Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 104

K'arfe uku dan wasu mintuna Neehal ta gama shirinta cikin wata rantsatstsiyar doguwar rigar abaya maroon colour, wadda ta ji kwalliyar stones milk colour, rolling mayafin abayar ta yi, ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, daddad'an turarenta mai daɗin ƙamshi ta feshe jikinta da shi, zoben gold ta zira a ɗanyatsanta na tsakiyar hannun damanta, na kusa da shi kuma ta zira zoben azurfa mai kyan gaske, yatsun hannun hagunta suma fashion ɗin zobuna masu kyau ta sa musu guda biyu, tsadadden agogon hannu na mata ta zira tare da abun hannu mai kyau, flate shoe mai kyau milk colour ta zira, wayoyinta dake kan mudubi ta kwasa ta zuba a cikin handbag ɗinta mai kyau itama milk colour. Light din ɗakin ta kashe ta janyo ƙofar ta fito ta sauko ƙasa. Bayan Haneefah ta kammala girkin da Neehal ta ɗora, ta na zaune a falo Neehal ta sakko, Haneefah ta bita da ido tana murmushi ta ce "Kaga amaryar ya Anwar, kin yi kyau sosai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Har na kai ki yin kyan?" Haneefah ta ce "Wane Ni, ke fa harkin fara irin shining ɗinnan na amare" Neehal ba ta kulata ba, ta nufi kitchen, Haneefah ta tashi ta koma kusa da Hajiya ta fara tashinta.

Hajiya ta buɗe ido a hankali tana salati, tashi zaune ta yi tana mutsitstsike ido, duban Haneefah da take dariya ƙasa_ƙasa ta yi ta ce "Ai dama nasan sai ke, dan Neehal dai ba za ta yi mun wannan muguntar ba, To ke da Allah, ina cikin baccina mai daɗi kin katsemun ko uban me zan miki idanna tashin Oho?" Haneefah ta tsuke fuska ta ce "Hajiya dan na tashe ki ki ci abinci ki yi Sallah, shine za ki ce mugunta, gani na yi ke bakya wasa da Sallah kuma lokacinta ya kusa" Hajiya ta ce "To yi haƙuri ai ban sa ni ba, yaushe ki ka zo gidan? ya kuma Maryam ɗin?" Haneefah ta ce ɗazu na zo ai, na tarar ki na ta sharar baccinki, Mommy kuma tananan Lafiya k'lu" sakkowar Mama ƙasa ya katse musu maganar da suke, Haneefah ta mik'e ta je ta yi hugging Mama. Mama na murmushi ta ce "Welcome, yaushe ki ka zo?" Haneefah ta ce "Na ɗan jima" Mama ta ce " sannunki, Ya Barrister ɗin?" Haneefah ta ce "Tananan klu" Mama ta kalli kofar kitchen ta ce "Neehal ba ta gama girkin ba ne, ta yi ta fito ku shirya ku tafi kar ku yi late" kafin haneefah ta ce wani abu Neehal ta fito daga kitchen d'in, Mama ta bita da kallo fuskarta ɗauke da mamakin ganin ta a shirye, Neehal ta ƙaraso kusa da su ta ce "Mama na gama abincin" Mama ta mata wani kallo ta ce "To sannu" Sannan ta juya ta kalli Haneefah ta ce "Kin taya ta girki ko?" Haneefah ta sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba magana nake miki ba Haneefah?" Haneefah ta ce "Mama ƙarasa mata miya kawai na yi, na ce ta je ta shirya dan mu yi sauri mu tafi" Mama ta ce "Ba na ce ko sauke abu ki dena taya ta da shi ba, ki barta ta dinga yin komai da kanta" Haneefah ta gyad'awa Mama kai. Neehal ta ɗan turo baki gaba ta wuce za ta ɗauki jakarta, Mama ta ce "Kun ci abincinne?" Haneefah ta ce "Na k'oshi Mama, ina gama cin abinci na fito, sai dai idan mun dawo" Mama ta dubi Neehal ta ce "Ke fa?" Neehal ta ce "Ni ma haka" Mama ta ce tunda kin cika cikinki da kayan zak'i ba, ki wuce kitchen ki d'ebo abinci ki ci kar na ɓata miki rai" Neehal ta ɓata fuska, amma ba ta da zaɓi sai bin umarnin Maman, kitchen d'in ta koma ta d'ebo abinci kaɗan a plate ta dawo falon ta zauna a ƙasa ta fara ci kamar ba ta so, ta na ci ta na yamutsa fuska, kaɗan ta ci Mama ta ce ta tashi su tafi, tun da ɓata musu lokaci kawai take ba cin abincin za tay ba. Neehal na duban Mama da Hajiya ta ce "Sai mun dawo" "Mama ta ce ƙarfe nawa za ku dawo?" Neehal ta ce "8" Mama ta ce "8 ina Hospital" Neehal ta ce "Mama yau fa Saturday me za ki yi a Hospital kuma?" Mama ta ce "Akwai patients d'in da zan duba ne" Neehal ta ce "Toh, idan mun tashi zan biya Zoo road na siyo popcorn a a'one" Mama ta ce "In ma a 10 ne ba damuwata ba ce, kin san Yayanki na gida ai, 8: 15 in ba ki dawo ba, ke da shi ne" Neehal ta ɓata fuska ta yi gaba, Haneefah ta yi wa su Mama sallama, Mama ta musu addu'a suka tafi, Hajiya na faɗin "Wai yaushe zaku kai ni gidan talabijin d'innan naku ne nima a hasko Ni a ciki?" Suna jin ta suka mata shiru. Parking space suka nufa suka shiga Mota Driver'n Neehal ya ja su zuwa *ASTV* fitaccen gidan TV'n da ya shahara a nan ƙasarmu Nigeria dama nahiyar Africa baki ɗaya.

Ƙarfe 8 kamar yadda Neehal ta ce suka tashi daga gurin aiki, bayan sun gama gudanar da shirin *'Yancin mata* wanda suke yinsa duk Ranar Asabar da misalin ƙarfe 7 na dare zuwa 8. Su na gamawa suka yi sallama da ma'aikatan gidan TV suka nufo gida, Neehal ta yi_ta yi Haneefah ta bita ta gidansu kamar yadda take yi wani lokacin amma ta ce ita gida za ta wuce, sai da suka biya suka fara sauke ta sannan suka wuce, da yake duk ba su da nisa, gabad'aya a cikin Nasarawa G.R.A suke har ASTV'n. Driver na parking Neehal ta fito, ganin Motar Dad a gurin alamun ya dawo ta ji daɗi a ranta, dama yau gabad'aya ta yi missing ɗinsa. Part d'in Mama ta nufa, ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, gabantane ya faɗi ganin Ameen zaune shi kaɗai a falon ya na latsa waya..........✍️
[7/21, 8:59 AM] Zee data: *⚡NEEHAL⚡*

_By_

_Zeey Kumurya_

*0️⃣3️⃣*

.Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗan kamshinsa da ya mamaye falon, numfashi ta sauke ta buɗe idanunta a hankali cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta cigaba da tafiya kanta a ƙasa, sallama ta yi masa cikin siririyar muryarta tana kyab'e fuska ita a dole fushi take da shi, ba tare da ya d'ago ba ya amsa mata sallamar a can ƙasan mak'oshi, har ta ɗan wuce shi za ta haura saman steps ya kirata ta hanyar faɗin "Miemah!" Tsayawa ta yi tare da juyowa amma ba ta ƙaraso inda yake ba, kamar ba shi ya kira ta ba ya wani waske abunsa yana ta aikin latsa wayarsa, sanin halinsa ya sa ta ƙaraso inda yake ta zauna a ƙasan kujerar da yake ta ce "Ga ni Yayah" Be kulata ba, kusan 2 minutes kamar ya manta da ita a gurin, sai kuma ya d'ago ya mata wani kallo, cikin daddaɗar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce "Sau nawa zan hanaki bulbula turare a jikinki idan zaki fita?" Turo baki ta yi gaba ta ce "Kaɗan fa na saka" ya ce "Ƙarya na yi miki kenan?" Girgiza kanta ta yi alamar a'a, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa, Neehal na son wucewa sama amma ta na tsoro tun da bai bata umarni ba, shikuma ya cigaba da al'amuransa kamar ya manta da ita a gurin, kuma ya na sane umarninsa take jira, ɗayar wayarsa da ke ajiye a kusa da shi ce ta yi ƙara alamun shigowar kira, dubawa ya yi, ganin sunan Dad na yawo akan wayar ya sa shi d'agawa da sauri. Dad ya ce "Muhammad ka dawo daga masallacin ne?" Ameen ya ce "Eh" Dad ya ce "Daughter din ta dawo ne" ya ce "Eh" Dad ya ce "Ok, ina son ganinka yanzu a part ɗina" Ameen ya ce "Ganinan zuwa yanzu" ya katse wayar tare da miƙewa ya nufi part d'in Daddy wanda akwai ƙofar da za ta sadaka da part d'in Daddy'n ta cikin falon Mama. Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan ƙaya ta haye sama. Ɗakin da Hajiya take ta lek'a, Hajiya dake zaune kan darduma ta na lazimi ta dubi Neehal ta ce "A'a kin dawo ne?" Neehal ta ce "Ba gashi kin ganni ba" Hajiya ta ce "To sannunki da dawowa, ina ja'irar ƙawar taki?" Neehal ta ce "Ta wuce gida, Mama ba ta dawo ba?" Hajiya ta ce "Sai bayan magriba fa ta tafi, na yi_na yi ta haƙura da zuwa asibitinnan ta huta itama amma ta ƙi, kamar wadda aka yi wa wahayi haka ta tafi a darennan, dan ma aikin Allah za ta yi, tun da duba marasa lafiya ne" Neehal ba ta ce Komai ba ta juya ta fice ta nufi ɗakinta. Tana ajiye jakarta ta fito ta nufi kitchen, cake ta ɗauko da meatpie saboda wata irin yunwa ta take ji, ɗakinta ta koma bayan ta ɗau drink a falo, sai da ta ci ta yi k'at, sannan ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala dan yin sallar isha'i.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.