Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 46 of 104

Misalin ƙarfe 2/:30mp Aunty Fauziyya ta aiki Neehal siyan kayan miyan gado, dan shi kaɗai ne aikenta tunda komai na abinci Uncle Umar ya siyo ya dire, sai kuma markad'e idan babu wutar Nepa. Babu musu ta karb'a kamar kodayaushe ta tafi. Yau ma kallon gidansu Ahmad ta yi ta wuce duk kuwa da yanda zuciyarta take azalzalarta akan ta shiga, amma tsoron abun da Uncle Umar zai mata idan Aunty Fauziyya ta faɗa masa yasa take ƙin shiga. Tana shan kwana Motar Ahmad na shigowa layin, cikin tsananin murnar ganinta Ahmad ya taka burki wanda har yasa ta tsorata ta yi baya. Da sauri ya buɗe murfin Motar ya fito, da mamaki ya ce "Princess." Neehal ta washe baki ta ce "Uncle ɗina ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, me yasa kwana biyu ba kya zuwa." Neehal ta ce "Uncle ne ya hana ni, ya mun faɗa sosai, He said in aka ƙara aike na na daɗe sai zane ni." cikin rashin jin daɗi Ahmad ya ce "Ayya I missed you alot dear." Neehal ta ce "Me too Uncle." Ahmad ya ce "Mu je gida in baki cake da sweet ɗinki." Da murnarta ta ce "Toh." Yanayin garin damuna ta fara shigowa dan shekaran jiya ma an yi ruwa, yau ma garin ya yi luf kamar hadari_hadari. Gashashshiyar kaza Ahmad ya bata da yoghurt, Neehal ta zauna ta ci ta k'oshi tay hamdala. Mantawa ta yi da wani tsoron Uncle Umar ta zauna ta shiga yi wa Ahmad hira, shi kuma yana ta aikin murmushi cikin jin daɗi da nishad'i, sai yanzu da ya ganta ma ya ƙara tabbatar da ya yi kewar ta sosai. Kiran sallar la'asar ne ya tashe su, Ahmad ya yi alwala suka fita tare ya rakata ta siyi kayan miyan sannan ya wuce masallaci ita kuma ta nufi gida. Zuwa lokacin hadari ya ƙara haɗuwa sosai har an fara Iska, sauri Neehal tay ta yi kar ruwa ya sauko tana waje, aiko ana idar da Sallah aka fara yayyafi, da gudu ta ƙarasa gidan dan har ta fara jik'ewa, kitchen ta nufa zata ajiye kayan miyan amma sai ta tarar da shi a kulle da mukulli, ga ruwan ya fara ƙarfi. Ƙofar falon ta dawo ta fara bugawa da ƙarfi tana faɗin, "Aunty! Aunty, na dawo ki buɗen ƙofa!" Amma Fauziyya tana ji ta ƙi buɗe ƙofar, gashi kaf tsakar gidan babu gurin fakewa, dan ko toilet babu duka suna cikin ɗaki, kitchen ne kawai kuma ta kulle. Gashi irin gidan nan ne da kana buɗe gate ɗinsa sai tsakar gida babu soro. Haka Neehal ta takure jikinta cikin ruwan dan bata da  yanda zata yi, cikin ikon Allah kuma ruwan ya tsuge kamar da bakin kwarya, Neehal ta runtse ido tana jin saukar ruwan ajikinta. A hankali kuma ya fara ɗaukewa, sai da ya ɗauke dif sannan Aunty Fauziyya ta buɗe ƙofar falon ta fito, Neehal na tsugunne a bakin ƙofar sai rawar ɗari take saboda sanyi ta ci kuka ta gode Allah. Aunty Fauziyya ta ɗauke kayan miyanta tare da faɗin "Kar ki shigar mun ɗaki kina yarari, ki jik'a mun ɗaki." Neehal ta miƙe ta cire komai na jikinta ta shanya a igiya, pant kawai ta bari sannan ta shige falon da sauri. Aunty Fauziyya tay dariyar mugunta ta ce "Gobe ma kya ƙara tafiya gantali Shegiyar yarinya kawai." Ita kam tana shiga ɗaki ta yi toilet ta cire pant ɗin jikinta ta rarumi towel ta ɗaura a jikinta sannan ta tsugunna ta yi fitsarin daya matse ta. Tana fitowa ta hau kan katifa ta ja bargonsu Aiman ta lullub'a. Kafin dare mura ta mata mugun kamu, ranar da tari ta kwana. Washegari duk masifar Aunty Fauziyya ba ta saka ta aiki ba, dan jikin nata ya yi zafi ba kaɗan ba, ta san ma ko ta saka ta ba iyawa zata yi ba shi yasa. Amma ta sha zagi da masifa, a cewarta cutar ma ta ƙarya ce da shegen rakin tsiya. Kwana huɗu ta yi a kwance, a ran na biyar ne ta fara samun sauƙi, shi ma sai da Uncle Umar ya ga ciwon ya ƙi ƙarewa sannan ya kaita chemist aka bata magani, aiko suna tafe yana mitar ta ja masa asarar kuɗin da ya siya mata magani, maganin da ko 1K bai kashe ba, alhalin kuma dukiyarta da duk wata kadararta tana hannunsa. Bayan ta warware aka cigaba da aikenta, kullum sai sun haɗu da Ahmad amma ta daina shiga gidansu sai dai su haɗu a ƙofar gida, yasan lokacin da ake aikenta, dan haka time ɗin yana yi zai fito ƙofar gida ya zauna zaman jiranta, saboda ta bashi labarin dukan da ruwa ya mata har ya sata zazzaɓi akan ta daɗe ranar, shi kuma saboda tsananin  tausayinta shi yasa ya daina tsayar da ita, dan kar a ƙara yi mata wata muguntar. Amma duk da haka bai daina bata abubuwan da yake bata abaya ba, idan ta je gurin mai kayan miyan akwai benci wanda dan customers aka tanade sa, anan take zama ta yi sauri ta cinye abun da ya batan sannan ta koma gida. Haka rayuwa tay ta tafiya da Neehal a gidan Uncle Umar cikin wahala da azaba kala_kala a gurin Aunty Fauziyya, gurin Ahmad kawai take jin daɗi, gashi ta yi magiyar a saka ta a makaranta an ƙi, har ta gaji ma ta dai na, sai ɗan lesson ɗin da Ahmad yake mata atsaitsaye.

Yau ma bayan ta gama shan ayyukanta tana zaune a kitchen tana juya miyar da Aunty Fauziyya take soyawa, ta shiga ɗaki ne shine ta ce Neehal ɗin ta cigaba da juya mata dan kar ta roqe. Wayar Aunty Fauziyya dake kitchen ɗin ce ta fara ringing, cikin ɗan daga murya Neehal ta ce "Aunty ana kiran ki a waya." Aunty Fauziyya bata amsa mata ba sai turo Aiman ta yi ya ɗauko mata wayar, kasancewar yau Friday ce suna gida. Aiman yaro ne mai k'iriniya baya abu cikin nutsuwa ko kaɗan, da gudu ya shigo kitchen ɗin ya ɗauki wayar, ya zo fita ya b'arar da taliyar da Aunty Fauziyya ta tace kafin ta bar kitchen ɗin, fiye da rabin taliyar ya zube a ƙasa. Neehal ta tashi da sauri tana faɗin "Ka ga ka yi ɓari ko?" Aiman bai saurare ta ba ya yi ɗaki da gudu yana kiran uwarsa, Aunty Fauziyya ta taso da sauri tana faɗin "Mene ne." Ya ce "Aunty Neehal ce ta b'arar miki da taliya." Ai bai ƙarasa ba Aunty Fauziyya ta fito a fusace ta shiga kitchen ɗin, Tafa hannuwa ta shiga yi tana faɗin "Eh lallai, tun da ba Ubanki ne ya nemo ba ba kuma Uwarki ce ta dafa ba ai dole ki b'arar." Neehal ta ce "Aunty ba fa ni na b'arar ba Aiman ne." Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce "Rufe mun baki zaki ne bayani ne, shegiya mai baƙin hali, kwashe mun ita tass da hannunki, idan kin gama kuma ki zo ɗaki ki karb'i hukuncinki." Neehal ta sa hannu ta fara kwashe taliyar, ga taliyar sai tururi take saboda ba a daɗe da sauke ta ba, Aunty Fauziyya tana barin kitchen ɗin Neehal ta ɗauki serving spoon mai taga-taga ta cigaba da kwashe wa da shi, saboda hannunta zafi. Sai da ta kwashe duka sannan ta debo ruwa ta d'auraye ta. Ɗakin ta nufa cikin tsoro ta ce "Aunty na gama." Aunty Fauziyya tay wani murmushi ta ce "To ƙaraso mana kika tsaya a bakin ƙofa." Cikin ɗari ɗari Neehal ta ƙarasa idanunta taf da ruwan hawaye. Aunty Fauziyya ta kamo hannunta, kuka ta saka ta ce "Aunty dan Allah ki yi haquri." Aunty Fauziyya ba ta kula ta ba, ta kamo hitar data jona a jikin socket ta ɗora a ƙafar Neehal bayan ta zubawa ƙafar ruwa. Wani irin zirrrrr Neehal ta ji ajikinta na shock ta ji kamar an d'aga ta sama. Ai bata san sanda ta k'wala ihu mai ƙarfi ba tare da fizge jikinta ta fice daga Falon da mugun gudu, gaba-d'aya jikinta rawa yake kamar mazari, cikin fitar hayyaci ta fice daga gidan gaba-d'aya, gudu take da dukkan ƙarfinta gani take kamar Aunty Fauziyya ta biyo ta zata ƙara sa mata shock ajikinta. A ƙofar gidansu Ahmad sukai cikibus, ya dawo daga masallaci da Darduma a hannunsa. Neehal ta ƙarasa gare shi ta riƙe shi gam tare da sakin kuka, har lokacin jikinta rawa yake. A ruɗe Ahmad ya shiga kiran sunanta "Princess! Princess what happened to you?" Yana ƙoƙarin d'agota daga jikinsa, ita kuwa ƙara k'ank'ameshi ta yi. Fahimtar da ya yi a firgice take sai kawai ya sunkuce ta ya shiga cikin gidan da ita. A kan kujera ya kwantar da ita, cikin kulawa ya ƙara tambayar ta da faɗin "Princess mene ya faru? kika fito ko takalmi babu a ƙafarki." Cikin kuka ta ce "Un... Uncle shocking Aunty ta samun a jikina." A ruɗe ya ce "Subhanallah shocking kuma Princess?" Bai jira amsar ta ba ya miƙe da sauri ya nufi ƙaramin kitchen ɗin dake falon ya ɗauko gwangwanin pick milk ta ruwa ya fasa ya juye ta a glass cup, sannan ya fito ya dawo gurin da take a kwance tana ta sauke numfarfashi. Ɗago kanta ya yi ya kafa mata cup ɗin a baki. Ba musu ta shiga sha. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta lumshe idanunta ta koma ta kwanta, Ahmad nata jera mata sannu cikin tsananin tausayinta. Ranshi ba ƙaramin ɓaci ya yi ba yau game da Aunty Fauziyya, ya rasa matsayin da zai ajiye matar akan rashin imani, da Mamy zata ji maganar nan yanda take da zuciya ya san tsaf zata iya kaita a kulle. Ƙura mata ido ya yi da idanunsa da suka fara canza launi saboda ɓacin rai, yana jin wani abu na fizgar zuciyarsa game da ta. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta akai_akai alamun bacci ya ɗauke ta, gyara mata kwanciya ya yi yanda zata fi jin daɗin baccin. Babbar damuwar Ahmad a duniya ɗaya ce a halin yanzu, jibi Sunday zai koma gidansu Abuja, tun last week ya gama abun da ya kawo shi Kano, amma saboda Neehal ya kasa koma wa gida, gashi parent ɗinsa sun matsu ya dawo, kasancewar shi kaɗai ne ɗansu Namiji, dama su biyu ne a gurin iyayensu daga shi sai ƙanwarsa mace, ƙanwar tashi ma ƙarama ce bata fi 4_5 years ba, 20 years ya bata. Sai bayan la'asar Neehal ta farka, ya je masallaci ya dawo ya tatar ta tashi. Ya ƙarasa kusa da ita ya ce "Kin tashi." Ta ce "Ehh, Uncle ka kai ni gurin Mamy na yi wanka, jikina babu daɗi." Ya ce "Mamy bata nan, amma bari na kai ki ki yi anan." Ta ce "Toh." Toilet ɗin dake cikin bedroom ɗinsa ya kai ta, Brush ya bata sabo da toothpaste ta wanke bakinta, sannan ya haɗa mata ruwa mai dumi ta yi wanka. Bayan ta shirya ya kawo mata abinci da drinks ta zauna ta ci. Tana gamawa ta ce "Uncle Thank you so much." Tattausan murmushinsa ya mata ya ce "Say Alhamdulillah." Itama murmushin ta masa ta ce "Alhamdulillah." Sannan ta tashi ta kwashe kayan ta kai kitchen, ta so tafiya gida amma ya zaunar da ita wai ta yi masa hira, ba musu ta zauna tana shan choculate tana masa hirar, shi kuma sai murmushi yake yana mata video a wayarsa. Sai gab da magriba suka fito daga gidan, a ƙofar gidan ya tsaya tare da hard'e hannayensa a ƙirji ya zuba mata ido. Neehal ta ce "Uncle bye." Tare da d'aga masa hannu, numfashi ya sauke cikin wata irin murya ya ce "Princess!" Ta ce "Na'am Uncle ɗina." Kusa da ita ya matso sosai ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce "I love You!" Neehal ta yi murmushi ta ce "Love You too Uncle." Lumshe idonsa ya yi cikin jin daɗi, a hankali kuma ya sunkuyo ya yi kissing forehead ɗinta sannan ya sakar mata hannunta, har ta fara tafiya ya ƙara kiranta, ta dawo da sauri, tsugunna wa ya yi dai dai tsayinta yana kallon cikin idonta ya ce "Princess, promise me you will never forget me in your life." Neehal ta ce "I promised you Uncle." ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai.  Fuskarta ya shafa ya ce "Thank you dear." Neehal ta masa bye_bye sannan ta juya ta fara tafiya, haka kawai ta ji jikinta ya mata wani irin sanyi. Shi kam Ahmad tsayawa ya yi yana kallonta yana jin jikinsa kamar babu laka ba tare da yasan dalili ba. Duk wannan abun da ya faru tsakanin Neehal da Ahmad Uncle Umar yana farkon layin akan machine ɗinsa yana kallonsu cikin tsananin ɓacin rai, yana shago Aunty Fauziyya ta kira shi akan ya zo gida babu lafiya, dan tun safe Neehal ta fita kuma har yanzu bata dawo gida ba, shine fa ba shiri ya baro shagon ya taho, yana shigowa layinsu Ahmad dai-dai lokacin su kuma su Neehal sun fito daga gidansu Ahmad, cikin shock ya tsaida machine ɗinsa ya tsaya yana kallonsu. Neehal ta juyo ta ga ko Ahmad ya shige gida idanunta suka sauka akan Uncle Umar wanda ya figo machine ɗinsa a fusace ya biyo bayanta..........✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.