Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 104

"Tunda ba ki kira ni kin ji ya na je gida ba, ni na kira ki na ji dafatan na barki lafiya."

Neehal ta sauke ajiyar zuciya dan ta gane Sadik ne, a hankali ta ce "Am sorry, tunda muka rabu aiki nake yi ne shi yasa." Sadik ya ce "Ok, amma ko ba haka ba nasan ko Number ta ba ki da shi." Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba. jin ta yi shiru ya ce "Ki je ki cigaba da abun da ki ke yi, sai da safe." Neehal ta ce "Allah ya kai mu, thank you." SadiÆ™ ya ce "Gud night daga haka ya kashe wayar."

.Washegari Friday Neehal ta dawo daga gurin aiki da yamma, ta na shiga Falon Mama ta ga Ameen zaune a kan kujera ya na latsa wayarsa, Neehal ta waro manyan idanunta cikin mamakin ganin sa, domin ba ya dawowa Ranar Friday sai dai Saturday or Sunday. Cikin murnar ganinsa ta nufi gurin shi ta na faÉ—in "Yaya yaushe ka zo.?" Kamar ba da shi take ba, ko d'ago kai ya kalleta ma bai yi ba, balle ya ba ta amsa. Neehal ta turo baki gaba ta wuce sama. Wannan weekend d'in gabad'aya Ameen ya É—auke wa Neehal wuta, ko gaishe sa ta yi ba ya amsawa. Ita kam Neehal ko a jikinta domin ta saba da wannan halin nasa, idan muskilancin nasa ya motsa.

*****************

Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu a first semester Level 3, Neehal da Haneefah tare suke tafiya a matakin karatu, sai dai ba department d'aya suke ba, Neehal ta na Department of Mass communication, ita kuma Haneefan ta na karantar Law ne. Neehal zuwa yanzu ta fara sabawa da Sadik, domin Sadik cikin 1 Month sai da yasan yanda ya yi ya shiga jikinta sosai, sam bai nuna mata sonta yake ba, suna mu'amalane a matsayin Yaya da K'anwa. Sosai Neehal take jin daɗin tarayya da Sadik, kusan kullum sai ya zo sun sha hira, ya yi ta bata labaran ban dariya da nishad'i, wani lokacin kuma idan an bata assignment a school tare suke yi, wani lokacin kuma ya yi ta tsokanarta ita kuma tai ta ɓata rai ta na turo baki gaba, haka za su rabu ta na fushi da shi, sai bayan ya tafi ya kira ta ya lallab'ata su shirya. A hankali kaso mafi yawa na damuwar rashin Anwar ya fara barin zuciyarta a sanadiyyar shigowar Sadik cikin rayuwarta.........✍️
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *⚡NEEHAL ⚡*

_By_
_Zeey Kumurya_

1️⃣5️⃣

Ina ma'abota karatun littattafan HAUSA masu ilimantarwa ,nishaɗantarwa,wa'azantarwa gami da sa canjin rrayuwa🗣️🗣️🗣️.

AƘIDATA! AƘIDATA!! AƘIDATA!!!.

Idan baki karanta ba inason nabaki shawarar ki nemi naki
.

AƘIDATA! Labarin wata haɗaɗɗiyar hamshaƙiya ƴar hamshaƙin mai kuɗi ce😍gata da izzah, taƙama,gadara,iko,ilimi,wayo da sauransu🥳Amma duk da wannan halaye nata tana da wasu wanda taɗaukesu AƘIDARTA, Akwai takun saƙa tsakaninta da matar babanta da kuma agololin da tazo dasu🥺

Ana bibiyar rayuwarta ta ko'ina hakan yasa rayuwarta taƙare aƙasar waje🥳
Bata da abokai da suka wuce dabbobi zomaye,maguna,tattabaru,dasauransu🥳sune abokan dariyarta da kukanta kuma suke ɗebe mata kewa🥳🥳🥳🥳

Bata tausasa lafazi ga kowa ciki kuwa hadda ma'aifinta ciki 🥳🥳🥳

🥳🥳🥳🥳Cikin rashin yaddarta tasaki jiki da direbanta wanda shine masomin ƙaddararsu 😳😳bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koyaci amanarta🥳🥳shin mezai faru idan tasan direbanta ma'aikacin sirri ne❔❔❔❔❔

Kutsen ƙaddara ya kutso rayuwarta ba tare da ta shirya ba, rayuwarta takoma wani gari dako ruwan famfo babu, sedai kududdufi wanda ake wanka da wanki aciki shine ruwan amfanin garin....  😳alhalin ita idanba ruwan jarka ba batasaba shan wani ruwaba🥳🥳🥳🥳🥳

Sabulun wanka kansa babu semai ƙarni alhalin tasaba wanka da shower jell🥳🥳🥳🥳🥳

Akwai tarin sarƙaƙiya da ƙulle ƙulle a cikin wannan labari me ban al'ajabi

ƘAƘA ƘARA ƘAƘA🥺🥺🥺

WIDAD🥳WIDAD🥳WIDAD🥳

Duk me son jin cikakken kabarin Widad da mahaifinta NASIR DAULA yanemi 2&3 akan farashi ƙalilan🥳🥳🥳🥳🥳daman part 1🥳🥳kyauta ne meso taimin magana nabata🥰🥰💞💞

LALLAI 🥳AYSHERCOOL ✍🏻ta dabance basirarta bazaka ganeta ba seka kranta AƘIDATA domin ta farantawa mu masoyanta fie da yadda tay AWATA KISSAR........! SAI MATA😊😊.

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻AƘIDATA TAYYI DABAN DATA KOWA🥳🥳

Normal gro duka littafi biyun #300
Idan kuma laya zaki siya #200

Vip #500.

Idan kuma se angama zaki siyi complete documment #700.

Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank

Se aturo evidence of payment through 07063065680.

Share please🙏🏻🙏🏻🙏🏻.

Neehal ce zaune a office d'inta ta na operating system, sai sauke numfashi take akai_akai alamun wani abu na damunta. Haneefah dake zaune a kujerar da take fuskantar ta tana latsa waya, lokaci zuwa lokaci ta na d'agowa ta na kallon ta. Ajiye wayar ta yi a kan table ɗin gabanta cikin kulawa ta ce "Wai Neehal meke damun ki ne.?" Ba tare da Neehal ta d'ago ba ta ce "Babu komai, me ki ka gani.?" Haneefah ta ce "Yanayinki ya nuna kamar wani abu na damun ki." Neehal ta ce "Babu gaskiya, idan ma da akwai ba zai wuce Rashin jin Ya Sadik ba ne da banyi ba yau." Haneefah ta ce "Kamarya rashin Ya Sadik.?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Tun jiya da yamma da muka yi waya har yanzu bai ƙara kira na ba, gashi last seen ɗinsa a WhatsApp tun 6:44 pm na jiya" Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ganin haƙansu ya kusa cimma ruwa ita da Sadik, domin ita ta bashi shawarar ka da ya nunawa Neehal ya na sonta a yanzu, ya bari sai ta shak'u da shi sosai sai ya sanar mata. Ita kuwa Neehal baiwar Allah, maganarta take bil hak'k'i ba tare da tunanin komai ba. "To ki kira shi mana ki ji ko lafiya." Cewar Haneefah cikin nazartar ta. Neehal ta ce "Kuma fa hakane, bari mu koma gida zan kira shi." Haneefah ta ce "To, Allah ya sa lafiya dai." Neehal ta ce "Amin." Bayan sun koma gida da yamma wanka kawai Neehal ta yi ta kira layukan Sadik amma duka ba sa tafiya. Zama ta yi a bakin gado tare da dafe kanta cikin damuwa, can kuma ta ja ɗan ƙaramin tsaki ganin damurwar na neman hana ta sukuni. A fili ta ce "To mene ma na damuwar haka akan shi.?" "Sadik ya cancanci ki damu dashi fiye da haka ma, duba da tarin kyautatawarsa a gare ki, gami da kulawar da yake nuna miki." Wata zuciyar ta ba ta amsa da faɗin haka. Mik'ewa tsaye ta yi zumbur kamar an tsikareta ta na sauke ajiyar zuciya, saboda wani tunani da ya ɗarsu a ranta. Wata doguwar rigar abaya purple color ta ɗakko ta zira a jikinta, turarukanta ta mutstsika ta yane kanta da ɗankwalin abayar, wayoyinta kawai ta kwasa a hannunta ta fice daga d'akin. A falon ƙasa ta tarar da Mama. "Ke ina zaki haka ki ke sauri kamar za ki tashi sama.?" Mama dake kallon Neehal tunda ta fara sakkowa daga kan steps ta fad'i haka." Neehal ta tattaro nutsuwarta ta na ɗan sosa kanta ta ce "Gidan Aunty za ni, kuma sauri nake saboda in yi in dawo da wuri." Cikin mamaki Mama ta ce "Gidan Aisha kuma da wannan sakaliyar yammar? Daga dawowarki daga aiki ko abinci ba ki ci ba.?" Neehal ta yi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Mama ta ce "Me ma za ki yi a gidan A'ishan?" Neehal ta ce "Gaishe ta zan yi, na dad'e ban je ba." Mama ta mata kallon tsaf ta ce "Ki bari gobe kya je." Neehal ta ce "Gobe fa sai six zan dawo daga school." Mama ta ce "To kya je wani time ɗin." Neehal ta marairaice ta ce "Please Mama." Mama ta ce "Ba fa za ki fita ba Neehal a yamman nan, idan Dad ɗinki ya dawo me zan ce masa?" Neehal ta turo baki gaba ta juya za ta koma sama. Mama ta katse ta ta hanyar faɗin. "Ki shiga kitchen ki zubo abinci ki ci." Neehal ta yi hanyar kitchen ba tare da ta ce komai ba, abincin ta ɗebo kaɗan ta koma sama. Ta na shiga ɗakinta ta ajiye shi a kan bedside ta hau gado ta kwanta, sosai ta ji takaicin hana ta zuwa da Mama ta yi har da 'yar k'wallarta, kiran Sallar Magriba ne ya tada ta. Bayan ta idar da Sallah ta ɗakko abincin ta fara ci, sai kuma yanzu take jin haushin kanta na damuwar da ta yi akan kawai yau rana ɗaya dan ba su yi waya da Sadik ba, tambayar kanta ma ta yi inda ta je unguwar su Aunty A'ishan gidansu Sadik ɗin za ta je neman sa ko kuma yaya? Sakin ranta ta yi ta cigaba da sabgarta duk da kewar Sadik ɗin na nuk'urk'usar ranta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.