Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 34 of 104
Goma saura Sadik ya ƙarasa gida, kamar yadda ya yi zato duka ƴan gidan nasu suna zaune a falon har Abbansu, bakinsa ɗauke da Sallama, gaba-d'aya suka zuba masa ido tare da amsa masa sallamar. Kusa da mahaifiyarsa ya je ya zauna a ƙasan kujerar da take ya mata sannu da gida, sannan ya gaishe da Abbansa da kishiyar Maamah wadda suke kira da Umma, k'annenshi kuma suka gaishe shi. Abbansa ya ce "Abubakar daga ina haka?" Sadik ya yi ƙasa da kansa tare da shafa sumar kansa, Abban ya kalli Maamah Wadda ke murmushi ƙasa_ƙasa yana murmushin shima, Umma kuwa tab'e baki ta yi ta ce "Hmmmm, Sadik dai ya soma ɓata wayonsa da yawon dare, da dai ba ya yi amma yanzu....." "Wacce irin magana ce wannan Ruqayyah kike yi?" Abba ya katse Umman a ɗan fusace, Maamah da annurin fuskarta ya ɗauke lokaci ɗaya jin kalaman Umma ta sauke numfashi cikin jin daɗin yanda Abban ya katse Umman ga aikabata mata ɗa da take ƙoƙarin yi." Sadik ma ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin yanda zugar Umman bata samu shiga ba a gurin Abban kamar yadda ta saba kodayaushe ba. Umma ba ta da aiki sai yi masa sharri a gurin Abbansa, kuma Maamah ba ta isa ta yi magana ba sai ta saka kuka ta ce tana nuna mata iko akan Sadik dan ta ga ita ba ta daƴaƴa maza, ai itama ɗanta ne ba zata cutar da shi ba. Shiru Umma ta yi ganin yanda Abban ya haɗe rai. Shima Abban shiru ya yi ganin yaransu na falon, miƙewa Sadik ya yi ya nufi bedroom ɗinsa dan yana da aikin da zai yi akan wani case da yake bincike akai.
Asalin Mahaifin Sadik mutumin Kano ne, ɗan kasuwa ne da yake da rufin asirinsa dai_dai gwargwado. Mahaifiyar Sadik kuma ƴar asalin garin Maiduguri ce kabilar Shuwa, aure ne ya kawo ta Kano. Fara ce kyakkyawa ga gashi har baya, a gurinta su Sadik suka gado kyau. Umma kuwa ƴar asalin jihar Kano ce, iyayenta a cikin gari suke, Maamah ba ta fi shekara 5 da aure ba Abba ya auro Umma, lokacin an haifi Sadik yana yaro. Ana zaton wuta a mak'era sai aka same ta a masak'a, domin kuwa Umma ce take da tsananin kishi da shegen makirci, ita kuwa Maamah da zuciya ɗaya take zaune da Umma, kuma duk kasancewarta Shuwa ba ta nuna wannan kishin na hauka, ga ta da haquri da addini. Su Sadik su biyar ne kawai a gurin mahaifinsu, a ɗakinsu su uku ne, Shine babba sai k'aninsa mai bi masa Bashir, sai autarsu Batul. Ita kuma Umma ƴaƴanta biyu kuma duk mata ne, kuma ta fi shekara goma kafin Allah ya bata haihuwar. Makirci kala_kala Umma ta dinga haɗawa Maamah a gurin Abba kafin ta haihuwa, wai Maamah tana mata gorin haihuwa. Hakan yasa Abba ya ce ƴaƴan Maamah itama ƴaƴan ta ne tunda Ƴaƴansa ne dan haka tana da iko akansu. Tun daga wannan rana fa Umma ta samu damar yiwa Sadik sharri iri_iri a wajen Abbansa, a matsayin tana faɗa masa gaskiya wadda Maaman take bo'yewa a cewar ta, kasancewar Abba matafiyi ne bai fiya zama a gari ba, saboda sha'anin kasuwancinsa. Haka Abba zai samu Sadik yay ta masa faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, itama Maamah bata tsira da faɗan Abban. Inda Allah ya taimaka kakarsu Sadik mahaifiyar Abba tana son su sosai, to wani sharrin idan Umma ta k'ulla ita take taka mata burki ta ci mata mutunci, ta kuma ta hana Abba ɗaukar hukunci akan Sadik ko Maamah. Ita kuwa Maamah kullum cikin tausar Sadik take tana ba shi baki akan Abinda Umma take masa, duk da abun na damunsa amma haka yake haquri ba ya nuna ɓacin ransa saboda nasihar mahaifiyarsa. Bashir ne ma sarkin zuciya wataran yake ƙoƙarin tankawa Umma idan ta ƙure shi akan abun da takewa Mahaifiyarsa da ɗan'uwansa, duk da shi ɗinma tana masa ba tsira ya yi ba, amma shi tana ɗan shayin shi ganin yaron a tsaye yake, Sadik kuwa haqurin mahaifiyarsa ya ɗauko shi yasa tafi raina shi kuma tafi tsanar shi.
Misalin ƙarfe 11 na dare Maamah ta kwankwasa masa ƙofa, yana zaune gaban laptop, ya d'ago ya dubi ƙofa tare da faɗin "Come in." Maamah ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin "Au Maamah ke ce, na ɗauka ma Basheer ne." Maamah tana murmushi ta ce "Ni ce Son ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah gashi muna ta fama." Maamah ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a." Ya amsa da "Ameen." Cikin ladabi. Maamah ta dube shi ta ce "Daga ina kake ne Sadik?" Sunkuyar da kanshi ya yi yana murmushi ya ɗan sosa kai ya ce "Gidan su Neehal." (Da yake Maamah ta san Sadik yana zuwa gurin Neehal.) Maamah ta yi murmushi ta ce "Ka baro su lafiya?" Ya ce "Eh, tana gaishe ki ita da Mama." Ta ce "Ina amsawa." Ta miƙe tay masa sai da safe sannan ta fice zuciyarta fal da farin ciki, kullum addu'arta Allah ya bawa Sadik mace ta gari yay auransa ko ya huta da addabar Umma da kuma faɗan mahaifinsa, tunda ba su isa dai sun bi shi gidansa sun masa ba.
Washegari Mama ta koma bakin aiki, Neehal kuma gidansu Haneefah ta je dan yi musu ban gajiya ita da Twins É—inta. Bayan sati É—aya, Neehal ta koma gurin aiki, kuma har yanzu babu wanda ya kira akan su Afrah. Kullum Mama cikin saka ran kira take amma sai ta ji shiru, abun yana É—aure mata kai sosai, dan yanda aka baza hotunan su Afrah a gidajen Televisions ya ci ace wani nasu ya gani, kuma kullum sai an yi cikiyar iyayensu a gidajen rediyo da Talabijin. Yau Juma'a Neehal aikin safe ta yi, 12pm da mintuna ta dawo gida, kasancewar Ran Monday za su yi resuming School Mama ta ce ta shirya ta je gidan Ameen, kar ta koma School ta zo bata samu damar zuwa ba, tunda every weekend tana gurin aiki, Monday to Friday kuma tana school. Ameen É—in kuma yana ta yiwa Mama mitar ta hana Neehal zuwa gidansa. Neehal murna kamar ta kashe ta dan ba Æ™aramin kewar Yayan nata ta yi ba, dan tunda yay aure ko waya ba su taÉ“a yi ba, kuma kusan kullum sai ya zo amma ba sa haÉ—uwa, duk time É—in da zai zo tana gurin aiki. Cikin Sauri ta shirya Twins É—inta itama ta shirya, ana sakkowa daga masallaci Driver ya tafi kai su, dan ita ba ta san gidan ba, duk da tana jin mararta na mata ciwo kaÉ—an_kaÉ—an amma ta daure, dan tana faÉ—a Mama cewa za ta yi ta fasa zuwan wani lokacin ta je, ita kuwa zuciyarta cike take da kewar Yayan nata, ba za ta so abin da zai yi mata tsaiko a ganin shi ba............âœï¸
[7/21, 9:01 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2ï¸âƒ£3ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.