Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 40 of 104
Ranar wata Laraba lokacin Neehal satin ta shida da kwanaki a gidan Mama, da yamma tana bitar haddadarta da zata bayar ranar Asabar, da yake tun bata fi sati da zuwa ba Mama ta nemi islamiyya ta saka ta, da ta je sai ta ɗora daga inda ta tsaya a haddarta ta gida. Gabanta ne ta ji ya yi wata mummunar fad'uwa, runtse idanta ta yi da sauri tana karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, mike wa ta yi tsam ta nufi bedroom ɗin Mama. Bayan ta yi sallama ta shiga Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. "Har kin gama haddar?" Jiki a sanyaye ta zauna a gefen Mama sannan ta ce "Eh." Mama ta ce "To ki je ki wanke panties ɗinki kar Magriba ta yi, dan nasan halinki da k'ailula sai ki yi awanni a wankin panties kawai." Ta ce "Toh." har ta miƙe sai kuma ta koma ta zauna ta ce "Mama yaushe zan koma gida?" Mama ta dube ta cikin mamaki ta ce "Gida kuma? Ke da kullum aka miki zancen komawar sai ki ce ba yanzu ba, amma yau kuma da kanki kike tambayar yaushe zaki koma." Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Mama ta cigaba da kallonta cikin nazartar ta, ta lura kamar wani abu na damunta dan wata nutsuwa ta ga ta yi, alhalin ta san Neehal da rawar kai da surutu, babu yanda za'ayi ta shigo bata ishe ta da hira ba, sai dai idan da wani dalili. Mama ta kira sunanta a hankali tare da kama hannunta ta ce "Neehal! Meke damunki? Ko baki da lafiya ne?" Girgiza mata kai ta yi alamun babu komai, Mama ta ƙara tambayarta da faɗin "Wani abun aka miki?" Nan ma girgiza kan ta ƙara yi, Mama ta ce "To me yasa kike son tafiya gida?" Neehal ta ce " Kawai ina son ganin Ummata da Abbana da Aunty." Mama ta sauke numfashi ta ce "To Shikenan, gobe Yayanki Ameen zai dawo, Ranar Saturday insha Allah sai na saka shi ya kai ki gida." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa duk da bata san wanda Maman ta ambata mata a matsayin Yayanta ba. Tashi ta yi ta koma ɗakinta dan yin abun da Mama ta sata. Washegari ma haka ta tashi tana jin kanta wani iri, gabanta kuma bai dena fad'uwa, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai take maimaita wa kamar yadda Mama ta koyar da ita a duk lokacin da ji ko ta ga wani abun tashin hankali. Ranar Ameen ya dawo gidan da yamma, shima ba wani jima wa ze yi ba, Ranar Sunday da zai koma. Neehal ba su haɗu ba ranar saboda wuni ta yi a ɗaki a kwance, Mama ta mata tambayar duniya ta faɗa mata me yake damunta amma amsar ɗaya ce babu komai, ƙarshe ma sai ta saka kuka, sai da suka yi waya da Abbanta da Ummanta da daddare, ta ji suna lafiya k'alau sannan ta ɗan ji daɗi a ranta. Duk da Neehal a lokacin yarinya ce amma tana da hankali, shi yasa Mama take jin daɗin zama da ita.
A Kano kuwa bayan su Umma sun gama waya da Neehal, Umma ta dubi Aunty ta ce "Aunty'n Neehal kin ga ikon Allah, yau kuma Neehal ce take cewa tana so ta dawo gida." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Kin san halin Neehal sai ita, may be ta gaji da Abujan ne take so ta dawo." Umma ta ce "Hakane, amma da fa da kuka take baro Abujan." Abba ya ce "Ai kin san ba ta taÉ“a dadewa kamar wannan lokacin ba, shi ya sa." Umma ta gyaÉ—a kai tana faÉ—in "Sai dai haka, amma yanzu tana dawo wa ana mata abu zaku ji tana ita gidan Mamanta zata koma dan tafi sonta." Abba ya yi murmushi ya ce "Ai soyayyar Yaaya da Neehal sai Allah, Allah ya haÉ—a jininsu." Aunty A'isha ta ce "Ai ita Yaaya tana son yara ne, musamman mata, Allah kuma bai bata ba, gashi duk yarinyar data É—auka a Family'nmu tana É—an yin kwanaki sai su ce su gida za su koma, kin san yara ba sa son zaman gida shiru kuma gashi ba'a fita, daga makaranta sai gida, haka take komar da su gurin iyayensu." Umma ta ce "Allah sarki, Allah ya bata nata itama, ai ba'a fitar da rai da rabo a rayuwa." Abba ya ce "Allah ya kawo masu albarka." Suka amsa da Ameen gaba-d'aya. Ranar sun jima suna hira a falon Umma gwanin sha'awa, da yake ranar girkin Umma ne, sai Kusan 12pm Aunty A'isha ta koma part É—inta. Misalin Æ™arfe biyu da mintuna na dare, Abba yana zaune akan sallaya yana lazimi bayan ya idar da sallar Nafila, Umma kuma tana kan gado a kwance amma ba barci take ba, tun da suka baro falo ta kwanta amma bacci ya Æ™i zuwar mata, sai wata irin faduwar gaba ce take riskarta akai_akai, addu'ar neman tsari daga sharri ta shiga karantawa a cikin zuciyarta, ana haka kawai suka ji an banko musu Æ™ofar É—akin baram............âœï¸
[7/21, 9:02 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2ï¸âƒ£7ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
A firgice Umma ta yaye bargon da ta lullub'a tare da tashi zaune tana kallon bakin ƙofar k'irjinta na dukan tara-tara. Abba kuwa ko kaɗan bai nuna razana ba, kallon mutanen da suke shigo musu ɗakin kawai yake a ransa yana faɗin, "La'ilaha'illa'anta subhanaka'inni'kuntu'minazzlimuun."Su su biyar ne, suna sanye cikin bak'ak'en kaya, fuskokinsu a ɗaure da wani baƙin k'yalle, hannunsa ɗauke da bindigu. Sosai hantar cikin Umma ta kad'a, addu'ar da take yi a zuci bata san sanda ta fito fili ba. Abba kuwa kallonsu kawai yake amma bece musu komai ba kamar yadda suma ba su ce ba, sai ƙare wa ɗakin kallo kawai suke. Cikin wata irin tafiya ta ƙasaita ɗaya daga cikinsu ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan bedside locker ya ɗan sunkuyo da fuskarsa dai-dai inda Abba yake. Cikin wata irin shakakkiyar murya ya ce "Na gaida Jarumi uban Jarumai." Sannan ya saki wata uwar dariya ya maida dubansa ga Umma ya ce "Ke! ki adana addu'arki zatai miki amfani a gaba dan yanzu baza ta hana mu yin abun da mukai niyya ba." Umma ta tab'e baki duk da yanayin tsoron da zuciyarta take ciki amma ta dake ta cigaba da karanto addu'arta, domin ta san ita ce kaɗai makaminta a wannan lokacin. Mutumin ya juyo ya yi wa ɗaya daga cikin yaransa inkiya da ido, cikin sauri yaron ya zagaya ta bayan Abba ya ƙarasa kan gado inda Umma take ya damk'o ta, Umma tana cizewa Abba kuma yana faɗin su sakar masa mata cikin tsananin ɓacin rai ganin wani k'aton banza yana taɓa masa ita, ganin Abba ya zabura zai miƙe wani daga cikin yaran ya riƙe shi, tare da ɗora masa bindiga a goshi, Umma ganin haka ta ruɗe ta fara kuka, a kusa da Abba yaron ya cillar da ita, shi kuma wanda ya riƙe Abba ya sake shi tare da koma wa baya. Babban nasu ya ƙara sakin wata kafirar dariya, ya daɗe yana dariyar sannan ya tsagaita ya zira hannunsa a aljihun gaban rigarsa ya ɗauko waya ya latsa ya haska wa su Abba da Umma yana faɗin "Kun san wannan?" A tare Umma da Abba suka kalli juna cikin al'ajabi, Abba ne ya fara ɗauke kallonsa daga kan wayar ya mayar ga mutumin ya ce "Eh na san sa, farin sani ma kuwa." Mutumin ya yi wani guntun murmushi sannan ya matso da fuskarsa kusa da su Abba sosai ya fara magana ƙasa_ƙasa wanda ni dai zeey ban ji ba. Zuwa can dai na ji Abba cikin d'aga murya wadda ke nuni da tsantsar ɓacin rai ya ce "Ba zan iya wannan haukan da shirmen ba, ƴar tawa guda ɗaya zan yarda in ɓata mata rayuwa in jefa ta a halaka, to bazan yi abun da kuke so ba ku yi duk abunda zaku yi, Allah ya fiku kuma da shi na dogara." Mutumin ya jinjina kai ya mai da dubansa ga Umma ya ce "Kema kin zaɓi mutuwa akan amincewa da buƙatar mu?" Umma ta saka kuka, cikin kukan ta ce "Ko me zaku mun ba zan taɓa amincewa da buƙatarku ba, kuma ƴarmu ko da bama raye Allah zai kare mana ita daga mugun nufinku, kuma da ku da wanda ya turo kun mun kai ƙarar ku gurin mai duka, shi zai mana maganin ku ya kawo ƙarshen ku da duk wasu irin hali da mummunar d'abi'arku, kuma......." Ƙarar harbin da ta ji ya katse mata zancenta ta runtse idanta da sauri, kafin ta yi wani yunk'uri ta ƙara jin wani saukar harbin, buɗe idonta ta yi zuciyarta na wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito, wata gigitacciyar ƙara ta saki ganin duk harbin da ta ji a ƙirjin Abba aka yi su, rungume shi ta yi k'am ajikinta tana kiran sunansa cikin fitar hayyaci, amma ko motsi ba ya yi, jini har ya fara ɓata farar jallabiyar dake jikinsa. Janye Abba suka yi da sauri daga jikinta itama suka sakar mata harbin a ƙirji, a take Umma ta bi bayan Abba ta zube a gurin babu alamun numfashi a tattare da ita. kafin kiftawar ido suka fice daga ɗakin a guje suka bi ta inda shigo suka fice daga gidan gaba-d'aya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.