Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 104
Ƙarfe 12 na rana Mama su na zaune a falo ita da Hajiya da uncle Mahmud da ya zo shima dan karÉ“ar lefen É—in, wayar ta shiga ringing, É—auka ta yi ta duba ta ga Ammin Anwar ce ke kiranta, murmushi ta yi ta d'aga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama, ba tare da Ammi ta amsa sallamar da Mama ta mata ba, cikin tsananin ruÉ—u da matsanancin tashin hankali ta ce..........âœï¸
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
0ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
Doctor an..an...an ka..kashe An...Anwarrrr!' ta fad'i maganar a rarrabe saboda tsananin tashin hankali. Suman zaune Mama ta yi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu, Ammi ba ta jira amsar Mama ba ta katse wayar. Ita kuwa Mama wayar ma sakin ta ta yi ta fad'i ƙasa. Ganin yanda Mama ta k'ame kamar gunki ga kuma wayarta da ta saka ta faɗi ya sa Hajiya a ruɗe ta ce "Ke lafiyar ki kuwa, kika zuba mana na mujiya ga waya kin saki ta fad'i ƙasa?" Uncle Mahmud da ya fuskanci da akwai wata matsalar ya taso ya dawo kusa da Mama, ganin yanda ta sandare sai ya ɗan girgiza ta, wani nannauyen numfashi ta ja ta sauke, saitin zuciyarta ta dafe da hannunta jin yanda ta ke bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga k'irjinta, sai a sannan wani uban gumi ya fara tsatstsafo mata ta ko wanne k'ofofin gashi na jikinta, duk da sanyin Ac'n dake falon. Kallo ɗaya za ka yiwa Mama a wannan lokacin ka hango zallar tashin hankali da ɗimuwar da take ciki, gabad'aya ta rasa a duniyar da take jinin jikinta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta ta cak da aiki. Ganin yanayin Mama Uncle Mahmud ya ƙara tabbatar da ba k'alau ba, a ɗan ruɗe ya ce "Doctor lafiya kuwa, me ke faruwa ne?" Mama ba ta bashi amsa ba, numfarfashi kawai take saukewa. A ruɗe Hajiya ta ce "Na shiga uku Ni Zainaba, Fatima ki faɗa mana me ya faru mana, yanayin da ki ka koma Lokaci ɗaya ya tada mana hankali" Mama ta runtse idanunta ta ce "Anwar ya rasu!" A gigice Hajiya ta mik'e tsaye ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta ce "Innalillahi_wa'inna'ilaihirraji'un, wanne Anwar d'in?, kar dai ki ce mun na Neehal" Uncle Mahmud innalillahi kawai ya shiga maimaitawa a fili domin mutuwar ta bige shi ba kaɗan ba, Hajiya ta saka kuka ta na salati ta ce "Allah ya ji ƙanka Anwar yaron kirki, mai biyayya, Allah ya sa aljannah ta zamo makoma a gareka, Ni Zainabu yaya Neehal za ta ji mutuwar nan?" Daidai nan Dad ya shigo falon a firgice, ganin yanayin su ya tabbatar masa da su ma sun ji mutuwar.
Mama ta shafe wasu mintuna a zaune a gurin, abu biyu ne yake ƙara dugunzuma mata hankali a kan mutuwar Anwar, na farko cewa da Ammi ta yi an kashe shi, na biyu kuma halin da Neehal za ta shiga idan wannan mummunan labarin ya riske ta. Hajiya kuwa ban da kuka babu abin da take, Dad ma kallo ɗaya mutum zai masa ya gane ya na cikin tsananin tashin hankalin mutuwar Anwar ɗin, musamman idan ya tuna halin da daughter d'insa za ta shiga idan ta ji mutuwar, Uncle Mahmud ne ma mai dauriyar cikin su, amma babu ƙarya wannan ahali mutuwar Anwar ya dake su ba kaɗan ba. Da k'yar Mama ta yi ƙarfin halin kiran Aunty Sadiya da Aunty A'isha ta sanar musu, su ma sun shiga tashin hankali da jin mutuwar Anwar d'in ba kaɗan ba, Ameen kuwa ta yi ta neman Number'nsa amma ba ta shiga, kuma duka layikansa ta yi ta gwadawa amma sun ƙi tafiya, dole sai haƙura ta yi ta ajiye wayar ta fara tunanin hanyar da za ta sanar da Neehal.
Neehal yau tunda ta tashi take jin wata irin faduwar gaba na riskar ta, shi ya sa ma ta shirya ta tafi gurin aiki, ko idan tana cikin mutane za ta ji sauƙin abin da yake damunta, amma tunda ta je gurin aikin ta kasa tab'uka komai, wayar da su ka yi da Anwar ne ma da safen nan ta ɗan sanyaya mata rai, kowa ya ganta sai ya yi mata sannu, dan su duk ɗaukarsu rashin lafiyar da take ne. Haneefah na tsaka da aiki, Mama ta kira ta, ba ta d'aga ba ta bari idan ta gama sai ta kira ta, ganin kiran da Maman take mata ba k'ak'k'autawa ya sa ta ɗaukar excuse ta fita ta d'aga kiran,Mama cikin dauriya dan kar Haneefah ta fuskanci da wata matsalar tace "Haneefah ku taho gida yanzu ke da Neehal" ba ta jira amsar Hannefan ba ta katse wayar, duk da Mama ta yi ƙoƙarin b'oye damuwarta amma sai da Haneefah ta fuskanci akwai wani abu a Muryar Maman, office d'in da Neehal ta ke ta nufa da sauri, Neehal ta na zaune ta kwantar da kanta a kan table ɗin office Haneefah ta shigo, taɓa ta yi ta na faɗin "Neehal taso mu koma gida tunda ba ki da lafiya" Neehal ba ta yi musu ba dan ita ma ta na bukatar zuwan gidan, dan har wani jiri_jiri ta ke ji daga zaunen da take, d'ago da kanta ta yi a hankali, wayarta ta ɗauka jikinta a matukar sanyaye ta zira a cikin jakarta, ganin yanda take Haneefah ta kama ta suka fito daga office din, Manager d'in gidan TV Haneefah ta sama ta masa bayani, sannu ya yi wa Neehal sannan ya haɗa su da ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan TV'n ya kai su gida.
Mama ce kaɗai a falo tana zaune ta na hawaye, su Dad sun wuce gidansu Anwar harda Hajiya da ta dage sai ta bi su. Jin shigowar su Neehal ya sa tai saurin share hawayen fuskarta ta mik'e tsaye, ganin yanayin Neehal gabanta ya faɗi, dan ta yi tunanin ko ta ji mutuwar ne, Haneefah ta ce "Mama ga ta mun dawo, nima dama tun d'azu nake son na ce mata ta dawo gidan saboda jikinta, sai kuma gashi kin kira ni" Mama ta kama Neehal a jikinta ta rungume, ta na sakin ajiyar zuciya jin ba su ji mutuwar ba, Haneefah kallon Mama kawai take yi ganin yanayinta, hakan ya tabbatar mata da tabbas da akwai wata matsalar ba iya ciwon Neehal ɗinne ya maida Mama haka ba, Neehal kuwa luf ta yi a k'irjin Mama ta na sauke ajiyar zuciya, wayar Mama ce ta yi ƙara, hakan ya sa ta sakin Neehal da sauri ta zaunar da ita, Dad ne ke kiran ta, ɗagawa ta yi ta kara wayar a kunne, daga ɗaya ɓangaren Dad ya ce "Doctor, Neehal d'in sun dawo?" Mama ta ce "Eh." Dad ya ce "To ku taho yanzu an kawo gawar." Mama ta ce "Ohk ga mu nan." Daga haka ta katse wayar, dama ta ce wa Dad idan ankawo gawar su kirata dan gawar ta na asibiti fiye da awa biyu Police na binkice a kanta, sai yanzu aka ba da ita. Mama da ma da hijabinta a jikinta, mukullin Motor kawai ta ɗauka ta dubesu ta ce "Ku taso mu je" Kallon ta Neehal ta yi cikin mamaki amma ba ta ce komai ba, sai Haneefah ce ta ce "Ina zamu Mama?" Mama ta ɓata rai ta ce "Siyar da ku zan yi" Haneefah ba ta ƙara cewa komai ba, ta kama hannun Neehal suka bi bayan Mama, a tunanin Haneefah asibiti za su itama Neehal haka. A bayan Motor suka tarar da Mama, sai driver a gaba, suma bayan suka shiga. Tunda suka shiga Motar idanun Neehal a lumshe suke, Haneefah ce ma take ɗan kallo hanya, a tunaninta Nasarawa Hospital za su sai ta ga sun yi hanyar Hotoro ba ta kawo komai a ranta ba, sai da ta ga sun shiga layinsu Anwar sannan ta fara tambayar kanta a kan mai kuma za su yi a gidan su Anwar d'in, gabanta ne ya yanke ya faɗi Lokacin da driver ya yi parking a ƙofar gate ɗin gidansu Anwar, ga mutane an taro a na ta d'aura rumfuna, duk wata alama da za nuna mutuwa a ka yi a gidan Haneefah ta gan ta, sai dai ko kaɗan ba ta yi tunanin Anwar ne ya mutu ba, ta yi tunanin dai wani dabanne a gidan, tunda mahaifinsu already ya rasu balle ta ce ko shine. Mama ta buɗe Motar ta fita, Neehal ta biyo ta ita ma ta fito, sai da ta fito ta gane inda suka zo, Mama ta kama hannunta kawai ganin yanda take jujjuya idanunta ta na bin layin da kallo kamar wata doluwa suka nufi cikin gidan, Haneefah jiki a sanyaye ta fito ta bi bayansu. Bin Mama kawai suke zuciyoyinsu na bugawa har suka shiga part ɗin Mahaifiyar Anwar inda suka tarar da Mutane damk'am a falon an yi jugum_jugum, masu kuka na yi masu salati na yi, Kakarsu Anwar ta na hango su Neehal ta rushe da kuka, cikin kukan ta ce, "Allah sarki, ga yarinyar da Anwar zai aura nan, Allah ya ji ƙanka Anwar, Allah ya saka mana, ya tona asirin azzaluman da suka kashe ka" ta ci gaba da rizgar kukanta, wani irin wul Neehal ta ji a kanta kamar an ɗora mata dutse, k'wace hannunta ta yi daga na Mama ta yi baya za ta faɗi, cikin dauriya Mama ta ruk'ota da sauri, Haneefah kuwa tuni ta durk'ushe a ƙasa dan ƙafafuwanta ba za ta su iya ɗaukar ta ba, jin wai Anwar ne ya mutu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.