Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 45 of 104

_By_
_Zeey Kumurya_

*3️⃣0️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*

.Sosai Ahmad yake jin nishad'i da farinciki a duk lokacin da suka kasance tare da Neehal, sai ya ji kamar kar ta tafi ta zauna tay ta masa hirarta da muryarta mai daɗin sauraro gami da sassayan murmushinta. Har cikin ransa yake jin wani abu game da yarinyar, a da yana tunanin tausayi ne kawai, amma yanzu duk da da akwai tausayin amma da wani abu daban da ya kasa gane ko menene. Babban tashin hankalinsa yanzu befi 1 month ya rage masa ya koma gidansu ba, dama a Abuja suke wani aiki ne ya kawo shi Kano, dan shi bai taɓa zuwa Kano ba sai wannan time ɗin, saboda duk Relatives ɗinsu a Abuja suke both na Mamanshi dana Dad ɗinsa. Mamy ma da a Abuja take, a wurin aiki ne aka yi  ɗin mijinta zuwa Kano shine suka dawo, itama ba tafi two years da dawowa ba. Zuciyarsa babu daɗi ya ƙaraso gida, zama ya yi akan kujera yana sauke numfashi, a hankali ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ya latsa ya shiga kallon pictures ɗin da yay wa Neehal d'azu, ta yi kyau sosai tana ta zuba murmushi.

Zuciyar Neehal cike da tsananin tsoro da fargaba ta ƙarasa gida, ba ta ga Aunty Fauziyya a tsakar gida ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙarasa kitchen ta ajiye kayan miyan sannan ta nufi falo, nan ma ba ta ga Aunty Fauziyyan ba, hakan ya sa ta wuce ɗakinsu tana sauke ajiyar zuciya. Yau wani daɗi take jin jikinta ya mata, to mamy ta dirje ta tass ta fitar mata da duk wani datti da daud'a dake jikin nata. Sai wajen magriba time ɗin su Aiman sun dawo daga islamiyya ta ji maganar Aunty Fauziyya, gabanta ya yanke ya faɗi saboda tsoro. Fauziyya wadda tun kafin la'asar ta kwanta take baccin asara sai yanzu yaranta suka tashe ta, ko sallar la'asar ba ta yi ba. "Neehal! Neehal!!" Ta shiga ƙwalawa Neehal kira, Neehal ta fito da sauri tana faɗin "Na'am Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta jefe ta da shi kamar kodayaushe, ta ce "Ina aiken dana miki?" Neehal ta ce "Na ajiye a kitchen." Aunty Fauziyya ta ce "Yau ma sai da kika gama yawon naki sannan kika dawo ko?" Neehal ta girgiza mata kai cikin tsoro. Aunty Fauziyya ta ce "Hmm, munafukar yarinya, zaki yi bayani ne idan wanda ya ajiye ki ya dawo gidan, zaki faɗa masa inda kike zuwa ne, in ma iskanci kike zuwa ki yi duk za ki masa bayani." Neehal dai tay shiru kanta na ƙasa. Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ƙara cewa "Taso ni mu je ki mun tsinta." Neehal ta tashi ta bi bayan ta, a k'aton farantin silver ta zubo shinkafa yar Hausa ta ajiye a gaban Neehal ta ce ta tsince mata, Neehal ta kalli shinkafar ta kalle ta, ta ce "Aunty ban iya ba." Rank'washinta Aunty Fauziyya ta yi sannan ta nuna mata yanda zata yi. Neehal fa ta duk'ar da kai ta fara tsinta, ga duhun Magriba ya kawo kai da ƙyar take gani. Fitila Aunty Fauziyya ta bata ganin magriba ta yi, Neehal ta ce "Aunty bari na yi sallah sai na cigaba." Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce "Dalla ni ki cigaba da mun aikina, algungumar yarinya kawai, sai ka ce da Sallar kike, ko kuma in kin yi lada zaki samu." Neehal ta turo baki gaba ta cigaba da tsintar, Nasihar Abbanta da yake mata a kodayaushe ta tuno, inda yake ce mata "Ƴar albarkata ko me kike yi idan kika ji an kira Sallah ki bar shi ki je ki yi Sallah, idan kin idar sai ki ci gaba." Tun tana ƴar k'ank'anuwarta yake faɗa mata haka. Hawaye ne ya zubo daga cikin idanunta, da sauri ta share su dan kar Aunty Fauziyya ta gani, Allah ya rufe wa Aunty Fauziyya ido ba ta ga canzawar da Neehal ta yi ba na gyara ta da Mamy ta yi, gashi kanta da hula shi yasa ba ta lura da gashinta da ya sha gyara ba, da yau Neehal ta shiga uku. Sai wajen isha'i ta gama tsintar, duk da shinkafar bata da tsinta sosai, amma saboda bata saba ba shi yasa ta daɗe, aiko da ƙyar ta iya tashi dan bayanta ya k'age, ga cizon sauro da ta sha, Aunty Fauziyya kuwa ko sannu sai ma tukwuicin harara ta samu. Kan kujera ta je ta kwanta, yau ta ci sa'a ba'a ce ta sauka ba. Bayan Uncle Umar ya dawo yana ɗakin baccinsu yana marking papers Aunty Fauziyya dake goge Uniform ɗin su Aiman ta dube shi ta ce "Baban Iman inata zuci_zucin ka dawo in faɗa maka wani hali da yarinyar can ta tsira." Ba tare daya d'ago ba ya ce "Wacce yarinya kenan?" Ta ce "Neehal mana." Ya ce "Me kuma ta yi." Ta tab'e baki ta ce "Hmm, yawon banza ta koya, idan na aiketa sai ta yi awa uku a waje, ƴar ƙarama da ita har ta san wani bin maza." Da sauri Uncle Umar ya d'ago ya dubi Aunty Fauziyya ya ce "Haba Fauziyya, yarinyar da ba ta fi shekara goma sha ɗaya ba ita zaki ce tana bin maza? Ki dai sake wata maganar ba wannan ba gaskiya." Aunty Fauziyya ta ce "Lallai Umar me kake nufi? Sharri zan mata ko me? Kuma idan ba maza take bi ba gidan ubanwa take zuwa idan na aike ta, har ta yi awanni." Uncle Umar ya ajiye red biron dake hannunsa tare da miƙewa a fusace ya ya fito falo. Neehal dake kwance rub da ciki akan kujera har lokacin, ta ɗan samu baccin gajiya ya ɗauke ta ji murya Uncle Umar a tsawace yana cewa "Ke Neehal! Neehal!" A firgice ta farka tare da buɗe ido, cikin muryar bacci ta amsa masa tana ƙoƙarin tashi zaune cikin tsoro. "Gidan uban wa kike zuwa idan an aike ki?" Uncle Umar ya tambaye ta cikin tsawa, Neehal ta manne jikinta ba ta ce komai ba, Uncle Umar ya ƙara daka mata wata tsawar da faɗin "Ba dake nake ba." Neehal bata iya ƙarya ba, hakan yasa ta fashe da kuka dan ta san idan ta faɗawa Uncle Umar inda take zuwa sai ya kusa kashe ta da duka. Masifa ya dinga surfa mata, ya kuma ce aka kuma aiken ta ta daɗe sai ya karya k'afarta. Ba ƙaramin tsorata Neehal ta yi da Uncle ɗin nata ba, hakan yasa washegari bata biya ta gidansu Ahmad ba. Shi kuwa tun da ya yawo daga inda yake zuwa aiki yake ta zuba idon ganinta amma ya ji ta shiru har yamma. Yau data koma da wuri Aunty Fauziyya ta ce "Ehh lallai, wato ni kika raina shi yasa ba kya jin maganata, shi da kike tsoronsa gashi ai kin ji faɗan sa." Ta ƙarashe zancen tare da jan k'wafa. Neehal kam tunanin Uncle ɗinta Ahmad ta shige ɗaki tana yi, ta san yanzu ya siyo mata kayan daɗinta yana jiran ta je ta ci. Yau kwana uku Neehal bata je gidansu Ahmad ba, kullum sai dai ta kalli gidan ta wuce.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.