Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 100 of 104

Bayan Kwana Uku ya kama ranar Laraba, ranar ne kuma za'a kawo lefen Neehal daga gidan su Sadik. Tun safe tana kwance akan gado ko falo bata fito ba, balle ta sauka ta ci abinci. A kwanaki ukun nan da suka wuce gaba-ɗaya bata jin daɗi, yanayin feeling ɗin data ke ji a cikin zuciyarta na ƙaruwa. Ji take kamar ta ce ta fasa Auran Sadik Ahmad take so, amma akan me to? Idan so ne ta san tana son Sadik, kuma babu wani abu da yake mata wanda bata jin daɗin sa, kullum cikin ƙoƙarin faranta mata yake, bare ta ce ga dalilin da yasa ta fasa auren sa. Sai daga baya ta gane Auren take tsoro gaba-ɗaya ba Sadik ɗin ne bata so ba. Mama bata bi ta kanta ba ayyukan ta kawai take, ta lura abun nata har da iskanci. Aunty Saudiya ce da suka zo tun safe ita da Aunty A'isha dan taya Mama aiki da kuma jiran masu kawo kayan lefen, duk da Maza ne za su kawo, amma sai an kawo za su tafi. Wajen sha biyu na rana ta shiga ɗakin Neehal, ganin tunda suka zo ba ta ga gilmawar ta ba. Ta zauna a gefen gadon tare da yaye bargon data lullub'e jikinta da shi, ta ce. "Neehal baki da lafiya ne?" Ta buɗe ido jin muryar Aunty'n, ta yunƙura ta tashi zaune tana hawaye. Aunty Sadiya ta ce. "Subhallahi! Neehal meke damun ki?" Ta girgiza kai ta ce, "Babu komai Aunty." Aunty Sadiya ta ce. "Babu komai amma kike kwance kin ƙi tashi kuma gashi kina kuka?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Aunty Sadiya ta kamo hannunta ta ce, "Please talk to me, ko da akwai wata matsala ne?" Ta ce. "No Aunty, just I'm scared" Aunty Sadiya ta ce. "Tsoron me kuma Neehal?" Ta ce. "Na auren nan." Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Ki daina jin wani tsoro babu abun da zai faru Insha Allah, wannan wani yanayi ne da kowacce mace take feeling idan Aurenta ya gabato, wani lokacin kuma shaid'an ne, sai yay ta saka maka wasu abubuwa a cikin ranka game da Auran, ka ji kamar a fasa." Ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. "Ki daina damuwa, ki yi ta addu'a kawai, muma duk mun ji irin wannan yanayin a namu lokacin Auren." Neehal ta gyaɗa mata kai. Aunty Sadiya ta ce, "Yawwa Daughter, ke fa amarya ce, farinciki ya kamata ki dinga yi, kin kusa tafiya gidan masoyinki." Ta rufe fuskarta da duka hannayenta biyu, Aunty Sadiya ta yi dariya tare da miƙewa ta ce. "Ki tashi ki shirya, sai ki sakko ƙasa ki yi breakfast, yau ai ranar farinciki ce bata damuwa ba." Ta amsa mata, tare da saukowa daga kan gadon ta nufi toilet. Zuciyarta na tuna mata exactly watarana kamar wannan, ranar da za'a kawo lefen ta daga gidan su Anwar, amma Allah bai nufa ba aka kashe mata shi. Ta tambayi kanta da faɗin. 'Ko wannan karon za'a bari a kawo mata lefen har a yi bikin nata? ko kuwa shima Sadik ɗin kashe mata shi za'ai?.........✍️
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

âš¡
*6️⃣0️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*

Da yamma Haneefah ta zo gidan, duk da tana fama da laulayi amma ta ce ba zata iya kwana bata ga lefen Besty ba. Bayan sun gaisa da su Mama ta hau sama gurin Neehal. A falo ta tarar da ita idanunta a lumshe tana sauraren karatun Alkur'anin da tasa a speaker. Haneefah ta ƙarasa inda take ta taɓa ta, tare da faɗin. "Amarya." Neehal ta buɗe idonta ta dube ta, ta yi murmushi ta ce. "Na'am Ango." Haneefah ta zauna a kusa da ita, ta ce. "Ya na ganki wani iri, ko baki da lafiya ne?" Neehal ta ce. "A'a k'alau nake, kawai yanayi ne." Haneefah ta ce, "Yanayin me? Ke da ya kamata a zo a tarar kina cikin farinciki da annashuwar kin kusa aure." Ta ƙarashe maganar da dariya. Neehal ta harare ta, ta ce. "Zan bar Maman shine zan dinga farinciki?" Haneefah ta ce. "Wannan duk na ɗan lokaci ne, kina jin zaƙin auren zaki ware, wuyarta ki shiga daga ciki, ke Auran fa da daɗi." Neehal ta ƙara hararar ta, ta ce. "Allah ya shirye ki, kin fi ƙarfi na." Haneefah ta yi dariya ta ce. "Ina Barrister? Na ɗauka zan shigo in same ki kina waya da shi kuna soyewa." Ta sauke numfashi ta ce. "Yana nan k'alau, ba mu jima da yin waya ba, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce. "Yana can Kogi State." Neehal ta ce. "Yaushe zaki koma ke?" Ta ce. "Next week in sha Allah, tunda Monday zamu gama exam." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin ƙoƙarin ganin ta ɓoye Mood ɗin da take ciki. Ta tashi ta sauka ƙasa ta ɗebo mata snacks ɗin da akaiwa masu kawo kayan lefen, ta haɗo mata da drinks.

Bayan Magriba kamar yadda aka ce, su Daddy suka karb'i lefen Neehal a gurin magabatan Sadik, suka kuma saka lokacin biki sati takwas, bayan Babbar Sallah da sati biyu kenan. Ba su wani jima ba suka tafi, Daddy ya sa ma'aikatan gidan suka shigar da kayan part ɗin Mama, aka baje su a falon ƙasa. Aunty Sadiya ta rangad'a guda, gudar da Neehal dake ɗakinta ita da Haneefah sai da suka jiyo. Wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta runtse idanunta ta shiga ambaton Hasbunallahu'wani'imal'wakil' a cikin ranta. Haneefah dake gwagwiyar goruba ta ajiye ta miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki ta fice daga ɗakin da saurin ta. Neehal ta ji wasu hawaye masu d'umi sun zubo a kan kuncinta, wanda ta kasa tantance na farinciki ne ko akasin haka, yau ita ce aka kawo lefen ta, hakan ya nuna mata ta kusa zama mallakin Sadik kenan? Ta kusa aure ita ma?  Kamar amsar tambayar ta sai ga kiran shi ya shigo wayarta. Ta saka hannu ta ɗauki wayar tare da buɗe idonta, ta ƙura wa screen ɗin wayar ido da idanunta dake ganin dishi_dishi saboda hawayen dake cikin su, ganin Sadik ne yake kiran sai ta mayar ta ajiye wayar, haka kawai ta ji bata son yin magana da shi.

Set ɗin akwati ɗai ɗai ɗai har goma sha biyu Sadik ya yo, sai kuma takalma da jakunkuna a cikin manyan adudu ɗin kaba da ake yi yanzu. Su Aunty A'isha fa suka shiga bubbud'ewa suna dubawa cikin farinciki, Haneefah kuma ta shiga yiwa kayan video. Kaya na gani na faɗa masu tsada da kyau aka zuba a lefen, Sadik ya yi ƙoƙari sosai, dan ya kashe kuɗi ba kaɗan ba. Mama ta rasa inda zata saka ranta dan farinciki, ashe za ta ga lefen ƴarta_ta kafin ta mutu, ta shiga addu'ar Allah ya nuna musu ranar bikin lafiya. Har bayan isha'i suna ta aikin kallon kayan, ba su kuma da alamar dainawa, su Dije ma sun fito suna kallon kayan. Sai kod'a kayan da faɗar kyawun su suke. Haneefah dai tana tsakiyar kayan zaune tana ta aikin ɗaukar hotunan su. Suna cikin duba kayan Haneefah ta dubi Mama ta ce. "Mamana yau kina cikin farinciki, dan haka bari na yi amfani da wannan damar na ƙara roƙar ki abun da nake ta nacin roƙon ki in ƙi yarda." Mama ta yi murmushi ta ce. "Haneefah da naci kike amma." Ta yi dariya ta ce. "Ni dai Mama ki amince mu ɗan warwasa, biki lami ai babu daɗi, kamar wadda za ai wa auren dole." Aunty Sadiya ta ce. "Gaskiya Ya Fateemah ki bar su, su warwasa, muma ma je a warwasa da mu." Aunty Aisha ta ce. "Gaskiya dai." Mama ta ce, "Shikenan tunda kun dage, sai a yi kamu kawai." Haneefah ta ce. "Yeee, yawwa Mamanmu, thank you so much, bari mu zo mu zaɓi atamfa mai kyau mu fitar da anko, dan event da anko ya fi kyau." Mama ta ce, "Kina fama da kanki, amma sai shegen son bidiri." Haneefah ta yi murmushi ta ce. "Mama bikin Besty ne fa, aiko jego nake na ajiye ɗan a gefe na wasu kwanaki in sha shagali na." Suka yi dariya Gaba-d'aya, Aunty Sadiya ta ce. "Allah ya shirya ki Haneefah." Suka ci-gaba da tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, a nan Haneefah ta sanar musu Sadik ma ya ce za'a yi dinner, Aunty Sadiya ta ce, ita ma Dinner ya kamata a fitar mata da nata ankon. Anan suka zaɓi atamfar da za'a yi ta kamu da kuma kalar fabric ɗin da k'awayen amarya za su yi na ranar Dinner." Haneefah ta haɗa video na kayan lefen da ankunan bikin ta saka a story. Tare da yin ɗan note na Allah ya sanya Alkhairi da kuma nuna farincikin da take ciki. Har da cewa, Yau tana cikin farinciki bikin besty ya kusa, dan haka ko marin ta akai ba za ta ji haushi ba. Neehal dai tana ɗaki bata san me suke ba, Sallar isha'i ce kawai ta tashe ta, ta tashi ta yi sannan ta koma ta yi kwanciyarta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.