Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 83 of 104
_By_
_Zeey Kumurya_
*5ï¸âƒ£1ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
Washegari da misalin ƙarfe goma na safe, Neehal tana cikin bacci ta ji muryar Hajiya tana tashin ta. Ta buɗe ido da ƙyar tana duban ta cikin muryar bacci ta ce "Bani da lafiyar ma ba zaki bar ni na huta ba?" Hajiya ta ce "To tafiya zan yi na tashe ki mu yi sallama ƴar nema." Ta tashi zaune tana hamma tare da yin salati. Ta dubi Hajiya ta ce "Kai Hajiya yanzu tafiya zaki yi kamar wadda ake kora? Ki ɗan ƙara mana kwana biyu mana." Hajiya ta ce "Ba zan zauna ba, yau a Gombe mahaifata zan kwana, in kuma na ƙara dawowa garin nan to sai dai in bikin na zo insha Allah." Neehal ta ce "Zaki yi shekaru kuwa baki zo ba, indai bikina ne." Hajiya ta riƙe baki ta ce "Ikon Allah, ka ga shashashar yarinya zatai wa kanta mugun baki, to in ba ki yi aure ba jiƙa ki su Faɗiman za su yi su shanye? ko kuma zama zaki yi kuna goga ƙafaɗa da ita a gidan?" Neehal ta sauko daga kan gado bata tare da tankawa Hajiya ba ta shige toilet. Hajiya ta ce "Kya shige banɗaki mana ja'irar kashi kawai, da kai kamar k'ullin magani." Ta ƙaraci mitarta sannan ta fice daga ɗakin. Bayan Neehal ta fito daga toilet ɗin ta saka kaya sannan ta hau gyaran dakin nata, tana cikin gyaran Mama da Daddy suka shigo. Daddy ya ce "Daughter da kanki kike gyaran ɗaki ke da ba ishashshiyar lafiya ce da take ba." Ta yi murmushi tare da ajiye filon dake hannunta ta ce "Ai na ji sauƙi Daddy na." Mama ta ce "Masha Allah, Allah ya k'aro sauƙi." Ta amsa da Amin, sannan ta gaishe su. Daddy ya ce "Jiya da daddare na zo ganin jikin naki na tarar kina ta bacci, kwakwa da dabidon da kika ce mun kina so yana cikin fridge na bawa Mamanki ta ajiye miki." Neehal ta ce "To Daddy na, na gode sosai." Ta kalli Mama ta ce "Allah yasa dai babu wanda ya ci mun." Mama ta ce "Tunda kowa irin ki ne ba, Ki sauka ƙasa ki yi break zamu je gidan Ameen yanzu mu dubo Hafsah." Neehal ta ce "Hajiya ta tafi ne?" Mama ta ce "Tana falo yanzu dai zata tafin." Bin su Mama ta yi suka sauka ƙasa tare, har parking space ta raka su, tay wa Hajiya sallama wadda direban Mama zai kai ta gidansu Aunty A'isha da Aunty Sadiya daga can zai wuce ya kai ta Gomben. Bayan ta koma cikin gidan ta haɗa tea ta sha ta ɗan ci Irish sannan ta sha maganinta. Suna zaune a falon ƙasa suna hira da su Dije suka ji ƙarar door beil, Zulai ta tashi ta je ta buɗe, a zaton Neehal Mama ce ta dawo amma sai ta ji muryar waɗanda bata taɓa tsammani ba wato Afrah da Amrah suna kwad'a kiran sunanta. Ta tashi tsaye da sauri tana kallon su cikin shock. Suka taho da gudu suka rungume ta. Ta tsugunna itama ta rungume su duka cikin tsananin farincikin ganin su. Ta d'ago su daga jikinta har lokacin fuskarta na ɗauke da mamaki ta ce "Sweethearts wa ya kawo ku?" Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ne, Aunty ina Mama?" Ta ce "Ta fita unguwa amma yanzu za ta dawo." Afrah ta ce "Aunty ya jiki? Daddy ya ce baki da lafiya kar mu zo mu cika miki kunne da surutu." Ta shafi kuncin yarinyar ta ce "Da sauƙi Darling ina Daddy'n." Amrah ta nuna mata bakin ƙofa inda yake a tsaye hannunsa hard'e a ƙirjinsa yana kallon su, ga trolley ɗin kayan su Afrah a gefen sa." Ta ƙura masa ido tunda suna ɗan nesa da juna baza su iya haɗa ido ba, yau sanye yake cikin manyan kaya wanda suka yi masa kyau sosai, tunda take bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba sai yau. Ya fara takowa a hankali zuwa inda suke, ganin haka yasa su Dije suka tashi suka nufi kitchen dan kawo masa drinks.
Ta ɗauke idonta daga kallonsa da sauri ta mayar ga su Afrah tana murmushi ta ce "Welcome dear, I missed you alot." Amrah ta ce "Missed you too Aunty." Ta ce "Ya school? Dafatan dai kuna karatu sosai?" Suka gyaɗa mata kai. Ta ce "That's is good, ina Ummi da Aunty Zahrah da Ammi?" Afrah ta ce "Suna gida mun bara su, Aunty Zahrah ta ce zata biyo mu Ummi ta hana ta." Ta zauna sosai a kan carpet ɗin falon ta ɗaura su duka akan cinyarta suna yi mata hira, ko ƙara kallon inda Ahmad yake bata yi ba. Shi ma bai ce mata komai ba sai zama da ya yi yana kallon su. Har su Dije suka dawo falon suka ajiye masu drinks da snacks. Ganin da gaske ba kula shi zatai ba ta yaranta kawai take sai ya cewa su Afrah su tashi daga jikinta ba su ga ba ta da lafiya ba. Yaran suka tashi da sauri suna faɗin "I'm sorry Aunty." Neehal ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kamo hannunsu da nufin su wuce sama, a hankali kanta na ƙasa ta ce "Ina kwana." Ya k'ank'ance ido yana dubanta ya ce "Lafiya, ya jikin naki?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Tare da miƙewa ya ce wa su Afrah su ya kai su gidan Mamy, da yamma sai ya dawo da su. Neehal ta ce "Daga zuwanku, dan Allah ka bari idan Mama ta dawo sai mu je tare." Ya ce "Ke da baki da lafiya kuma zaki fita, idan kin ƙara warwarewa sai ku je, tunda za su kwana biyu a nan." Bata ce komai ba ta saki hannun yaran ba don taso ba. Ya kama hannunsu suka juya za su tafi, ta kalli abubuwan da su Dije suka ajiye masa ta ce "Uncle ko ruwa baka sha ba zaka tafi?" Ya yi mata ɗan murmushi ya ce "Idan na dawo zan sha." Ta ce "Shikenan sai kun dawo ɗin, Allah ya kiyaye." Ta d'agawa su Afrah hannu tana faɗin su gaishe mata da Mamy. Bayan fitar su ta zauna akan kujera zuciyarta cike da farincikin zuwan yaran. Ta miƙe dan kai trolley ɗinsu ɗakinta sai ta ga ƙaramar waya keypad akan kujerar da Ahmad ya zauna, da alama dai tasa ce ya manta ta. Wayarta ta ɗauko akan centre table da sauri ta kira shi dan ta sanar masa ya manta wayar tunda bai yi nisa ba ya dawo ya ɗauka. Ringing biyu ya d'aga, ta ce "Uncle ka manta ƙaramar wayarka a nan." Ya ce "Ohh, ki ajiye mun ita kawai Princess, idan na dawo anjima sai na karb'a." Ta ce "Tom Allah ya kai mu." Daga haka ta katse kiran. Ta ɗauki wayar ta ja trollin su Afrah ta yi upstairs. Tana shiga ɗakinta ta ji cikinta ya fara juya mata hakan yasa ta kwanta, ba jimawa da kwanciyar tata bacci ya ɗauke ta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.