Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 97 of 104
Da ƙyar Ahmad ya iya jan ƙafarsa ya je parking space, yana zuwa ya buɗe Motar da ya zo da ita ya shiga ya zauna ya ɗora kansa akan sitiyarin Motar, yana jin zuciyarsa tamkar zata soye saboda zafin da take masa. Ganin abun yake tamkar almara, domin bai taɓa tunanin zai ƙara rasa Neehal a karo na biyu ba. Amma ya yarda da ƙaddara, ya kuma yarda wani ba ya taɓa auran matar wani. Zai dage da addu'a akan Allah ya cire masa sonta ko da ba duka ba daga cikin ransa, ya kuma ba shi mace ta gari wadda zata kula da shi da marayun ƴaƴansa. Sai dai ya rasa me yasa wani b'arin na zuciyarsa yake tabbatar masa da bai rasa Neehal ba, yake nuna masa kamar zai mallake ta a gaba. Ya sauke numfashi tare da addu'ar idan rabonsa ce ita, Allah ya ba shi, zai je ya dage da addu'a. Sunan Allah yay ta maimaita a ransa, har ya ɗan samu nutsuwa. Cikin dauriya ya kunna Motar ya fice daga gidan bayan an buɗe masa gate ya nufi gidan Mamy. Yanda Mamy ta ganshi ya shigo a sanyaye kamar mai cuta ta san da matsala, a ɗan rikece ta tambaye shi me nene? Kamar zai ɓoye mata sai kuma ya sanar mata. Itama Mamy ta ji ba daɗi a ranta sosai, domin ta yi wa Ahmad sha'awar Neehal, dan ta yaba da hankalinta da nutsuwarta. Amma sai ta kwantar masa da hankali, ta ce ya je ya dage da addu'a Allah ya zaɓa masa abin da ya fi Alkhairi.
Har bayan Magriba Neehal bata daina kuka ba, Mama ta yi rarrashin ta yi nasihar ta yi faɗan amma ta ƙi barin kukan, har ta gaji ta ƙyale ta. Tana jin wayarta nata vibrate ana ta kiran ta amma ta ƙi bi ta kanta. Ga kanta dake ciwo saboda kukan da take. Bayan Magriban ne Ameen ya zo gidan, lokacin tana ɗakinta a kwance akan gado. Bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta Neehal ɗin, ta sanar masa tana ɗaki tana kuka, ko abinci bata ci ba tun safe. Bai tambaye ta dalilin kukan ba ya tashi ya shiga ɗakin. Ya zauna a gefen gadon ya kira sunanta, ta tashi zaune da ƙyar tana goge hawayen fuskarta, idanunta sun yi jajur. Cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi yay mata Ƴar nasiha, akan kuka ba maganin damuwa ba ne, komai yake damun ka, ka kaiwa Allah kukan ka, shi zai maka magani. Sai gashi ta yi shiru, ya ce ta je ta wanke fuskarta ta zo ta ci abinci. Ba ta musa ba, ta tashi ta yi abin da ya ce. Mama ta cika da mamakin ganin cikin mintuna ƙalilan ta saki ranta, Alhalin ita tun yamma take fama da ita. Sai da ta ci abincin ta sha maganin ciwon kai sannan Ameen ya bar gidan.
Washegari kamar yadda Dad ya ce, Sadik ya zo gidan da yamma. Har part É—in Daddy'n akai masa iso ya je ya same shi. Daddy yay masa Æ´an tambayoyi, sannan ya ce ya bashi auran Neehal ya turo magabatansa. Ai Sadik ji ya yi kamar ya rungume Daddy dan tsananin farin ciki, yay ta zuba masa godiya. Ranar Neehal ta sha kalamai da soyayya a gurin shi kala_kala, ita kuwa tay ta masa dariya tana tunanin ranar da aka É—aura musu aure kuma sai ya kusa mutuwa dan farinciki. Bayan sati É—aya mahaifinsa da abokinsa da Yayan Maamah suka zo nema masa auren Neehal, tare da kuÉ—in na gani ina so. Daddy da Kawu Musa da Uncle Mahmud, da mijin Aunty A'isha, su suka karb'i kuÉ—in, aka saka ranar biki bayan Æ™aramar Sallah da yardar Allah, lokacin Neehal sun yi graduation ba jimawa. Su Sadik baki ya Æ™i rufuwa, saboda farincikin nan da watanni biyar zuwa shida zai angonce da masoyiyarsa. A É“angaren Ahmad kuwa a washegarin ranar da ya zo ya koma Abuja, yana zuwa ya sanar da su Ummi abun da yake faruwa. Sun ji ba daÉ—i sosai har Abban su Ahmad, amma suka ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Ahmad ya bawa zuciyarsa haquri, bai bari damuwa ta masa illa ba, duk da ko d'igo babu abun da ya ragu na son Neehal a cikin zuciyarsa. Daga ya ji abun zai dame sa sai ya dinga maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da hasbunallahu'wani'imal'wakil, ga zuciyarsa kullum cikin Æ™arfafa masa gwiwar Neehal tasa ce take, kar ya fidda rai da samun ta. Kuma babu abun da ya canza wa Neehal daga yanda suke before, idan ya kira wa su Afrah ita a waya, ta ce su ba shi wayar yana karÉ“a su yi magana har da Æ´ar tsokana wani lokacin, sai dai ba ya mata zancen soyayya ko kaÉ—an, zumunci kawai suke yi. Itama Neehal É—in ta yi Æ™oÆ™ari ta cire damuwar rabuwa da shi daga ranta. Ta yarda cewa Allah ya yi Sadik ne mijinta tun fil azal, ba Jameel, Anwar da Ahmad ba, tunda su sun rasu, Ahmad kuma shi yasa Allah ya raba su tun a farko, dan da a ce ba su rabu da shi ba a lokacin da take gidan Aunty Fauziyya, da ko soyayya ba za ta yi da Jameel da Anwar ba, tunda ga shi kuma tun lokacin yake son ta. Ta kwantar da hankalinta suna shan soyayyar su da Sadik. Sai dai tunda aka tsayar da lokacin bikin su take jin wani irin feeling a cikin zuciyarta, feeling É—in da ta kasa tantance ko na mene ne, sai dai yana mata yanayin kamar tsoro ko fargaba, amma kuma tsoron da fargabar na mene? Sai kuma wani abu guda É—aya, É—an sakin fuskar da ta fara samu daga gurin Ameen da kulawa ya daina yi mata yanzu, sai ta gaishe shi ma ya Æ™i amsawa, ita kuma hakan na damun ta matuÆ™a, ba ta son ta ga yana yi mata irin wannan shariyar, sai ta ji duk ranta babu daÉ—i........âœï¸
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*5ï¸âƒ£9ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
Haka rayuwa tay ta tafiya, bikin Neehal na Æ™ara kusantowa. Æangarorin biyu na amarya dana ango suna ta shirye-shiryen bikin, duk da dangin Angon ba kowa ke son auren ba. Sai dai kamar yadda Uncle Mahmud ya roÆ™i alfarma tun ranar da aka kawo kuÉ—in Auren, akan a É“oye batun auren sai abun ya matso daf sannan a bayyana saboda tsaro, a cewar sa idan ma wani ne yake kashe samarin da Neehal zata aura kamar yadda ake hasashe, to lokacin da zancen bikin zai fito kafin ya gama duk wani shirinsa an yi bikin an gama Insha Allah. Hakan ce ta kasance kuwa domin ba kowa ya san da maganar bikin ba, sai na jiki_jiki wanda ya zama dole. Ita Mama kam ta ce babu wani shagali da za'ai da bikin, É—aurin Aure kawai za'ayi a kai amarya gidan ta. Sai dai fa shi Ango Sadik da bai san da shirin Mama ba yana ta shirye-shiryen haÉ—a gagarumar dinner shi da abokanansa. Haneefah ma ta ce baza su yi biki lami ba, sai sun cashe ko da na rana É—aya ne, tana nan tana ta yiwa Mama naci da magiya akan ta amince. Ita kam Neehal tsarin Maman ya mata dai-dai, dan ita ba gwanar son harkar taro ba ce dama. A wannan azumin na bana Neehal suka ziyarci Æ™asa mai tsarki ita da Mama, Mama ta cika alÆ™awarin data É—aukar mata tun last year. Sun je sun yi Umrah, satin su biyu a can suka dawo. Bayan Sallah da sati É—aya suka fara final exam É—insu. Neehal ta maida hankalinta sosai akan karatu, ta watsar da duk wani feeling da take ji a cikin ranta ta duk'ufa ga karatu, domin tana son yanda ta fara karatun ta successfully ta gama successfully. A gefe guda kuma zuciyarta cike take da murnar kammala karatunta da zata yi this year.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.