Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 35 of 104
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
*Whatsapp OR* *Call 08066268951*
.Cikin Æ´an mintuna suka Æ™arasa gidan Ameen dake Lamido Crescent. Driver ya danna horn mai gadi Ya zo ya buÉ—e masa madaidaicin gate É—in gidan, tun daga farfajiyar gidan zaka tabbatar da gidan ya haÉ—u gami da tsaruwa. Bayan ya yi parking Neehal ta fito Twins suka biyo bayanta, sallama suka yi da driver sannan ta nufi inda take hango Æ™ofar shiga ainihin cikin gidan, Mota É—aya ta gani a harabar gidan, hakan yasa take tunanin da Æ™yar in Ameen yana gidan. Hafsah tana É—akinta a kwance ta ji Æ™arar door beil, a tunaninta Ameen ne ya dawo daga masallaci hakan ya sata tashi da sauri ta fito ta sakko Æ™asa ta buÉ—e Æ™ofar falon. Kamar a mafarki ta ga Neehal tsaye a bakin Æ™ofa, haÉ—e rai ta yi sosai kamar ba ta taÉ“a dariya ba ta shiga Æ™arewa Neehal kallo, wadda ke sanye cikin doguwar riga pink colour, an mata ado da royal blue, rigar ta ci guga har wani É—aukar ido take, ta yi kyau sosai kamar ka sace ta. Neehal ta danne zuciyarta tana murmushi ta ce "Sannu da gida Aunty Amarya." Ƙara haÉ—e rai Hafsat ta yi ta ce "Yawwa." Sannan ta juya ta koma ciki, Neehal ta shiga Falon bakinta É—auke da Sallama Twins na biye da ita, suna ta murna sun zo unguwa. Kan kujera suka yi da gudu suka haye, Hafsah ta dube su kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa. Amrah ta dubi Hafsah ta ce "Ina kwana." Kafin ta gama rufe baki Afrah ma ta gaishe ta, ta amsa musu tana bin su da kallo. Neehal ta Æ™araso cikin falon ta zauna jikinta a sanyaye, a hankali ta ce "Ina yini Aunty." Hafsah kamar an mata dole ta ce "Lafiya." Daga haka ta yi wucewarta sama. Neehal ta bi ta da kallo duk murna da dokin zuwan da take ya koma ciki, gaba-d'aya ta ji dama ba ta zo ba, kamar ta tashi ta koma gida haka take ji, amma ta daure saboda idan ta koma gida ba ta san me zata cewa Mama ya dawo da ita ba. Falon ta shiga Æ™arewa kallo, babu Æ™arya falon ya haÉ—u, domin kuwa an narkawa Hafsah kaya. Komai dake cikin falon Dark and light purple ne. Neehal ta É—auko wayarta daga cikin handbag É—inta ta kira layin Haneefah ta sanar mata ta je gidan Ameen yau amma Haneefan ba ta É—auka ba. Su Afrah kuwa tsalle_tsalle suka hau yi a falon, Neehal ta musu mgn su bari, ta nuna musu kusa da ita ta ce su dawo su zauna. Suka dawo suka zauna suna turo baki gaba. Har mintuna goma suka wuce Hafsah ba ta dawo gurinsu ba, kamar ma ba baÆ™i ta yi ba ta koma ta yi kwanciyarta. Afrah da ta gaji da zama ta dubi Neehal ta ce "Aunty bari na kira Aunty'n da ta hau sama." Neehal ta ce "Ban aike ki ba." Yarinyar ta É“ata fuska. Neehal ta bi Æ™asan Falon da kallo, tiles É—in ta gani kamar da datti. A hankali ta tashi ta shiga duba falon ko za ta ga tsintsiya, a bakin Æ™ofa ta ganta tare da mopper, É—auka ta yi ta shiga share falon, bayan ta gama ta yi mopping É—in shi, tana cikin yi Hafsah ta sakko, da mamaki take duban Neehal, can kuma ta tab'e baki ta ce "Ina kika samu ruwan da kike mopping?" Toilet É—in dake falon Neehal ta nuna mata da hannunta ba tare da ta yi magana ba, Hafsat ta wuce kitchen tana tab'e baki. Amrah ta dubi Neehal ta ce "Aunty zan ci abinci." Neehal ta mata shiru, har sai da yarinyar ta Æ™ara maimaita mata sannan ta ce "Ba ki ci abinci ba ne a gida?" Amrah ta gyaÉ—a mata kai tana keÉ“e fuska, Neehal ta yi shiru kawai dan bata san me zata ce mata ba. Hafsah ta fito daga kitchen hannunta É—auke da ruwa da lemo ta ajiye a gaban yaran, ta dubi Neehal a yatsine ta ce ki shiga kitchen ki dafa muku abin da zaku ci. Neehal ta mata wani kallo sannan ta ce "Toh." a ranta tana faÉ—in 'Ai ba yunwa na ce miki ina ji ba.' Daga haka Hafsah ta koma sama, ashe Ameen ne ya mata waya yana hanya shi yasa ta yi sauri ta sakko ta kawo wa su Neehal drinks dan kar ya dawo ya ga bata basu ba. Bayan Neehal ta gama mopping É—in ta koma ta zauna tana duban su Afrah dake shan lemo, Hafsah ta Æ™ara sakkowa hannunta É—auke plate ta ajiye a gaban Neehal, A hankali Neehal ta ce "Thank you." Hafsat ba ta ce komai ba ta juya ta koma sama. Cake ne da cincin da dubulan a cikin plate É—in, Neehal ta ce su Amrah su sakko su ci, ita kuwa ko kallon snacks É—in bata Æ™ara yi ba. Su ma kaÉ—an suka ci suka ce sun k'oshi. Neehal ta duba time a wayarta ta ga uku saura, lumshe idonta ta yi ta kwanta akan kujera tana jin cikinta na juya mata, zuciyarta kuwa cike take da mamakin dalilin ya sa Hafsah ba ta k'aunarta, dan ita ba ta taÉ“a tunanin irin wannan tarb'ar daga gare ta ba, yanda tasan amare idan ka je gidajensu kamar su mai da mutum ciki dan murna amma..... Ƙarar buÉ—e Æ™ofar falon ya katse mata tunanin da take. Da Sallama ya shigo falon duk da be yi tunanin da mutane a ciki ba, dan yasan Hafsah ba ta zaman Æ™asa. Waro ido ya yi ganin Twins fuskarsa na nuna mamakinsa na ganinsu. Su ma suna ganinshi suka nufe shi da gudu suna faÉ—in "Uncle!." Dan É—an zuwan da Ameen yake gida sun saba da shi. Ameen ya d'aga su É—aya bayan É—aya ya shilla yana murmushi, yaran suka shiga Æ™yalÆ™yala dariya sannan suka gaishe shi, ya amsa musu cikin kulawa. Afrah ta ce "Uncle nan gidanka ne?" Ameen ya mata murmushi tare da gyaÉ—a mata kai. Neehal wadda ta tashi zaune tun shigowar shi, cikin boye É“acin ran Hafsah da dauriyar ciwon cikin da take ji ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Ameen ya zauna a gefen ta yana kallonta cikin nazarta yanayinta ya ce "Yawwa." Neehal ta yi Æ™asa da kanta ganin yana binta da wani irin kallo, a sanyaye ta ce "Ina yini." Ya amsa da "Lafiya k'alau, ya aiki?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ina Haneefah fa, kika zo ke kaÉ—ai?" ta ce "Tana Abuja ta je gidan Yayan Abbansu sai Sunday zata dawo." Ameen ya gyaÉ—a kai tare da bin falon da kallo, sai kuma ya dawo da dubansa ga Neehal ya ce "Ina matar gidan?" Neehal ta ce "Yanzu ta hau sama." Ameen ya miÆ™e hannayensa riÆ™e dana Twins suka hau saman, Neehal ta bi su da kallo tare da jan numfashi. Duk murna da d'okin ganin Yayan nata da take takaicin Hafsat ya sa ta ma dena. Ko minti biyar Ameen be yi da hawa saman ba suka sakko tare da Hafsah, wadda ta faÉ—aÉ—a fara'a akan fuskarta. Tana duban Neehal ta ce "Sister na bar ki ke kaÉ—ai ko? Sorry toilet na shiga ne." Mamakin Hafsat ne ya kusa kashe Neehal, shanye mamakinta ta yi ta kirkiro murmushi ta ce "Ba komai Aunty." Hafsah ta dubi Ameen da ya zauna yana kallonsu ta ce "Honey Ka ga hira da Sister ta É—auke mun hankali ko girki ban daura ba, duk da ma na tambaye ta mai za su ci ta Æ™i faÉ—a mun, na ce kuma ta shiga ta girka da kanta ta Æ™i, sai ka ce wata bakuwa." Ameen yana duban Neehal ya ce "Why?" Neehal ta ce "Yaya mun ci fa snacks mun k'oshi." Ameen ya ce "Snacks ai ba abinci ba ne, ki shiga kitchen ki dafa muku abun da zaku ci." Neehal ba za ta iya musu da Yayan nata ba, hakan yasa ta miÆ™e ta nufi kitchen É—in." Hafsah na murmushi ta ce "Ko ke fa yar Æ™anwata, amma da kin Æ™i sakin jiki kamar wata baquwa." Neehal dai bata tanka mata ba ta shige kitchen zuciyarta cike da mamakin kissa irin ta Hafsah. Duk da bata jin dadi haka ta dafa musu jallop É—in taliya kafin ta gama an shiga sallar Asr, hakan yasa da ta gama ta juye a warmer sannan ta dawo falon, Twins ne kawai a falon suna kallon cartoon É—in da Ameen ya kunna musu, Ameen ya fita Masallaci ita kuma Hafsat tana sama. ÆŠakin dake falon Neehal ta shiga ta yi Sallah, bayan ta idar ta fito falo ta tarar har Ameen ya dawo, Hafsah ma ta sakko. "Sannu da aiki my sister, Allah ya saka da Alkhairi ya baki miji na gari, bari na je na ga me aka girka mana haka ne, duk muna nan k'amshi ya buÉ—aÉ—e mu yawun mu sai tsinkewa yake." Hafsah ta faÉ—i haka cikin iyayi tana murmushin da be kai zuci ba. Neehal ta yi É—an murmusa kawai, dan mgn ma bata son yi saboda yanda take jin cikinta. Hafsah ta miÆ™e ta shiga kitchen É—in, É—auko warmer ta yi gaba-d'aya tare da plates da pork ta ajiye akan dinning, sannan ta É—auko drinks shima ta aje. Ta dube su duka ta ce "Ku taso mu ci abincin." Neehal dai kamar ta ce ta k'oshi, amma ta san ko ta faÉ—a Ameen ba kyale ta ze yi ba sai ta ci, hakan yasa ta miÆ™e tana taune lips d'inta ta nufi dinning É—in. Ameen dai kallonta kawai yake amma ya gane akwai abun da ke damunta. Duban Hafsah ya yi ya ce "Ku ci kawai I am full." A karamin plate Hafsah ta zuba wa Twins na su abincin ta ajiye musu Æ™asan carpet É—in dake tsakiyar falon. Da kanta ta zuba wa Neehal abincin sannan ta zuba nata itama, ba kunya ta shiga durawa cikinta taliyar dan ta mata daÉ—i ba kaÉ—an ba. Neehal ta kasa cin abincin sai juya pork É—in take a cikin taliyar, har taliyar ta fara sanyi. Da Æ™yar dai ta daure ta tsakura ta kai bakinta, a hankali ta shiga taunawa cikin nutsuwa, Hafsat kuwa tana zuba lauma tana harararta a fakaice. Cokali uku Neehal ta ci ta ajiye pork É—in da sauri saboda murd'awar da cikinta ya mata, dafe cikin ta yi tare da taune lips É—inta sosai, duk yanda taso daurewa amma ta kasa, Ameen dake latsa wayarsa amma hankalinsa gaba-d'aya yana kanta ya ce "What happened?" Hafsah cikin nuna damuwa itama ta ce "Sister me ya faru?" Neehal cikin sanyi ta ce "Cikina." Ameen ya miÆ™e da sauri ya Æ™araso dinning É—in yana mata sannu, miÆ™ewa ta yi ta nufi toilet É—in dake falon da gudu ta fara kela amai. A rude Ameen yake faÉ—in "Sannu, Sorry, dama ba ki da lafiya?" Neehal dai bata samu damar ba shi amsa ba, bayan ta gama ya taimaka mata ta fito tana numfarfashi ta kwanta a Æ™asa, Twins suka bita da kallo. Sai da ya tsaftace toilet É—in sannan ya fito, sai a sannan Hafsah ta yiwa Neehal sannu, tana pretending kamar ta damu, nan kwa a zuciyarta ji take kamar ta Æ™arasa ta dan tsanar da take mata. Neehal ta fara nuk'urk'usu a Æ™asa tana hawaye, sosai Ameen ya rude dan ya san wahalar da take sha a ciwon ciki, hakan ya Æ™ara konawa Hafsah rai, dan ko first night É—insu da bata da lafiya be rude haka ba sai a kan wannan figaggiyar yarinyar. Neehal ta riko hannun Ameen a wahalce ta ce "Yaya cikina kamar zan mutu, ka kai ni gurin Mama Please." Ameen ya tashi ya haura sama da sauri ya É—akko car key É—insa ya É—auki Neehal kamar jaririya ya yi waje da ita, Twins da ganin halin da Auntinsu take ciki yasa su kuka suka bi bayanshi da gudu. Takaici kamar ya kashe Hafsah ganin yanda Ameen ya wani gigice, tsaki ta ja ta É—auki handbag da takalman su Neehal ta bi bayansu. Har ya kwantar da Neehal a bayan Motar su twins kuma ya sa su a front seat. ajiye takalman ta yi a gaban Motar fuskarta É—auke da jimamin Æ™arya, Ameen bai bi ta kanta ba ya ja Motar ya danna horn, mai gadi ya taso da sauri ya buÉ—e masa gate ya fice daga gidan...........âœï¸
[7/21, 9:01 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.