Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 104

Da daddare Mama ta na part d'in Dad suna tattaunawa akan maganar Ameen ɗin da Hameedah, ya na faɗa mata yanda Mommy'n Hameedah ta takura masa da zancen ayi_ayi aurensu. Mama ta ce "Ni kaina Gen. na matsu Ameen ya yi aure, na gaji da yawo da hankalin da yake mana." Dad ya ce "Hakane, nima ina son na ga ya yi auren, amma bari na kirashi na ji ra'ayinsa a kan Hameedan, tunda ni bai taɓa mini batun ta ba da kansa." Mama ta ce "Toh." Dad ya kira Ameen a waya ya sanar masa ya na son ganinsa yanzu. Bayan 10 minutes sai gashi ya zo, ya zauna a ƙasa ya na duban Dad ya ce "Ga Ni Dad" Dad ya ce "Dama akan maganar Hameedah ne, tunda auren Neehal ɗin Allah bai nufa ba, dama shi muke jira a yi sai mu yi zancen naka, to yanzu ka na son Hameedan ne?" Ameen ya d'ago ya dubi Dad, cikin nutsuwarsa ya ce "Ni fa Dad ba na son Hameedah, Ina da wadda nake so!" Da sauri Mama da ta k'ura masa ido ta ce "Kamar ya ba ka son ta?" Dad ya d'aga mata hannu ya na ɗan murmushi, sannan ya dubi Ameen ya ce "Wa ce wadda ka ke so ɗin?"..........✍️
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

1️⃣0️⃣

Shiru Ameen ya yi tare da sunkuyar da kansa ƙasa. Mama ta na duban Dad ta ce "Kai ka biye masa ai, ban da haka mene aibun Hameedan da zai ce ba ya son ta?" Dad ya ce "Haba Doctor, kin san dai ba zan yi masa auren dole ba tunda ba ya sonta Shikenan." Dad ya maida dubansa ga Ameen ya ce "Kai muke sauraro." Ameen cikin dakiyarsa ya ce "Hafsah!"
"Hafsah kuma?" Mama ta tambaya cikin mamaki. Ameen ya gyad'a mata kai. Mama ta ce "Dama har yanzu ku na tare da ita ?" Nan ma kan ya kuma gyad'a mata. Dad ya na murmushi ya ce "Masha Allah, A Ina ita Hafsan take? 'Yar waye?" Mama ta ce "Hafsat fa 'yar gidan Alhaji Nuhu Ɗan gaske" Dad ya ce "Allah sarki, to Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Insha Allahu a satin nan zan samu shi Mahaifin nata mu yi magana, a san abun yi." Mama ta ce "To Allah ya tabbatar da Alkhairi" Dad ya ce "Amin" Ameen ya mik'e kansa a ƙasa ya fice daga falon, Mama ta bishi da kallo cikin mamakin shi, maida kallonta ta yi ga Dad bayan ya fice ta ce "Al'ameen halinsa sai shi, yarinyar nan Hafsat ba irin son da ba ta nuwa masa ba a baya, amma ya nuna ba ya son ta, yanzu kuma da bakin shi ya dawo ya ce ita yake so?" Dad ya ce "Haka Al'amarin Allah yake, kin san matar mutum kabarinsa, wata ƙila duk wannan abun da ake itace matar tasa" Mama ta ce "Hakane, Allah ya sa Albarka ya sa da mu za'a yi." Dad da fara'a ta ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce "Amin." Mama ta ce "Um, sai wata fara'a kake kamar an maka wani albishir ɗin." Dad ya yi 'yar ƙaramar dariya ya ce "Wlh ba ki ji yanda farin ciki ya lullub'e ni ba da Ameen yau ya furta mun ya fidda mata, dama ni tsoro na kar mu bashi mata a zo a samu matsala zumuncinmu ya ɓaci." Mama ta ce "Gaskiya kam, amma Ni na so Ameen ya auri Hameedah, ko dan yanda take k'aunarsa, ga ta kuma jininsa ce, yanzu idan Family suka ji zancen nan ya kake ganin za su ɗauki maganar, tunda kowa ya na tunanin Ameen Hameedah zai aura, ita kanta Hameedan ban san wanne hali za ta shiga ba idan ta ji wannan zancen." Dad ya gyad'a kai ya ce "Nima na so hakan Dr. Amma kin san yaran yanzu ba'a musu dole, ni ba na so a samu matsala ne, shi ya sa ban tursasawa Ameen a kan lallai sai ya Auri Hameedah ba, itama Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta." Mama ta ce "Amin ya Allah." Wayar Dad ce ta fara ringing, dubawa ya yi sai kuma ya saci kallon Mama, ƙin d'aga wayar ya yi har ta katse, aka kuma kira ya kuma ƙin d'agawa. Mama ta ɗauke kai kamar ba ta gani ba, kiran da aka kuma yi ya sa Mama mik'ewa tsam ta zagaya ta ɗauki wayar ta duba, Dad ya yi murmushi ya na kallonta ya ce "Ba wata ce take kirana ba sarkin kishi." Mama ta haɗe rai ta ce "Hubby! Har yanzu dama ka na tarayya da Alhaji *Kabir Ginyau* ?"  Dad ya riko hannun Mama tare da zaunar da ita a gefensa ya ce "Ehh, amma ba tarayya irin wadda muka yi da ba, kawai dai mu na gaisawa ne sama_sama." Mama ta ce "Amma..." Dad ya d'aga mata hannu cikin lallami ya ce "Kin ga Dr. Dan Allah kar ki tada hankalinki a kan dan Kabir ya kira ni, yanda kike tunanin abun kwata_kwata ba haka yake ba." Mama ta yi shiru kawai ta na kallon shi.

Washegari da safe Neehal ta na kitchen ta na aiki Ameen ya shigo part d'in, ganin ta a kitchen d'in ya sashi shiga kitchen d'in. Neehal ta juyo ta na kallonsa jin k'amshin turarensa, a hankali ta ce "Ina kwana Yaya?" Ameen ya ce "Lafiya k'alau, ina Mum fa?" "Ta na d'akinta" Neehal ta bashi amsa ta na satar kallonsa, shima kallon nata yake yi hakan ya sa suka haÉ—a ido. Neehal ta É—auke idonta da sauri ta na turo bakinta gaba. "Idan kin gama ki kawo mun nawa abincin part d'ina." Ya fadi haka tare da juyawa ya fice, Neehal ta bishi da kallo kawai.
Mama ta na zaune a kan darduma ta na karatun Alkur'ani mai girma ya shigo d'akin, sai da ta kai ƙarshen aya sannan ta rufe ta d'ago tare da amsa masa sallamar da ya yi. Ameen ya zauna a gefenta ya ce "Ina kwana Mom, dafatan kin tashi lafiya?" Mama ta ce "Lafiya k'alau, and you?" Ya ce "Alhamdulillah." Mama ta ce "Masha Allah, am Ameen dama ina son na tambayeka." Ameen ya dubi Mama amma bai ce komai ba. Mama ta ajiye Kur'anin hannunta a kan bedside locker, sannan ta fuskance shi da kyau ta ce "Me ya sa ka ce ba ka son Hameedah?" Ameen cikin nutsuwarsa da sanyin muryarsa ya ce "Mama! Kin san wace Hameedah kuma kin san halinta, kwata_kwata ba ta da qualities d'in matar da zan iya aura." Mama ta ce "Na san da haka Ameen, amma ba ka tunanin yanda Family'n Dad d'inka za su ɗauki abun? Kowa zai yi tunanin Ni na hanaka auren Hameedah saboda ba ma shiri da Mahaifiyarta." Ameen ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa sannan ya ce "Kar ki damu kanki Mama da su, su faɗi duk abun da za su faɗa." Mama ta tsura masa ido kawai ba ta ce komai ba. Kawar da zancen ya yi ta hanyar faɗin "Yaushe wacce old Woman d'in za ta tafi?" Mama ta ce "Bansani ba, tunda uwar tawa ma ce Old Woman." Ameen ya mik'e ya na faɗin "Tunda ba za ki faɗa mun ba zan tambaye ta da kaina." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa daga d'akin. D'akin Hajiya ya leƙa ya tarar da ita a kan darduma ta na lazimi ta na gyangyad'i, ya yi murmushi kawai ya juya ya fice. Neehal ta na gab da kammala aikin da take Mama ta shigo kitchen, Neehal ta kwab'e fuska tare da turo baki gaba, don Mama ta fuskanci ta gaji. Mama ta dube ta, ta ce "Sannu Daughter." Neehal ta ce "Yawwa Mama, kin fito." Mama ta ce "Eh, amma ba yanzu zan fita ba, kawo na ƙarasa aikin ki je ki yi azkar ɗin safe dan nasan ba ki yi ba." Neehal ta ce "Toh Mama." Harta fita daga kitchen d'in sai kuma ta dawo, Mama ta kalle ta da alamun mamaki amma ba ta ce komai ba, Neehal kanta na ƙasa ta ce "Yaya ya ce in kai masa breakfast ɗinsa part ɗinsa." Mama ta ce "Yanzu dawowa ki kai ki masa?" Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce"Ki wuce ki yi abin da na ce miki, zan bayar a kai masa." Ɓata fuska ta yi sannan ta juya ta fice. Bayan ta gama azkar ɗin ta sakko ƙasa ta na breakfast Mama ta ce mata, "Za ki aiki ne yau?" "A'a." ta bata amsa. Mama ta ce "Idan kin gama ki shirya ki je gidan Sadiya, daga nan sai ki biya gidan A'isha, su na ta complain kin dena zuwar musu 2 days." Neehal ta yi murmushi ta ce "To Mama, bari na kira besty mu je tare."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.