Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 74 of 104
Har ɗakin Sadik Maamah ta kai shi ta zaunar da shi a bakin gadonsa. Cikin tausasawa ta ce "Kar abun da Rukayya ta faɗa ya d'aga maka hankali Sadik, ka dai san halinta ba sai na faɗa maka ba, zata iya yin ko wanne irin sharrin dan ganin auran ka da yarinyar nan bai yiyu ba. Ka dogara da Allah, ka kuma dage da addu'ar neman zab'insa ka ji." Sadik ya d'aga mata kai yana sakin ajiyar zuciya. Sai da kwantar masa da hankali sannan ta bar ɗakin. Kwanciya ya yi bayan fitar Maamah zuciyarsa na tariyo masa abun da Umma ta faɗa akan Neehal, tabbas ya san Saurayinta ya rasu kafin su haɗu, har Haneefah ma ta tabbatar masa da an kusa bikinsu lokacin da ya rasun. Amma bai san da wani ba bayan shi ba. Wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake da mamakin cewa wai ba su Mama ne suka haifi Neehal ba, shi ko kaɗan ma bai yarda da wannan batun ba. A yanda yake jin Neehal a cikin ransa koma me za'a faɗa a kanta ba zai iya rabuwa da ita ba, ko yaya take yana son abarsa kuma a haka zai aure ta. Balle ma ya san bata da wani aibu. Tashi zaune ya yi a ransa yana faɗin 'Dole ma ya yiwa Maamah magana ta faɗawa Abba ayi_ayi a saka ranar bikinsu kowa ma ya huta.' Ko da suka yi waya da Neehal yau sai da ta gane kamar yana cikin damuwa har ta kasa shiru ta tambaye shi. Amma ya ce mata babu komai, dan Maamah ta gargad'e shi akan kar ya sake ya yiwa Neehal zancen. Umma kuwa bayan ta koma ɗaki Yayan Abban su Sadik wanda suke kira da Kawu ta kira ta sanar masa ƙarya da gaskiya akan yarinyar da Sadik yake nema. Kawu ya dinga masifa a waya kamar zai ari baki yana faɗin "Shi Surajon (Abba) ba shi da hankali ne yana ji yana gani zai salwantar da rayuwar ɗansa har zai da ce wannan abun ba wata matsala ba ce? To ina nan zuwa a cikin satin nan in same shi, domin kuwa wannan yarinyar dole Sadik ya rabu da ita." Cikin jin daɗi Umma ta yi masa sallama, zuciyarta fari k'al kamar takarda.
Bayan kwana biyu Ranar Laraba Neehal ta dawo daga gurin aiki da Yamma, tana zaune a ɗakinta tana operating system Mama ta shigo ɗakin, bayan ta yi Sallama Neehal ɗin ta amsa mata ta ce "Neehal Ahmad ya zo, yana ƙasa." Ta d'ago kanta da sauri ta ce "Uncle Ahmad kuma?" Mama ta ce "Ki yi sauri ki je kar ki bar shi yay ta jiran ki, na san ki da shiririta." Neehal ta ce "Toh." Sannan ta miƙe ta ɗauki Hijabi ta zira ta fito. Haka kawai ta ji zuciyarta na d'okin ganin sa, ko dan ta kwana biyu rabon ta da shi ko a waya ne. Yana zaune hannunsa tallafe da fuskarsa idanunsa akan steps, wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke jin takun tafiyarta. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon. Ya miƙe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya ƙarasa gabanta ya tsaya daf da ita kamar zai rungume ta, cikin wata irin murya ya ce "Princess!" A hankali ta ce "Na'am Uncle." Ya kamo hannunta tay saurin k'wacewa tare da yin baya ta zauna akan kujera. Ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta ya ce "Princesss mai ya faru idan na kira wayarki bakya ɗauka, ko wani laifin na miki?" Ganin yanda yake magana cikin damuwa sai ta ji tausayinsa mai tsanani ya cika mata zuciya, har ta fara da na sanin abun da ta yi masa. Cikin raunin murya ta ce "I'm sorry Uncle, ka koma ka zauna akan kujera." Ya girgiza mata kai tare da faɗin "No Princess, please tell me me ya faru." Ta ce "Seriously babu komai Uncle ɗina." Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa jin yanayin da ta yi magana ya tabbatar masa babu komai ɗin. Ya koma ya zauna sosai tare da zuba mata idanunsa. Cikin marairaicewa ya ce "But Princess why? Na shiga damuwa sosai da ƙin d'aga kira na da kike, har na fara tunanin ko ba lafiya ba. Na karb'i Numbern Mama a gurin Ummi na kira ta, dan nasan in ma ba lafiya zata sanar mun, amma jin bata ce mun akwai matsalar komai ba sai hankalina ya ɗan kwanta, amma kewarki gaba-d'aya ta hana ni sukuni. Kwana ukun nan da ban ji muryarki ba gaba-ɗaya bana cikin nutsuwata, yau dai na kasa jurewa na ce sai na zo na gan ki." Ta lumshe idonta cikin sanyin murya ta ce "Nima na yi kewar ka Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce "To me yasa kika daina ɗaukar kira na." Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa ta ce "Babu komai fa Uncle ka yarda da ni." Ya ce "Uhm, salon ki tayar mun da hankali ne kawai ko?" Ta ce "A'a, i'm sorry ba zan kuma ba." Ya ce "Shikenan Princess." Ta ce "Ina yarana, me yasa baka zo mun da su ba?" Ya ce "Bari na yi sai next week idan sun yi hutun school sai na kawo miki su." Ta ce "Allah ya kai mu, Ya su Ummi?" Ya ce "Duk suna nan lafiya lau." Hira suka sha sosai yau, dan ita kanta sai yanzu ta tabbatar ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Anan ya yi Sallar Magriba, yau kam ya ci abinci kaɗan a gidan saboda gudun ɓacin ran Princess ɗin tasa. Sai kusan isha'i ya tafi zuciyarsa cike da nishad'i, saɓanin kwana biyun da suka wuce wanda ya yi su cikin damuwa. Itama Neehal anata ɓangaren cike take da farincikin kasancewa da Uncle ɗin nata a yau. Bayan ya koma gidan Mamy tai ta tsokanarsa tana faɗin "Ai fa yanzu dole yay ta musu zarya a Kano tunda zuciyarsa tana nan." Murmushi kawai yake mata baya cewa komai.
Bayan Sallar isha'i Mama tana falon sama tana kallo wayarta dake hannun kujerar da take kai a zaune ta fara ringing. Ta É—auko ta duba tare da d'agawa ganin Aunty A'isha ce ke kiran. Ba tare da gaisuwa ba Aunty A'isha ta ce "Adda Fateemah! Yanzu Mai_gidan su Abban Neehal ya kira ni ya sanar mun cewar an samu nasarar kama mutanen da suka kashe Abban Neehal É—in da Ummanta........âœï¸
[7/21, 9:32 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*4ï¸âƒ£8ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
Cikin hanzari mai nuni da tsantsar mamaki Mama ta tari numfashin Aunty A'isha da faɗin. "Da gaske A'isha?" Aunty A'isha ta ce "Dagaske mana Adda, shi Alhaji Alin ne tun bayan rasuwar su Abban Neehal ba jimawa ya kamu da rashin lafiya, aka fitar da shi Saudiyya ake yi masa magani. Ashe duk wannan shekarun da suka wuce abun yana ransa, sai a ƴan watannin da suka wuce ya samu lafiya ya dawo Nigeria. Shine yana dawowa yasa aka duk'ufa da binkicen waɗanda suka yi kisan a lokacin da ya samu labarin har yanzu ba'a gano su ba. Yanzun nan shi ya kira ni da kansa muna gama waya da shi na kira ki, ya sanar mun cewa tunda ya dawo ƙasar nan yake neman mu, amma bai samu labarin inda muke ba, sai daga baya tunanin ya je gadon ƙaya inda muka zauna ya zo masa, to a wurin wata mak'ociyarmu aka samo masa Number ta." Mama ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Alhamdulillah, Allah mun gode maka, yanzu ya ake ciki game da waɗanda suka yi kisan? Ya sanar miki ko su waye suka yi?" Aunty A'isha ta ce "A'a bai sanar mun ba, ya dai ce mun suna hannun Police a halin yanzu, ranar Monday za'a shiga kotu a yanke musu hukunci tunda sun amsa laifunsu, sauran bayani kuma ya ce sai mun haɗu." Mama ta ce "Ki ji wani ikon Allah A'isha, shekara fiye da goma sai yanzu Allah ya toni asirinsu, Allah ya ƙara tona asirin duk wasu masu laifi a cikin duniyar nan." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, wallahi adda ba ki ji yanda na ji daɗi ba, Alhaji Ali ya cika ubangida na gari da ya tsaya tsayin daka ganin jininsu Abban Neehal bai tafi a banza ba." Mama ta ce "Allah ya saka masa da Alkhairi ya biya shi da gidan Aljannah." Aunty A'isha ta ce"Amin ya Allah, ya ce akai masa Neehal yana son ya gan ta." Mama ta ce "Aiko bai faɗa ba dole mu je har gida mu yi masa godiyar wannan jajircewar da ya yi, gobe gobe ma Insha Allahu za mu je, a wacce unguwa yake da zama?" Aunty A'isha ta ce "A rijiyar zaki, ya turo mun da address ɗin gidansa ta message." Mama ta ce "To Insha Allahu da safe za mu je, bari in je in sanar da Daddy wannan abun al'ajabi da farincikin." Aunty A'isha ta ce "Tom shikenan da safen zan biyo ta nan sai mu wuce, nima bari in je in sanar da Abban Maryam, in kira Sadiya itama in sanar mata." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben, sai mun yi waya." Daga haka suka yi sallama.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.