Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 24 of 104
Bayan sun dawo daga karb'o É—inkin Sadik ya kira ta, maganar farko da ta fara masa a kan kuÉ—in nan ne, ya ce mata nata ne ai ita ya bawa ta yi hidimar biki. Neehal ta ce ya dawo ya karb'i kuÉ—in, Mama ta sai mata komai, kuma ita ma ta na da kuÉ—i a hannunta tunda duk wata ta na É—aukar albashi. Sadik ya ce ya riga da ya bata ba zai karb'a ba, Neehal tai ta masa magiya a kan ya zo ya karb'a kamar wani abun, da ya gaji da magiyar ma sai ya kashe wayarsa. Da Neehal ta faÉ—a wa Mama abun da ya ce, sai Maman ta ce ta yi masa godiya tunda ya riga ya bata ba za a matar masa ba, itama za ta kira shi ta masa. Kamar yadda Sadik ya bawa Neehal kuÉ—i 100k haka ya je ya bawa Haneefah 50k ita ma.
************ABUJA************
Yau tun sassafe Hameedah da ta tashi take ta rufzar kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu, sosai hankalinta ya tashi ganin dagaske bikin Ameen za'a yi. A haka Mommy ta shigo ta same ta Misalin ƙarfe shida na safe, ganin irin kukan da take Mommy ta fara mata magana cikin faɗa. "Haba Hameedah, wai kukan nan ba zai ƙare ba ne, sai kin je wani ciwon ya kama ki a aikin banza, ki barmu da wahala." Cikin kuka Hameedah ta ce "Mommy ta yaya ba zan damu ba, bikin Ya Ameen fa za'a yi da wata ba da ni ba, Mommy ba ki san Yadda nake ji a cikin zuciyata ba ne, wlh Mommy kamar zan mutu haka nake ji." Mommy ta ce "To ba nace ki kwantar da hankalinki ba, indai Auren ku da Ameen ne kamar an yi an gama." "Tun yaushe ki ke faɗin haka Mommy, amma babu abun da ki ka yi akai gashi har auren ya matso, kuma kin ce mun za ki san yadda za ki yi auren nan bai yiyu ba, amma ban ga wata alamar hakan ba." Mommy ta sauke numfashi ta ce "Hameedah ki dena damuwa da matsowar auren kusa, ai ba ki ga an ɗaura Auren ba, kuma wallahi ko da an ɗaura Ni Suwaiba ba zan bari su samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auran nasu ba, sai na zame musu masifa da bala'i wadda za su yi da na sanin yin auren." Hameedah ta ce "To Mommy ai idan sun yi auran Ya Ameen ba zai aure ni ba, domin ya sha faɗa ba shi da ra'ayin auren mace biyu." Mommy cikin tarar numfashi ta ce "Kar ki damu da wannan, duk zancen banza ne, shi ya ma isa, ki rubuta ki ajiye Ameen dole sai ya aure ki indai ina numfashi." Hameedah ta yi shiru ta na sauke ajiyar zuciya, maganganun mahaifiyarta ta sun ɗan sanyaya mata zuciya, domin ta san ta idan ta ce za ta yi abu tofa sai ta yi shi. Mommy ganin Hameedah ta yi shiru ta dena kukan sai ta ce mata, "Yanzu zan shirya zan tafi nemo mafita daga nan zan biya Kano ganin kayan lefen." Da sauri Hameedah ta kalle ta ta ce "Yanzu Mommy sai kin je kin ga kayan, ki na farin ciki da auran kenan.?" Mommy ta ce "Ba ki ji ina na ce miki zani ba ne, yanzu daga nan Katsina zan wuce gidan Haj. Rakiya daga nan za ta rakani gurin wani malami, ta sanar mun aikinsa tamkar yankan wuk'a yake, sai na gama da nan sannan in wuce Kanon, kin san idan ban je ba yanzu sai ya zama abun magana, tun kwana uku da suka wuce Yaya ya kira ni akan in je inga kayan, ina sane na ƙi zuwa a washegarin ranar dan Family duk yawanci ranar suka je, ɗazu ma Yayan ya kuma kirana ya ce mun ya ban zo ba? gashi har gobe za'akai kayan. Shi ya sa zan je kar a ce Yayanka Uwa ɗaya Uba ɗaya ɗansa zai yi aure ba ka je ganin lefe ba, yanzu sai ya zama abun magana." Hameedah tay shiru ba ta kuma cewa komai ba jin abun da mahaifiyar tata ta faɗa. Kafin ƙarfe 7 Mommy ta gama shirinta na tafiya Katsina, bayan ta cewa Abban Hameedah Kano za ta ganin lefe. Sai washegari da safe Mommy ta je Kano, Mama ta tarb'e ta ba yabo ba fallasa harma ta tambaye ta ina Hameedah ita ba ta zo ba.? Mommy ta kada baki ta ce "Ba ta da lafiya ne, itama rashin lafiyar Hameedan ne ya hana ta zuwa tuntuni ganin kayan." Mama ta mata addu'ar samun sauƙi. Baƙin cikin da Mommy ta ji a ranta lokacin da ta na kallon kayan ba zai misaltu ba, saboda ganin yanda aka kashewa lefen kuɗi, zuciyarta na faɗa mata da tuni wannan uban kayan ƴar ta za'a kaiwa fa, Takaici da hassada bai barta ta gama ganin kayan duka ba. Washegari a ka kai kayan inda aka tsaida Ranar biki sati uku masu zuwa.
Shirye-shiryen biki ya kankama ta ko ina, kasancewar mahaifin Hafsat Babban Mutum ne a Æ™asar nan kuma sananne ya sa tun saura sati bikin a ka fara sanarwa a gidajen Radio, amarya an shirya events kala_kala, shi dai ango ya sanar mata ba kowanne zai halarta ba. ÆÂangaren Mama kuwa Events biyu kawai za ta yi, daga Dinner sai Yini/Mother's day. Su Neehal kam k'annen Ango suma suna ta shirye-shiryensu. Kasancewar wannan shine karon farko da Mama da Dad za su fara aurar da É—a ya sa tun ranar Larabar satin bikin gidan ya fara cika da baÆ™i ta ko ina zuwa ake, Dangin Mama da dangin Dad. Hameedah wadda har rama tay saboda damuwa da ta sawa ranta itama ta zo bisa tilastawar mahaifiyarta wadda take ta kwantar mata da hankali akan ta daina damuwa ko anyi Auren Ameen É—inma babu inda auren zai je zai lalace, ganin yanda Mommy'n take ta sintiri gidan Malamai sai hakan ya Æ™ara kwantarwa da Hameedah hankali. Yau Alhamis, yau ne kuma Ranar Dinner d'in da Aunty Sadiya ta shirya musu su Dangin Ango, Dangin Amarya kuwa tuni suka fara shagulgulan bikinsu.............âœÂï¸Â
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*1ï¸Â⃣7ï¸Â⃣*
*ðŸâ€Â¥Ã°Å¸â€Â¥ FITATTU HUÆŠUðŸâ€Â¥Ã°Å¸â€Â¥*
      _Zangon farko 2022_
 _Allahamdulillah kuna ina💃ðŸÂ½! Nace kuna ina?? Masoya wa Æ´an nan shahararrun Marubutan wanda ake masu take da *(TAURARI MASU HANNUN LU'U LU'U)*_
_Uhm kada na cika ku da magana, nasan kun matsu kuji wannan taurarin kuma Jaruman wannan shekarar ta 2022 wanda suka wasa alƙalaman su domin farantawa masoyan su rai_
_Munyi duba da halin rayuwa na rashi da ake fama dashi, wannan dalilin ya sanya muka haÉ—e kanmu tare da AlÆ™alamanmu, waje guda, wajan ganin mun sauÆ™aÆ™a kuÉ—in da zaku sayi wannan FITATTU HUÆŠUN da zasu zama Abun Æ™watance a gareku, muje zuwa💃ðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½._
*AUTAR MANYA* _fitacciya Æ´ar zamani wacce ta nishaÉ—an tar daku a littafin ta mai suna *AURAN BARE* a yanzu ta shirya tsaf domin bawa masoyanta farin ciki a cikin littafin ta mai taken 💃ðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸâ€Â¥ *BAƘAR FATA* kuna jin sunan kun san na musamman ne kada ku bari ayi babu ku_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.