Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 73 of 104

Hafsah ta cika ta yi fam kamar zata yi bindiga saboda baƙin cikin bin bayan Neehal da Ameen ya yi, a haka ya sakko ya same ta. Ta yi saurin ɓoye ɓacin ranta ta k'ak'alo murmushi ta ce "Baby har ka sakko." Ya zauna a kusa da ita cikin kulawa ya ce "Eh, bari na je na yi sallah, idan na dawo sai mu wuce gida ko? Ta ce "Ai na ɗauka a nan zamu kwana." Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Ta yi murmushi cikin ranta tana jin wata irin k'aunarsa na ƙara cika mata zuciya. Ita kanta ta san ta yi dace da mijin kere sa'a, dabi'un Ameen suna bala'in burge ta, more especially muskilancinsa yana bala'in tafiya da imaninta. Yana ɗaya daga cikin abun da ya ja hankalinta a kansa, gashi ya iya kula da mace, ta tabbatar za a bashi lamba ɗaya a wannan fannin, ta san sai a tara maza ɗari kafin a samu wanda iya tarairayar mace da nuna mata tsantsar k'auna kamar Ameen ɗinta. Ya miƙe ya fice daga falon, ta bi shi da kallo. Komai nasa kyau yake mata, tafiyarsa ma kaɗai abun burgewa ce. Tana son Ameen over shi yasa bata son ɓacin ransa ko kaɗan, duk abun da ta san zai ɓata masa rai ko yaya ne gudun shi take. Shi yasa take danne duk abun da take ji a ranta a duk lokacin data gan su tare da Neehal, dan ta san bata isa ta nuna masa ɓacin ranta ba akan haka. Ta tsani Neehal over, tsanar da ita kanta bata san adadinta ba, tun lokacin data samu labarin ba su Mama ne suka haife ta ba ta ji yarinyar gaba-d'aya ta fice mata a rai.. Maganar Mama data dawo falon ne ya katse mata tunanin da take. Mama ta ce "Au Ameen ɗin fita ya yi?" Hafsah ta ce "Eh ya je masallaci." Mama ta ce "To mu je sama ke ma ki yi Sallar, na ji an fara kira." Hafsah ta miƙe ta bi bayan Mama. Bayan ta idar da Sallah Mama ta kawo mata abinci, tana cikin ci Ameen ya dawo gidan. Neehal kuwa tana ɗakinta ta ƙi fitowa, har sai da ta tabbatar sun bar gidan sannan ta fito falo. Anan ta tarar da Mama, ta zauna a kusa da ita ta shiga bata labarin zuwan ta gidan Uncle Umar. Cikin farin ciki Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin wannan labarin, dama kullum fata na da addu'a ta Allah ya waiwayo da hankalin danginki gare ki, ku dinga zumunci kamar kowan ne ahali." Neehal ta ce "Nima Mama na ji daɗi sosai, ba ki ga yanda Uncle Umar yake mun magana ba, cikin kulawa kamar ma kunya ta yake ji akan abubuwan da yay mun a baya." Mama ta ce "Haka muke so dama, Allah ya ƙara shirya mu ya nuna mana gaskiya da sani akan abubuwan da muke aikatawa ba dai_dai ba." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci, bari na je part ɗin Daddy." Neehal ta ce "Toh." Tare da miƙewa, ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta ta kira Uncle Usman ta sanar masa sauyawar da Uncle Umar yay mata. Daren yau ba su yi waya da Ahmad ba, tana ganin yana kiran ta ƙi picking. Washegari da safe ma tana ganin kiran sa lokacin tana gurin aiki shima ta ƙi ɗauka. Bayan Magriba Sadik ya zo gidan kamar yadda ya saba zuwa, sun jima suna hira a gurin da suka saba zama. Har yake yi mata zancen shi kam zai turo iyayensa a yi maganar aurensu  ya matsu ya ganta a cikin gidansa a matsayin matarsa ta sunna. Cikin jin kunya ta ce masa babu matsala zata yiwa Mama maganar idan ta koma ciki.

Zuciyar Sadik Cike da farinciki ya koma gida, a main Parlour ya tarar da iyayensa da k'annensa kamar kodayaushe. Ya yiwa iyayen nasa sannu da gida ƙannansa kuma suka yi masa sannu da zuwa ya shige ɗakinsa. Bayan shigar sa ɗakin ba jimawa Batul ta zo ta ce ya je Abbansu yana kiran sa a part ɗinsa. Ya amsa tare da tashi ya biyo bayanta suka fito. Abba yana zaune shi da Umma da Maamah, kamar yadda tsarinsa yake idan zai yi magana da ƴaƴansa a gaban su Maamah yake yi. Sadik ya samu guri ya zauna a ƙasa bayan ya ƙarasa falon Abban. Abba ya dube shi cikin kulawa ya ce "Abubakar na kira ka ne akan maganar yarinyar da kake zuwa gurinta, kamar yadda na ce zan yi bincike akanta da iyayenta na yi, kuma Alhamdulillahi na samu kyakkyawan sakamako kamar yadda ake fata dama. An tabbatar mun yarinyar tana da tarbiyya, mahaifinta kuma mutumin kirki ne. Dan haka na yarje maka ka cigaba da zuwa gurin ta." Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Maamah na farinciki. Sadik kuwa ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bayanan Abba, daman ya san babu wata matsala da za'a samu a gurin Neehal. Maamah ta ce "Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Abba ya ce "Ameen." Tare da mayar da duban sa ga Sadik wanda kansa ke ƙasa ya ce "Ashe ma yarinyar nan ce mai aiki a gidan TV na ASTV?" Sadik ya shafa kansa ya ce "Eh ita ce Abba." Abba ya ce "Masha Allah, Allah ya yi mana jagoranci." Umma da baƙin cikinta ya kasa b'oyuwa akan fuskarta ta tari numfashin Abba ta ce "Alhaji wacce yarinya na ji kana magana a kanta? Ba dai Neehal ɗin nan ba ta gidan Alh. Tafida?" Abba ya ce "Ita mana, ai yarinyar da mahaifinta sanannun mutane ne a ƙasar nan." Umma ta jinjina kai irin ta ga mugun abun nan ta ce "To  gaskiya Alhaji baka yi bincike yanda ya kamata ba, indai akan yarinyar nan ne?" Abba ya ɗan canza fuska ya ce "Kamar yaya kenan?" Umma ta tab'e baki ta ce "Ita yarinyar fa su Alhaji Tafidan ba su ne asalin iyayenta ba." Sadik ya d'ago da sauri ya kalle ta, Maamah zata yi magana Abba ya riga ta da faɗin "Kamar ya ba su ne iyayenta ba Ruqayyah? Ban gane me kike son faɗa ba." Umma ta ce "Ina nufin riqon ta suke Alhaji ba ƴarsu ce ta cikinsu ba, riqonta kawai suke amma ko dangi ba su haɗa ba." Abba ya ce "Wannan ai ba wata matsala ba ce, indai tana da asalinta ai shikenan." Umma ta ce "Hmm, hakane. Amma kuma akwai wata matsalar bayan wannan." A harzuk'e Maamah ta ce "Wai ni Rukayya dan Allah me Yaron nan ya tsare miki a gidan nan ne, duk abun da zai yi sai kin san yanda kikai kika kawo masa cikas, akan wane dalili zaki takurawa ɗana? Me ya tsare miki?" Abba ya d'aga mata ya ce "Ya isa haka Kaltum, barta ta ƙarasa maganarta." Umma ta harari Maamah sannan ta cigaba da magana. "Abu na biyu Alhaji, wanda na same sa daga majiya mai ƙarfi akan yarinyar, na so in ɓoye maka kar in faɗa a mun wata fassarar daban, amma na kasa saboda yanda ba zan bari a cutar da ɗan cikina ba, haka ba zan bari a cutar da naka ba. Ita  yarinyar ce duk wanda zata aura sai an kashe shi..." A zabure Sadik ya miƙe tsaye yana duban Umman, zuciyarsa na wani irin bugu ba tare da ya ji ƙarshen zancen nata ba." Abba ya haɗe rai sosai ya ce "Kin ga Rukayya, bana son shirme wannan wacce irin magana ce mara ma'ana?" Umma ta ce "Wlh Alhaji ba ƙarya ba ne, nima na girgiza da na ji zancen dan da farko ma ban yadda ba sai da aka tabbatar mun, samari har biyu sai an saka ranar Aurensu sai a wayi gari a tarar an kashe su idan....." A fusace Abba ya katse ta da faɗin, "Wannan duk ba hujja ba ce Rukayya, Babu mai kashewa da rayawa face Ubangiji, suma waɗanda suka rasun kwanansu ne ya ƙare. Dan samarin yarinya guda biyu sun rasu baza a ce daga ita ba ne, Ubangiji ne ya karb'i abinsa. Dan haka kar na ƙara jin wannan maganar mara kai da tushe, kuma wannan dalilin ba zai sa na hana Sadik cigaba da neman Auren yarinyar ba." Yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakin baccinsa. Maamah ta sauke ajiyar zuciya cikin jin daɗin yanda mai gidan nasu bai goyi bayan abokiyar zaman tata ba a wannan karon. Miƙewa ta yi ta kama hannun Sadik dake tsaye kamar an dasa shi suka bar falon, ba tare da ta kuma kallon inda Umman take ba. Umma ta yi ƙwafa tare da raka su da harara, a fili ta furta "In kun san wata baku san wata ba ai, wallahi indai ina raye Sadik ba zai auri wannan yarinyar da Ubanta yake da arzik'i ba, mu zuba mu gani, shege ka fasa."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.