Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 104
A falo Neehal ta tarar da Mama zaune ta na kallo, Neehal ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a gefen ta, Mama ta juyo ta kalle ta ta ce "Sai yanzu?" Neehal ta ce "Ki yi hak'uri Mama akasi a ka samu." Mama ta ce "Da Ameen ya na nan sai ki faɗa masa akasi a ka samu, kin san ba ya nan shi ya sa ki ka yi daren ai." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, "Ina Haneefan Kuma?" Mama ta tambayeta ta na maida duban ta ga TV. Kafin Neehal ta ba ta amsa Haneefah ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama, suka amsa mata a tare. "Ina ki ka tsaya kuma?" Cewar Mama ta na kallonta. Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ta na kallon Neehal. Neehal ta ɗauke kanta daga kallonta ta na ɓata rai. Mama ta tab'e baki ta maida hankalinta ga kallon da take. Haneefah ta ƙaraso ta zauna a saman carpet ta ce "Mama mun dawo, duk su na gaishe ku." Mama ta ce "Muna amsawa, ya kuka baro su?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta tashi ta haye sama, Haneefah ta bi bayanta. Ta na ajiye card d'in da Sadik ya bata a kan mudubi ta ce "Ga card nan ya ba ni, ashe ma Barrister ne." Neehal ta tab'e baki ta ce "Sai ki nemi ma'ajiya ki killace shi ai, daga ganin mutum ba ki san shi ba, sai uban surutu ki ke zuba masa." Haneefah ta ce "Kin manta ne, I'm Jornalist fa." Neehal ta ce "Ke dai kika sani."
************************
Rayuwa na ta tafiya kwanaki na ta wucewa, cikin ikon Allah har an yi sadakar arba'in É—in Anwar, su Neehal har wannan lokacin cikin hutu suke ba su koma school ba. Sosai Haneefah suke zumunci ita da Sadik, tamkar 'Yan'uwan juna tun da, dan Mama da Mommy'n Haneefah duk san Sadik a bakin Haneefah. Neehal ce dai sama_sama suke gaisawa, shi ma sai dai idan suna tare ya kira Haneefah sai ta bata su gaisa. Dad sun je sun samu Mahaifin Hafsat sun yi magana, sai dai har yanzu Hameedah da mahaifiyarta da sauran Family ba su da labarin Ameen ba Hameedah zai aura ba, kuma Æ™arshen watan nan Insha Allahu za'a kai kuÉ—i gidansu Hafsat É—in. Haneefah ta na kitchen ta na dafa Indomie da daddare ta ji Mommy dake zaune a falo ta na k'wala mata kira. Haneefah ta amsa tare da faÉ—in "Ina zuwa Mommy." Sai da ta kammala ta juyo Indomie'n a plate sannan ta fito. Ta na ajiye plate É—in a kan Centre table ta ce "Ga ni Mommy." Mommy ta ce "Wayar ki a ke ta kira." Haneefah ta Æ™arasa inda ta ajiye wayar ta É—auka ta duba missed call d'in, Saurayinta ne wanda za ta aura ya mata 1 missed call sai kuma Sadik da ya mata 2 missed call, kiran Saurayinta ta fara bi amma bai d'aga ba, bayan ta katse ta kira Sadik. Ringing biyu ya yi rejected ya kira ta. Haneefah ta d'aga tare da yin sallama, ya amsa mata ya Æ™ara da faÉ—in. "K'anwata Ya kike? Ya Mommy?" Haneefah ta ce "Ina lafiya Yayanah, Mommy ma haka, kai fa?" Sadik ya ce "Lafiya k'alau nake, am Haneefah dama ina so mu yi wata magana dake yanzu idan babu damuwa." Haneefah ta ce "Alright, to bari na ci abinci minti goma i will call you back." Sadik ya ce "Ok sai kin gama." Bayan ta gama ci ta koma d'akinta sannan ta kira sa, rejecting ya Æ™ara yi sannan ya kira ta. Bayan ta d'aga ya ce"Haneefah, Magana za mu yi a kan k'awarki Neehal." Haneefah ta yi É—an murmushi domin tun kafin yau ta gano nufin Sadik a game da Neehal. Ta ce "Ina jin ka Ya Sadik." Sadik ya É—an numfasa ya ce "Haneefah, tun kafin nu haÉ—u da ku na san ku a Television, kasancewar ni ma'abocin kallon labaranku ne, Sosai ku ke burge ni saboda yanda ku ke yin komai na ku cikin nutsuwa, ga shiga ta mutunci da kamala wanda yake nuna kun fito daga gidan tarbiyya. Ranar da na ganku a unguwarmu ji na yi tamkar mafarki nake dan farin ciki, hakan ya sa na kasa hak'uri har sai da na tsaya na muku magana, kuma wannan ita ce rana ta farko da na taÉ“a tsaida mace na mata magana." Ya É—an numfasa sannan ya cigaba da magana. "Haneefah maganar gaskiya, zuciyata ta kamu da matsanancin son k'awarki, amma ban san me ya sa nake tsoron tunkarar ta da maganar ba............âœï¸
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£*
Ya ƙara yin shiru a karo biyu sannan ya cigaba da magana kamar haka. "Abun da ya sa nake tsoron tunkarar ta da maganar saboda ina tunanin kamar ba za ta amince ta karb'i tayin soyayyata ba." Haneefah ta ce "Ya Sadik na ji batun da ka zo mun dashi, kuma na ji dad'i sosai, amma maganar gaskiya tunkarar Neehal da maganar soyayya a yanzu abu ne mai matuƙar wahala, domin har yanzu ba ta warware daga rasuwar tsohon saurayinta Anwar ba." Sadik ya ce "Allah sarki, ai dole dama sai a hankali za ta warware daga rad'ad'in mutuwar ta sa, Allah ya ji k'an sa ya gafarta masa." Haneefah ta ce "Amin, amma kar ka damu ka bar komai a hannuna zan san ta yadda zan ɓullo mata." Ta yaya kenan?" Sadik ya tambaye ta. Haneefah ta ce "Ka bani nan da wani lokaci, na san me zan yi." Sadik ya ce "Shikenan Na gode, sai na jiki." Daga haka suka yi sallama. Haneefah ta yi shiru kawai ta na tunanin ta yanda za'a yi Neehal ta amince da soyayyar Sadiƙ. Ta dad'e ta na tunanin abun kafin ta mik'e ta koma falo. Mommy har yanzu ta na zaune a falon, Haneefah ta zauna a kusa da ita ta ce "Mommy kin san me?" "Sai kin faɗa." Cewar Mommy da ta juyo ta na kallonta. Haneefah ta ce "Ya Sadik ne ya ce min wai ya na son Neehal." Mommy ta faɗaɗa fara'a a fuskarta ta ce "Kai Ma sha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin, amma fa Mommy akwai matsala."
"Matsala kuma ta me Haneefah?"
"Mommy Neehal mana, na san ba za ta taɓa amincewa da soyayyar Ya Sadik ba, saboda kwanaki mun yi magana da ita, ta ce mun ita ba za ta ƙara kula wani ɗa Namiji da sunan soyayya ba, Tun da Anwar ya rasu." Mommy ta ce "Zancen banza, to haka za ta yi ta zama ba ta yi aure ba ko kuma me take nufi? Mace ma take yin Aure mijinta ya rasu kuma ta sake wani auran su zauna lafiya, balle ita da yake Saurayinta, yarinta ce kawai ke damunta." Haneefah ta ce "To ai ita Mommy dan ta ga ankashe Jameel da Anwar wai karta ƙara yin soyayya da wani shima a kashe shi." Mommy ta ce "Wannan duk ba hujja ba ce, mutuwa da rayuwa duk na Allah ne, su ma da suka mutun kwanan su ne ya ƙare, Allah dai ya ji k'an su, ita kuma Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta." Haneefah ta ce "Amin."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.