Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 26 of 104

6:30 pm, Ameen ya mik'e ya dubi Neehal dake ta hawaye ya ce "Tashi mu je." Fuskarsa babu walwala ko kad'an ya yi maganar, Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan k'aya ta yi gaba, sai da ya kulle qofar part d'in sannan ya bi bayanta, har ta nufi part Mama ya tsayar da ita Neehal ta tsaya cike da mamakinsa gami da tsoro, domin ta kasa gane me yake nufi da ita, bayan zaman banzan daya sa tayi na fiye da awa ɗaya bai ishe shi ba sai ya k'ara tsayar da ita, to me yake nufi da ita ne? Gurin bikin ne baya son taje ko kuma me?" Dan ita zuwa yanzu ta hak'ura da kwalliyar kayanta kawai take so taje ta saka ta tafi tunda lokaci ya k'ure, gashi Sadik sai kiranta yake a waya ta k'i d'agawa, tafi son sai taje gurin kwalliyar sai ta kira shi ya je ya d'auke ta su wuce. Ameen ya nufi parking space bayan ya mata alamar ta biyo shi, harabar gidan Neehal ta kalla taga duk babu mutane an tafi gurin kwalliya wasuma sun fara tafiya gurin bikin. Bata da zab'i wanda ya wuce bin nasa, Motarsa ya shiga mazaunin driver, hakan yasa ita kuma ta shiga gurin mai zaman banza ta zauna zuciyarta na mata k'una, tana rufe murfin Motar ta fashe da kuka, Ameen ya dube ta da sauri ya ce "Me ne haka?" Neehal cikin kuka ta ce "Yaya wai me kake so na maka ne kake ta tsaida ni? alhalin kafi kowa sanin inda za ni, ga mutane suna ta jira na, kasan Mama ma Idan tasan ina gida har yanzu sai ta yi fad'a." Ameen ya tab'e bakinsa bai ce komai ba, yay wa Motar key suka fice daga gidan. Neehal ta cigaba da kukanta, a d'an fusace ya dube ta ya ce "Kar na k'ara jin kukan nan, yana cika mun kunne." Yanayin yanda yay maganar yasa Neehal ba shiri ta had'iye kukanta, Handkerchief d'insa ya zaro daga aljihu ya mik'a mata tare da fad'in "Share hawayenki, kuma kar na k'ara ganin ko d'igonsu." Ba musu ta karb'a ta share hawayen ta ci gaba da kukan zuci. Tafiyar mintuna k'alilin suka yi ya faka a gaban wani shago, wayarsa ya d'auka ya yi kira, mintuna uku wata matashiyar mata ta fito fuskarta d'auke da fara'a, Ameen ya zuge glass d'in Motar bayan ta qaraso suka gaisa tana tsokanarsa da ango ka sha k'amshi, nuna mata Neehal wadda idanunta ke lumshe ya yi ya ce "Gata nan, sai ki yi sauri please dan time ya qure." Matar ta yi murmushi ta ce "Kai dama wa ya fad'a maka sai i'yanzu ake zuwa makeup? ai tun rana ake zuwa."  Neehal wadda ta yi dif kamar bata Motar ta bud'e idanta da sauri jin an ambaci makeup Tana kallon Matar, a hankali ta sauke numfashi ta ce "Ina yini." Matar ta amsa fuskarta d'auke da fara'a, ta k'ara da fad'in "Kai Masha Allah qanwar taka kuma kyakkyawa da ita, harma ta so ta fi ka kyau." Ameen ya yi murmushi kawai ya juyo da dubansa ga Neehal ya ce "Ki je ta miki, inanan ina jiran ki." Neehal ta ce "Amma Yaya kayana fa suna gurin Haneefah." Yana latsa wayarsa da ake ta kira ya ce "Zan kawo miki wasu." Neehal ta waro Ido ta ce "Yaya wasu kayan kuma? Anko ne fa wanda zan saka, kenan ni daban zan tashi?"  A ɗan hasale ya ce"Kin san bana son musu ko?" Neehal ta turo Baki gaba cikin qoqarin maida hawayen da ya tarar mata a Ido ta bud'e Motar ta bi bayan Matar wadda ta koma cikin shagon nata tun sanda Ameen suka fara magana da Neehal. Ameen ya bita da kallo harta shige shagon sannan ya ja Motarsa ya tafi dan zuwa masallaci jin an fara kiran Sallah. Neehal ma sai da ta yi Sallah tukunna aka fara mata makeup d'in, zuwa lokacin wayarta ta gaji da shan kiran Haneefah da Sadik harda ma da Mama. Matar da kanta ta yi wa Neehal kwalliya, sab'anin wasu a shagon da yaranta ne suke musu, gata da sauri cikin abun da bai wuce 30 minutes ba ta tsantsarawa Neehal kwalliya irin light d'innan amma ta yi masifar kyau, kowa dake shagon sai da ya furta "Wow, Masha Allah." Har wasu na tambayar ko Neehal amarya ce? Matar na ba su amsa da fad'in "K'anwar wani classmate d'ina ce da muka yi Secondary school, auransa ake shine ya kawo ta, a yi mata kwalliya." Bayan ta kammalawa Neehal kwalliyar ta kira Ameen a kan ya kawo wa neehal kayan da za ta saka, ya shaida mata ta fito bakin shagon ta karb'a. Neehal ta cika da mamaki ba kad'an ba ganin kayan da Ameen ya kawo mata, wata had'ad'd'iyar wedding gown ce sky blue, sai head Royal blue da takalmi da su sark'a harda pos wanda duk bata san da su ba, babu b'ata lokaci ta zira kayan me make up ta kafa mata had'ad'd'en d'aurin da ake yayi, nan fa Neehal ta qara fitowa bayan ta gama shiryawa tsaf, babu ta yanda za a yi ka ce ba amarya ba ce, matar ta ba ta turaruka masu sanyi da dad'in k'amshi ta feshe jikinta da shi. Neehal ta kasa d'auke idanunta saga kan mudubi saboda ganin kyawun da ta yi, sai tambayar kanta take a ranta tana fad'in "Ashe make up zai mata kyau sosai irin haka?" Matar ta mata pictures a wayarta sannan suka fito, dan itama matar zata je bikin, Ameen ya yi invited d'inta. Tunda suka fito Ameen ya kafe Neehal da Ido, ganin wani irin sihirtaccen kyau da ta yi, tana tafe tana faman rik'e Riga saboda jan k'asar da take ta baya, duk da kuwa takalmin k'afarta yana da tsini. A hankali ta bud'e front seat ta shiga, Matar kuma ta shiga baya, zuciyar Neehal cike take fal da tarin tambayoyi ga Ameen, akan hanata zuwa gurin kwalliyar da ta yi niyya da ya yi, ya kawota wani wajen daban, sannan kuma ya bata wasu kayan daban wanda suka yi colour d'aya da nashi, Amma dole tabar tarin tambayoyinta a ranta saboda ba su kad'ai ba ne a Motar kuma ba taga fuskar hakan a gurin shi ba dan tana shigowa ya wani tsare gida.

     Wurin biki ya cika ya tumbutsa da 'yan'uwa da abokan arziqi, anata cashewa amma har takwas na dare ta yi amarya da ango ba su qaraso ba. Haneefah kuwa tana gurin ne kawai  amma hankalinta gabad'aya yana gurin Neehal, gashi sai kiranta take a waya ba ta d'auka, Sadik ma ya zo ya fi mintu talatin a harabar gurin, ganin Neehal ba ta zo ba kuma yana ta kiranta ta qi d'auka sai kawai ya tafi, kuma bai yi tunanin kiran Haneefah ya ji ko suna tare ba. Amarya Hafsat kuwa da tawagarta sun dad'e da qarasowa gurin, ango kawai take jira su shiga cikin gurin, ranta idan ya yi dubu ya b'aci saboda kiran Ameen da take ta yi amma ya k'i d'auka, gashi bata san me ya tsayar da shi ba ya qi qarasowa gurin har wannan lokacin, har ta gaji da d'adin bakin da abokanan Ameen suke mata na fad'in ya kusa qarasowa. Fadeelah dake zaune gefenta a bayan Motar da suka zo ta dube ta ta ce "Ki qara kiran Al'ameen ki ji wai yana ina ne har yanzu be ƙaraso ba?" Hafsat da ranta ya kai qololuwar b'aci ta ce "Sau dubu nawa zan kira shi yana qin d'aga mun waya Fadeelah? ni na gaji da kiran shi, Idan aka qara wasu mintinan bai zo ba zan koma gida ne kawai, haba wannan ai wulaqanci ne." Kafin Fadeelah ta kuma cewa wani abu wani abokin ango mai suna Salman ya leqo ta glass ɗin Motar yana faɗin "Ranki ya daɗe angon naki ya ƙaraso ki fito." Hafsat ta saki ajiyar zuciya tare da gyad'a masa kai. Neehal kuwa yana parking Motar ta yunƙura za ta buɗe murfin Motar ta fito amma sai ta ji ya riƙe hannunta, ta juyo tana kallon shi cikin tsananin mamaki sai ta ga ya ɗauke kansa, sai da matar da ta yiwa Neehal make up ta fita daga cikin Motar sannan shima ya fito bayan ya sakar wa Neehal hannun, bai bi takan abokansa da suke ƙoƙarin cinye shi d'anye ba na rashin zuwansa da wuri ba ya zagaya ya buɗe wa Neehal Motar, a hankali ta ziro k'afarta ta fito cikin tsananin mamakin Ameen da ya kusan kashe ta da shi na abubuwan da yake mata a yau kamar ba shi ba, dai_dai lokacin itama Hafsat an buɗe mata Mota ta fito, akan idonta Ameen ya buɗe wa Neehal Mota.............✍️
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.