Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 80 of 104
_By_
_Zeey Kumurya_
*5ï¸âƒ£2ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
A hankali take tafiya kamar bata son taka ƙasa, as always shi kuma tunda ya hango ta ya ƙura mata ido. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta zauna a kan carpet ɗan nesa da shi tare da kawar da kanta gefe, su Afrah kuwa gurinsa suka nufa, wayoyinsa guda biyu ya basu bayan ya kunna musu game, cikin murna suka karb'a suka fara yi. Ba tare da ta kalli inda yake ba kamar an mata dole ta ce, "Ina yini." Bai amsa ba sai tashi da ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna ganin yanayinta ya kira ainihin sunanta. "Fateemah." Ta d'ago ta dube shi cikin mamaki dan ko da can bai taɓa kiran ta da Fateemah ba. A hankali ta ce "Na'am." Ya ce "Jikin naki ne har yanzu?" Ta girgiza masa kai, ya ce "To me ya faru na ga ranki a ɓace, ko nine ba kya son gani ko kuma kawo miki su Afrah da na yi ne ba ki ji daɗi ba?" Ta ɗan saki fuskarta ta ce "A'a ba komai Uncle." Ya ƙara matsowa kusa da ita ya sassauta murya ya ce "To me yasa ba kya farin ciki, Please be happy, bana so na ganki a haka Pleaseee.." ya ƙarashe maganar da jan kalmar ƙarshe cikin wani irin wani salo da yasa ta ji wani iri a jikinta. Ta ɗan yi murmushi tana kallon shi ta ce "To na yi Uncle, ya kuka baro Mamy?" Shima yana murmushin ya ce "Lafiya k'alau, tana ta tambayar ki, ta yi zaton ma tare zamu zo." Bata kuma cewa komai ba ta miƙa masa wayarsa dake hannunta, ya karɓa tare da faɗin. "Oh, na ma manta, thank you." Yana ƙoƙarin zira wayar a aljihu ba tare daya latsa ta ba ta ce "An kira ka fa." Ta yi maganar cikin ɓata fuska. Cikin mamaki ya zaro wayar ya duba dan ba permanent sim ɗinsa ba ne a ciki bai yi tunanin wani zai kira shi a wayar ba. Tab'e baki ya yi bayan ya ga mai kiran ya saka wayar a aljihu ba tare da ya bi bayan kiran ba. Neehal ta ɗauke kanta daga kallon sa ta ɗan turo baki gaba. Ya saka tafin hannunsa ya taɓa goshinta ya ce "Har yanzu da sauran zazzaɓi a jikinki Princess, kina shan magani kuwa?" Ta ce "Uhm." Kawai. Ya ƙura mata ido cikin nazartar ta, ya lura kamar akwai abun da ke damunta tunda ta fito, ko kuma wacce ke cikin ɓacin rai. Ya ɗauke hannunsa daga goshinta ya d'ago hab'arta cikin tsare gida ya ce "Neehal me yake damunki?" Ta lumshe idonta tare da girgiza masa kai tana ƙoƙarin saka hannunta ta cire nasa daga fuskarta. Ya riƙe hannun nata ya ce "Please talk to me Princess, ko kina so ki ganni a cikin damuwa nima?" Ta yi shiru. Ya ƙara tambayar ta, nan ma bata tanka masa ba. Ya sauke numfashi ya cire hannunsa daga hab'arta tare da sakar mata hannunta ya ce "Okay, Good bye Dear, tunda na fuskanci kamar nine ba kya son gani." Ta buɗe idonta da sauri sai hawaye sharr wanda bata san sanda suka zubo ba. Ya dafe kansa tare da faɗin "Oh my God, Dan Allah Princess me yake damunki ne, ko na miki wani abun ne da baki ji daɗi ba?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe yana kallon ta. Ita kanta bata san me ya saka ta a cikin wannan yanayin ba, kuma ta yi ƙoƙarin ta danne kar ya fuskanta amma ta kasa. Ta turo baki gaba sosai ta ce "Ka ce mun tunda Maman twins ta rasu baka ƙara kula wata mace ba, and now kuma naga wata ta kira ka harda text, who is she?" Ta yi maganar iya gaskiyar ta. Sai yanzu ya gane bakin zaren, shi dariya ma ta ba shi ba kaɗan ba, amma yanda take a sama ɗin nan in ya dara ya san da matsala, musamman yanda ta tsare shi da kyakkyawan idanunwan nan nata tana jiran amsa. Ya danne dariyarsa ya ce "Oh wai Jamila, she is my cousin sister, ƴar ƙanwar Dad ce." Ta juya masa idonta ba tare da ta ce komai ba, amma bata gamsu da abun da ya faɗa ba. Ya yi ɗan murmushi tare da matsowa daf da ita, ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta ya ce "Princess ce kaɗai a zuciyar Uncle ɗinta, tun a da, da yanzu da kuma har abada, daga ita kuma babu ƙari." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunyar gano tan da ya yi. Ya yi ƴar dariya ya ce "Ashe Babin Uncle ta fara sonsa har da su kishi?" Ta juya masa baya a shagwab'e ta ce "Ni ba kishi nake ba?" Ya ce "To me kike? Jealous? Kamar zata yi kuka ta ce "Ni fa Allah ba kishi nake ba." Ya juyo da ita da hannunsa ya sa tafin hannunsa ya share mata hawayen data zubar d'azu, zuciyarsa fess da yanda ta nuna tana kishin nasa. Ya zubawa fuskarta ido yana jin kamar ya mayar da ita cikin jikinsa saboda k'auna. Jin maganar Afrah a kusa da shi yasa ya ɗauke idonsa daga kallon ta ya mayar kan yarinyar da take miƙo masa wayarsa tana faɗin "Daddy kiran Sallah ake a cikin wayar." Ya karɓa ya ce "To aje a yi alwala a yi Sallah." Ta ce "Tom Daddy." Ya yi mata peck a goshi itama ta mayar masa tana dariya sannan ta nufi upstairs da ɗan gudunta tana cewa Amrah sai ta riga ta hawa saman. Jin haka itama Amrah ta kawo masa ɗaya wayar ta bi bayan ta. Neehal ta bi su da kallo cikin k'auna. Ya ce "Princess zan wuce?" Ta juyo ta ce "Sai yaushe?" Ya ce "Gobe da safe Insha Kafin na wuce." Ta ce "Allah ya kai mu." Ya miƙe tsaye yana faɗin "Amin." Itama miƙewar ta yi, ya ja karan hancinta ya ce "Bye, I love You." Ta ce "Allah ya kiyaye." Ya ɓata fuska tare da langwab'ar da kansa ya ce "Ba feedback?" ta yi murmushi bata ce komai ba, ya ce "Shikenan." Ta ce "Thanks you for coming, and..." "Kawo miki twins ko?" Ya ƙarasa mata dan ya san haka zata faɗa. Ta yi murmushi tare da gyaɗa masa kai. Ya yi mata murmushin nan nasa mai kyau tare daga mata hannu sannan ya juya ya tafi. Ta sauke ajiyar zuciya bayan ya fice, a ranta tana faɗin 'Ko sallama bai yi da ƴaƴansa ba.' Ta juya ta haye upstairs, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana ƙoƙarin shimfid'a darduma, su Afrah suna taya ta. Amrah ta ce mata "Aunty ina Daddy? Ya tafi?" Ta ce "Eh ya tafi gidan Mamy, amma gobe da safe zai dawo." Mama ta ce "Ki je ki yi alwala ki zo ki yi Sallah, tunda kin warke sai ki shiga kitchen ki yi masa something special gobe in ya zo sai ki ba shi ya tafi da shi" Ta ɓata fuska ta zauna a bakin gado ta ce "Mama ban fa warke ba, cikina ma tun safe ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Daga haka ta tayar da Sallarta. Miƙewa ta yi itama ta shiga toilet ta fito ta tayar da Sallar.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.