.
    Nan ma shiru ta kasa magana. Tofa yasan an kai Æ™ololuwar É“acin rai kenan, dan haka ya sake tausasa harshe cikin komawa serious ya ce, “Mawaddat miya faru? Ko baki da lafiya ne?â€.
       Hawayen da take riÆ™ewa ne tun É—azun suka kufce mata, da rawar murya irin ta mai kuka ta ce, “Papa bazan iya ba, bana son damuwa gida zan dawo. Wannan ba rayuwan da zan iya yi bane...â€
   “Kwantar da hankalinki sanarmin mike faruwa?†ya faÉ—a like bai san komai akai ba. Da Æ™yar ta iya masa bayanin abinda ya farun kamar yanda Daddy ya sanar masa. Anan É—in ma murmushi ya sake yi É“oyayye. Kafin ya ce, “Mawaddat rayuwar aure haka take, a komai ita mace Æ™arÆ™ashin ikon mijinta ta ke, wajib ne kuma yimasa biyayya in har shima bai keta dokar UBANGIJI ba ko jagorantar ta saÉ“a masa. Anan kam ba'a yarda ta masa biyayya ba sam, dan ba'ama wani biyayya ko tarayya wajen saÉ“ama ALLAH......â€
     “Bazai yiwu ba Uncle You, domin ni da kai da shi duk mun san matsayin wannan zaman ba sunansa aure ba, Please Uncle kace masa ya sakeni idan ma bazai yi haka a yau ba zan dawo gida idan kwanakin da akai yarjejeniyar sun cika ya sakenin, zan iya É—aukar komai amma banda kan aiki na, domin shine rayuwata, shine farin ciki na, shine mafarkina, shine babban burina tun kafin nasan kaina, shi waye da rana tsaka zai datse hakan da tunanin nuna gadara ko Æ™arfin ikon abinda bashi da ikon!â€.
    “Mawaddat aure kona kwana É—aya ne sunansa aure, da auren nan baida kimar da za'a kirasa ko kwallonsa da wannan martabar da muhimman mutane basu taru cikin shigar kamala domin É—aurashi ba. Da wasu mutane basu ajiye muhimman ayyukansu ba domin halartarsa. Ki kwantar da hankalinki komai ya tafi cikin tsarin da muke fatansa, Aliyu kuma zanyi magana da shi duk da nasan shima ba son hanaki aikinki yake gaba É—aya ba tunda ya sanar miki next week zakiyu resuming be a good girl mana sweetheart, maybe ma yana tsokanarki ne dan yaga yaya zakiyi. Dan haka ina son ki zama jaruma mana kamar yanda ya sanki.....â€
    “Amma Uncle fitan yanada muhimmanci fa yau. Kasan inada case É—in yarinya da ke aibiti, tun juya kuma ya kamata naje na shigar da case É—in courtâ€.
   “Kar ki damu indai wannan ne yanzu zan fita ni zanje da maman yarinyar mu shigar da Æ™aran, ke kuma sai ki cigaba da shirinki matsayinki na lawyer É—in nata hakan yay miki ko?â€.
      A hankali ta ce, “Ehâ€.
    “Yauwa É—iyar albarka na. Ki daure kinji, kar Aliyu ya samu na tsokanarki, bamma so ki bari yaga hawayen nan, maza ki sharesu ki zauna kurum kamar ba'ai komai ba Kinga kinyi winningâ€.Â
  Ta gamsu da zancen nasa É—ari bisa É—ari, dan dolene itama ta mannama velleger É—in can haukan da sai ya gagara barci a yau. Da ga haka ta miÆ™e bayan sunyi sallama da Uncle Yousuf da ke dariya daga can ta nufi bedroom. Fuskarta taje ta wanko da canja kayanta zuwa wando da riga marasa nauyi na zaman gida, ta sake dawowa falon É—auke da laptop É—inta. Dai-dai nan ya fito shima, alamunsa sun nuna yay wanka dan sanye yake cikin Æ™ananun kaya da sukai matuÆ™ar amsarsa sai Æ™amshinsa mai sanyi da ke tashi. Zaune ya kai idonsa a kanta sai dai fuskarsa babu walwala, duk da taji motsin nasa ko sau É—aya bata nuna alamar hakan ba balle ta É—ago, lap-top É—inta kawai take Æ™oÆ™arin kunnawa. Shi kuma sai ya tsira mata idanun nan nasa na macizai da take kira, Æ™in É—agowar tata bai hanata jin kaifin idanun nasa a kanta ba, amma ta dake ta cigaba da abinda take yi.Â
    “Break fast fa?â€.
   Ya faɗa a dake still dai idanun nasa a kanta. idan kujerar da ya ke zaune ta motsa to itama ta motsa. Cije lips ɗinsa yay yana wani sake ƙanƙance idanunsa a kanta. Kusan minti ɗaya yana kallon nata kafin ya miƙe tsam zuwa inda ta ke, lap-top ɗin ya ɗauke da ga jikinta ya ajiye gefe, karon farko ta ɗago ta kallesa da idanunta da suka kaɗa saboda kukan da tayi, fuskarta na nuna matuƙa ranta a ɓace. Nunawa yay kamar baiga kallon da take masan ba, kafin ta furta abinda ke bakin nata ya kwasheta gaba ɗayanta a cikin hannunsa yayi sama da ita kamar wata ƴar baby, (🤣dama abu ba abu ba sai masifa).
     “Bana son wulaÆ™anci malam miye haka? Dalla sauke niâ€. Ta faÉ—a cikin matsanancin É“acin rai tana kai masa Æ™ananun duka a Æ™irji, amma ko gezau kansa tsaye ya nufi hanyar kitchen da ita, saman cabinet ya direta, ya juya ya sakama Æ™ofar key. Dai-dai ita kuma tana dirowa da ga inda ya É—auratan ta iso ga Æ™ofar. Wani shegen kallo ta watsa masa da faÉ—in, “Matsa minâ€.
  “Idan kinyi abinda nace kenanâ€.
Ya faÉ—a cikin halin ko'in kula yana saka key É—in cikin aljihun wandonsa da jingina da Æ™ofar yana mai harÉ—e Æ™afafunsa waje guda. Ƙarshen É“acin rai Lulu ta gama kaiwa, dan haka cikin kaushin murya ta ce, “Kasan na iya fiye da abinda kake tunanin ka'iya na rashin mutunci ko. Aliyu! Ka buÉ—e Æ™ofar nan ka bani hanya na wuce kafin na saka dana sanin sani naâ€.
     Jikin ƙofar ya bari da ɗan taɓe baki batare da yace komai ba ya nufi frizzier ɗin da ke kitchen ɗin ya buɗe, sai da ya ƙarema kayan ciki kallo sannan ya rufe ya nufi store. Daga sama har ƙasa yake bin store ɗin da aka tsatstsage da kayan abinci kala da iri da kallo shima, har da su doya da airish da ruwa da kayan miya da akaima ajiya irin wadda bazasuyi saurin lalacewa ba. Shi sai abin ma ya so bashi mamaki da dariya, to su da suka jibge waɗan nan kayan matar gidan ta iya abinci ne?....
   Shigowar Lulu a fusace ya saka tunaninsa yankewa, ya juyo gaba ɗayansa yana dubanta, huci take sosai idanunta sun juye gaba ɗaya har wani tara ƙwallan masifa sukeyi. Gashi yanda yaga sun ɗan kumburo tun ɗazun ya fahimci kuka tayi, yaji ba daɗi a ransa, dan sam baya son ganin wani ya shiga damuwa a dalilinsa, sai dai dolene yay abinda yayin dan ya fahimtar da ita da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu komai sai da izini... Da sauri ya dubeta jin tana ƙoƙarin saka hannu a aljihunsa alamar son zaro key. Hannun nata ya riƙe yana ɗan waro idanu waje, duk yanda taso fisgewa bai sakar mata ba sai da ya zare key ɗin da ga aljihun nasa, sai kawai ya maƙalashi jikin belt ɗinsa ta inda yasan bazata ce zata ɗauka ɗin ba yana sakin wani shegen murmushin mugunta. Da sauri ta ɗauke kanta da ga dubansa gaba ɗaya tana jin kamar ta fasa ihu, a zuciyarta kuwa tace (ɗan iska).
    “Yanzu mi zaki dafa mana? Dan yunwa nake ji nikam ga shi nace su Ammah kar su Æ™ara aiko abinci injiki.â€
   Harara ta watsa masa cikin gatsali ta ce, “Ashe zaka mutu da yunwa kuwa a gidan nanâ€.
       “Zadai mu mutu, dan kema dai duk tsiya dole ki nema ai. A yanzu ma haka idan kina son fita da ga kitchen É—in nan ki nema mana abinci, inba hakaba ALLAH anan zamu yiniâ€. Ya Æ™are maganar yana fitowa da ga store É—in. ÆŠaya da ga cikin kujeru huÉ—un da aka sakama table a tsakkiya yaja ya zauna. Hankalinsa kwance ya jawo wayar ya fara buga game É—in ball, ya kuma Æ™ure Æ™arar yanda ta cika kitchen É—in da hayaniya. Lulu data gagara fitowa a store kanta ta dafe, sai faman haÉ—iyar rai take zuciyarta na Æ™una. Ta rasa yaushe ne guy É—in nan yay mata irin wannan rainin har haka, bata taÉ“a haÉ—uwa da mutumin da ke latsata a yanda yake so da gadararsa irinsa ba, ya bala'i bala'in shigar mata hanci da yawa. Gadararsa da son nuna shi É—in wani ne da iya taurin kai na cimata zuciya. Fitowa tai a bisa shawarar da zuciyarta ta bata, ta cije lips É—inta tana jin kamar idan ta Æ™arasa garesa ta shaÆ™esa kawai, amma sai ta ture tunanin gefe. Kujerar dake kallon wadda yake zaune ta dafa cikin É—an sassauta zafinta dan ta fahimci ihun da take masan kamar tunzurashi yake da jin daÉ—in latsata. “Aliyu kafa san aiki nakeyi ka É—akkoni ka kawo nan, kai miyasa baka bambance lokacin shiririta dana serious?â€.
    Batare da ya É—ago ya kalleta ba hankalinsa ma akan game É—in sa ya ce, “Yima mijinki girki ne ba serious ba?â€.
   “Kai kasan mijin ma, Ka bani key na wuce, idan abincin kake so ai kasan gidan abinci, dan in har abinda zan girka zakaci ka siyama kanka wahala dan ban iya ba ma sai kabi wani sarkinâ€.
    “Hummm ashe kuwa in dai ba zakiyi abinda nake so ba kuma ya dace ga matar aure to aikin ma zai gagareki yi ne, duk da a farko banda wannan niyyar. Dan haka kina da zaÉ“i kenan, yin yanda nake so kuma na tsara a gidana, ki samu yanda kike so kema. Ko Æ™in yi, kema ki Æ™i samu. Abinci kuma duk yanda kika iya kiyi zanci a hakan ko baiyi baâ€.
      Luuuu tai da idanunta kamar zata lumshe su sai kuma ta buÉ—e, komai ma ya gundireta, tama rasa yaya zatai da mutumin nan mai shegen taurin kai da gadara. Wai miyasa ma ta amince ne da wannan tsarin da shi? Miyasa bata bada damar a nema wani ba?. Tsaki taja mai Æ™arfi da kai hannu ta dafe kanta, sai kuma ta janye tana mai watsa masa hararar zaka banbance tsakanin aya da tsakkuwa ta bar wajen. Da kallo ya É—an bita ganin ta nufi hanyar store, tana shiga yay mata gwalo da sakin murmushi nan nasa da take kira na mugunta yana kashe ido É—aya a hankali ya ce, “2-0 Madamâ€........âœï¸
  Â
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.