Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 25 of 104
*RAHMA REAL LADINGO* _Marubuciyar *RUWAIDA* ba sai na tsaya baku labarin Wacece ita ba, sunanta kaÉ—ai zai sanya ku san cewa tayi fice a duniyar marubuta yanar gizo yanzu ta shirya tsaf domin kawo maku Nagartaccen littafin ta mai suna *DATTIJON ARZIƘI* 💃ðŸÂ½ðŸâ€Â¥ Uhm Kuna jin sunan kun san daban yake_
*NIMCYLUV SARAUTA*
_matashiyar marubuciyar wacce alÆ™aminta yake kan ci, wacce ta faÉ—a kar daku a littafin ta mai taken *MOON* *AURAN FANSA* yanzu ma ta shirya tsaf a cikin littafinta mai taken *TSINTACCIYA* 💃ðŸÂ½ðŸâ€Â¥ Kuna jin sunan ba sai an tsaya magana ba_
*MSS FLOWER BATOOL*
_Ƙasaitacciyar marubuciyar nan wacce littattafan ta suka karaÉ—e nahiyar makaranta littattafan Hausa, wacce ta wa'azantar daku a *ƳAR SO* yanzu ma ta shirya ta gyara Alkalamin ta, ta ciro maku littafinta mai suna 💃ðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ *SULTAN* Uhm sunan kaÉ—ai zai sanya kusan akwai????????_
_Zaku iya fara payment a yanzu haka domin samun damar zama mace ta farko wacce ta siyi wannan littafan, nasan a kullum masoyan mu a shirye kuke da ganin labaranmu, nasan ba zaku bamu kunya ba, zaku iya biyan naku ta hanyar👇ðŸÂ¾_
*GUDA ÆŠAYA 300*
*GUDA BIYU 500*
*GUDA UKU 600*
*GUDA HUÆŠU 800*
ACCT NO: 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK
EVEDANCE OF PAYMENT
0814 210 5218
MASU TURA KATI KUMA SU TURA TA NAN👇ðŸÂ¾
0816 788 8934
GA MUTANAN NIGER KUMA SUYI MAGANA TA NAN👇ðŸÂ¾
+227 96 51 58 05
💃ðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½ðŸ’ƒðŸÂ½Mun shirya tsaf domin sanya zuÆ™atan masoyan mu farin ciki, Muna fatan zaku fara bibiyar FITATTU HUÆŠU tun a ZAGON FARKOðŸ‘ÂðŸÂ»ðŸ˜Â.
Dan Allah share fisabilillahi HabibatiesðŸ‘ÂðŸÂ»ðŸ‘ÂðŸÂ»ðŸ‘ÂðŸÂ»ðŸ‘ÂðŸÂ»ðŸ‘ÂðŸÂ».
FITATTU HUÆŠU âœÂðŸÂ¾
*Team fittattu huɗu*🥰
Misalin k'arfe hud'u da mintuna na yamma Neehal ce ke shiryawa a bedroom d'in Mama saboda d'akinta cike yake da bak'i 'yanmata, sauri take ta yi ta gama shirin nata saboda su Haneefah dake jiranta za su gurin kwalliya. Doguwar rigar abaya ta zira ta d'ora hijabi akai, turarukanta masu sanyin k'amshi ta feshe jikinta da shi, tana gama shiryawa wayarta dake kan mudubi ta fara vibrate, d'auka ta yi ta duba ta ga Ameen ne yake kiranta, a fili ta furta "Yaya kuma?" Kafin ta d'aga wayar ganin tana k'ok'arin tsinkewa ta kara a kunnenta bakinta d'auke da sallama. Ameen ya amsa mata ya k'ara da fad'in, "Ki kawo mun coffe part d'ina yanzu." Neehal ta ce "Ok gani nan." Kamar za ta yi kuka ta yi maganar, domin a haka ma tasan sai ta sha jarabar su Haneefah na jiranta da suke, gashi Yayan nata ya k'ara tsayar da ita, zata k'ara b'ata musu time. Fitowa ta yi daga d'akin ta shiga d'an k'aramin kitchen d'in dake saman wanda ba su fiya amfani da shi don cika umarnin Ameen É—in.
Cikin mintuna qalilan ta gama had'a masa coffee ɗin, kafin ta gama ta window'n kitchen d'in ta hango Haneefah ta zo ta shiga d'akin Mama fuskar nan tata a cukule, ta san bayanta ta biyo. Bayan ta juye masa a k'aramin tea flaks ta d'auka ta nufi part d'in nasa tana ta sauri. Da sallama ta shiga falonsa, ba ya falon sai k'amshinsa kawai ke tashi a ciki, bedroom d'in sa ta nufa ta tsaya a bakin qofa ta fara knocking, mintuna biyu ya bud'e qofar tare da tsayawa yana kallon ta. ba tare da ta kalle shi ba ta mik'a masa flaks d'in, cikin d'akin ya koma yana fad'in "Kika sake sa ya fad'i ya zube wani zaki sake had'awa." Neehal ta d'ago tana duban bayansa tare da turo bakinta gaba, shiga d'akin ta yi ta ajiye masa a kan bedside, ta juya zata fita ta tsinkayi muryarshi yana fad'in ta d'auko masa cup, ba tare data amsa masa ba ta je ta d'auko masa ta dire, zata kuma fita ya ce ta zuba masa coffe d'in a cikin cup, kamar ta zunduma ihu dan takaicin tsaida ta da yake gashi har 5 ta kusa, ga Haneefah tana ta kiranta a waya, zuba masa ta yi ta mik'a masa, ya karb'a yana bin hannunta da ya sha jan lalle da kallo, lallen ya kama ya yi kyau gwanin sha'awa. "Ki jira ni a falo." Ya fad'a cikin had'e rai, Neehal ta marairaice ta ce "Yaya gurin kwalliya za mu tafi fa, su Haneefah na jiran...." Wani kallo ya watsa mata wanda yasa ba shiri ta had'iye sauran managarta ta juya ta nufi qofa ta fice daga d'akin. Tana fita kiran Haneefah na k'ara shigowa cikin wayarta, sai da ta zauna a kan kujera sannan ta d'aga wayar, cikin k'ufula Haneefah ta ce "Wai Neehal ina kika shiga ne tun d'azu inata neman ki amma ban ganki ba, kuma kin san jiran ki muke fa amma kika shanya mu, idan ba za ki taho ba mu za mu yi tafiyarmu kawai." A sanyaye ta ce "Ki yi hak'uri Haneefah Yaya ne ya kira ni ina part d'in shi." Haneefah ta ce "Yaya kuma? Me kike masa toh?" Neehal ta ce "Coffe na had'o masa, yanzu kuma ya ce na jirashi a falo ban san me zai kuma saka ni ba." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka, Haneefah ta ce "Yanzu dai kinga 5 ta kusa, kuma muna da yawa wad'anda za'ayiwa makeup d'in nan, bana so kuma mu yi late a gurin zuwa dinner nan." Neehal ta ce "Idan 5 d'in ta yi ku wuce kawai zan taho ni kad'ai ko'a Napep ne." Haneefah ta ce "Shikenan." Tare da katse wayar. Neehal tana zaune a falo Ameen ya shanya ta, har k'arfe biyar ta wuce, su Haneefah suka yi wucewarsu gurin kwalliyar, gashi dinner d'in k'arfe bakwai na dare ne, kuma bata son ta yi African time.
Ameen bai fito daga dakinshi ba sai da 6 ta wuce, zuwa lokacin Neehal harta fara hawaye, gashi Haneefah nata kiranta ita har angama mata makeup d'inta, kuma kayan da zata saka yana gurin Haneefah ta tafi da shi a had'e da nata, da sai ta hak'ura da kwalliyar ta zira kayanta kawai ta tafi, card admin d'inta ma dana Sadik duk yana hannun Haneefan." K'amshi turarensa da ta ji ya k'ara cika mata hanci shi yasa ta d'agowa da sauri ta kalle shi, shima ita d'in yake kallo hakan yasa suka had'a Ido, saurin É—auke idonta ta yi tana yaba tsananin kyawun da ya yi a cikin zuciyarta, ya fito sak angonsa cikin dakakkiyar shadda mai tsadar gaske sky blue wadda aka maka aiki da Kalar Royal blue, tunda Neehal take ba zata iya tuno ranar da ta ganshi da hula ba a rayuwarta, domin shi mutum ne ma'abocin saka k'ananun kaya, idan ka ganshi da manyan kaya Juma'a ce ko kuma Sallah ko kuma idan za shi d'aurin aure, kuma suna masa kyau sosai idan ya saka, yau kam gashi harda babban riga (Malin_Malin) a kan kayan. Kiran shi ake ta yi a waya amma ya k'i picking, Neehal kanta na k'asa ta ce "Yaya dan Allah ka barni in tafi, su Haneefah fa har an gama musu kwalliyar za su tafi ni kaÉ—ai na rage." Ameen ya mata banza tamkar ba da shi take ba, tsadadden agogon hannunsa kawai ya kalla sannan ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon ya shiga latsa wayarsa hankali kwance. Sosai ran Neehal ya b'aci a kan abunda Ameen ya mata, haka kawai ya tsaidata kuma babu abunda zata masa, ita kuma bai barta ta je ta yi uxurin gabanta ba. Kiran Sadik ne ya shigo wayarta domin sun yi da shi zai d'auko su daga gurin kwalliyar ya kaisu gurin bikin, ba ta san me zata fad'a masa ba, shi yasa ta k'i d'aga wayar ta barta harta gaji ta katse.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.