Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 104
Neehal ta na shiga kitchen ta dakko tukunya ta d'aurayeta ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora, wayarta dake kan ce ta fara ringing, dakkowa ta yi ta sauri ta duba, sunan *HEART CRUSH* ta ga ya na yawo akan screen ɗin, ɗagawa ta yi da murmushi akan fuskarta ta ce "Aloo" daga ɗaya ɓangaren Haneefah ta ce "Na bi Aloo d'in da gudu, dan iskanci na kiraki tun ɗazu amma shine ba za ki iya biyo bayan kirannawa ba" Neehal ta na murmushi mai sauti ta ce, "Sorry Bestynah, time ɗin da kika kira ina bacci ne, ban jima da tashi ba mama ta tura ni kitchen girki, so nake na ɗan rage aikin dama na kira ki ke da MY HUSBAND" Haneefah ta tab'e baki ta ce "To me miji, mun dai kusa miƙa ki gidansa kowa ya huta da rashin kunyarki" Neehal ta yi 'yar ƙaramar dariya ta ce "Na ji ɗin, ya kike ya Mommy?" Haneefah ta ce "Mommy tana Lafiya nima haka, ya Mama da Hajiya da Husband d'in naki?" Neehal ta ce "Suna lafiya ƙalau" Haneefah ta ce "Masha Allah, dama kiran ki na yi in ji ko kin dawo daga school" Neehal ta ce "Tun 12 na dawo" Haneefah ta ce "Da wuri haka?" Neehal ta ce "Kin manta yau Saturday lecture ɗaya gareni 10_12" Haneefah ta ce "Hakane fa, na sha'afane" Neehal ta ce "Yaushe za ki fito ne?" Haneefah ta ce "Ni yanzuma na gama shiryawa shiyasa na ƙara kiranki" Neehal ta ce "Toh ki zo mana, sai ki tayani na ƙarasa girki sai mu wuce kawai" Haneefah ta ce "In zo in taya ki girki ko kuma ki ce in zo in ƙarasa Miki girki?" Neehal ta ce "Ni dai koma yaya ne ki yi sauri ki zo" Haneefah ta ce "Toh Mommy ganinan" Neehal ta yi dariya ta ce "Sai kin ƙaraso" ta kashe kiran ta lalubo number'n masoyinta kuma mijinta nan da watanni biyu masu zuwa insha Allah wato ANWAR, kiransa ta yi amma no Answer, ajiye wayar ta yi batare data ƙara kirannasa ba, dan tasan ya na wani uzurinne da ya hanashi d'aga wayar tata, komawa ta yi ta cigaba da aikinta.
After 15 minutes Haneefah ta ƙaraso gidan, Mama tana sama har time ɗin, Hajiya ce kawai kwance akan kujera bacci ya ɗauketa, Ameen kuwa part ɗinshi ya yi bayan ya dawo daga ɗakin Mama. Kitchen Haneefah ta nufa bayan ta ajiye handbag d'inta da mayafinta a kan kujera, Neehal tana cikin yanka cabbage Haneefah ta yi sallama a kitchen d'in, da sauri Neehal ta ajiye abun hannunta tare da juyawa cikin farin cikin ganin besty'ntata ta amsa mata sallamar, itama Haneefah cike da murnar ganinta ta ƙaraso inda take, rungume juna suka yi Neehal tana faɗin "Welcome dear" Haneefah ta saketa tana faɗin "Thank you" Neehal ta ce "Yau gabad'aya ban ji d'uriyarki da takurarki ba, na yi missing komai naki dai kawai" Haneefah ta ce "Nima haka darling, ina Mama fa?" Neehal ta ce "Ta na sama may be" Haneefah ta ce "Na ga mutuniyartamu ana ta shan bacci ai" Neehal ta ce "Hajiya rigima, ta kusa tafiya ai mu huta da magana, yawwa dear dan Allah ɗan ƙarasa mini girkinnan na je na shirya kar mu yi latti" Haneefah ta harari Neehal ta ce "Ba wani dan ki shirya, kawai dai ki ce kin ga ji da aikin" Neehal ta b'ata fuska ta ce "Kamar kin sani kuwa" Haneefah ta ce "Hmm, yarinya idan ma za ki daure ki na girki ta daɗin rai ki daure, dan idan aka kai ki gidan ki dole ki yi" Neehal ba ta ce komai ba ta fice daga kitchen d'in.
Ta na fitowa falo ta ji mayen k'amshin turaren Ameen da har time É—in bai bar falon ba, tunawa ta yi ashe fa ya dawo, kallon saman steps ta yi ta juya kamar wata mara gaskiya tana tafe ta na waige ta buÉ—e Æ™ofar falon a hankali ta fice ta nufi part d'in Yayan nata dake kusa da nasu part d'in.......âœï¸
[7/21, 8:59 AM] Zee data: *⚡NEEHAL ⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*0ï¸âƒ£2ï¸âƒ£*
A hankali ta tura ƙofar falonsa, ta yi sa'a kuwa ƙofar a buɗe ya barta, shiga ta yi gabanta na ɗan fad'uwa saboda sanin halin Yayannata da kuma tsoronsa da take masifar ji. Ya na zaune a kan kujera 2 seater ya jingina bayansa a jikin kujera idanunshi a lumshe hannunshi dafe da kanshi, Neehal ta ƙaraso kusa da shi a hankali idanunta k'ur a kansa, gabantane ya fadi ganin irin ramar da ya yi, dan ɗazu kwata_kwata bata lura ba, a ɗan ruɗe ta ce "Yaya!" Bai motsa ba balle ya nuna ya ji ta. Ba ta damu ba ta zauna a kusa dashi kamar za ta yi kuka ta kuma faɗin "Yayah ba ka da lafiya ne?" Shiru yay mata kamar ba zai amsa ba, sai kuma can ya d'ago da kansa ya na ɗan sauke numfashi ya dubeta, kallon ta ya yi na 3 seconds kafin ya daukey idonshi daga kanta tare da girgiza mata kai alamar a'a. Idanunta na kawo ruwa ta ce "Gashinan ka rame, Please yaya mai ke damunka?" Haɗe rai ya yi sosai har sai da gabanta ya fadi amma bai ce komai ba, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta wanda ta kasa tantance na banzan da ya yi da ita ne ko kuma na ganin shi cikin damuwa da ta yi ne?" Ta na hawayen ta ce "Yay......" cikin tsawa ya dubeta ya ce "Kin san bana son takura ko? tashi ki fita" turo ɗan karamin bakinta ta yi gaba ta na share hawayen fuskarta ta tashi ta fita, Bin ta ya yi da kallo ta ƙasan ido har ta fice, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida idanunshi ya lumshe zuciyarsa na masa ɗaci.
Haneefah ta dubi Neehal da ta tsaya jiki a sanyaye tun da ta dawo kitchen d'in ta ce "Besty me ya faru na ganki haka?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya idanunta na cikowa da k'walla ta ce "Yaya ne" Haneefah ta ci gaba da juya miyar da take dan in da sabo ya ci ace ta saba da rashin shirin Neehal da Yayannata, kamar ba za ta kula da zancen ba sai kuma dai ta ce "Me yay miki kuma yau" Neehal cikin raunananniyar murya ta ce "Besty ba ki ga yanda Yaya ya rame ba, amma na tambayeshi meke damunshi shine ya ce mun bakomai, na roƙe shi ya faɗamun shine ya koro ni" Ta ƙarashe zancen hawaye na zubo mata akan kuncinta, Haneefah ta juyo ta fuskance ta, ta ce "Ni fa daɗina dake saurin kuka, yanzu mene abun kuka anan?" Neehal ta ce "Ba za ki gane ba ne Besty, amma ba ki ji yanda nake ji araina ba, ganin shi cikin damuwar da na yi" Haneefah ta ce "Tom shikenan ki yi masa addu'a, koma me ya ke damunsa Allah ya yaye masa ya kuma bashi lafiya" Neehal ta ce "Ameen" Haneefah ta ce "Yawwa ko ke fa, to share hawayennaki 'yar Mama, kin san fa ke amarya ce ba na son na ga kina damuwa, kar mu kaiwa ya Anwar ke a rame" Neehal ta yi Murmushin yaƙe, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, ta rasa me ya sa a duk lokacin da a ka yi zancen bikinta sai ta ji fad'uwar gaba, daurewa kawai ta ke yi, fita ta yi daga kitchen d'in domin ta je ta shirya, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da Mama zaune ta na karatun Alkur'ani mai girma, zama ta yi har Maman ta kai ƙarshen aya, Mama ta d'ago ta dube ta, ta ce "Kin gama girkinne?" Girgiza mata kai Neehal ta yi, Mama ta ce "Toh menene kuma na ganki haka?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Mama Yaya ne na ga kamar bashi da Lafiya, kuma na tambayesa me ke damunsa ya ƙi faɗamun sai ma koroni ya yi" Mama ta ce "To ke halin Ameen ɗinne ba ki sani ba ko me? Kin san ba faɗa miki zai yi ba, wa ya aike ki?" Neehal ta b'ata fuska ta ce "To ba Yayana ba ne?" Mama ta ce "Kin ga Yayanki ai, Ni tashi ki je ki ƙarasa mun girki kar time ya k'ure ki bar Ni da shi" Neehal ta tashi tana turo baki gaba ta fita. Bedroom ɗinta ta shiga, rage kayan jikinta ta yi ta shiga toilet dan yin wanka.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.