Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 104
Washegari, bayan ta idar da sallar asuba ta yi karatun Alkur'ani mai girma izifi biyu, sannan ta É—auko materials É—inta na school ta É—an dudduba, gari na fara haske ta tashi ta gyara É—akinta, sannan ta faÉ—a toilet ta yi wanka. 7:30 ta sakko Æ™asa cikin shirinta na zuwa gurin aiki, ta na sanye da hijabinta wanda ya zo mata har Æ™asa, Mama ta na kitchen ta na haÉ—a breakfast, Æ™arasawa kitchen d'in ta yi ta ce "Morning Mum" Mama ta ce "Morning dear, har kin fito" Neehal ta ce "Ehh, kin san yau Sunday za mu haÉ—a labaran week d'in gabad'aya dole sai na je da wuri" Mama ta ce "Amma dai za ki tsaya ki yi break ko" Neehal ta ce "Idan na je can zan ci, bari na É—iba cake" Mama ta ce "A'a ki dai tsaya ki ci abincin ko kaÉ—anne nasan halinki ba ci za ki yi ba" Neehal ba ta musa ba, ta haÉ—a tea a Æ™aramin cup ta d'ebi irish d'in da Mama ta soya kaÉ—an, ta koma falo ta ci. Kayan ta dawo kitchen ta ajiye bayan ta gama ci, ta yi wa Mama sallama, Maman ta mata addu'a ta fice. Sai da ta biya part d'in Dad sharp_sharp ta gaishesa sannan ta fito ta tafi........âœï¸
[7/21, 8:59 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*0ï¸âƒ£4ï¸âƒ£*
Bayan Mama ta gama haɗa breakfast din ta ɗibi na Dad ta haɗa masa a cikin tire, tana ƙoƙarin fita Dije mai aiki ta shigo kitchen d'in, ta risina ta ce "Ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya kalau Dije, yawwa dama na gama sai ki haɗa wanke_wanke ki yi ki gyara kitchen d'in" cikin girmamawa Dije ta ce "Toh Hajiya" Mama ta fita daga kitchen d'in, Zulai mai aiki ta na mopping a falon, ganin Mama ya sa ta ajiye mopper ɗin hannunta ta taho da sauri ta na faɗin "Sannu da fitowa Hajiya" Mama ta ce "Yawwa mun tashi Lafiya" Zulai ta ce "Lafiya ƙalau Hajiya" tana ƙoƙarin karɓar kayan hannun Mama, Mama ta ce "Ki barshi ki je ki ci gaba da aikin ki kawai, idan kun gama sai ku ɗibi abinci a kitchen ku karya" Zulai ta ce "Toh Hajiya" ta koma ta cigaba da aikinta, Mama kuma ta nufi part din Dad.
Dad ya na bedroom d'insa, Mama ta ajiye masa breakfast d'insa a kan dinning sannan ta nufi bedroom d'in nasa, da sallama ta shiga ya na zaune akan gadonsa ya na operating system, d'agowa ya yi ya na duban Mama tare da amsa mata sallamar da ta yi, Mama ta zauna a gefensa ta na faɗin "Ga abincinka can na kammala." Dad ya yi murmushi ya ce "Godiya nake matar Aljannah" Mama ta yi murmushi ta tashi ta ɗauke system ɗin gabansa ta ajiye a kan bedside locker ta ce "Mu je ka yi breakfast idan ka gama sai ka cigaba da aikin" Dad ya yi murmushi ya mik'e ya bi bayan Mama suka fita zuwa falonsa, Mama ta koma ta ɗauko tea plaks ta dawo ta yi serving ɗin su suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bayan sun gama Mama ta yi hamdala ta na goge bakinta da tissue ta ce "Wai Ni kuwa Dad ya ku ka yi da Son jiya?" Dad ya ce "Na masa magana a kan ya kamata zuwa yanzu a ce ya na da iyali shima ya ce Insha Allah bayan bikin daughter zai fitar da mata shima" Mama ta sauke numfashi ta ce "Amma Dad me ka fuskanta ya na damun Ameen, tun jiya da yawo gabad'aya hankalina ya kasa kwanciya da yanayin da na gan shi" Dad ya ce "Nima a nawa ɓangaren hakane Doctor, abun da ya ƙara tayar mun da hankali da Muhammad ramar da ya yi da kuma yanda ka na kallonshi za ka hango zallar damuwa a tattare da shi, kuma duk abin da yake damun Muhammad ba ƙaramin abu ba ne, dan kin san Muhammad tun ya na ɗan ƙaramin shi, yaro ne mai juriya, haƙuri, kawaici gami da tawakkali, zai yi wuya ka gane ya na cikin damuwa ko ka fuskanta, idan har ba shi ya furta maka ba, wannan dalilin ya sa nasan lallai abin da yake damunsa ba ƙaramin abu ba ne" Mama ta sauke wani gwauran numfashi tare da dafe kanta ba ta ce komai ba, Dad ya kama hannunta cikin lallami ya fara mata magana da faɗin "Kinga Doctor ki kwantar da hankalinki, Insha Allahu ba wata matsala ba ce, ba na son in ga kina damuwar nan, kamar yadda ya ce mu dinga yi masa addu'a ki dinga yi masan, Insha Allahu koma meke damunsa Allah zai yaye masa" Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya sa" Dad ya saki hannunta tare da mik'ewa ya na faɗin "Yawwa ko kefa, ba na son na ga ki na yawan damuwar nan ko kaɗan, dama naga kwana biyu kin ɗan faɗa" Mama ta mik'e itama ta na faɗin "To ba dole ba Dad ka ga ina rama, autatah za ta tafi, ai ahakanma ina ƙoƙarin b'oye damuwata dan kar ta damu itama" Dad da ya fara tafiya ya ce "To ya za'ai sai haƙuri, Ni kaina na fara kewar daughter tun yanzu"
Bayan Mama ta gama gyara part d'in Dad ta haÉ—a masa ruwan wanka ya yi, ta dawo part d'inta ta baro shi ya na aiki tun da Yau Sunday ba fita zai yi ba. ÆŠakin Hajiya ta shiga ta tarar da ita ta na haÉ—a kaya, Mama ta zauna a gefen gado ta ce "Hajiya ashe kin tashi, har Gen. ya na cewa zai zo ya gaishe ki, na ce ya bari sai anjima dan nasan da k'yar in kin tashi" Hajiya ta ce "Na tashi mana, ko zan zauna ina ta barci har wannan lokacin kamar wata marar aikin yi" Mama ta ce "ai na san ki ne Hajiya da son bacci" Hajiya ta ce "To yau ban yi ba, tun É—azu na tashi nake haÉ—a kayana ba sai goben ta yi Mahmud É—in ya zo ba in yi ta kame_kamen ban gama shiri ba" Mama ta ce "Ai da kin barshi Hajiya na haÉ—a miki ko kuma na turo su Dije su haÉ—a miki, tun da ko karyawa ba ki yi ba" Hajiya ta kama hab'a ta ce "Rufa mini asiri, masu aiki da haÉ—a mun kaya, lalacewar tawa bata kai haka ba, kema na hutashsheki tun da ba wani abu na aiki nake a gidan ba, dan haÉ—a kaya dai ba zai kun wahala ba" Mama ta ce "Shikenan bari na kawo miki abincinki" Mama ba ta jira amsar Hajiya ba, ta mik'e ta fice.
Ƙarfe 11 Ameen ya shigo falon Mama, su na zaune ita da Hajiya suna kallo, Mama ta bishi da kallo har ya zauna a gefenta, cikin muryarsa kamar baya son magana ya ce "Morning Mum, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya k'alau and you?" Ya ce "Fyn" Mama ta ce "Masha Allah, yau za ka wuce Lagos ɗin ko sai gobe?" A hankali ya ce "Sai gobe da safe" Mama ta ce "Allah ya kai mu" Hajiya dake saurarensu ta keɓe fuska ta ce "In Mutum bai kula ni ba, sai me? Daga yau ma ba ƙara gani na za ka yi a gidanku ba, sai wani lokacin kuma" ɗan Murmushi Ameen ya yi bai ce komai ba, sai ma mik'ewa da ya yi ya nufi part d'in Dad, Hajiya ta bishi da harara" Mama ba ta ce komai ba, sanin da ta yi ba'a shiga tsakanin Hajiya da Ameen, dan Hajiya ko wata ta yi ba ta zo gidan ba, da kanshi ya ke zuwa har Gombe ya ɗauko ta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.