Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 89 of 104

Ranar Sunday kamar yadda Ahmad ya faɗa da hantsi ya sauka a Kano a gidan Mama. Neehal tana bacci su Afrah suka tashe ta cikin murna. Ta tashi da ƙyar dan bata jima da kwanciya ba, suka sanar mata Daddy ya zo. Sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har yau ba su kuma magana da shi ba, tun ɗan chat ɗin nan da sukay ta message. Ta tashi ta shiga toilet ta wanke baki da fuska, sannan ta fito ta ɗauki Hijabi ta fice. A falon sama ta gan shi yaransa a jikinsa suna masa surutu. Ta zauna akan carpet kanta a ƙasa ta ce "Sannu da zuwa Uncle." Ya d'ago ya dube ta cike da d'okin ganin ta, ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Sauke su Afrah ya yi daga jikinsa ya ce su tafi gurin Mama, sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kusa da ita. "Princesss!" Ya kira sunanta a hankali. Ba tare da d'ago kanta ba ta ce "Na'am." Ya lumshe ido ya buɗe ya sauke su akan fuskarta ya ce "I missed you so much." Ta d'ago ta kalli fuskarsa itama saboda azalzalar da zuciyarta take mata akan hakan, ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Ya tallafi fuskarsa da hannunsa ɗaya ya ce, "Wow, Princess kin ƙara kyau, Please karki daina mun wannan murmushin." Kamar zuga ta ya yi sai ta ɓata rai tare da ɗauke kanta daga gare sa. Cikin damuwa ya ce "Why Princess?" Ta turo baki ta ce "Babu komai." Ya ce "No, akwai Princess, tell me what happened? Bana son na gan ki cikin damuwar nan." Ta yi shiru, ya kamo hannunta ya ce "Please." Ta k'wace hannunta ta ce "Ba kai ne ka daina kula ni ba, yanzu ma na san dan su Afrah ka zo ba dan ni ba." Ya yi shiru yana kallonta, yana tunanin abun da yasa yay mata hakan ko kuma ya ce sukai wa juna." A hankali ya ce "Ke kika fara daina kula ni Princess, idan baki manta ba ranar dana tafi na kira ki da daddare Twins suka ɗauka, nay ta jiran kiran ki idan kin dawo tunda sun ce mun ba kya nan, amma baki kira ni ba, dana kira da safe kuma sai na ji Twins ne suka ɗauka again. That is why na ƙyale ki, may be haka kike buƙata, i thought ina takura miki ne. But I'm sorry." Sai ta ji bata kyauta masa ba, amma ita kunyarsa ce tasa ta yi haka, yanzu ma kawai daurewa ta yi har ta iya kallon sa bisa tilastawar zuciyarta. Ta marairaice ta ce "Ka yi haquri Uncle." Ya yi murmushi ya ce "Babu komai Princess, Princess bata taɓa laifi a wajen Uncle ɗinta." Cikin shagwab'a ta ce "Kuma ni baka takura mun ba." Ya ce "To me yasa kika daina kula ni?" Ta juyar da kai gefe ta ce "Kunyar ka nake ji, ban san ta yaya zan maka magana a time ɗin ba." Ya matso ya juyo da fuskarta ya ce "Let me hug you, sai ki daina jin kunya ta." Ta ja baya da sauri kamar zata yi kuka ta ce "Ai na daina since." Ya yi murmushi yadda duk ta tsorata ya ce "Shikenan, amma idan kika ƙara mun haka, i know what I do." Ta kawar da zancen da faɗin, "Ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau, Mamy ta ce "Kun je gidanta jiya." Ta ce "Uhm." Sai kuma ta shagwab'e fuska ta ce "Wai dagaske tafiya zaka yi da Twins yau?" Ya ce "Eh mana, Gobe za su yi resuming School, hutun nasu babu yawa 2 weeks ne kawai." Ta ce "Shikenan, but i will miss them." Ya ce "Ki bi mu, mu tafi tare." Ta ce "Soon, Insha Allah zaku ganni, Relatives ɗin Dad ma suna ta complain bana zuwa." Ya ce "I was so surprise fa, ace kin zauna a Abuja for some years amma Allah bai taɓa haɗa mu ba." Ta ce "To ai bana fita, daga gida sai School, in kuma zan fita tare da Mama ne." Ya ce "Haka ne, Mummy's girl." Sai ta yi murmushi, ta tuno Ameen saboda shi yake yawan faɗa mata haka. Sai bayan Azhar suka tafi suka bar Neehal cikin kewar su, su ma yaran kuka suka saka da za su tafi, wai sai da ita za su tafi. Da ƙyar Ahmad ya lallashe su ya ce zata biyo su itama soon.

*One week later*

Ranar Friday da safe Mama tana gyaran part ɗin Daddy Ameen ya kira ta a waya, ta ɗauka suka gaisa, daga yanda ta ji muryarsa ta san ba k'alau ba. Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Cikin damuwa ya ce "Muna asibiti Mum, ta yi Miscarriage." Mama ta ce "Subahanallahi, yaushe?" Ya ce "Cikin daren jiya." Cikin jimantawa da damuwa Mama ta ce "Allah ya bata lafiya, yanzu tana ina?" Ya ce "Hospital." Mama ta ce "Wanne?" Ya faɗa mata wani private Hospital ne dake kusa da su." Mama ta ce "Bari ta shirya ta zo." Daga haka su kay sallama. Ta kira Daddy ta faɗa masa, sannan ta ƙarasa aikin da take cikin sauri ta shirya ta tafi ita kaɗai, tunda Neehal tana wurin aiki.

Jikin Hafsan da sauƙi ta tarar da ita, tunda tun daren jiyan akay mata ƙarin jini da wankin ciki. Tana kwance akan gadon marasa lafiya, sai mahaifiyarta da mahaifinta a ɗakin. Mama tay mata ya jiki, suka gaisa da parent ɗin nata cikin fara'a da mutunta juna. Kusan wuni Mama ta yi a Hospital ɗin tare da mahaifiyar Hafsah, Daddy ma ya zo ya duba ta da rana, da yamma kuma su Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka sun zo. Mama ta kira Driver ya kawo su Dije tare da abincin data saka su, su girka. Ƴan'uwan su Hafsat ma suna ta zuwa duba ta. Tun zuwan Mama ta fuskanci Ameen yana cikin damuwa da b'arewar cikin Hafsat, ko tantama bata yi ya k'walla fa ransa akan cikin ne Allah kuma ya yi ba mai fitowa doron ƙasa ba ne. Tay masa addu'ar Allah ba su wani. Sai can yamma Mama ta dawo gida, lokacin Neehal itama bata jima da dawowa ba. Mama ta sanar mata abun da ya faru, ta ji ba daɗi sosai akan barewar cikin itama, dan duk sun san Hafsan na da ciki, har tana ta murna a ranta sun kusa samun new Baby. A daren ranar aka sallame su Hafsah, mahaifiyarta ta so tafiya da ita gida amma Ameen ya nuna bai so hakan ba, Mahaifin Hafsah kuma ya goya masa baya, ya ce tunda jikin nata da sauk'i ta wuce gidanta kawai. Dole mahaifiyar ta_ta, ta haqura, ta ce zata samo mata dattijuwar da zata na kula da ita har ta samu sauƙi, kamar wata wadda ta haihu, bayan kuma already tana da masu aiki ƴan'mata har guda biyu.

A daren Mama tana part ɗin Daddy suna hira ya ce mata. "Son fa ya kira ni d'azu in nemar masa alfarma a gurin ki." Mama ta ce "Alfarmar me?" Ya ce "Wai Daughter yake son ki ba su ta je ta musu ɗan kwana biyu, kafin Hafsah ta gama warwarewa." Mama ta ce "Ba tana da masu aiki ba, me kuma Neehal zata je tay musu?" Daddy ya ce "Kin san ɗan naki, ba ya cin abinci masu aiki." Mama ta ce "Ohh girki zata je tana yi masa kenan? To ban yarda ba, idan dan abinci ne zan na badawa akai musu." Daddy ya ce "Dama sai da ya ce mun baza ki bari ba, shi yasa ma ya kira ni, in lallame ki, ki barta ta je Doctor, kin ga akwai abubuwan da dole masu aiki baza su iya yi masa ba tunda matarsa bata da lafiya, amma ita Neehal ɗin zata iya masa." Mama tay shiru, Daddy ya ce "A taimaka mana ƴar Amaryata." Ya ƙarashe zancen da dariya. Mama ta ce "Ka ce mun amarya mana tunda zaku yaudare ni kai da ɗanka." Ya yi dariya sosai ya ce, "Yanzu dai kin bari ya zo ya ɗauke ta da safe? Just 1 week za ta yi ta dawo." Mama ta ce "Ka san ba zan iya har 1 week babu ƴata a gabana ba." Ya ce "Idan kuma da Allah yasa an yi auranta fa?" Ta ce "Aure daban, wannan na san gidan miji na kai ta ba gidan Ameen da basa shiri ba, Neehal rigima da shiririta shi kuma masifaffe, ta yi abu kaɗan ya rufe mun ƴa da masifa, na yarda dai tay musu kwana biyu ta dawo." Daddy ya ce "To hakan ma, mun gode, bari na kira shi na sanar masa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.