Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 75 of 104
Mama ta dafe kanta tana sauke numfashi, zuciyarta cike da d'oki da zumud'in jin asalin zancen, domin tana san wa ya kashe su Abba ko kuma wa ya turo a kashe su, da kuma son sanin ko mutum ɗaya ne ya yi kisan su Abba da su Anwar? A ɓangaren Aunty A'isha itama tunanin da take yi kenan. miƙewa Mama ta yi ta nufi part ɗin Daddy cikin sauri dan ta sanar masa halin da ake ciki.
Cike da mamaki da kaɗuwa Daddy yake duban Mama bayan ta gama sanar masa da abun da yake faruwa. Zuwa can ya nisa ya ce "Allah buwayi gagara misali, dama an ce duk wanda yay kisan kai da wuya ya mutu Ubangiji bai toni asirinsa ba, saboda haqqin rai ba ya taɓa barin mutum ya zauna lafiya a duniya." Mama ta ce "Wannan haka yake, Allah ka raba mu da mummunar ƙaddarar da zata kai mu ga dana sani, su kuma azzaluman mutane irin waɗannan Allah ka cigaba da tona musu asiri!" Daddy ya ce "Amin Amin Doctor." Mama ta cigaba da magana. "Mutum bai ji ba bai gani ba kawai saboda rashin imani a zo har cikin gidansa a kashe shi saboda neman duniyar da kowa sai ya bar ta, mutane ba sa tuna Allah a ransu, ba sa tunanin inda suka kashe mutum ya je suma komai daren dad'ewa za su je." Cikin jimantawa Daddy ya ce "Ai ke dai ki bar mutum kawai Doctor, amma in dai duniya ce gata nan ta ishi kowa, kuma Duk *abin da mutum ya shuka* dai *shi zai girba* , walau na sharri ko na Alkhairi." Sun zanta akan al'amarin sosai sannan Mama ta miƙe dan zuwa ta sanar da Neehal itama.
Tana kwance ruf da ciki akan gadonta, system ɗinta na gabanta tana latsa ta cikin kwarewa, idanunta sanye da siririn glass mai ɗan duhu, wanda bata fiya amfani da shi ba, sai irin wannan lokacin idan zata yi using da laptop. Mama ta shigo ɗakin tare da zama a bakin gadon bayan ta yi sallama. Neehal ta amsa mata tare da tashi zaune ta cire glass ɗin fuskarta ta ajiye a gefen ta. Mama ta ce "Aikin ne har yanzu baki gama ba." Ta ce "Na kusa ƙarasawa saura kaɗan, zuwan Uncle Ahmad ne ma ya tsayar da ni." Jinjina kai Mama ta yi tare da juyowa ta fuskance ta sosai ta ce "D'azu Auntinki ta kira ni take sanar mun an kama waɗanda suka kashe su Ummanki." Neehal ta waro Ido waje cikin kaɗuwa ta ce "Su waye Mama?" Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Aunty A'isha ta sanar mata. Kuka ta saka cikin kukan take faɗin "Mama me su Umma suka musu da suka kashe su? Su waye waɗannan mutanen da suka raba ni da mahaifana rabuwa ta har abada a rana ɗaya? Me nay musu suka zaɓi mayar da ni marainiya?" Kuka take sosai mai ban tausayi, mutuwar su Umma ta dawo mata sabuwa fil a cikin ranta, duk da a lokacin da suka rasu tana ƙarama amma har yanzu ba ta daina hango gawar iyayenta kwance cikin jini ta acikin idanunta ba, kuma har ta koma ga mahaliccinta ba za ta taɓa mantawa ba. Mama ta rungume ta a jikinta cikin tsananin tausayinta, tare da rarrashinta da kalamai masu taushi har ta samu ta bar kukan. Mama ta d'ago ta tana share mata hawaye ta ce "Komai rubutacce ne daga Allah, Ubangiji ya riga ya tsara rana ɗaya Umma da Abba za su rasu kuma a lokaci ɗaya, ko da waɗan can Mutanen ba su kashe su ba idan kwanan su ya ƙare dole su bar duniya. Dan haka addu'ar mu kawai suke buƙata a halin yanzu, ita ce kawai soyayyar da za mu nuna musu. Mutuwa dole ce Neehal, mu ma nan zaman jiranta muke, fatanmu Allah yasa ta zo mana cikin sauqi." Cikin matuƙar sanyin jiki Neehal ta ce "Haka ne Mama, Allah ya ji k'an Umma da Abba da ma dukkan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya, mu kuma Allah yasa mu cika da imani." Mama ta ce "Ameen dan darajar Annabi." Lumshe idonta ta yi bata kuma cewa komai ba, cikin zuciyarta kuwa ji take dama a bata dama ta kashe azzaluman mutanen da suka kashe mata iyaye da hannunta, saboda wata muguwar tsanar su data cika mata zuciya. A hankali ta yi baya ta kwanta akan gadon saboda sarawar da ta ji kanta ya yi mata lokaci ɗaya. Mama ta janyo system ɗin da take amfani da ita ta yi saved na aikin da take sannan ta kashe ta, ta ɗora ta akan bedside locker. Shafa fuskar Neehal ta yi cikin raunin zuciya da tausayinta, cikin kulawa ta ce "Ki yi addu'a idan kina jin zuciyarki babu daɗi ba wai ki yi kuka ba, idan kin kasa barci kar ki kwanta ki yi ta tunane_tunane, ki tashi ki kaiwa Allah Kukanki." Ta gyaɗa mata kai ba tare data buɗe idonta ba. Mama ta kashe mata light ɗin ɗakin sannan ta fice zuciyarta babu daɗi. Iyayenka ko da ace baka san su ba kana jariri suka rasu idan ka girma aka baka labarinsu dole ka ji feeling a kansu da son kasance tare da su, balle ita da tana da ɗan wayonta suka rasu, dole abun ya dinga taɓa mata zuciya. Kuma da a ce mutuwa suka yi kamar kowa ba kashe su a kay ba, abun ba zai dinga damun ta over ba. Amma yanzu gani zata dinga yi kamar da ba'a kashe su ba da suna raye har yanzu....
Washegari kafin ƙarfe goma sha ɗaya na safe sun gama shiryawa dan zuwa gidan Alhaji Ali, Neehal dai kamar mai cuta komai a sanyaye take yin sa. Daren jiya kam ko wayar love ɗin data saba bata iya yi ba, da ta tashi da safen nan ma ko bi takan wayar bata yi ba. Sai da Mama ta ce mata ta kira gurin aikinsu ta sanar musu ba zata samu damar zuwa yau ba sannan ta ɗauki wayar. A time ɗin ne ta ga missed call ɗin Sadik, Ahmad har ma da Ameen wanda kiran nasa ya bata mamaki. Ahmad kam har da text yay mata ya sanar mata ya wuce Abuja, dama tun jiya ya faɗa mata sammako zai yi ya koma. Bata bi kiran ko ɗaya daga cikinsu ba saboda tana cikin mood ɗin da ko doguwar magana bata son yi.
A lokacin itama Aunty A'isha ta ƙaraso gidan, bayan sun gaggaisa suka rankaya suka tafi a Motar Mama wanda direban Maman ne zai kai su. Suna tafe suna ƙara jimanta al'amarin a tsakanin su. Neehal dai ta yi shiru kawai tana sauran su. Aunty A'isha ta dube ta, ta ce "Daughter baki da lafiya ne?" Mama ce ta bata amsa da faɗin "Tun jiya dana faɗa mata zancen nan shine duk ta koma haka." Aunty A'isha da itama dauriya kawai take dan mutuwar tsohon Mijin nata da abokiyar zamanta ta dawo mata sabuwa dal a ranta. Ta kwantar da kan Neehal a ƙafaɗarta bata ce komai ba. Mama ta ce "Na kira Hajiya na faɗa mata, ta ce zata zo kafin Monday a yi zaman kotu da ita." Aunty A'isha ta ce "Allah ya kai mu, ya kuma sa a ƙarƙare shari'ar a ranar, kin san shari'ar ƙasar nan tsaf zasu iya cewa sun d'age shari'ar." Mama ta ce "Ai tunda waɗanda suka yi laifi sun amsa babu buƙatar wani jan magana na daban, hukunci kawai za'a yanke musu dai_dai da abun da suka aikata." Aunty A'isha ta ce "Haka muke fata dama." Bayan sun ƙarasa gidan Alh Ali Aunty A'isha ta kira shi ta sanar masa, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidansa ya aiko ya shigar da su. A wani babban falo aka sauke su, dattijuwar matarsa ta karɓe su hannu bibbiyu dan ta san da zuwan nasu. Alh.Ali ya yi mata bayanin komai. Kuma ta shaida fuskar Aunty A'isha dan kafin Abba ya rasu suna ɗan zuwa tsohon gidansu idan abu ya samu. Tana ganin Neehal ta ce "Wannan yarinya kamar an tsaga kara ita da mahaifiyarta." Da kanta ta yi musu jagora har falon Alhaji Ali. Yana zaune shi kaɗai a falon yana kallon labarai suka yi sallama, ya amsa musu cikin sakin fuska. Suka ƙarasa suka zauna matar tasa ta ce "Ga iyalan Alh.Muhammad sun ƙaraso." ya yi murmushi yana duban Neehal ya ce "Masha Allah, wannan ce Amaryar tawa?" Suka yi murmushi dukan su, Neehal ta ƙarasa ta tsugunna a gabansa ta gaishe shi. Ya amsa mata cikin fara'a da kulawa, su Mama ma suka gaishe shi, ya amsa musu. Aunty A'isha ta ce "Ya jiki kuma Alhaji? Ashe cuta ka sha Wlh ba mu da labari." Ya nuna ƙafarsa ya ce "Ciwon Ƙafa ne ya sako ni a gaba, na fi shekara biyar a zaune bata takuwa, kuma tunda muka je Saudiyya ake ta maganin, sai yanzu Ubangiji ya kawo sauqi." Mama ta ce "Subhallahi, Lallai kasha jinya Alhaji, Allah Ubangiji ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Suka amsa da "Ameen." Ya dubi Aunty A'isha ya ce "Ya ƙarin haquri rashin su Alhaji Muhammad, tun bayan rasuwar su ba mu ƙara haɗuwa ba, na samu labarin ma kin yi aure." Aunty A'isha "Haquri Alhamdulillah, ai tun bayan dana gama takaba na yi aure." Ya ce "Masha Allah, Allah ya raya zuri'a ya ƙara haqurin zama da juna. Su kuma Alh. Muhammad Ubangiji Allah ya ji k'ansu ya gafarta musu." Suka amsa da Ameen gaba_ɗaya. Daga nan suka shiga tattaunawa akan abun da ya kawo su. Inda Alhaji Ali ya sanar musu da cewa. "Bayan ya dawo daga Saudiyya ne ya bibiyi al'amarin, inda aka tabbatar masa har yanzu ba a gano wand'anda suka yi kisan ba, hankalinsa ya tashi ya dinga faɗa akan rashin tsaurarara bincike na ƙasar nan da ba'ayi, sannan ya saka lauyoyi da jami'an tsaro su binkito masa. To ana cikin haka ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kisan su Abba ya fito daga gidan yari bayan shekaru takwas daya shafe a gidan yarin, bisa laifin fashi da makami da aka kama shi da shi, dama irin ƴan daban nanne da masu kuɗi da ƴan siyasa suke amfani da su dan cimma wata buƙata ta su, daga zarar buƙatar tasu ta biya kuma da su da banza duk ɗaya ne a gurinsu. Bayan ya fito ya nemi wanda sukay kisan su Abban tare wanda shine yakasance kamar babbansu a jan ragamar aikin, ya buk'aci daya ba shi cikon kuɗin aikinsa, shi kuma wancan ɗin sai ya hana shi ya ce ya cinye. To saboda baƙin cikin cinye masa kuɗin da aka yi shine ya ɗauki alwashin sai ya tona musu asiri in ya so kowa ya rasa duk a kama su. Da kansa ya kai kansa Police station ya faɗi laifinsa, aka kuwa yi ram da shi nan take, sannan ya faɗi inda sauran biyun suke su ma aka je aka kamo su. Da farko su sun musa, amma da suka ji wahala sai suka fadi gaskiya, suka ce tabbas su sukai kisan amma su ma wani mutum ne ya ba su kwangilar yin kisan. Yanzu haka suna Bamfai a tsare, Ranar Monday Insha Allahu za'a yi shari'ar a babbar kotun jiha, dan yanke musu hukunci dai_dai da abun da suka aikata. Sai dai har yanzu sun ƙi faɗar wanda ya saka su aikin, dan su yaran biyun dama ba su san shi ba, babban nasu ne ya san shi. Amma ana saka rai Insha Allah za su faɗi koma waye a zaman kotu, lauyoyinmu suna ta faɗi tashi akan haka. Na samu duk wannan bayanan ne ta bakin amintaccen lauyana wanda shi ne lauyan da zai tsaya a gaban kotu a matsayin lauyan iyalan Alhaji Muhammad Gabasawa dan ganin kotu ta bi musu hak'k'in su." Sai bayan Azhar su Neehal suka baro gidan nasa zuciyoyinsu cike da al'ajabi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.