Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 68 of 104
_By_
_Zeey Kumurya_
*4ï¸âƒ£4ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
*🌈NIMCY'S LIBRARY🌈*
_Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba É—aya akan 3k gaba É—aya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus É—in da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3kðŸ˜, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daÉ—iâ¤ï¸ðŸ¤¨_
So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own...
Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
The new emir
Izzar so
Sai na auretaðŸ˜
Tsintacciya
E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny
Bunus ya fara 6/2/2022
Share fisabilillahiðŸ˜
Ahmad ne ya fara juyawa ya kalli ƙofa jin ana sallama tare da amsa Sallamar. Neehal kuwa bata san time ɗin data miƙe tsaye ba jin sallmar Ameen cikin kamilalliyar muryarsa. "Yaya! ga mahaifin su Afrah." Ta faɗa a diririce ba tare data san ta yi hakan ba. Ameen dake tahowa inda suke ya mata wani kallo bai ce komai ba. Ahmad kuwa bai lura da yanayin da Neehal ta shiga ba wanda ita kanta in za'a kashe ta baza ta ce ga dalilin da ya saka ta a ciki ba, idanunsa suna kan Ameen. Ameen ya miƙa masa hannu bayan ya ƙaraso inda suke ba tare da ya ce komai ba. Da fara'a Ahmad ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha. Ahmad ya ce "Barka da yamma." Ameen ya ce "Yawwa, ina maka murnar bayyanar kids ɗinka." Still fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Thank you." Ameen ya juya ya nufi sama ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Neehal ta sauke numfashi tare da komawa ta zauna tana bin bayan Amee da kallo, wanda ya tafi ya bar musu k'amshinsa a falon. Muryar Ahmad da ta ji yana faɗin "Princess." Shi yasa ta juyowa ta kalle sa. Ya ce "Zan wuce, na ga time ɗin sallah ya yi." Ya ƙarasa maganar tare da duba agogon hannunsa. Neehal ta ce "Gidan Mamy zaka koma?" Ya ce "Eh." Ta ce "Ka gaishe ta Please." Ya ce "Zata ji Insha Allah." Ya miƙe tsaye yana jifanta da wani kallo mai cike da tsantsar k'auna. Ta miƙe itama kanta a ƙasa ta ce "Thanks for the visited." Ya ce "Thank you more and more Princess, nine da godiya ba ke ba, kasantuwar mu yau a tare ya sanya ni a cikin farincikin dana manta rabon da na yi kamar sa." Ta d'ago ta kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba ta ce "Nima na yi farin cikin kasancewa da kai Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai alamar tabbatarwa. Ya tsaya kawai yana kallonta yana jin kamar ya tafi. Kiran Sallar da aka gwad'a a masallacin dake cikin layin nasu ne ya sa ya sauke ajiyar zuciya. A hankali ya matso daf da ita, hannunta ya kama cikin murya mai kama da rad'a ya ce "I love You....!" Ta lumshe idonta tare da ƙoƙarin zame hannunta daga nasa jin taku ana sakkowa daga sama, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma hannunta da ya kai saitin bakinsa sumbata tare da faɗin "Bye." Sannan ya sakar mata hannun ya juya ya nufi ƙofa ya bar ta anan sandare cikin wani irin yanayi da bata san ya za ta fassara shi ba. A hankali kuma ta buɗe idonta ta ga har ya fice daga ɗakin. Ta juya dan ɗaukar wayarta tana sauke numfashi suka yi 4 eyes da Ameen tsaye a cikin falon. Ta yi kamar bata gan shi ba, ta sunkuya ta ɗauki wayarta ta nufi upstairs. Ameen ya bita da kallo sannan ya tab'e ɗan bakinsa ya fice daga falon. Sai da ta zauna akan kujera bayan ta ƙarasa falon sama sannan ta latsa wayarta, message ɗin Sadik ta gani 11 minutes ago. Ta buɗe da sauri ta karanta. Ajiyar zuciya ta sauke ganin ya ce, tunda abu take yi yanzu zai je ya yi Sallah ya dawo tunda lokacinta ya gabato. Ta miƙe ta shiga ɗakin Mama. "Mama! Mama!" Ta shiga kiran sunanta bayan ta shiga, Mama ta fito daga toilet fuskarta da ruwa alamun alwala ta yo ta ce "Na'am Daughter wannan kiran fa?." Neehal ta yi murmushi ta ce "Wani labari zan baki mai daɗin gaske." Mama ta ce "To bari mu yi Sallah sai ki bani, Ahmad ɗin ya tafi ne?" Neehal ta ce "Eh, ya tafi yanzu nan." Mama ta ce "Amma ba a yau zai koma Abujan ba?" Neehal ta ce "Eh, akwai ƙanwar Ummi a nan Kano gidanta zai koma, amma gobe zai wuce Abujan." Mama tana shimfid'a Darduma ta ce "Allah ya kai mu." Neehal ta juya ta fice daga ɗakin zuwa nata dan yin Sallah. Bayan ta idar ba jimawa wayarta ta fara vibrate, ta ɗauko kamar yadda ta zata Sadik ne yake kiran ta. Ta d'aga tare yin sallama, ya amsa mata. A hankali ta ce "I'm sorry Yaya Sa..." Ya katse ta da faɗin "No Darling kar ki damu, na san abu kike yi time ɗin. Daga unguwa ma nake na biyo in ganki in kuma yi miki sallama." Neehal ta ce "Sallama kuma?" Ya ce "Eh, gobe in Allah ya kai mu zan tafi ibadan sai ranar Friday zan dawo." Neehal ta ce "Allah ya kai mu, ya tsare hanya ya kiyaye mun kai." Ya ce "Ameen ya Allah, na ce miki zan dawo kuma bayan mun yi Sallah Abba ya kira ni ya sanar mun in zo gida zamu fita tare da shi yanzu." Neehal ta ce "Idan kun dawo ba sai ka zo to." Ya ce "Idan mun dawo da wuri zan zo in sha Allah." Cikin shagwab'a ta ce "Idan ba ku dawo da wuri ba sai nan da 5 to 6 days zan gan ka kenan?." Ya ce "Um'um Dear, ai za mu yi video call ko?" Ta ce "Shikenan Husby nah." Ya ce "Yawwa wifey." Daga haka suka yi sallama ya kaste wayar. Ta tashi ta tafi ɗakin Mama ta fara fara labarin Ahmad tun farkon haɗuwar su, duk da wasu abubuwan ta manta wanda ta riƙe kawai ta faɗa mata. Mama ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, Allah ya biya shi taimakon da yay miki." Neehal ta ce "Ameen, shi yasa nake son twins over, ashe....." Sai kuma ta yi shiru. Mama ta ce "Uhm? Ashe soyayyar Mahaifinsu ce ta shafe su." Neehal ta rufe fuska tana murmushi. Mama ta ce "Gobe idan ya zo ya kamata ki bishi ki je ki gaishe da ƙanwar Ummin nasu." Neehal ta ce "Gaskiya kam, dan tana da kirki kuma tana sona, har wanka ta taɓa mun." Cikin takaici Mama ta ce "ita matar Umar ɗin duk zuwa gidansu Ahmad ɗin da kike bata taɓa bibiya ta ji me kike zuwa yi ba, yanzu da ba shi da hali fa cutar dake yake babu ruwanta ko? Saboda ba ita ta haife ki ba, halin wasu mutanen sai dai mu ce Allah ya shirye su kawai yasa su gane." Neehal ta ce "Ameen Mama." Mama ta ce "A cikin week ɗin nan ya kamata ki je gidan A'isha da Sadiya, kin jima ba ki je ba." Ta ce "Toh Mama Insha Allah zani, ni Gombe ma nake son zuwa, duk sanda Hajiya ta zo sai ta mun complain akan rashin zuwa na." Mama ta ce "Na ji Ameen yana cewa yana son zuwa Gomben nan kusa shi ma, sai ku tafi tare. Ga Abuja ma kin daɗe baki je ba, Jiya da muka yi waya da Umma ma sai da ta ce ƙin daina zuwar musu yanzu." Neehal ta ce "Insha Allah, duk a cikin month ɗin nan zan je musu." Mama ta ce "Allah ya yarda, shi ma Uncle ɗin naki ya kamata ki lek'a musu." Neehal ta ɓata fuska dan ta gane Uncle Umar Mama take nufi. Ta ce "Ni fa Mama bana son zuwa yana kora ta da cin mutunci." Mama ta ce "Ki je dai, ai ba zama zaki yi ba, ganin su kawai zaki yi ki dawo, kin fi shekara biyu fa baki je ba." Ba don ta so ba ta ce "Toh." Mama ta ce "Yawwa my Daughter, ki yi haquri watarana sai labari, nina faɗa miki watarana sai sun zo suna neman ki har inda kike, komai lokaci ne. Kuma har abada su jininki ne ba'a taɓa sauya wa tuwo suna." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa. Mama ta ci gaba da yi mata nasiha cikin taushin murya, daga ƙarshe kuma ta saka mata albarka tare da tarin addu'oi. Kiran Sallar isha'i ne ya tayar da su suka yi Sallah. Bayan sun idar ba jimawa Ameen ya dawo gidan kamar yadda Mama ta ce masa in an yi isha'i ya dawo Daddy yana neman shi. Ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo da sallama. Suka amsa masa a tare. Kan Neehal a ƙasa ta ce "Ina yini Yaya." Ko kallon inda take bai yi ba balle ya amsa mata, ya samu gefen gado ya zauna fuskar nan a haɗe. Neehal ta tashi ta fice daga ɗakin. Bayan ta fita Mama ta dube shi ta ce "Kana ji tana gaishe ka amma ka ƙi amsa mata." Ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba. Cikin takaicin wannan halin nasa Mama ta ce "Bari na kira Dad ɗin, na ji bai shigo ba har yanzu." Ya ce "Tom." Tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Ɗakin Neehal ya buɗe ya shiga, tana kwance a kan gadonta tana latsa waya. Bata san ya shigo ba sai k'amshinsa ta ji ya cika mata hanci. Ta juyo da sauri sukai ido huɗu fuskar nan a haɗe, ta tashi zaune da sauri cikin tsoron yanayin data gan shi ta ce "Yaya!" Bai amsa mata ba sai harara da ya zabga mata. Tayi ƙasa da kanta da sauri. Ya fi mintuna biyar a tsaye bai ce komai ba, daga baya kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Ta sauke ajiyar tare da tashi ta je ta kulle ƙofar ɗakin dan yanayin data gan shi a ciki na ɓacin rai ta ɗauka dukan ta ma zai yi, duk da bata san abun da ta yi masa ba. A ranta tana mitar ya yi auren ma amma ba zai barta ta huta da masifarsa ba, gashi shi mutum ne wani iri da baka sanin lokacin da ka yi masa laifi, abun da kai a tunaninka ba laifi ba ne shi a gurinsa laifi ne. Duk da ta san yana da haquri, musamman ma ita ya yi haquri da ita a baya, ta saka masa ciwon kai lokacin da ya dawo daga karatu kafin ta saba da shi, dan a lokacin duk abun da ta san baya so shi take yi, shi kuma idan ya gaji da ɗauke kai daga abubuwan da take yi, ya kamata ya hukunta ta. Daga baya kuma da ta ƙara girma ta yi hankali sai ta ci maganin zama da shi, ta gane mutum ne shi mai sauƙin kai da kawaici, shi abun da kawai ba ya so a rayuwarsa raini, idan har zaka raina shi to baza ku taɓa shiri ba. Gashi da kyauta kamar mahaifiyarsa, bata neman komai ta rasa saboda kafin ma ta buƙata ya siyo mata, duk weekend ɗin duniya idan ya dawo daga Lagos da guzurin tsarabarta yake tahowa. Sometimes idan yana gari shi yake koya mata Assignment idan ba ta iya ba, haka ma hadda yana jiye mata ko kuma ya ƙara mata inda za ta ɗora. Daga shekara biyar zuwa yanzu ne ya sauya mata gaba-d'aya, ya fara shashshare ta over dama gashi muskili, sai ran da ƴan mutuncin suke kansa shine zai ɗan sakar mata fuska.........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.